NAMANTA KOMAI
By yasima Suleiman
NAMANTA KOMAI
Episode 5 to 7
GIDAN SU SUHAILA. Aunty Rukayyah ce ta shigo d'akin ta na ta fad'a "Waike Suhailah mi yake damunki ne? Ace tunda aka fara hidimar aurenki ba ruwanki da komai, ba ruwanki da kowa! To malama ba damu zakiyi fushiba da Dadyn ki za kiyi fushi, shida kike ganin ya miki shishigi a rayuwa, ta qara so cikin d'akin wai ma kina ina ne inata magana kinyi banza dani.?" Turus tayi ganin ba Suhailah ba labarin ta, ta ja guntun tsaki, ta lek'a bayi nan ma ba ta nan, "Ina yarinyar nan ta shiga ne!?" Ta fito tsakar gida tana tambayar mutane ko akwai wanda yaganta!? amma kowa yace rabonshi da ita tun jiya, wasu kuma suce tun da asuba, nan da nan aka bazama neman Amarya, amma bata ba labarin ta, aka kira Dady akan ba Amarya fa kada a d'aura Aure, Dady yayi murmushi, yace "Aure kam ba fashi sai an d'aura." Ahmad ne yazo ya sami Dady, yace su kwantar da hankalin su yasan gunda take, bayan d'aura Aure zaije ya d'auketa ya wuce da ita, kawai a had'a mata kayan ta, sannan hankalin danginta ya d'an kwanta, bayan d'aura Aure Ahmad yaje ya d'auketa gunda tayi da Yusuf, tun lokacin da ta bude k'ofa ta fara gudu ne ya kira Su ya sheda masu cewa ya ganta kuma Suna tare lafiya lau. Sunji haushi, duk da cewa dama ba wanda zai rakata Abujar amma sun so ko yar hud'uba ce a mata harma yanda kan Suhaila yake rawa, amma hakan bai samuba kuma ta kashe wayarta.. Bayan ya d'auketa sai ya wucee da ita Abuja...
***********
Yana isa yayi parking din motar ya fito abinshi ya shige gidan gonarshi. Amfi minti talatin da tsayawarshi, masu aiki sun kwashe yan kayan Suhailah dake cikin motar, amma ita Suhaila bata fitoba, a ranshi yace "wai yarinyar nan mi take nufi ne??" ya koma wajen motar ya sa k'afa ya d'an shureta, amma maimakon ta tashi sai ta qara juyawa tana murmushi, ta cigaba da baccinta. kilan Suhaila taci gaba da mafarkinta ne....
Tsaki yayi aranshi yace "kyaji dashi yarinya kin riga kin zama matata" komawar shi yayi cikin gida, yaje yayi wankanshi da ruwa masu d'imi, yaji jikinsa yad'an warware da gajiyar tuk'i yasamu guri ya kwanta sai bacci.!! Sai k'arfe biyu ya farka, ya tashi ya lek'a d'akinta da ko ina amma bata ba labarin ta, tsaki yaja wato har yanzu tana cikin motar kenan, ya gane bata da niyar shigowa ciki, yaje gun motar ya kuwa hangota tanata bacci abinta, bai ma tsaya bata lokacinshi ba wajen tada ta, kawai d'auko ta yayi ya kaita d'akinta da yasa aka gyara mata cikin d'akunan dake sama, ya ajiyeta, a ranshi yace " Hmmm.!! mata akwai fi'ili ita kuma nata borin kunyar haka take yinsa" ....
Yayi d'an guntun tsaki chikin ranshi ya kashe wutar d'akin ya wuce abinshi... Duk da kasan cewar gurin gidan gona ne, gidan ya tsaru fiye da tunaninku masu karatu, "ni kaina M. Jabo dana shiga gidan saida naji kamar ace gidan J.S d'inane, habawa da zamu soye a gurin ba kad'an ba dan zaiyi d'ad'in soyewa.." Ahmad mutunne mai tsari, gaban shi da bayan shi, yadda yake a tsare physically, haka duk wata harka tashi take a tsare, haka mazauninshi abinshi gwanin burgewa.... YANDA ABIN YAKE AKAN YUSUF... Bayan fitowar Yusuf daga wajen Suhaila, bai tsaya ko inaba sai wajen Ahmad, ya gaya mashi duk yadda sukayi da ita, abunda bai gaya mashiba kawai shine ya rungume ta, for the first time (a karon farko)duk tsawon rayuwarsu, sanin Ahmad ne da halinsa yasa ko giyar wake ya zuk'a bazai furta ma Ahmad hakan ba.. Wannan sirrinshi ne har kabarinshi sai ku masu karatu da ni Jabo yar gane-gane dana gano... Ahmad yayi murmushi chikin ransa, yayi ma Yusuf godiya ya dafa kafad'arshi ya wuce abinshi, aranshi yake cewa "wannan yarinya daban mamaki take," ya karbi makullen motar, amma bai tafiba a lokacin sai da aka d'aura Aure akayi reception, mutane suka fara watsewa Sannan ya kama hanya, Yusuf har ya fara jin Ahmad ya bashi haushi a lokacin... Ya za'ayi ya ijiyeta awa sama da biyu, bayan ya gaya mishi tana chan tana jira, tsaki yaja, "duk nina janyo mata ai," duk da dai yasan bashida yadda zayyi dashi tunda Kudin da Ahmad ya bashi duk rayuwarshi ba wanda ya taba bashi su, duk akan ya kula mashi da duk wani moves din Suhailah .....!!!
****************
Washe gari da Suhailah ta tashi daga bacci, ta tashi da matsanancin ciwon kai, kuma duk inda ta juya jikinta ciwo yake mata, tana Wash! Wash!! haka ta tashi dak'er ta zauna, ta kalli nan ta kalli chan, bata gane ina take ba sam, jeem tayi, ta dan girgiza kanta, amma bata gane komai ba, ta ta shi ta rik'a tura k'ofofin da suke d'akin har ta gane bandaki ta tura kai ciki, nanma kalle kalle ta rik'ayi sai kuma ta tsaya kunne kunne, a ranta tanajin kamar akwai abinda akeyi a gurinnan Amma bata gane ko miyeba, kuma tanajin kamar akwai abinda ya dace tayi yanzunnan amma bata iya tuna miye, lokacin taji cikin ta na k'ugi alamar yunwa takeji kamar ta mutu, ta mik'e tsaye, ta nufi k'ofa kenan zata bude idonta ya kai ga mirror d'in d'akin,duk abunnan sai yanzu ta kula da fuskarta a mirror, ta kalli kanta sosai,nan take gabanta ya fad'i tsoro ya kamata,ta tambayi kanta ta madubi, ko Wacece wannan....." who are you..."abun mamaki abun tsoro, ta kasa ba kanta amsa, ai kuwa sai ta sa ihu, k'walla ne ke kwarara daga idanuwanta sabida kukan da take baji ba gani.......
Can cikin bacci Ahmad yaji ihunta, Ahmad da sauri ya fito daga d'akinshi, a dai- dai lokacin da yayanshi Surayya da Rukayyah suka fito daga nasu d'akin, suka iso inda yake kowacce ta kama hannu d'aya Suna murje ido alamun yanzu suka tashi daga bacci, had'e da murmushi a fuskarsu, suna murnar ganin Dadyn su, dan jiya koda ya iso sunyi bacci, suna isa dai-dai k'ofar d'akin Suhailah ta bud'e k'ofar ta fito tana yan hawaye, daganinta duk a tsorace take, yara kuwa da ganinta sai suka hau tsalle suna murna, da sauri suka je suka rungume ta, suna "oyoyo Mumy!!! oyoyo Mumy!!! " nan da nan Suhaila cikin dubara ta goge k'wallan idonta.. Yaran sun bata sha'awa, ta d'anyi murmushi ta rungume su itama, ita kam gaskiya tayi mata yawa, yanxu ita take da way'annan yaran k'yawawa haka,..???
Rukayya ta juya tace "Dady yaushe ka kawo mana Momy....??" yace "jiya kuna bacci tazo..." Suhailah a aranta tace "Idan way'annan y'ay'anane, kenan wannan shine mijinna...?" ta saki baki tana kallon su ba tare da tasan takamaiman gaskiyar abunda takeji ba, ta k'ara d'ago kai ta kalleshi aranta tace "amma mijina fa ya had'u gaskiya, y'ay'anmu kuma masha Allah, kamar y'ay'an larabawa" koda yake, itama Ba daga bayaba wajen kyau... Yaran basu ko wanke baki ba suka ce " Momy yunwa mukeji kuma Momy ke zaki bamu abinci," haka suka ja ta suna murna zuwa dinning table, da basu kaita gurin ba, da batasan ko inane dinning table ba, kamin su k'arasa Dady yace "kunyi brush kuwa??" Surayya tace " no Dady, yanzu muka tashi," " maza ku wuce a muku brush,"
"Dady mu Momy zata mana," suka fada suna kallon Suhailah, sai ga wata mata ta fito, ta duk'a har k'asa ta gaida Suhaila, ta amsa a sake, suka mak'ale ma Suhaila ala dole ita zata musu, yace " kunsan dai ba zakuci abinci ba sai kunyi brush" suka turo baki na shagwaba "Momy muje ki rakamu" haka suka ja Suhaila tana kallo aka musu brush sun k'i yarda a musu wanka, sannan suka fito, suna rik'e da hannun ta, cike da nishadi. Suka k'arasa ta bubbuda abincin, ta zuba musu dankali da Egg tana basu Suna bata, itadai ci take amma bakinta wani iri take jinsa tunda batayi brush ba, sukaci suka k'oshi sannan sukace "Momy yau ke zaki mana wanka." haka suka jata har bayin dakinsu, tace " kowa yayi wanka mu gani kun iya wanka" ai kuwa suka fara wanka suna wasa da ruwa, abin nema ya samu, saida suka gaji suka ce "mun k'are suka fito, oya kowa ya shirya mu gani, suka shafa mai kamar yanda sukaga nany dinsu tana musu, suka shirya kansu tsaf cikin wando da riga mai kama da irin wanda ta sanya, purple riga da black jeans.
Momy kayan mu irin d'aya da naki, Suhaila kam dadi take ta ji wai tanada 'ya'ya, har biyu, yan mata dasu, aranta tace " kenan kullan haka nake musu wanka na shiryasu? Gasu kyawawa dasu, tayi murmushi, kyaufa yayi, har cikin zuciyarta takejin sonsu, itakam har ta mance da ciwon da jikinta yake yi, duk da yayi tsami sosai, kuma da d'an tabo a hannunta, ta kula yaran akwai mai kula dasu, da kuma wata tsohuwa da ta hango a gidan, amma batasan ko wacece wannan tsohuwar ba. Rannar haka suka wuni tare da y'ay'anta, cike take da nishadi, da ta d'auki Rukayya, sai Surayya ma tace sai ta d'auketa, haka sukayi bacci a jikinta suna kallo a palo, ta rasa gane komai itakam. Nanny dinsu tazo ta kwashe su ta kai su d'akinsu, ta manta sam da ciwon da kanta da jikinta keyi, sai da tayi shirin bacci sai tace bari tayi wanka itama, ta shiga toilet itama tayi wanka, kamar yanda y'ay'an ta sukayi, ta fito ta shafa mai, ta saka tufafi har a lokacin dai ba ta jinta dai-dai ta kwanta ta fara tunanin wacece ita haka!!!..
Post a Comment