IDAN ZUCIYA TA GYARU
By yasima Suleiman
IDAN ZUCIYA TA GYARU
Episode 1,2,3
****************
Ita dai bata ce komai ba sai dai ta ce, "Sala zanje wata unguwa yanzu zan dawo." "To mai tsada a dawo lafiya, sai ki kula da masu sonki a hanya, don na sanki da farin jini, yau Allah kadai ya san samarin da zaki dawo da su gidan nan in dai kin saki jikinki." Bata ce komai ba sai dai tana jin haushin abinda Sala din ke yi, wai yaushe ne Sala zata hankalta ta san duniyar ba matabbata ba ce ba? Shin yanzu rayuwarta bata zame mata ishara ta hankalta ba?, ita kam ta dawo daga rakiyar Sala din, da wannan tunanin ta fice. Can bayan layinsu gindin wata bishiya ta hango motarsa ta nufeshi da yanayin tafiyarta mai daukar hankali, ya zuba mata idanu, wani irin dadi da doki ya dinga ji kamar ya fito ya rikota har ta iso inda yake ya bude mata motar ta shiga ta zauna, ya zuba mata idanuwa ransa yayi fari tas, itama din kallonsa take yi tana murmushu sai ya ja motar kawai ya tafi. Can gidansa na hutawa da ake ginawa da sunanta ya nufa har ciki ya shiga da motar, ya riketa a jikinsa suka shiga cikin gidan. Wani irin yanayi suka ji kamar sun shekara basu hadu ba, sai yanzu ma suke jin wani shauki da tsananin soyayya yana ratsasu, gaba daya sun manta da bakin ciki sun kuma manta da ba tare suke ba auransu ya kare, don haka nema aka hana saki uku domin a sannan Allah kan jarrabi ma'auratan da son juna bayan sun haramta ga juna, har sai matar tayi aure da wani namijin ya sadu da ita sun rabu sannan ta halatta ga mijinta na baya, amman su da yake shaidan yayi musu fitsari a ka ko tsoron Allah ba sa yi. Sai da dare ya raba sannan Zainabu ta tuna da komawa gida, sai ta tuno ashe fa ita ba matar Mustafa bace yanzu, ranta ya baci hankalinta yayi mugun tashi, sai ta kama kuka, ya riketa a jikinsa yana tambayarta abinda ya faru. Ta ce, "Zumana tunawa nayi yanzu zamu rabu zan tafi na barka, ashe kai din yanzu ba mijina bane ba, bani da damar da zan iya rayuwa da kai yanzu." Hankalinsa shima yayi mugun tashi yaji duk ya tsani kansa, amman sai ya daure ya ce, "Zainabu ai ke din tawa ce, kullum zamu kasance tare, ko da bama gida daya zuciyoyinmu suna manne da juna kada ki karaya ni din naki ne kin ji ko?" Ya dinga mata magana mai dadi da tattausan lafazi wanda ya dinga shigarta, ranar dai anan suka kwana, sai da safe ya kaita bayan layinsu ya cika ta da kudi, nan din ma da kyar suka rabu. Tun daga wannan rana suka koma kamar da kullum suna tare, gidansa kam yaka kwana biyu har uku ma bai leka ba, Zainab sam bata gabansa burinsa da rayuwarsa ya tarkatasu ga Zainabu gaba daya, wani irin barin kudi yake mata wanda bai taba yi mata ba, tayi kyau matuka domin dai tana jin dadi da samun kudi a gurin Mustafanta. Zainab kam ta zama abar tausayi domin ganin Mustafa ya zame mata jidali, idan ta ganshi din ma bai ko kulata idan zata shekara tana masa magana bai kallonta, don yace saboda ita ne aka sanya ya rabu da Zainabu rayuwarsa, don haka ta shirya mugun zama a gidansa domin bata gabansa, daran da ya gaya mata wannan magana ta yi kuka matuka kamar ranta zai fita.
Gidan ya yi mata fadi, bata da abokin magana, Zainabu ce daman abokiyar hirarta gashi yanzu bata nan, ga kulle da yake mata har ta manta rabonda ta fita, ta yi kuka har ta gaji duk ta rame ta fige kamar ba ita ba.In da Allah ya kwace ta da bikin Sumayya ya tashi shima din Momi ce tace to fa biki ya tashi babu maganar hana fita, don haka ko yana nan ko baya nan Zainab zata gida. Ji yayi kamar ya mutu amman da yake Momi ce babu damar musu, don haka ya ce to kawai. Itama kanta ta lura ba da son ransa ya kyaleta ba. Sanda Zainab din tazo gidan kowa ya tausaya mata ranar da aka kawo kayan lefe, har tayi da na sanin hada auran nan, amman Zainab ta ce ita baya mata komai kawai dai bata jin dadi ne, gudun bakin mutane ya sanya ta ce Zainab din ta zauna har a kammala bikin tun da saura sati biyu, domin ya sauya gaba daya ko dariyarsa ba a gani, da yazo ya gaisheta yake ficewarsa ya bar gidan. Ai kuwa taji dadin haka din domin daman kadaici ya isheta, sai ta zage ta bata magunguna na cin abinci da gyaran jiki da fata, sai gata ta koma kamar jaka sai taci abinci sama da sau shida a rana, don haka kafin sati guda har ta mai da jikinta tayi kyan gani, sai dai duk shigowar da Mustafa yake yi gidan bai taba nemanta ba, ita din ma bata yi gigin neman sa ba don tasan bata gabansa, Momi ce ma takan ce ta kai masa abinci idan ya zo amman idan ta gaishe shi ma da kyar yake amsawa don haka da ta ajiye abincin take barin gurin. Ran Momi din yana baci matuka da abinda yake yi, amman ta lura dan nata yayi nisa da son Zainabu don haka taga gwara kuma ta fara yi masa addu'a da rokon Allah akan Allah ya karkato da zuciyarsa ga Zainab din. Ranar kamu ne gurin lakca da wata malama Binta tayi musu taji tana tallan wani littafi na koyar da yanda mace zata mallake mijinta ta zauna da shi lafiya, sunan littafin (Matsalolin Ma'aurata da hanyoyin maganceshi. Na Fauziyya D Sulaimana)
Ai kuwa a daran ta siyo shi a Jujin Labbu store ta siya guda biyu-biyu domin har da Sumayya zata baiwa, don yanda taji malamar na zuga littafin ta san lallai akwai abin karuwa a cikinsa. An yi biki an gama lafiya Sumayya ta tare a gidan masoyinta da take masifar so Mu'awiya, shima din yana sonta matuka, sai Zainab ta dinga sha'awar inama ace ita ce ta sami mai sonta haka, don bayan sun kai amarya sun koma gida kusan kwana tayi tana kuka don ganin yanda Mustafa ya nuna sam bata gabansa, ga kuma Maganganun da taji Hajiya Saratu tana gayawa Momin nasu. "Oni Saratu, naga ranar da yaron nan zai rabu da Zainabu karuwar yarinyar nan, wallahi na gaya miki Kubra kullum yana tare da ita, don da aka gaya mini ban yadda ba sai da mukaci karo da shi a Ni'ima Quest Palace yana kallona ina kallonsa yaron nan har gaisheni yayi ita kuwa wata uwar harara ta maka mini tana wani kara mannewa a jikinsa, shi ya sanya nace ki yadda ya auri Zubaida wallahi itace maganin karuwar tasa Zainabu, ki dubi yanda matarsa ta zama 'yar kallo kowa ya gane sam bata gabansa, ke kuma kina kallo danki yafi karfinki sai mace daya ke yawo da hankalinsa kamar tamaula." Hankalin Hajiya Kubra yayi mugun tashi, lallai biri yayi kama da mutum, amman za tayi masa magana ta nasiha da jan hankali ba da fada ba, sai dai ko kusa bata yadda ya auri Zubaida ba don gwara Zainabu yanzu a gurinta don dai ta gano shine silar lalacewarta, kuma da shi kadai take mu'amala shima haka, amman Zubaida fa har da turawa iskanci take kowa ya sani, amman don kada taji haushinta sai ta ce, "Saratu bawai naki yadda Baba ya auri Zubaida bane, a'a ki duba ki ga wannan yarinyar Zainab ba don mai hakuri bace ai da tuni auran ya watse, don dai taki sanar da kowa halin da take ciki ko iyayanta bata gayawa, wallahi da tuni nasan sun raba auran, don haka ya sanya ma banyi masa maganar Zubaida ba sam." Hajiya Saratu ta kwabe fuska tana fadin, "Ke dai baki so ba amman wallahi ki gwada hadashi da Zubaida zaki sha mamaki wallahi, sai ta raba shi da 'yar iskar yarinyar can."Don su bar maganar ya sanya ta ce, "Shi kenan zan tuntubi Alhaji da maganar." Wannan hirar ya sanya hankalin Zainab ya kuma tashi ta tabbatar bata da rabo a jikin Mustafa, ba zai taba sonta ba Zainabu ce dai burinsa abar sonsa har abada ko da aure ko babu aure, sai dai cikin dare ta tashi ta kai kukanta ga Allah mahaliccinta ta kaskantar da kanta matuka ta nemi zabinsa na alkhairi duniya da lahira. Washegari tun da safe Hajiya Kubra tace mata ta hada kayanta yau zata koma gidanta, sai taji gaba daya hankalinta ya tashi kamar ta dora hannu a kanta tayi ta zunduma ihu take ji, amman ta sanyawa ranta dangana ta hau hada kayanta. Sai dai idonta yana zubda hawaye don tana ji ne kamar za'a kaita kabari da ranta. Da kanta Hajiya tayi kiransa akan ya zo ya dauki matarsa da daddare, sai yaji wani kunci da bacin rai, amman ya daure ya ce shi kenan zan shigo Insha Allah. Karfe tara na dare Zainab ta kammala shirinta, Momi ta gama gyara ta tayi kyau matuka kamar wata sabuwar amarya koda yake ita din ce, ya iso gidan sanye da manyan kaya kamar wani mutumin arziki. A daki ya tadda Momi din tana karatu, ya shigo da sallamarsa ya zauna bisa kafet yana gaisheta. Ta zare medicated glass din dake idonta tana amsawa fuskarta a sake matuka, don haka ya dan ji dadi a ransa. Ta gyara zama tana dubansa na kusan sakan goma sannan ta fara magana, "Baba duk da nice na haifeka ya dace na nemi afuwarka bisa raba ka da nayi da iyalinka, lallai yanzu na gano kuskure na sanda bani da hanyar da zan gyara maka auran ka, sai dai duk da haka ina neman afuwarka.....haba Momi kin wuce komai a gurina, ke ce kika haifeni don haka ba zan taba kullatar ki ba, kin isa da ni kada ki kuma tunanin kina da laifi a gurina kece sama da ni, ba za kiyi laifi a gurina da zan kullace ki ba, na yafe miki kema ina neman ki yafe mini duk laifin da na yi miki." Ta ji dadin abinda ya ce don haka ta dora da cewar Shi kenan Baba komai ya wuce a gurina sai dai zan kuma neman wata alfarma a gurinka, nasan baka son Zainab hasalima saboda biyayya ka aureta, don haka yanzun ma ina son kayi mini biyayya ka zauna da matarka zama na gaskiya da auratayya kamar kowanne ma'auraci, na sani Zainab mai hakuri ce da juriya domin tunda take da kai wallahi bata taba zuwa tace min kayi mata wani abu ba, don idan na matsa mata da tambaya kuka take saka mini, don haka ka rike matarka da amana da gaskiya, yau na danka maka amanar Zainab idan ka cutar da ita kai da Allah, ka kuma ji tsoron Allah bisa abinda kake aikatawa domin dai yana kallonka." Jikinsa yayi matukar sanyi da maganganun Momin tasa, sai yaji kunyarta da nauyinta yake ji, domin baya tantama taji har yanzu yana tare da Zainabu amman bata yi masa hargagi irin can baya ba, don haka yake jin dole zai kula Zainab tunda ta damka masa amanar ta a hannunsa, ya daure ya ce, "Momi kiyi hakuri Insha Allah zan zama mai miki biyayya har karshen rayuwata."Taji dadi har cikin ranta ta ce, "Shi kenan Baba tashi kaje Allah ya shi maka albarka ya tsareka ya kuma shiryeka." Ya mike yana amsawa har lokacin kunyarta yake ji ya gaza daga kansa sama. Sai da ya kai bakin kofa sannan ta ce masa, "Ka jira matarka a mota zata fito ku tafi." Ba tare da ya tsaya ba ya ce mata "To." Ya fice. Yayi zaune cikin mota cike da tunanin Zainab, sai ya ji wani tausayinta ya ratsa shi, wato ashe zargin da yake mata da babu ruwanta ba itace sanadiyyar rabuwarsa da Zainabu ba, sai yake jin lallai ya zalunci yarinyar, wata kila ma alhakin ta ne ya sanya ya rasa rabin ransa Zainabu, har ta iso bai sani ba yana ta tunani. Sai da tayi masa sallama ta windo sannan ya ankara ya bude mata gaba ta zauna, duk a tsorace take da shi, gani take kamar zai hauta da masifa kamar yanda ya saba yi mata amman sai taga bai ko kalleta ba yaja motarshi. Shiru motar babu magana sai sautin wakar Sani Aliyu dan dawo da ya sanya, ita kam har lokacin jikinta rawa yake yi, a kofar Sahad store na Zoo road yayi parking, ya dubeta da kallonsa wanda a da sai Zainabu yake yiwa ya ce, "Ki fito muje store din,bai tsaya yaji abinda zata ce ba ya fice, tayi dan jim cike da mamaki amman dai tasan lallai ita din yake nufi domin dai ai daga shi sai ita a motar babu Zainabu, don haka ta fita da sauri tabi bayansa don kada tayi laifi. Sun jera gwanin sha'awa har cikin shagon ya fara diban abinda yake bukata, ya dubeta yaga binsa kawai take yi sai ya ce, "Ki dibi abinda kike so mana." Ita kam ba don kada tayi laifi ba da babu abinda zata dauka, amman gudun kada ya hauta da fada ya sanya ta dauki turare kala uku masu kyau da tsada sai alawowi kala biyu da biskit. Sanda ya kammala diban abinda yake bukata ya kalli dan keken kayan nata sai yaga turare da biskit kawai, bai ce komai ba ya hau diban kayan mata yana zuba mata, ya manta ba Zainabunsa ba ce domin duk wani abu da Zainabu ke so shi ya sanya mata, turare ya sanya yafi kala goma, banda mayuka da su shaving powder da shaving cream din ga sarkoki da kananan kaya, tun tana mamaki har ta zuba masa ido kawai, gurin biyan kudin ne ta zaro ido domin jin yawan kudin da aka ambata ammab babu ko dar ya zaro ya biya. Sanda suka fita kuma ya tsaya yana dibar fanice da gasashshiyar kaza, ita dai ta shiga mota tana tunani. Sanda suka isa gida shi ya shigar mata da kayan har dakinta wanda bai taba shiga ba tunda yake gidan ba kusan shekara biyu, kai bata jin ko hanyar ma ya taba bi, bayan ya ajiye ya dubeta "Ki taddani a sama don acan zaki kwana yau." Wani irin dadi ya dinga fisgarta, ta zauna tana duban siyayyar da Yayi mata lallai Mustafa dan gayu ne na karshe, ta dinga daga kayan tana dubawa sai Zainabu ta fado mata, wai ko yayi zaton Zainabu ce domin dai duk abinda take amfani da shi ne ta dinga jin dadi da farin ciki, lallai ta fara samun matsayi a zuciyar Mustafa tunda har zai siyo mata abu irin na Zainabunsa. Ta bude kayanta ta dauko littafin da Momi ta siyo mata na matsalolin ma'aurata ta fara dubawa, sai taga zata bata masa lokaci kada yayi fushi kuma, don haka ta maida shi ta ajiye ta fada bandaki, tayo wanka fes da ita tayi amfani da shaving cream din ta tsaftace gashin duk dake jikinta, ita kanta sai taji dadi a jikinta musamman sanda take shafa roll on, sai taji wani irin dadi da kamshi yana shigarta,Ta fesa dukkanin turaren da ya siyo mata sai taji wani irin kamshi mai dadi yana tashi a jikinta sai ta dinga tuno da kamshin Zainabu, lallai kam dole Zainabu taso turare tunda dai Mustafa yana so, bata mantawa duk sati sai Zainabu ta siyo turarirrika banda wanda ake hada mata.
Ta sanya kayan bacci a cikin wanda ya siyo mata, sanda ta kalli kanta a madubi sai taji kunya ta kamata, ji tayi kamar ta cire amman sai ta tuno da abinda Anti Fauza ta ce a matsalolin ma'aurata, "Idan kika tsaya kunya lallai zaki rasa mijinki, don haka ki saki jiki ki kyautatawa mijinki." Don haka kawai ta danne kunyar ta ta nufi sashinsa a ranta tana tunanin abinda zai biyo baya. Sanda ta shiga ta tadda shi a falonsa zaune yana kallo daga shi sai gajeren wanda babu ko singilet, gashin kirjinsa ya kwanta lambus sai wani sheki yake yi, kunya da wani irin shauki ya kamata ta shiga da sallamarta. Sai taga ya tsareta da idanuwansa, a ransa dadi yake ji da kamshinta sai yake gani kamar ba kanwarsa ba Zainab da yake yiwa masifa ba, yau kam ta sake masa gaba daya, kayan da ta sanya sun tsokano shi matuka har ya gaza dauke idonsa daga kanta, ya fara tunanin irin surarta ashe ita ma din ba baya bace ba. Ya dai daure ya ce mata "Ki dauko plate ki zuba mini naman nan ki hado mini da ice cream din." Ta mike da sauri ta dauko ta kawo gabansa ta ajiye, dan yana kan kafet ne, tana shirin tashi yayi magana, "Baki gyara kazar ba ko da kaina zan gyara, ko baki san yanda Zainabu ke ciyar da ni ba? Kiyi hakuri da halina Zainabu ta shagwaba ni da yawa, don haka kike jin koda yaushe ina zancenta." Bata ji haushinsa ba don ta san Zainabu ta cancanci haka a gurinsa, sai dai tayi alkawarin zata yi masa abinda ya zarce wanda Zainabu ke masa indai shine zai sanya ya sota kamar Zainabu. Ta gyara zama ta fara bare masa amman sanda ta mika masa sai yaki buda bakinsa, ta dubeshi da sauri taga ya tsareta da idanuwansa wanda suka sauya zuwa wata kala, kirjinta ya buga sanda ta tuno abinda yake nufi, anya kuwa zata iya haka din, amman tana son ko yaya ne Mustafa ya sota don haka ta daura damarar murje kunyarta, babu musu ta zauna bisa cinyarsa yanda Zainabu ke masa ta fara ciyar da shi amman kirjinta sai bugawa yake yi don kunya da tsoro. Ta yadda namiji bashi da kunya, ko da yake tasan shi din daban yake gurin gwadawa mace soyayya, tun tana jin nauyi har ta saki jiki, sai da ya ci ya koshi sannan ya mike yana fadin "Ki kashe TV idan kin gama,kamar ta bar kayan a gurin sai kuma ta tuno Zainabu da tsafta bata barin komai a gurin sai ta gyara tana da tsafta matuka, don haka kullum cikin gyara take, nan da nan ta gyara gurin sannan ta kashe tibin ta nufi dakin baccin nasa,ta dauko filo bisa gadon ta yadda akan kafet ta kwanta a kasa, bai ce mata komai ba yana kallonta har ta kwanta. Sai dai ta gaza bacci sai juye- juye take yi, wata irin soyayyar Mustafa ke ratsata, ta san Allah ya jarabceta matuka da tsananin son sa wanda take ganin bai mata ko digonsa, so take kawai ta ji ta a kirjin Mustafa yana lelenta yanda yake yiwa Zainabu, idanuwanta suka dinga zubda kwalla, ji take tamkar ta tashi taje gurinsa. Shi kuwa namijin duniyar yana sane da Zainab, ya riga ya san tuntuni tana sonsa tun farkon auransu ya fuskanci halin da ta shiga, a da yana ganin zata gaji ta daina ne sai dai yanzu ya lura tayi nisa, shima din yaji yana son ta yana son kusantarta, domin dai tayi masa yanda yake son mace kuma zai kyautata mata ko domin ya sami albarka a gurin Mahaifiyarsa. Da wata irin murya wacce bata taba jin yayi amfani da ita ba ta ji ya ce, "Zainabu!" Bata amince da ita yake ba don haka ta kuma takurewa kamar mai jin sanyi. Ya kuma kwantar da murya ya ce, "Zainab ina miki magana fa, ki zo nan kusa da ni." Wani irin farin ciki da dadi ya isheta, kamar kada ka mike amman ta gaza share shi don haka ta mike a nutse da yanga ta nufi gadon ta zauna daga nesa ta ce "Gani." Ya tashi zaune yana dubanta ta hasken dum light ya daure ya ce, "Zainab kina sona kin yarda da ni?" Ta dukar da kanta idonta ya ciko da kwalla domin dai bata san me zata ce masa ba, sai hawaye ya fara biyo kuncinta, domin ta jima tana addu'ar Allah ya nuna mata wannan rana da Mustafa zai gwada mata soyayyarsa, a da can kuma har ta fidda rai. Ganin ta yi shiru ya sanya ya dago idonta sai yaga hawaye na bin kuncinta, tausayi da sonta ya fara ratsa shi ya jata jikinsa yana lallashi, lallai ya yadda da abinda Zainabu ke cewa, wata rana zai so Zainab domin ta dace ya sota din ko domin hakuri da kawaici da biyayyarta, sai dai yasan ba zai taba son mace a duniya kamar Zainabu ba, yana jin Zainab ce kadai ta sami kashi hamsin ma. Ya dinga tausarta da gwada mata soyayyarsa wacce take jinta kamar ba a duniya take ba, Mustafa daban ne a cikin maza, dole idan kana tare da shi ka kyautata masa domin shima din bawan mace ne. Da safe kam kasa tashi tayi duk jikinta ciwo yake komai ya fita daga ranta, domin dai Mustafa ya wahalar da ita jiya sai dai tana alfahari da hakan, domin ya nuna mata soyayyar da take mafarkin samu. Ya fito daga wanka yana share kansa a gaban madubi, ta kura masa ido tana daga kwance tana kallonsa, tana son sa matuka a zuciyarta, sai dai bata san yana kallonta ba, tausayin Zainab yake ji musamman yanda tayi hakuri ta jure a daran jiya da shi, ya kuma amince zai iya komai domin ta. Ya juya ya dubeta sai tayi sauri ta runtse idanuwanta wai ita dole bacci take yi, ya yi murmushi gami da sungumarta kamar wata 'yar bebi yayi bandaki da ita, dariya ta kwace mata don ta gane ya gano ta, gashi daukar mace bata yi masa wahala sam shi, haka nan yake daukar Zainabu har goyata yake yi a tsakar gida
** *** *** ***
Zaman lafiya da soyayya mai tsafta suke gudanarwa a cikin gidansu, ta yadda Mustafa namijin duniya ne da ya cancanci mace ta bauta masa da biyayya da kyautatawa tunda dai shima yana yiwa mace bauta da kudin shi da jikinshi, wani irin shiga rai ne da shi, baya jin girman kai ko kunyar gwadawa mace soyayya ko a gaban waye, su da kansu 'yan uwa sun san yanzu Zainab ta zama sarauniyar mata a gurin Mustafa, ko da yaushe yana tare da ita in dai ba yana ofis ko gurin Zainabunsa ba, Momi tafi kowa murna da farin cikin haka. Sai dai duk yanda yake gwadawa Zainab soyayya tasan bata kai matsayin Zainabu ba a gurinsa, sai take jin kishin Zainabu yanzu matuka domin a da can bata san waye Msutafa ba bai kuma gwada mata soyayyarsa ba, amman yanzu da take son sa matuka sai take kishinsa, musamman da ta san ba soyayyar aure ce yanzu a tsakaninsu ba suna zama ne na la'ana a gurin Allah, don haka ta zage dantse gurin ganin ta mantar da shi Zainabun, ita da zai ji shawarar tama da Zainabun tayi auran kisan wuta ta dawo ya aureta da dai wanna muguwar rayuwar da suke yi.Amman abin da kamar wuya, domin Mustafa yayi nisa a son Zainabu, kusan duk wani abu da ya sai mata sai ya saiwa Zainabu, sau da yawa ma Zainabun yake fara saiwa sannan ya sai mata, idan kuma yana gida kome yake yi idan tayi kiransa a waya dainawa yake yi sai ma ya manta da kowa a gurin a gabansa sai ita, idan ta ce yaje kuwa babu bata lokaci zai fice, sai dai duk abin su basu kwana yanzu komai dare zai dawo gidansa. Abin ya fara damunta matuka domin yanzu kam ba zata iya hakura ta baiwa Zainabu Mustafanta ba, don tana ganin a yanzu tafi kowacce mace hakki a kansa. Yau da safe sun tashi ranar asabar ce, don haka yana hutun karshen sati, ta ci kwalliya da 'yan bingilallaun kayan da yake so, sai kai wa da komowa take gurin shirya masa abincin da zai ci, shi kuma yana kallo rabin hankalinsa yana kanta, shima din ya ci kwalliyarsa da kananan kaya. Sai wayarshi ta fara kiran "Honey! Honey! Honey!" Ya san wayar Zainabu ce domin kidanta daban ne, Yayi dariya gami da amsa kiran yana fadin, "Tuba nake zumana yanzu nake shirin kiran ki, domin nasan yau ne zamu gyaran gashin ko?" Daga can bangaren ta kwantar da murya da shagwaba ta ce, "Zumana ka manta ma ko, to kayi zamanka zani kawai ni kadai, tun da ka fara mantawa da al'amurana ma." Ya kwantar da murya yana fadin, "Ni na isa, yanzu dai ki shirya don bana son jira kin sani sai kiyi flashing dina sai na fito muje ko zumana." Tayi 'yar dariya tana fadin, "Zumana I love you too."Yayi dariya shima ya ce, "Me too Zainabu na." Sannan ya kashe wayar. Zainab da ke ajiye masa snacks bisa tebur ji take kamar ta kwace wayar ta wurgar, ko kunyarta baiji yake gwadawa Zainabu soyayya a gabanta, ai idan da mutunci ma ya dace ya dinga boyewa a ganinta idan da adalci, wato ko mutuwa zata yi babu ruwansa. Idanuwanta suka ciko da kwalla, ire-iren wadannan abubuwan da yake mata ne ya sanya take kishin Zainabu matuka yanzu. Ya dubeta sanda take shirin tafiya babu ko dar a zuciyarsa ya ce, "Zainab zo mana ki bani ruwa kishi nake ji." Kamar kada ta dawo amman dai ta dake ta dawo din ta zuba masa a kofi ta mika masa, ya amsa yana sha yana dubanta. Sai da ya kammala shan sannan ya dubeta yana fadin."Bebita kinga yanda kika kara girma kuwa, zo nan ki gaya mini me kike ci." Bata juyo ba tayi gaba da sauri tana fadin, "Miya ta zata kone bari na dawo." Ta yi haka ne don kada ya ga kukanta, domin ta kai makura a tsananin son sa, ta shiga kicin ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, sai dai tayi mai isarta sannan ta fita falon. Sai ta taddashi tsaye yana neman makullin mota, gabanta ya fadi domin dai tasan fita zai yi gurin Zainabunsa ta jaraba. Ta tsaya tana kallonsa cike da takaici, har ya nemo makullin ya dubeta da kulawa sannan ya matsa jikinta yana mata salon nasa da yake kuma makalle zuciyarta amman taki tanka masa, shi ko a jikinsa ma. Ya ce, "Zan tafi bebina ki kula da kanki." Ta gaza jurewa ta dubeshu da haushi ta ce, "Wai kana nufin ba zaka zauna ka ci abincin ba ma, kana ganin yanda na dage nake shirya maka abinci?" Ya dubi agogon hannunsa sannan ya ce, "Kada ki damu ai da sauran lokaci ki zuba mini cikin warmer zan dawo na ci." Daga haka kawai sai ya fice da sauri yana amsa wayar Zainabu da wasu kalamai da ranta ya gaza dauka. Ta zube a kujera ta dafe gefenta tana fadin, "Lallai na gamu da babban aiki, yanzu ta yaya Mustafa zai san daraja ta ya tabbatar nima macece kamar Zainabu da nake son ya dinga sona da kyautata mini?" Ta sani ko ya sha giyar wake bai isa ya kirawo ta a gaban Zainabu ba, ko itace tayi kiransa a dakile yake amsawa sai wayar tayi kira kusan sau uku ma, don haka ma da taji ta kirashi sau daya bai daga ba ba ta kuma kiran sa don ta san yana tare da Zainabun sa." A bakin hanya ya taddata tsaye tana jiransa, tun daga nesa ya hango motoci na ta yi mata signal amman ko kallonsu bata yi, yasan Zainabu shi kadai take so. Tayi kyau matuka ta ci kwalliya da wata shadda (dark green) dinkin doguwar riga ce sai dai ya kamata daga kirji ga wani aikin sama da tasha tayi kyau matuka, shi kam kullum Zainabu kara masa kyau take yi kamar ana sake kerata, sai dai bai san tsabar kwalliya bace da gyaran jiki, domin ko da yaushe zaka taddata da hadin gyaran jiki na kurku da kwai da banbita da lalle da madara ta shafa a jikinta kafin ta shiga wanka, shi ke sanya fatarta kyau da taushi kamar ta dan jariri. Yayi parking a gabanta yana kallonta da murmushi da dubansa, ta bude motar da sauri ta shiga,ya tuka motar suna tafe cike da shauki da soyayya suna hira. Ya kaita gurin gyaran gashin har halawa da kunshi za'a yi mata, don haka ya kame a mota yana ta karatun jarida, sai dai idan lokacin sallah yayi ya tashi yaje ya yi, sai karfe hudu da rabi aka kammala mata, ta yi kyau matuka jikinta sai wani silbi yake yi, ya dinga kallonta tamkar ya lasheta don so, su kansu matan dake gyaran jikin sun san da irin soyayyar dake tsakaninsu, domin Zainabu kam ta jima tana zuwa gurinsu kuma duk shine yake kawota koda yaushe. Bayan sun shiga mota ya daga bakin glass ya jata jikinsa yana fadin, "Kai Zainabu kin ganki kuwa kamar wata tarwada." Ta kwanta luf a jikinsa tana masa kissarta da yaudararta, can dai ta ce, "Yallabai muje gida mana tukunna." Bai yi gaddama ba ya ja motar yana fadin, "Ai dole na biya kudin wannan kwalliyar gaskiya. Zainab kam yau duk iyakacin hakurinta ta kai makura saboda bacin rai har wani zazzabi zazzabi take ji yana kamata da ciwon kai, amman a haka nan ta daure tayi masa girkin dare domin dai na rana ya sandare ta mikawa maigadinsu, amman har takwas ta wuce bai dawo gidan ba. Tayi wankanta ta yi kwalliya mai kyau tayi kwance bisa doguwar kujera tana kallon agogo, sam hankalinta baya kan tibin da ta kunnan ya tafi ga tsananin tunanin Mustafa. Sai karfe goma sha daya da kwata ya shigo gidan fuskarsa cike da annuri, ta dago ido tana kallonsa wani malolon bakin ciki ya tokare mata kirji, da kyar ta iya yi masa sannu da zuwa, ya rike ta yana dariya yana fadin,Bebina kin gaji da jirana ko? Bari na watsa ruwa ko naji dadi a jikina." Ya wuce samansa kai tsaye. Ta bishi da kallon takaici amman dole yau za a yi ta ta kare don ta gaji da wannan cin kashin da yake mata. Ta koma dakinta tayi wankan ta gami da daukar kamshi, ta sanya wasu kayan bacci masu kyau matuka komai na jikinta kana iya gani, sanda ta isa dakinsa yana kallo ya mike da sauri ya tarota yana fadin, "Kai bebina irin wannan kwalliya haka gaskiya kin yi kyau Zainab matuka." Bata kula shi ba har suka zauna a kujera ya saketa yana sauya tasha. Ta dubeshi ta ce, "Ya Mustafa ina son magan da kai ne ko zan samu dama?" Ya Juyo yana dubanta ya ce, "Me zai hana? gani a kusa da ke me ya faru ne sanar da ni." Ta sunkuyar da kanta sannan ta fara magana, "Akan abinda kake mini ne, duk lalacewata dai ni matarka ce don haka ya dace ko kaka ka dinga bani daraja da girman da Allah ya bani na aure, ka duba ka fita tun safe da sunan zaka dawo nayi ta ajiyar abinci baka dawo ba, yanzu ma ga na dare can ko kallo bai isheka ba, shin kana ganin kana mini adalci kenan? Duk sanda na kirawoka in dai kana tare da Anty Zainabu baka iya min maganar arziki, amma ni a gabana zaka kirawota kuna zancen soyayya, shin ni mai ya sanya baka gudun bacin raina sai nata, kai ko kunyar boye halin da kuke ciki baka yi, don haka ni kam na gaji wallahi, akan gyaran gashi ka tafi tun safe bayan ni ko kofar gida ka hanani zuwa balle ka kaini gyaran gashin, idan baka ga zaka iya zama da ni ba sai sai ka sallameni ka zauna da Zainabu taka, idan ya zo kowa ya san halin da kuke ciki.....
ke malama ya isheki haka" Ya daka mata tsawa jikinsa har tsuma yake yi ya mike kamar zai dake ta yana cigaba da fadin, "Me kike nufi yey? Ko kina tunanin dan son da nake miki zai iya sanyawa na rabu da Zainabu ne, don kinga na sakar miki fuska shine zaki kawo mini wata maganar banza? To karya kike yi baki isa ba wallahi. Da kike cewa na zabi daya kin sani ai Zainabu bata da na biyu a gurina don haka sai kije ki gayawa duk wanda zaki gayawa, fitar mini daga daki stupid tun ban babballa ki anan ba,ta hasala matuka da maganganunsa, sai taji sam ta daina jin tsoronsa ko shakkarsa, don tana ganin ya zama mutum mai zalunci wanda yafi son kanshi da wani, don haka ta mike a hasale tana fadin, "Don ka wulakantani akan dadironka a matsayina na matarka ai kayi a banza....." Ya dauketa da wani mari mai zafi, wanda ya sanya ta gigice ta koma gani duhu-duhu, ta dafe kuncin ta cike da zafin zuciya da haushin Mustafa, sai taji ta tsane shi duk tsananin son da take masa da hakurin da take dashi yau ya kau,kamar ta kuma cewa wani abu amman sai ta fasa kawai ta fice daga dakin nasa ranta yana suya. Sanda ta isa dakinta ta fada gado tana kuka sosai, ta daukarwa kanta alkawarin Mustafa ko dan gwal ne ta rabu da shi, gaba daya auransa ya fice mata daga ranta domin dai ta lura in dai tana tare da Mustafa zata rayu ne cikin bakin ciki da takaici kawai, gwara ta barshi ko Allah ya hadata da mai sonta, kusan haka ta kusa kwana sai daga karshe ne dabarar yin sallah da neman zabi a gurin Allah ya fado mata ta mike da zama ta dauro alwala ta fara gayawa sarki mai duka halin da take ciki. Shi kuwa ji yayi haushi da takaicin Zainab ya shige shi, har tayi tsaurin ido da zata zagi Zainabu a gabansa? da ta kwantar da kanta kamar mutuniyar kirki ashe lumfu-lumfu tayi masa, sai dai bata sani ba duk son da yake wa mace bata isa ta nuna shi da yatsa ba, ko Zainabu ta san halinsa bata kawo masa wargi.ya kashe fitilar dakinsa bayan ya kulle kofar ya haye gadon cike da takaici, sai ya fara nemo layin Zainabu yayi sa'a kuwa ya samu don haka ya fara zuba mata halin nasa. Ta shagwargwabe masa tana fadin, "Zumana babu kyau fa, ya dace ka kula da Zainab kaga tun safe muna tare ya dace ka bata lokacinta itama, ni kam bana son abinda kake yi mata gaskiya." Yayi wata ajiyar zuciya a ransa yana fadin, "Kece kika damu da ita amman ita zarginki ma take yi." Amma a fili sai ya ce, "Kin santa da saurin bacci har ta yi bacci fa ni kuma idon nawa babu alamun bacci shi ya sanya na bugo miki ko kya gayan abinda zai sakani baccin." Ta yi dariya tana fadin, "Shi kenan rufe idonka kaji." Babu musu ya rufe idonsa kuwa ta fara gaya masa wasu maganganu dake kara sanyata ta shiga ransa matuka har bai jin zai iya hada sonta da na wata ma, sun raba dare suna hira sai da bacci yaci karfinsu sannan suka rabu. Da safe ko ta kanta bai bi ba ya kuma ficewarsa duk da ranar ma hutu ce yakan zauna a gida ne idan bai tare da Zainabu, ai kuwa kiran Zainabu yayi a waya ya ce ta tadda shi a gidansa na shakatawa, bata yi musu ba ta hau gyaran jikinta. Kwanaki uku ya kwashe ba tare da ya nemi Zainab ba, ko girkin da take ajiye masa baya kalla, kullum yana tare da Zainabu har sai ta koreshi gida, idan ya koma gidan ma hayewarsa yake sama yana kallo ko yayi ta bincike bisa desktop dinshi. Zainabu tana zaune a tsakar gida tana saka lalle a kafarta Sadiku ya shigo gidan, ta dubeshi sai ta fara gaisheshi. Kamar jira yake ya hauta da masifa yana fadin, "Malama kada ki kuma gaisheni, kada ki kuma nunawa kin sanni 'yar iska mara mutunci, mai zubar da kima da darajarta, ace kin rabu da namiji yayi miki saki uku amman kina manne da shi kamar cingam kuna watsewa, waye zai aureki a haka, Allah ya shiryaki sha- sha-sha sokuwa kawai." Ta murguda baki tana fadin, "Meye ya shafeka da rayuwata da zaka matsa mini, babu ruwanka da rayuwata." "Wallahi ki rufe mini baki ko nazo na tattakaki, sokuwa kawai, na yi zaton auran da kika yi zuciyarki ta gyaru ashe kina nan da halinki na masifa da bin maza.....kai Malam ya isheka." Sala ta fito daga bandaki zaninta yana kokarin faduwa don masifa, sauri-sauri take yi ta fito ta dirar masa, banda ma kashin ya matseta da bazata iya zama ta karasa ba. Ta dora da cewar "Mutumin banza mutumin wofi, kaje ka fara gyara gidanka sannan ka gyara na wani kana zaune da mace ta asirceka ta mallakeka amman ka zo kana zagin wasu, inace tuntuni nayi maka tsakani da Abula eye? Don haka ka fita daga harkarta." Ya juya ya fice cike da bacin rai ya rasa hali irin na Sala da har yanzu taki ta farga ta san Annabi ya faku, amma dai ba zai fasa sauke nauyin da ke kansa na tunatar da su ba, wai matarsa ce ta mallakeshi don kawai tana masa biyayya shi kuwa yana kyautata mata shi kenan Sala ta sanyata a gaba da tsana da tsangwama ko 'ya'yansa bata kauna.
Ta dubi Zainabu ta ce, "Abula ta kenan kinga yanda aka sanya miki ido, ni bawai na hanaki hulda da Mustafa bane, a'a ki dai saki jiki ga masu sonki ki dubi kanwarki kiga yanzu yanda take fantama da kudi, ke din ma babu laifi amman dai nafi so ki koma Abulanki ta da can dana sani kin ji ko?" Domin dai ta rabu da jidalin Sala ya sanya ta ce, "Kinji fa Sala, baki ga ina fita yanzu sosai ba, ai na rabu da Mustafa tuni yanzu samari kala-kala nake kulawa." Sala ta ji dadi ta ce, "Yauwa ko kefa diyar albarka, kinga ke da Jamila kun share mini hawayena wallahi, Allah dai ya shi muku albarka." Ta shige daki tana sambatu, ran Zainabu ya baci matuka ta rasa abinda ya sanya Sala ta kasa gane gaskiya, ita kam ta gama harkar bariki, Mustafa don tana son sa ne shi ya sanya take tare dashi, ko Asma yanzu dake da gidan kanta ai tana bata labarin irin wuyar da take sha, gashi anyi sababbin 'yan mata an fara daina yayinsu don haka gwara ta koma yin aikin ta ma, ita tana jin auren kisan wuta ma kawai zata yi ta koma wa Mustafanta ta huta da wannan galla firin a titi domin ta dandana rayuwa mai dadi a gidan auranta tasan yafi komai daraja da mutunci in dai mace tayi dace da namijin da yake sonta da kaunarta, don haka ita kam ba zata koma harkar banza ba. Yana Ofis a zaune wayar Momi ta shigo, ya dauka da sauri jikinsa yana rawa don yayi zaton Zainab ce ta kai kararsa muryarsa da ladabi yake gaida Momin. Ta amsa sannan ta dora da cewar, "Daman cewa nayi yaya jikin Zainab din, domin jiya Farida (Yarinyar da take riko kanwar Zainab din) ta je wurin nata ta ce bata da lafiya, na kira wayarta kuma a kashe."Gabansa ya fadi domin dai ko kusa bai san bata da lafiya ba amman sai ya dake ya ce, "Da sauki Momi don har abinci ta ci kafin na fito ta kama aikinta kuma." Momin ta ce, "Allah ya sawake, sai dai ka dinga kulawa da ita don kasan mai karamin ciki ba a so tana yawan aikin wahala don kada cikin ya sami matsala." Wani irin banbarakwai yaji zancen, da gaske ne tana da ciki Zainab shi yaya aka yi bai lura ba tuntuni, amman ya daure ya dinga cewa Momin to kawai, sai dai hankalinsa gaba daya yayi gida. Ya duba agogo karfe biyu da kwata da sauran lokacin tashi daga ofis amman dai ya matsu ya koma don ya tabbatar da gaskiyar abinda aka gaya masa. Ana ta kiraye-kirayen sallar Magariba ya shiga gidan don bai iya tsayawa yayi a hanya ba, ya daura awlawa ya nufi masallacin da ke cikin unguwarsu don bada farali. Ko lazimi bai zauna yi ba ya koma gida da saurinsa ya nufi sashin Zainab. A kwance ya tadda ta tana dafe da ciki tana ta juyi tana kuka, ya isa da sauri yana tambayarta abinda ke damunta, ya jawota jikinsa yana tambayarta abinda ya faru. Da kyar ta daure ta ce, "Yaya Mustafa cikina ne ke ciwo tun safe yake mini ciwo na jika kanwa na sha da MMT yayi kamar ya lafa sai dai yanzu ya matsa mini matuka." Bai jira komai ba ya sungume ta bayan ya sanya mata hijab ya fice da ita da saurinsa suka nufi asibiti.Acan dinma likita ne ya hau bincike a kanta bayan anyi mata allurar kashe radadi (pain reliever) sannan ya hau mata hoto (scanning). Ya gano abinda ke damunta don haka ya kalli Mustafa dake ta hada gumi ya ce, "Oga Madam na dauke da ciki na wata uku, sai dai rashin hutu ya sanya za'a yi asarar ciki.....Innalillahi wa innan ilaihi raji'un, yanzu likita yaya za'a yi? Ina son cikin nan bani son nayi asararsa." Ya kuma duba cikin kwamfutar yayi dan wani nazari sannan ya ce, "E to idan aka yi kokari ta sami bed rest sannan ka daina kusantarta na tsahon watanni biyu zuwa uku ina ganin za'a yi sa'a ya zauna, amman sai an kula sosai." Mustafa ya ce, "Nagode likita za'a yi yanda kace din, yanzu zamu iya tafiya gida kenan?" Ya ce, "E zaku iya tafiya, bari na rubuta muku magunguna sai ku tsaya a dakin shan magani ku siya." Ya rubuta musu ya basu. Ji yake kamar ya goyata tunda ance ba'a son ta motsa jikinta, amman dai ya ciccibeta tana fadin zata iya ya kyaleta tunda cikin yayi sauki amman ko sauraronta bai yi ba sai da ya kaita har cikin motar ya zaunar da ita, ya koma ya sayi magungunan sannan ya dawo ya tada motar, a gida ma daukar ta yayi cak sai da ya kaita har tsakiyar gadonta sannan yayi magana.
"Kada ki sake ki tashi zan kawo miki abinda za kici." Bai jira yaji abinda zata ce ba ya fice. Ta bishi da kallo a ranta tana mamakin halinsa kamar ba shine yayi mata tijara ba, ki dubi yanda yake wani lelenta ko kuma albarkacin cikin ta ne, shi dai ya sani ita kam ai ta fita daga harkarsa kamar yanda ya bukata, bata so ace ya san bata da lafiya ba ma. Ya shigo niki-niki da kayan abincin da ya dafa, indomie ce ya dafa da kwai sai lemo da ya hada mata da shi, har tsakiyar gado ya zauna ya ja farantin gabanta ya debo ya ya mika mata bakinta, kamar kada ta karba sai kuma taga ya tsare ta da idonsa don haka kawai sai ta karba ta fara ci, sai da tace masa ta koshi sannan ya kyale ta ya fita da kayan. Ya jima bai dawo ba har tayi zaton ko ya kwanta ne, can sai gashi jaye da akwatin kayansa, tana kallon ikon Allah ya bude bangaren wardrop dinta da ya kama jera kayansa, ya wuce madubi ya jera kayan shafarsa da turaruka, sannan ya wuce bandaki ya ajiye sauran yayo wanka daga nan ya sanyo kayan baccinsa ya haye gadon kusa da ita,danuwanta biyu tana kallonsa amman sai ta rufe idonta wai dole bacci take yi, ya jata jikinsa yana shafar kanta, tayi kokarin ta kwace amman ta kasa a cikin kunnenta ya fara magana "Mai ya sanya baki sanar dani kina da ciki ba Zainab, wato kina so nayi asarar abinda na dade ina nema, ko baki son sa ne ke?" Ita dai bata tanka masa ba sai haushi ma da ya kuma bata, ya cigaba da magana "Na dawo nan kusa da ke don ba zan yadda ki dinga hawa sama ba kada wani abun ya sami Bebina, sannan zanfi kulawa da ke, gobe kuma zan sanya Momi ta turo Farida da wata mai aikin ko tsinke bani son ki taba a gidan nan kin ji ko?" Ta kulu matuka ta janye hannunsa daga kanta tana fadin "Wai ina ruwanka da ni ne, kai da kace na bar maka gidan ka ko ka manta ne, ni fa Zainab ce wacce baka kauna." Ya yi dariya ya ce, "Yan mata kema kinsan ai ina sonki, sai dai bani son kina shiga sha'ani na da Zainabu, amman na daina ko da ambaton sunanta a gabanki tunda baki so, hakan yayi miki?" Bata ce komai ba illa rufe idon ta kawai da ta yi, amman ko babu komai ta sami natsuwa a cikin ranta, don ta san tana da matsayi a zuciyar Mustafa din. Washegari din kuwa ya taho da Farida da magajiya wata daga cikin masu aikin Momi, har da Momi ma suka zo ta dubata da jiki kamar ta lasheta don so, Allah ya cika mata burinta Mustafa zai yi dan kansa. Zainab kam ta zama 'yar lele ta kuma yadda lallai Mustafa yana sonta domin numfashi ji yake kamar ya yi mata, yana ta lallabata gashi sam ya daina maganar Zainabu a gabanta, ko waya ta bugo masa sai ya fice waje sannan zai amsa, daga baya ma idan ya shiga gidan sai ya kashe wayar tashi gaba daya. A bangaren Zainabu kuwa ya kuma manne mata domin yanzu Zainab tana cikin hutun likita ne, don haka yana manne da ita, ita kanta zaman haka ya fara damunta don haka ranar wata lahadi tana kwance bisa cinyarsa yana shakar kamshinta ta fara yi masa magana. "Zumana na yanke shawarar zan koma aikina domin dai kasan zaman haka ba zai yiwu gareni ba, sannan ya dace zuwa yanzu mu tsaida magana guda daya, zanyi auren kisan wuta mu komawa auranmu, domin dai ka san ba zan iya rayuwa da wani namiji ba idan ba kai ba."Ya sha kunu matuka kamar wanda aka aikowa da mala'ikan daukar rai sannan ya ce, "Zainabu na mai ya sanya kika bijiro da wannan tunanin a ranki ne yanzu? Kina ganin abinda nake bai wadatar kine da kike harin komawa aiki, ina sane fa da mayun mazan dake sonki a gurin aikin naku kamar su cinye ki, ko kina zaton zasu maidaki haka zikau ba tare da sun nemi wani abu a gurinki ba, kina kuma sane da yanda nake kishinki ko matuka, ki bar wannan magana bana sonta." Ta kama shafar sajensa da salonta tana wani narke idanuwa ta ce, "Zumana ka amince mini, kaga aiki zai sanya idanun mutane su kauce daga kanmu domin yanzu an sanya mana ido matuka,ki bar batun aiki zan samo miki da kaina, wai ni kin manta da super market dinki ne? Zan kawo miki takaddun zan danka komai a hannunki ai shi kenan rigimar ko?" Ta yi dariya tana fadin, "Zumana kenan, to daya maganar fa? Kasan dai girma ke kamamu kullum ya dace ace mun zama ma'aurata sai muji dadin faranta ran juna, ya dace mu bar wannan muguwar rayuwar na gaji da ita haka nan bana son mu mutu cikin sabo." Maganar ta shige shi matuka amman dai yana tunanin wani abu daya, ya nisa ya ce, "Zainabu tuntuni nake wannan tunanin, sai dai ina jin tsoro ki yi aure, wallahi duk namijin da ya sameki a matarsa ba karamin yaki za'ayi kafin ya sakeki ba, ke bama na jin zai sake ki din ko da za'a kashe shi ne, shine abinda ke bani tsoro bani so na rasa ki Zainabu na." Gaba daya kamanninsa suka canza tashin hankali ya fito muraran akan fuskarsa kamar zai fasa kuka. Ta dinga kallonsa da so da kauna ta riko shi tana wani lelensa kamar dan jariri ta ce, "Zumana kana zaton zan iya sakarwa wani jikina har yayi kurarin rabuwa da ni? Kai ne kadai kake samuna a Zainabu ma.....
" "Kinga babu wani wayo da zaki yi mini, mai ya sanya shegun tsofaffin can ke nacin binki yanzu eye? ke da kanki kin san kin fita daban cikin mata, sai dai kiyi mini alkawarin kin daina sanya turare, kin daina gyaran fatarki da jikinki,ke kome za kiyi ke kyakykyawa ce babu wanda zai iya rabuwa dake Zainabu mu bar wannan zancen haka ya isheni." Ta langabar da kai ta ce, "Shikenan mun barshi, amman dai dole ka samo mana mafita idan ba haka ba wallahi zan maka yajin aiki, don nima ina son na mutunta kaina na gaji da yawon haka."Ya dinga dariya yana fadin, "Lallai da na haukace, ai idan kika yi mini yajin aiki nima sai na yiwa kowa sai nazo kofar gidanku na tare." Ta hankade shi ta mike tana wani yauki da kwarkwasa, sai dai bai bata damar hakan ba don shaidan ya gama yi musu fitsari bisa kansu.
Cikin Zainab yana girma tana samun kulawa matuka daga Mustafa har ya kai ta fara zuwa awo, tana jin dadin yanda yake mata amman tasan yana tare da Zainabu, sai dai bai wa kowacce zancan daya, don haka ko da wasa Zainabu bata san Zainab tana da ciki ba, kai ita tana zaton har yanzu bai kulata ma don haka idan ta tuno ta kan masa korafi, sai dai yayi dariya kawai a ransa ya ce, "Kina nan ai ta kusa haihuwa ma." Don haka ko da wasa bata yi zaton tana dauke da katon cikin Mustafa ba. Yau da safe tan jera kayan gugar da aka kawo mata daga wanki taji Sadiku ya shigo yana gayawa Sala Zaid ya zo da matarsa babu lafiya, yana mata bayanin ciwon daji ne ya kamata. Sala ta kama salati tana fadin, "Haba ba daji ba ai ko gona ce ta kama matar yaron nan, yaro yaki ya dawo mahaifarsa ya makale a can kasar larabawa, ni kam gwara da ya dawo gida tunda dai ai cimarmu ba iri daya ba ce dole mutum ya kamu da cuwuka kala-kala a kasarsu." Ya ce, "Lallai kam, idan dai kin sami lokaci ki shiga dubata, har Zainabu ma ki gaya mata tunda dai iyalansa na tsaye a kan hidimarmu, nima da daddare zamu shigo da Hafsat mu dubata." Sai taji tausayin matar ya kamata, don dai tasan yanda ciwon daji ke yiwa mutum illa, lallai zata je ta dubata domin dai ai Zaid mutuminta ne don dai baya kasar ne, don duk gidan Malam shine ke kulata sanda tana karama, har yakan mata soyayyar karya Sadiku yayi ta hanashi yana fadin halayenta, shi dai sai yace ai addu'a za'a yi mata ba kyara ba. Da yamma ta shirya cikin atamfa riga da zani na English Ghana tayi kyau matuka, ta yafa babban gyale don tasan halin Malam yana iya rarakota da bulala, don dai duk iyakacin shigarta bata bi ta kofar gidansa sai dai tayi yanke, ko da ta kama lallai zata bi ta kofar gidan nasa ne ko kuma idan ya zama dole gidan sa ne ko makotansa ta sanya babban gyale don binta yake da katuwar bulalarsa wani lokaci ya zanbada mata ma. Suna kofar gidan Malam din Zaid da Sadiku suna hira bisa fararen kujeru, ta dinga kallon Zaid din tana dariya saboda ganin irin gemun da ya tara a fuskarsa, ba don tayi masa farin sani ba ai da baza ta gane shi ba. Ta isa gurinsa tana dariya ta ce,Lallai ya Sheikh yanzu kake Shekh din naka, ai nafi shekara goma sha biyar ban ganka ba kace haka ka koma." Ya yi dariya yana shafar gemun nasa ya ce, "Yaya son ranki, har yanzu kina nan da tsiwarki kice." Ta yi dariya kawai sannan ta gaisheshi tayi masa yaya mai jiki ta shige cikin gidan. Sadiku sai wani harararta yake, ita kam ko kallonsa bata yi ba don taga irin hararar da yake mata tunda ta dososu, Zaid din ne ya dan daki kafadarsa ya ce, "Haba mutumina wai kai har yanzu kuna 'yar tsama da Zainabu ne, ya dace asan dai an girma." Ya ja tsaki sannan ya ce, "Kai don Allah baka ga shigar dake jikinta ba, ai da gani kasan bata da mutunci, wannan don zata zo gidan malam ne ma don ta san halinsa. Zaid ya ce, "Sadiku tuntuni na gaya maka kyara da aibatawa basa gyara mutum sai dai su kuma sanya shi ya bazama cikin sabo domin zai dinga gani kamar an tsane shi ne, ka tuna sanda tana yarinya idan ta fito babu dankwali ka korata da masifa ai bata sanyawa sai dai ma ta hadaka da Sala, ni kuwa da nake mata ta nasiha da lalama sai kaga ta koma ta saka har gyale ma duka, don haka ka dinga binta da nasiha da addu'a." Ya yi kwafa yana fadin, "Baka san halin shegiyar yarinyar nan bane ta wuce duk yanda ka santa da can wallahi, amman zaka gani da idonka ne wata rana tunda kana garin." Da haka suka bar zancan Zainabu suka fada na maganin da suke zance akan na hausa, domin dai anyi na baturen ya ki yi tuntuni. Zainabu ta shiga gidan da sallama, Inna Babar Zaid ce a tsakar gida tana wanke allon karfe, ta daga kai tana kallonta sannan ta ce, "Lallai yau kece a gidan namu 'yar gayu?" (da yake suna mata wasa na kamar jika da kaka ne). Ta zauna tana dariya tana fadin, "Yanzun ma ba gurinki na zo ba da zaki yi mini ciwon baki ba, ina 'yar uwarki tsohuwar take ne?" "Ban sani ba ai ta isheki riga da wando, don kinga bata nan a tsakar gidan? To tana sashen Malam yanzu zaki ganta sai ki fada a gabanta." Ta yi dariya tana tashi ta ce, "Kinga nifa dubiya na zo, shiya sanya bana son shigowa gidanku ku ishi mutum da kaudi." "E dole muyi miki kaudi tunda ke baki son ayi miki zance aure kinfi so kiyi ta gararamba a titi, wallahi da Malam zai ji ta tawa da yayi miki dan banzan duka ya balla kafafun yawon kowa ma ya huta. " Ta shige inda take zaton Aisha Matar Zaid tana can tana ta dariya, yanda ta ga Aisha sai taji duk jikinta yayi sanyi wani irin tsoron Allah ya kamata, domin dai gaba daya cikinta a nannade yake da bandeji, duk tayi wani duhu matar da ta sani fara tas du da sau daya ta taba ganinta. Ta zauna jikinta ya mutu matuka tsoron Allah ya shigeta ta dubeta tana mata sannu da jiki. Da kyar ta iya amsawa don tana jin jiki, Inna ta shigo dakin hannunta da ruwan rubutun da ta wanke a kofi. Zainabu ta dubeta ta ce, "Inna ashe haka jikin yayi zafi, kai abin gwanin ban tausayi wallahi, Allah dai ya sauwake ai banyi zaton ciwon ya kai haka ba." Inna ta ce, "Ai da sauki ma akan sanda suka iso, su na bature kawai suke yi shi kuwa ciwon daji maganinsa karfiyan ayar Allah, da tun farko sun dimanci Ayatul Kursiyyu da bai yi haka ba, kinsan ya taba kama Malam a kafarsa amman da ya dukufa Ayatul Kursiyyu cikin ruwa yana tofawa ya sha ya shafa ko yayi ta tofawa haka nan sai gashi Allah ya kawo sauki kamar bai taba yi ba, itama yanzu ita ake mata shine jikin yayi dan dama, don ma ta kama makarfafa ne, don hanjinta ta kama al'alamrin sai dai godiyar Allah." Zainab ta jima tana jimamin ciwon Aisha har ta koma gida ta kasa tsinana komai sai tunani, to wai su kenan ma da suke bauta da tsantseni ga Allah, yanzu idan irinta wannan ciwo ya kama yaya zata yi? Ta dinga jin wani tsoron Allah yana shigarta matuka, lallai ya dace ta nutsu haka ta san Annabi ya faku ta kama kanta, kusan ranar nan haka ta wuni sukuku babu walwala. Shi kuwa Mustafa shima yau da tashin hankali ya tashi domin dai Zainab na nakuda mai zafi kuwa, nan suka kwasheta suka yi asibiti amman har dare bata haihuba, ga nakuda mai zafi ce matuka don haka dai daga karshe sai aiki aka yi mata aka zaro diyarta budurwa mai kyau sai dai taki yin kuka kwata-kwata, daga karshe dai da aka yi bincike sai aka tadda zuciyar yarinyar ce a kumbure. Hankalin iyayen ya tashi matuka, su kansu likitocin sun shiga damuwa don dai basu taba cin karo da irin wannan matsala ba sai dai suna jin labari a kasashen turawa, daga karshe dai sun bada shawarar lallai ayi gaggawar fita da yarinyar kasar waje, sai dai sun bata taimakon gaggawa.
Washegari da safe Mustafa ya fara neman visa, ya sha wahala ya dawo gida wujiga-wujiga da shi, sai da yayi wanka ya zarce asibitin amman ya sha kashe kudi kafin ya samu.Kwanaki uku bayannan suka tafi kasar Germany don acan ne ya gano akwai kwararren asibiti. Sunyi sa'a da amincewar Allah aka samu yarinyar nan bayan an bata magunguna, har ma ta fara numfashi daidai, sai a sannan ya sami nutsuwa domin dai Allah ya jarabce shi da tsananin son diyar. Ranar da ta cika kwana bakwai suka yi waya da Alhaji Abdullahi ya ce, "Ai ta samu yarinya don har nono ta fara sha yanzu haka." Alhaji yaji dadi matuka ya ce, "To Allah ya kara afuwa, Yaya sunan ta ne ko baka yi mata huduba ba don ga Rago zamu yanka." Ya yi dariya yana sosa keya ya ce, "Baba tuntuni nayi mata huduba da Zainabu, don har babarta ma ta sani." Alhaji yaji dadi matuka ya ce, "Shikenan Allah ya rayata, ka zama dai na Zainabu Baban Zainabu kenan ko?" Suka yi dariya gaba daya. Ya kalli Zainab dake kallonsa da murmushi don ganin yana dariya ta ce, "Baban takwara kana son dai sunan nan matuka." Ya yi dariya kawai yana shafa kansa idonsa akan diyarsa da yake matukar kauna. Kwana daya, biyu, uku, hudu shiru babu Mustafa ko wayarsa babu. Hankalin Zainabu ya tashi matuka ta fara nemansa a waya amman sai ace suna kulle. Shi kam saboda rudewa ko wayoyinsa bai dauka ba ma sai da ya isa can nema ya siya, Allah ya sanya yana da lambarta a kansa don haka sanda suka yi kwana takwas lokacin ya dawo hayyacinsa ya fara neman layinta. Bata yi zaton shi bane domin dai yau kwanaki sha daya kenan rabonta da shi ko a waya, don haka tayi fushi matuka da shi sai ta maida hankalinta gaba daya ga matar Zaid Aisha, kullum acan take wuni don haka sam bata ta tashi, domin ta yanke shawarar aure kawai zata yi ko ya so ko yaki. Watansu guda yarinyar ta murje tayi kiba sannan suka dawo gida Nigeria, yayi neman Zainabu amman taki daga wayarsa, har sakonni ya aika mata na baya garin ne amman taki bashi amsa domin dai tana ganin kamar ya raina mata ajawali da zaiyi tafiya ba tare da ya sanar da ita ba, don haka shi duk a rikice yake so yake kawai ya iso gida Nigeria ya isa gareta. Sanda suka iso ya nufi gidansu amman sai ya tadda bata gidan wayar tata kuma tana kira taki dagawa lokacin tana gidan Malam, don jikin Aisha ya matsa mata matuka sai kiran sunan Allah kawai take yi, ga 'ya'yanta nata kuka gwanin ban tausayi, Zaidu ma kam hawaye yake matuka yana ta sanar da ita kalmar shahada, a haka har Ubangiji ya karbi ranta, hankalin Zainabu ya tashi matuka komai ya fice mata daga kanta na rayuwar duniya.
Haka nan ta dinga kallon Zaid yana hawaye sai ya dinga tuno mata da Mustafa ta san irin soyayyar da Mustafa ke mata ita Zaid ke yiwa matarsa, lallai ba zata yadda ta mutu da wannan mummunan aiki ba, zata mutu a hannun mijinta Insha Allahu da kalmar shahada, zata tuba ga Allah Mahalccinta. Haka nan aka yi makokin Aisha kwanaki bakwai cur duk tana gidan, tun Mustafa bai san inda take ba har aka sanar da shi tana gidan zaman makoki, don haka shima yaje ya yiwa su Malam din gaisuwa matuka ya so yaga Zainabu bai samu ganinta ba har akayi kwanaki goma. Ta fito da yamma tana sanye da doguwar riga idanuwanta sunyi fari kal suna ta kyalli don babu kwalli gyaran gashi zata, ya sha gabanta a mota kamar ta shareshi sai taga ya fito yana mata magiya, don kada ya tara mata mutane ya sanya ta shiga motar tashi. Kai tsaye gidan shi na shakatawa ya wuce da ita, ya jima yana rarrashinta sannan ta fito ta bishi cikin gidan, ya zauna a gabanta yana kallon idonta ya ce, "Zainabu fishi haka anya kuwa kinyi mini adalci, ki dubi yanda na koma don Allah, kiyi hakuri kome na yi miki." Bata kalleshi ba ta ce,
"To wai meye abun damun kanka, kayi tafiyarka ba tare da sani na ba ai me nace maka." Ya kwantar da murya ya ce, "Zainabu ai gwara ki mareni ko ki zageni da ki dinga fushi da ni haka, Ofis din mu ne suka turani wani aiki ba tare da na san an shirya tafiyar ba amman kiyi hakuri zumata." (Ya yi haka ne wai don baya son ta san Zainabu ta haihu kada ta kuma zarginsa). Ya jima yana lallashinta sannan ta sauko, ya kwantar da kai zai nemi abinda ya saba nema amman ta yi kicin-kicin da fuskarta tana fadin, "Mustafa gaskiya na gaji da wannan mummunar rayuwa, mutuwar Aisha ta tsoratani domin su da suke tsantseni da aikata sabo ma kenan kaga yanda cikinta ya koma sai da komai na kayan cikinta ya lalace, to kaga kadan kenan daga cutukan da Allah ke dorawa bawa, yanzu kam na tuba Allah ya ga zuciyata, don haka aure kawai zanyi ko kana so ko baka so, domin ba zan yadda haka kawai ina fagamniya na fadi na mutu ba me zance da Allah." Maganganunta suka shige shi matuka har ya ji tsoron Allah shima ya ratsa shi, don haka ya janye daga jikinta ya jingina da kujera yana mai da numfashi sannan ya ce, "Zainabu kin yi tunani mai kyau, gaskiya ya dace zuwa yanzu mu tuba bisa laifukanmu tunda dai kwanakinmu kara gaba suke yi, amman batun aure ki kuma saurarata zan san yanda zamu yi, amman ba zan so ki auri wanda zai ki sakinki ba."
Post a Comment