NAMANTA KOMAI
By yasima Suleiman
NAMANTA KOMAI
Episode 1
....Alhaji Rabo....Alhaji Rabo....! Sunan da take ta k'ara nanatawa a cikin ranta kenan, ta fa'di wannan Suna yafi a k'irga, Mtswwwa..., sunan ko da'di babu. Sai zagaye da'kinta take,ta kasa zaune ta kasa tsaye..., Ta K'ara le'ka Window (Taga) d'in dakinta dake sama,ta hango mutane sai kai da kawowa suke cikin harabar gidansu,daga cikin runfunan da aka kafa kuwa na daurin aure har mutane sun fara taruwa. lallai yau ake yinta,! "Yama za'ayi dady yamin haka?,Ashe dama ba sona yake ba, ni kuwa duk rayuwata babu wanda nake so duniya Kamar dadyn na." Wasu k'walla masu zafi Suka gangaro daga idonta. "Yanzu ya za'ayi na sulale nabar gidan kafin a d'aura auren nan ba tare da wani ya ganni ba?"
Wannan tunanin take yi a ranta,gashi aure kam ba fashi, har mutane sun fara taruwa,lallai yau akwai Masifa,Wasu qwalla masu zafi Suka gangaro daga idonta. Tunanin ta da'ya yanda zata sulale tabar gidan kafin a d'aura mata mugun auren nan..! *** Kayan haushi! Ba d'an aike ba wanda ta aika a kira mata.!Gashi lokaci sai k'ara k'urewa yake. A dai-dai lokacin taji an yi knocking k'ofar d'akinta,tasan Yusuf ne ...dan haka kai tsaye Tace "shigo"' gabanta na ta dakan uku-uku.!! ,Saboda tunanin yaudarar da take shirin yi mishi.! Duk da ba laifinta bane,Ba tare da ta kalli inda yake ba cikin murya mai ban tausayi.., tace;" Yusuf yanzu kana ji kana gani zaka bari ayi min haka,Dama duk da kake cewa kana sona tun yarintarmu ba da gaske kake ba...
." ta d'anyi shiru jin bai ce komai ba yasa taci gaba da cewa; "to ni yanzu na yanke shawarar kawai mu gudu dani dakai sai Muyi aurenmu!! aurenka ya fiye mani auren wannan Alhaji Rabo d'in. Tayi taku biyu zuwa uku tana kallon window tace; " Alhajin da ban taba ganinshi ba bare har ayi zancen aure,wallahi ga ra kai ko banza tare muka tashi,kuma nasan kana so na ko?" Ta juyo ta kalleshi "kaga Daga baya mu dawo bayan an daura aurenmu,babu mai iya rabani da kai a lokacin...."
Ta baro window ta tako ta tsaya dai- dai gabanshi a inda yake tsaye tsakar d'aki,ta k'ara marairai cewa ta ri'ko hannayenshi "Yusuf ni dama can ina sonka,kawai nasan Dady ba zai yadda Muyi aure bane shiyasa kaga bani biye ma harkarka wani lokaci, amma wallahi inasonka, ko ka daina sona ne?" K'walla Suka k'ara gangaro mata daga ido ta dora kanta a kafa'darshi Ta bashi tausayi,duk duniya babu Abunda yake So da K'auna irin Suhailah a rayuwarshi,ya d'ora hannunsa a bayanta yana dan jijjigata,karo na farko da suka taba ha'da jiki, duk da yaso yin hakan ba Sau daya ba amma yasan bala'in da yake biyowa baya a duk lokacin da yaso yin hakan saboda bata bashi dama,Yanzun ma yayi hakanne dan ya San yayi mata na bankwanane,dan Ance fad'an da baka iyawa,to ka Mayar dashi wasa.... Shi kam babu yadda zayyi yaja da Alhaji Rabo....,
Don ma batasan hardashi a yan ya'kin neman auren alhaji rabo ba.Ina xaija da rabo wajen ya'kin auren Suhailarshi...ya D'ago ta yayi mata murmushin k'arfin hali yace; "ya kike So ayi yanzu?" duk da idonta yayi ja fuska ta kumbura sai da ta yi d'an murmushi,ta sa bayan hannayenta ta goge k'wallan dake zuba a idonta,tace " "Guduwa xamuyi, Xansa hijabi har qasa Zan kuma yi yadda zanyi in fita ba tare da wani ya ganni ba,sai mu tafi Sokoto gidan Anti Rukayyah kafin su koma tunda suna nan bikina kaga sai Muje a daura mana aure a wani masallaci. Yanzu ga wannan jakar da na ha'da yan abubuwan da nake So ne,katafi da ita zan samu a daidaita sahu da na fita gida sai ya kaini can gaba da university, kai kuma sai ka daukeni acan. Hakan yayi!?" Ka'da kai yayi alamar Eh,ya karbi y'ar k'aramar jakar da ta mi'ko mishi yayi murmushi ya mi'ka hannu ya ri'kota yaso yayi mata na bankwana,tayi baya da sauri ta watsa mashi harara,Kamar yadda Suka saba a baya, ya fita yana fad'in to sai mun ha'du....
Post a Comment