NAMANTA KOMAI
By yasima Suleiman
NAMANTA KOMAI
Episode 11 to 15
Amadadin Marubuciya Hauwa M. Jabo
Suhaila 'ya ce a gurin Alhj Ibrahim, wanda suke kira da Dady, itace yarinya ta hud'u kuma itace Auta, Dady yana matuk'ar sonta ne sabida tsananin kama da sukeyi da mahaifiyarsa. Asalinsu buzaye had'e da fulani, Alhaji Ibrahim murzajjen d'an boko ne, irin masu tara suma dinnan aka, yazo birni gun wani aiki na idanu, a k'auyen Tambuwal cikin birnin Sokoto inda yaga gari ya masa sai ya dawo nan da zama, anan k'auyen ya hadu da mahaifiyar su Suhaila, har suka yi aure, ta haifa mishi yara hud'u mata biyu maza biyu. Rukayyah itace babba, sai kuma Al- Ameen sai Suhaila da Suhail wayanda su twins ne, sune k'anana. Harkar gyaran ido ta karbeshi ba kadan ba, inda ya koma birnin Sokoto da zama, anan ya had'u da Alhaji Isma'el, da kuma Alhj Sulaiman sai aka koma kasuwanci. Alhaji Sulaiman shine mahaifin Su Ahmad, yaransa biyar Mahmoud shine babba, sai Zainab, sai kuma Ahmad da Fatima, sai autarsu Khadija. Sun shaqu iya shak'uwa su ukunnan, tare suke duk wata harka ta kasuwanci.
*********
Wata rana Ahmad ya dawo daga makaranta sai ya hango kamar ana butsul- butsul a ruwa, har ya wuce sai kawai ya dawo yana lek'awa sai yaga abin yayi yawa, koda ya matso sai yaga mutum ne, baisan lokacin da ya fada cikiba ya tsamota. Yarinya ce 'yar kimanin shekara 8, ya kwantar da ita ya rik'a matsa mata cikinta a hankali tana fitar da ruwanda tasha baki hanci, har ta fara tari, ta bude ido a hankali, sai ta sake rufewa, Ahmad dai yaga abin ba nashi bane sai ya d'auketa ya kaita gidansu, mamarshi na ganinta ta fara salati, da yake ita tasan ta, "ina ka samo Suhaila ?? " Yama Ammi bayani, " ai banga ta zama ba" ta dauko mayafi ta yafa ta sungumi Suhailah sai gidan Alhaji Ibrahim ta maida musu bayanin komai, Anata godiya, bayan kwana biyu Suhaila ta ware waras, Mama ta kirata, "Ke wai garin ya kika fad'a ruwa?" "Ba wannan ne ya turaniba!" Cikin rashin fahimta Mama ta k'ara tambayarta, "wanene wannan?" Suhaila kuwa ta tsaya kai da fata akan Ahmad ne ya jefata ruwa, Mama cike da mamaki, take jimamin lamarin, sai da Dady yazo ta mishi bayani abin da Suhailah ta gaya mata, shikan bai yardaba sam, dan yasan halin Ahmad tsab, dan haka bai d'auki maganar da mihimmanci ba, mama ta yafa taje ta sami Hajiya Sa'adatu mahaifiyar Ahmad ta bata labarin da Suhaila ta gaya mata, tace kawai a jawa Ahmad kunne kada ya k'ara aikata irin haka, an kuwa yi sa'a Ahmad yana gida, "kai Ahmady" na'am ya fito d'akin su, cikin girmamawa ya gaida Mama, ta amsa a sake, "dama Suhaila ce tace wai kai ka jefata ruwa ranar " "waye Suhaila Ammi!?" Ya tambaya "yarinyar da ka kawo shekaran jiya kace ta fad'a ruwa mana, har ka fito da ita" shiru yayi chan kuma yace "akan me zan jefata ruwa Ammi? Mi ta mini da zan jefata ruwa?" " mudai yanzu ba wannan ne gaban mu ba, kawai ka fita harkar yarinyar nan idan ba zaka taimaketa a matsayin k'anwarka ba, to kuwa ka rabu da ita" Mama tace "kai tashi ka tafi abinka, kilama shiririta ce irin ta Suhaila" cike da mamaki ya wuce d'akin shi, lokacin Ahmad yanada shekara sha biyar, amma akwai natsuwa gun shi, gashi komai nashi a tsare, iyayen sukaci gaba da hirar su. Tun daga wannan rana Ahmad ya d'auki tsanar duniya ya d'aurawa Suhaila, gashi ba wani saninta yayiba dan ko ganinta yayi bazai ganeta ba, amma ko sunan ta bayason ji wannan kenan....
***********
Da yake su uku suke kasuwancin su komai yana tafiya yanda ya kamata duk da cewa Alhj Sulaiman shine shugaba, dan kusan 50%(rabin dukiyar kaauwanci) dukiyar shi ce, sauran rabin kuma na Alhaji Isma'el da Alhaji Ibrahim ne. Alhaji Isma'el ya d'auki ki'yayyar duniya ya d'aura musu ba tare da sun saniba, anan ne yayi nasarar lik'awa Alhj Ibrahim satar kudin company kusan M.200, kuma akayi bincike akaga kudin gurin Alhj Ibrahim, wanda duk sharrin Alhj Isma'el ne, ba tare da wani dogon bincike ba suka cireshi a shikinsu, suka dawo su biyu. Abin yama Alhaji Ibrahim zafi ba kad'an ba, sharri harma na sata, gashi da zuciya kamar me, bak'in cikin haka yasa yabar Sokoto ya dawo Katsina da kasuwancin sa.
******************
BAYAN SHEKARA DAYA. Alhaji Ibrahim yazo Sokoto ganin gida da iyalinsa anan ne Suhaila ta sami accident ta fito daga gidan yayar ta Rukayyah itada Suhail mota ta kad'e ta, shima Ahmad ya fito gun wani cafe yaga mutane, yana zuwa yaga taro, ba abinda akayi mata gata kwance, shida wani bawan Allah suka samo taxi da police aka kaita asibiti, duk da ko lokacin bai ganeta ba kuma bai kiyaye fuskar taba, wannan bawan Allah ya gano iyayenta da taimakon suhail. Dady ya riga ya koma Katsina, yace Rukayyah ta kula da ita dan ayyuka sun masa yawa, an mata duk abinda ya dace. Kullum Ahmad yana zuwa dubata, duk da baisan wacece itaba, ranar ta tashi ta mik'e zaune yana zaune yana karanta wasu takardu Anti Ruky na sak'a, dan mayyar sak'a ce, tayita kallonsa, suna hada ido, sai ta masa murmushi, tace " inasonka kaji " shima ya mata murmushi, yace " nima inasonki" ta k'ara murmushi har haqoranta da take 6an6ara suke bayyana "to zaka aureni idan na girma irin na Anti Rukayyah da uncle?" Yace "Eh mana" yeeeee tace sannan taci gaba, " to kaga Anti Rukayyah tana cema uncle Honey, ni mi zaka cemini!?" "Aike kyakyawa ce so zan rik'a kiranki da beautiful" ta zunburo baki "ni banason sunan, ko Dady Some times (wani likaci yana cemin beauty, fadi wani mai d'ad'i" ta ya mutsa fuska a yangace irin na yarinta, "kina son Dear" a haf, ta d'auke kai gefe, tace "ai ko mama tsohuwa dear take cema Dady" dariya yayi sosai har fararen hak'oransa suka bayyana.....
"Kenan ke ba kya son Dear ko,?" Tace "Eh mana, ko Dady fa nace maka haka yake kiran Mama" "to wane suna kikeso?" " ko wanne ma just mai kyau irinka" dariya yayi, wannan yarinya too funny, "to gashi na fad'i har biyu kince ba suyi ba" "To tsaya " yace "na tsaya" ta k'ara lankwashe k'afafuwanta, "ni ban ma san sunan da zaka kirani dashiba" yauwa my princess ya miki?" tayi murmushi "Eh yayi na yan gayu ko? " yace "sosai" " to yaushe zamuyi Aure ?" Kai kai kai babbar magana, yace "Sai kin warke kin kuma girma" "kada ma ki girma kice bakya sona" tace "Laaa to a d'aura mana aure" dariya ta kubce masa, haka sukayi ta hira abin dariya, gashi tace kota girma shine mijinta, yarinta gatanan, dama Suhaila sai dai idan bata samu guriba, kullum cikin fara'a take da labari kala- kala, Ya fito zai wuce kenan yayi karo da Alhaji Isma'el, ya mishi bayanin abinda ya zo yi, sai yace bari ya gaisheta yana ta saka mishi albarka yaron kirki dashi, kamar gaske, Alhaji Isma'el yana ganin Suhaila ce, da yake yasanta dan tana yawan zama gun Dady, suna fitowa ya kuwa mummurd'e ma Ahmad kunne akan kada ya k'ara zuwa gunta, kuma ya hadashi da Abbanshi, aka hanashi zuwa gun Suhaila asibiti gaba d'aya ba tare da yasan dalili ba, haka yake satar hanya ya lallab'a yaje gunta suyi hirarsu ya samu natsuwa da nishadi, dan ta iya ban dariya ga wani sonta da yakeyi, "Anti please ki kawo min hoton matata gobe," dariya anti Rukayya tayi, tace dashi to, aka kuwa kawo masa hotunan ta kala kala, haka yake zuwa hira a asibiti gun Suhaila da Anti Rukayyah, idan ya gaji ya dawo gida, Anti Rukayyah ke jinya so itama batasan Ahmad ba, "ranar Ahmad yazo duba Suhailah sai kawai yaji muryar babban yayan su Mahmoud, tuni yabi ta window ya gudu, Suhaila tanata kiranshi saida ya tsallaka ya lek'o yace da ita "zan dawo soon My Princes" tun daga wannan ranar Ahmad bai k'ara zuwa gun Suhaila ba, sabida goben ranar aka sallamesu daga asibiti, tayi tambayar Princes har ta gaji, ba wanda yasan wanda take nufi, bare asan ina yake, haka ta mak'ale sonshi a zuciyarta tun yarinta... Tayita baiwa iyayenta labarinsa amma ba wanda ya gane mi take nufi har ta gaji ta hak'ura da zancensa, amma lokaci zuwa lokaci takan tuna abinta...
**************
Suhaila tayi karatu sosai, abinka da yaran tsofin y'an boko, har saida ta kammala Dgr d'inta na farko, kuma duk lokacin bata kula samari burinta ta zama likitar mata dan ta rik'a taimakon yan uwanta mata, musamman ganin yanda mata suke wahala, da kuma wasu abubuwan da mace ya dace tayi su, amma sai kaga ba mace Dr. sai namiji, abinda tasa gaba takeyi ba ruwanta da kowa, Yusuf ne kawai suke shiri, shima cousin dinta ne, shiyasa yake samun damar shiga gidan nasu, amma da yake bashida karatu sosai da kanshi yasan Dady bazai bashi Suhailah ba, yanda Dady yake son Suhailah kamar bashida wasu yaran, duk da cewa a hakan shi Yusuf yana nuna mata so sama- sama, itace bata bashi fuska sosai.
*******
Dady sun shirya da Abban Ahmad ne bayan wani bincike da akayi aka gano Alhaji Isma'el yana ma company zagon k'asa, tuni aka raba hanya, tun daga lokacin ne Alhaji Isma'el yasha alwashin saiyaga bayan Abban Ahmad kota halin k'ak'a, a haka har yayi nasara ya sace Alhj Ibrahim dan kawai ya bashi dukiyarsa, shiko yace sai dai a kasheshi, haka yayi ta gana masa azaba kala-kala, anyi neman duniya ba'aga Alhj Ibrahim ba, har suka barwa Allah, sai komai na kasuwanci ya dawo gun yayan Ahmad, shi yaci gaba da kasuwanci. A lokacin Ahmad yana Holland yana karatunshi, acan yayi Aure ya auri wata baturiya, ya musuluntar da ita, yayan shi kuma yana Nigeria yana tafiyar da kasuwan cin mahaifinsu. Har Allah yayi ikonsa, Alhaji Isma'el ya sami nasarar kawar da yayan Ahmad wato Mahmoud a duniya, ta hanyar bata musu mota ba tare da sun sani ba, suka yi accident dashi da matarsa da driver duk suka rasu, hakan ne yayi sanadiyar dawowar Ahmad gida Nigeria dan tafiyar da ayyukan companyn mahaifinsa, da taimakon Dadyn Suhailah, Ya rasa matarsa ne ta hanyar CS da aka mata aka ciro Baby girl, ya had'a da yarinyar yayan shi ya kaiwa kakarsa Rabi da nanny dinsu 'yar bak'a ta rik'e.
**********
" Wace ce wanchan yarinyar" Ahmad ya tambayi wani abokinsa gun dinner din Al-Ameen yayan Suhailah, yana nunata da yatsa, "nima ban santaba amma inaga 'yar gidan ce, dan tun dazu sai kaiwa da komowa takeyi" Ahmad ya tabe baki, "kamar na santa, but na manta inane na santa" " My be kasanta, ko na tambayo ne?" Ya fada yana kannewa Ahmad ido? Murmushi kawai yayi, yace "nida mace kuma sai dai kallo, ko kuma idan na hadu da My princes d'ina" Aliyu dariya yayi dan yasan labarin princes tin suna yan matasa,har hotunan ta da ya frame dinsu duk ya sani, amma bai bari iyayensa suka saniba, har suka girma, Wannan shine gani na farko da Ahmad ya yiwa Suhailah tun bayan daya gudu a windon asibiti kuma gashi bai ganeta ba. Hatta lokacin da Dady ya masa maganar Auren da yake yasanta ne a suna tun lokacin da ta mishi sharrin nan wai ya tashi kasheta a ruwa, so bazai tuna fuskar ba, gashi ya tsaneta ba kadan ba. Shiyasa da aka mishi maganar auren ya amincine kawai dan kunyar da yakeji ta Dady bawai dan yana sonta ba. Kuma har akayi auren sau d'aya yazo gunta, shima dak'yar ta fito, yana ganinta sai ya gane itace wacce ya gani bikin Al Ameen. Anan ne ya sami sunan Alhaji Rabo. Ya baiwa Yusuf amanar kula mishi da duk wani moves nata, ba tare da yasan Yusuf ma yana ciki ba, lol.
*********
Suhaila kyakyawa ce uwa uba gata 'yar lukuta, dan jikinta tem tem yake, a cike take abinta, abinka da ruwan buzaye ruwan fulani, sai ta fito color dinda duk wanda ya kalla sai ya k'ara kallawa, gashin nan kuwa kamar ita ta baiwa kanta, 'yar gayu ce ta sosai, ga tsabta kamar hauka, sai dai akwai bala'en daukar kai, da jiji dakai, Run fil azal haka take a halitta... MU KOMA LABARIN MU. GIDAN AHMAD......í ½í¸
Post a Comment