NAMANTA KOMAI
By yasima Suleiman
NAMANTA KOMAI
Episode 3 to 4
Yusuf yana tafe yana mamaki, wai yau Suhailah ce har da rungume shi. Lallai ya tabbata ba ta son wannan auren, shida tunda yake sonta bata taba ba shi fuska ba, sai sama-sama take kula shi, wai shine yau take cewa suyi aure hadda su runguma. Abinda yasan ba zai taba yiwuwa ba, koba komai ya ji dad'in rungumar shi da ta d'an yi,amma yana bak'in cikin rabuwa da ita,wanda dama yasan ranar na zuwa amma baiyi zaton ta nan kusa ba. Yana fita, Suhailah tayi irin shigar da ta sabayi,wando da riga, ta kawo hijabi data d'auko cikin kayan Antinta Rukayyah, hijabin yakai mata har k'asa zunbulele dashi, ta sa cover shoes flat (rufaffun takalma), yadda ba yadda za'ayi aji sautin tafiyarta, ta k'arasa tattara 'yan abubuwan da dake buk'ata ta saka a wata k'aramar jaka, ta jiyo wata yar uwarsu tana "ina amaryar?" Tayi tsaki, "wai amarya, zaku ga amarya ai," ta kashe wayarta ta jefa a hand bag (jakar ratayawarta) dinta ta lallab'a ta fice ta baya ba tare da kowa ya gantaba.
*********
Ta samu a daidaita ta shige. Sun wuce State University (jami'ar Ummaru Musa) ta katsina da nisa sosai, sannan tace ma dan adaidaita sahu ya sauke ta.. Ya ce "wallahi hajiya dan kin birgeni yasa na kawo ki har nan gurin, amma yadda k'asarnan ta lalace wallahi da sai nace ko ke yar yankan kai ce cikin wannan uban hijabin haka, ke hajiya gaskiyar magana kawai hajabin yafi kama da na mai dasa bomb!!... Tayi murmushi, "wato masu hijabi sune yan yankan kai ko da saka bomb?" Yace "sosai a Nigeria ma su hijabi su ke saka bomb kuma kema kin sani sai dai idan kink'i fada", tace Hmmm! Suna hakane dan su nisantar da zukatan ya'yan musulmi daga saka hijabi, bayan hijabi shine sutura ta mutuncin duk wata 'ya mace, kuma hijabi umurnin Allah S.W.T ne, shi ya umurcecmu da mu rik'a sakawa cikin Al Qur'ani suratul Ahzab ayata 53 (hamsin da uku) ... Yananan baro-baro ayar hijabi,so please ku daina tsoron masu hijabi",...... Yace "Allahu Akbar, kawai mu dai masu hijabi idan sun daina saka bomb to zamu daina tsoron su". Dariya ya ba ta sosai,dan shi kam yana tsoron masu babban hijabi....
Ta duba taga babu gida gaba babu baya, sai gaban ta ya fadi. "hajiya wai mi zakiyi anan ke kadai?" Tayi murmushi tace "kar ka damu wayanda za su daukeni yanzu nan za su zo", dan ta lura yana shakkar ya barta a wajen.. Ta bashi kud'i d'ubu biyu, nan da nan ya washe baki ya fara godiya ya na sa mata albarka yaja kekenshi ya k'ara gaba. A hak'ik'anin gaskiya Suhaila a tsorace take, ga rana na dukanta, gashi babu ko 'yar bishiyar da zata labe a kusa, motocin dake wucewa ma duk sun daina wucewa, ga k'ishin ruwa ya dame ta, a ranta ta ce " lallai Yusuf ma ya raina mani wayau". Ta kalli agogon hannunta, awarta biyu tana jiran shi a inda mai a daidaita ya sauketa,ga yunwa ta fara damunta, kenan awa biyu da rabi da d'aura aureta da Alh. Rabo, ta k'lyalkyace da dariya, ita sunan ma ya daina bata haushi, dariya yake bata. "Wai Alhaji Rabox", yau zaka ga rashin rabo kuwa, dan guduwa xanyi, ta murgud'a baki ita kad'ai. Ta kasa tsayuwa waje d'aya sai kai da komo take. Ta sa k'afa ta harbe wani dutsi dake gabanta ta kuma bi dutsen da kallo,d'aga idonta keda wuya sai ta hango motarsa, tayi ajiyar zuciya cikin ran ta tace "sai yanzu dan wulak'anci amma za ta rama," ta je inda ta aje kayanta a gefen titi ta d'auko hijabin data aje da jakarta a dai-dai lokacin da motar ta tsaya, bata ko kalle shi ba , ta jefa jakarta a bayan motar,inda taga ya aje waccan jakar ta dazu data bashi, ta bud'e gaba ta zauna,tayi kyacci tace "haba Yusuf" sai kuma tayi shiru, Amma za ka sani, zan rama da ni ka ke zancen, wai dan wulak'anci sai yanzu ka ga damar zuwa ko?", yace "Eahhhhh"......
Jin murya da ba tayi zato ba,muryar da tun da ta ji ta ta kasa samun natsuwa, yasa ta juya da k'arfi ta kalleshi, ta bala'in jin tsoro,ta zaro Idanuwa! "Alhaji Rabo" tana tunanin kai wannan mutumin dai ko aljani ne yake yi mata wobuwa,ta juya inda ta aje jakarta,ta ga lallai jakar tace, wadda taba Yusuf a wajen, so ina ya samo ta? Da k'arfi ta bude k'ofar mota ta zuba aguje,gudu take iya k'arfinta tana tunanin Allah yasa mafarki take, gudu take kamar me, kai ko mafarki ne ta wahala cikin wannan mafarki, ya kamata ta farka hakanan, ta juya taga inda tabar shi a motar ma bai motsa ba, yana cikin mota abun shi zaune, ta juya taci gaba da gudunta, kamar daga sama sai ta hango shanu sunyo kanta, ta rasa yadda zatayi,sai kawai ta duk'e nan inda taja birki,.......
Haka suka yi ta wuceta har ta ji alamun sun gama wucewa tayi ajiyar zuciya, ta mik'e tsaye, tashinta keda wuya sai wani k'aton sa.. í ½í° yasa k'ahonshi ya d'auketa ya wurgar da ita kan titi ji kake timmm! Subhanallah! Ta sa ihu,amma kamin ta kai k'asa dan olo har ta some. Ahmad yana hangota, ya k'araso da sauri inda wannan k'aton san ya wurga da Suhailah ya jijjigata amma yaga bata motsi, ya dauke ta tsaf ya sakata mota, ganin ba bu wani ciwo jikinta sai dan k'warzane a gwuiwar hannunta na haggu yasa bai wani tad'a hankalinsa sosai ba, ya tada mota yaci gaba da tafiyar shi ba tare da ya tsaya ko ina ba, ya d'an tausaya mata ganin k'wallan da suka gangaro daga idonta... Koda ya tsaya yasha mai a kaduna yaga ta ma gyara kwanciyarta amma bata san abunda ake ba, sai ya k'ara kwantar mata da kujerarta dan taji dadin bacci, ya kula daga suma ta wuce bacci ne. Daga nan bai tsaya ko inaba sai gidan gonar shi dake Abuja chan hanyar keffi.......
Post a Comment