0
NAMANTA KOMAI

By yasima Suleiman

NAMANTA KOMAI Episode 5 to 7



NAMANTA KOMAI

 Episode 8 to 10


 Ta kwanta sai juyi take, amma ba abinda yake zo mata, duk tunanin duniya tayishi amma bata tuna komai akan kanta, iyakanta abinda ya faru da ita yau take iya tunawa, yaranta mijinta sai wankan da sukayi, juyi take tana baiwa k'wak'walwarta wahala, Amma shiru, dagyar ta tuna wasu abubuwan da tun tana shekara goma suka faru, daga nan bata k'ara tuna komaiba. tashi tayi ta shiga dube- dube a d'akin nata, ta bud'e wannan ta bud'e wan chan, anan taga wasu littafai, ta dauko, abin mamaki sai taga tana iya karanta wa, littafin da yafi jan hankalinta shine KULA DA MIJINKI yanda ake kula da mijine, ta d'auko ta jujjuyashi sai kawai ta koma bakin gado ta zauna, ta fara karantawa, tanayi tana murmushi ita kad'ai, har saida ta karanceshi tsab sannan ta koma ta kwanta...

 Bayan ta kwanta sai ta fara tunanin ina mijinta? Tun ganin da tayi wa wai mijinta da safe, bata sake ganinshiba, sai ta sauko k'asa, nan ta zauna palo tana jiran isowarshi domin itafa kanta a d'aure yake, gata matar aure harda miji uwa uba harda yaya biyu, tirkashi!!!, dole tayi mashi tambayoyin da in ya bata amsa zata iya gane ita wacece dan jinta takeyi kamar TA MANTA KOMAI..... Tashin hankali baa sa maka rana,da alama dai Suhaila ta yi loosing Memory d'inta ne a yanda na fahimta,... Can kuma Ahmad, sai tunane-tunane yake shin abun nan, pritending take kamar bata san komai ba, dan yasan kissar mata yawa gareta, ko kuwa akwai wani abune?? Gani yake kamar ta amincene ta zauna da shine a matsayin mijin nata, shine take basarwa, to lallai yana ganin hakanne, ta amince ta zauna dashine dinne, yayi dan murmushi wanda ya fito da kyanshi a bayyane, kai mata akwai iyayi, kalli yanda ta fuske kamar ba itaba a bayyane yace "Mata! Mata!! ya kada kai ka barsu kawai....."

 Amincewa tayi dan ya zama dole, domin kuwa bakin alk'alami ya riga ya bushe, an riga an d'aura masu Aure shi da ita, kuma ba saki har abada, Ahmad kenan da masu aikin gidansu suka saka masa suna Alhaji Rabo..... Na zama mijin Suhaila kenan, yayi murmushin da bai kai ciki ba, amma azuciyarshi har yanzu inya tuna wasu abubuwa sai yaji wani baqain ciki da zuciyarshi ke tafasa, kuma har yanzu ya kasa cire wannan abu a zuciyar shi, wanda duk sadda ya tuno abin yake jin zafi har yaji ya tsaneta, amma yayi ma mahaifinta alk'awarin zai rik'eta amana a matsayin matarshi, amma ya za'ayi yayi hakan,!? bai saniba har yanzu,!! Shiyasa lokuta da yawa sai yaji Kamar yacema mahaifinta ya fasa aurenta,amma kuma sai ya kasa....!! 


************* 


SHEKARA UKU DA SUKA WUCE Shekara uku da ta suka wuce,... lokacin da mahaifan Suhaila suka dawo daga umra, Ahmad tuni ya riga ya koma k'asar Holland, basu sake haduwa da Ahmad ba, dan bai sake zuwa Nigeria ba, sai lokacin da ya samu labarin rasuwar yayan shi da matar yayan shi, sun kuma bar baby dinsu Surayya Just 2month da haihuwa, yana nan gida yazo ta'aziyyar yayan shi, sati daya aka yiwa Ahmad waya aka gaya mashi ya dawo gida, domin matarshi na cikin mawuyacin hali,rabon suyi sallama, yana isa akayi mata C.S aka ciro babyn cikin ta, ita kuma ta rasu,ya sama Baby dinsa Suna Rukayyah...sunanda matarshi takeso take kuma k'auna kenan shi kuma ya saka mata Rukayyah..

 ******** 

Rasuwar yayanshi sunyi magana sosai da Alh Ibrahim mahaifin Suhaila, inda ya gaya mashi abubuwan da yawa da bai sani ba, wanda yake zaton shine yayan nashi ke cewa zai gaya mashi, Amma kuma Allah ya masa cikawa, asalin samun gonar da suke ciki yanzu kenan wadda da tana hannun yayan nashi ne kamin ya rasu, duk makircin da Alh ismail ke k'ullawa,wanda ya janyo accident d'in motar yayan shi, ya yi sanadin rasuwar yayan nashi da matar yayan shi, amma har yanzu dai ana kan bincike, dan a gano gaskiyar abinda ya faru, wannan dalilin yasa Ahmad yasa ya tattaro ya dawo gida don yaci gaba da harkar bussines din mahaifinshi da yayan nashi.!! Ba'a dade ba, Alh Ibrahim ya neme Ahmad da ya auri y'arshi y'ar autarshi Suhaila, wacce duk cikin yaran shi yafi k'aunarta sabida tsananin kama da takeyi da mahaifiyarsa. Ahmad kuwa ya kuma amince da auren Suhaila amma ya amince ne bawai dan yana sontaba hasalima ya tsaneta tun tana yarinya data mishi wani abu, kawai dan ya lura Alh Ibrahim mahaifin Suhaila mutun ne mai mutunci kuma shi kadai ya yadda dashi a cikin abokan mahaifinsa, bayan an bashi Suhaila akace kuma an bashi lokaci har sai ya shirya sannan ayi auren, 

************

 A ranar a aka aje maganar auren sa da Suhaila, Ahmad ya samu kanshi dayi ma duk mutanen dake aiki a gidan su Suhaila, k'ananan ma'aikatan kampanin Alh Ibrahim kyautar kud'i dubu goma goma, shi kanshi bai san dalilin yin hakan ba, sai dai kawai ya tsinci kanshi cikin farin ciki da annashuwa, dukda yasan bayason Suhaila, tun daga ranar suka sa mashi suna Alhaji Rabo wanda kowa a gidan da sunan yake kiransa Ita kuma marainiyar y'arshi da da yar yayanshi, kakarshi da nanny dinsu ne suke kula dasu, har suka dan girma, suka fara wayo kullun cewa suke yaushe za'a kawo masu Momy d'insu, hakan yasa Ahmad ya bijiro da xancen auren Suhaila, amma badan yana sontaba, Su kuma yaran ganin Suhaila yasa suke tunanin mamansu ce, ga kuma madam din TA MANTA KOMAI. Sabida lokacin da zai tafi daurin auren haka yace masu zaije ya kawo masu Momy dinsu.... 


************** 


Cikin dare Suhaila ta farka cikin bacci amma ta kasa motsi,gabanta ya fadi ita da ta kwanta a palo, miya kawota daki, al'amarin ta fa sai d'ad'a jagule mata yake! "Waima ina mijinta ne!?" Yayanta ne gabanta, Surayya ta rungumeta a dama Rukayyah a hagu...tayi murmushi ta k'ara rungumesu, babu shakka y'ay'anta na sonta, ashe suma sun farka cikin darene suka dawo wajenta, gaskiya yarane kyawawa babansu kyakykyawane, Itama ba daga baya ba, ai kuwa dole su bada result mai kyau da haka bacci mai d'ad'i ya k'ara kwashe ta...... "Bayanin waye Suhaila & Ahmdy yana zuwa next page gobe."

Post a Comment

 
Top