NAMANTA KOMAI
By yasima Suleiman
NAMANTA KOMAI
Episode 18 to 20
Amadadin Marubuciya Hauwa M. Jabo
Fitarshi da kamar minti biyar Nanny dinsu Auntie 'yar bak'a tazo ta lallabasu, da k'yar suka yarda suka bar ta, 'yar bak'a ta tafi dasu dan tayi masu wanka da shirin bacci dama dare yayi, ga dukkan alamu Ahmad shi ya turo ta. Fitarsu da kusan minti goma, sai ga Ahmad ya shigo d'akin cikin k'ananan kaya bak'in wando da farar shirt, duk da hankalinta a tashe yake, dan jinta take a rude, a ranta ta yaba da shigarshi, da alama daga wanka ya fito, sai k'amshi yake, ta dago kai ta dube shi tayi mashi murmushi wanda ya kasa gane mi yake nufi, sai ya basar dai-dai lokacin da yake shirin zama saman wata kujera da ya jawo daga gaban mirror ya kawota gab da bakin gado kusa da inda take zaune ya zauna, ya k'ura mata fararen idonsa, bakinshi kamar ya shafa lipstick sai maik'o yake, sai ya burgeta har cikin ranta, yace "miye maganarki?" yana tsotsa minti a hankali, ta kauda kanta daga dubanshi ta tunzuro baki kadan, wai ita ala dole shagwaba, dan a littafin data karanta ance shagwaba tana sanya mace ta saye zuciyar mijinta lokaci daya,namiji zai ga yanda kika k'ask'antar da kanki gabanshi kina harkar yara, bare kuma shi dama namiji kamar rak'umi yake a gun mace, idan baki iya sarrafashi ba to kuwa zai zame miki kamar ingarmar doki da zai zo yafi k'arfinki, dole sai ana hadawa da shagwaba da lallabawa, a book din an kawo misalin yanda za'a rik'e miji a nuna mishi fushi, ba wai da daure fuska da kunbure kunbure ba, da su gaba ba, no da kissa da kisisina irin ta mata, an kawo misalan yanda ake yiwa miji shagwaba da tasirin shagwaba a gun miji, wanda sune Suhailah take jarrabawa. A sanyaye a shagwabe take maganar, tace "nasan bani da lafiya, amma ya kamata ai kayi mani bayani," yanda ta mishi magana cikin sanyin murya, da yanda ta shagwabe masa ya burgeshi, wanda yake ganin kamar gaba d'aya ta sauko ta barwa Rabbana komai. Yace
"wane irin bayani zan miki kuma? Bayan kin san baki da lafiya mi zan miki?" Ido ta dago ta mai wani kallof,, saida yawu suka sark'eshi, saida yayi guntun tari, a ranshi yace "wato yarinyar nan ba k'aramar 'yar rainin hankali bace" duk suka yi shiru na wani lokaci sanna ta cigaba da cewa, "dama haka muke zama tuntuni baka zama gida? Kuma bama magana?" Dariya yayi sosai, ya kalleta, sama har k'asa ya girgiza kansa, sai kuma ya d'aure "Please kada ki nemi ki bata min lokacina, inada ayyukan da ya dace nayi, idan kin hada wani plan sai ki nemo ni, but now, game is over for you" ya mik'e zai wuce da sauri ta rik'e hannunsa, sokoko yayi yana kallon ta, ta zaunar dashi ya kuwa zauna. "Zan maka tambaya uku zuwa biyar duk lokacin da kake free sai ka bani amsa" " please wacece ni? Miye sunana? Ina iyayena? Kuma inane naje da yarana suke murnar dawowata?" Ta kalleshi sosai, taci gaba "nifa ba abinda na sani a kan kaina, bare wani nawa kai kanka ban san sunanka ba, amma nasan kai mijina ne, tunda ga yaranmu nan da nake tunanin yan biyu ne, suma da ace banga gashin kaina da nasu iri daya bane wallhy da nace ba yaran mu bane, dan Allah duk lokacin da kayi free ina jiran amsoshi na" ta mik'e da sauri zata nufi hanyar bayi, dan kuka na neman subuce mata, rik'o hannun ta yayi ya juyo fuskarta suka fuskanci juna "Thank God da kika san cewa I am your husband, yanda kika gane cewa ni mijinki ne, wannan ma ya zame miki assignment kije ki gane amsar sauran tambayoyin ki" ya nunata da hannu,"shame on u da kika yi failing game dinki ranar farko, kin kasa winning duk zamanki smart girl,"
sauke kafada yayi, but still you try, u can go on, may be next episode u can win, but now u fail Zeroooo" ya fadi zero din yana zare ido, yanzu muna 1-0. Ya kalleta kallon kinyi missing yace, "zaki zama fa gud player but u need more & more training" tsaye tayi tana kallon sa, gabaki daya ya k'ara batar da ita, ya k'ara dagula mata lissafi, ya k'ara sata wani duhu bayan wanda take ciki, ta yanda bata ma san ta inda zata kamo lamarin ba. "kina iya wucewarki, ina jiran next episode" ya fada yana murmushi juyawa yayi ya wuce abinshi, har ya kai bakin k'ofa sai kuma ya tsaya yace "idan kin shirya wani din ina d'aki na ki kirani, da kin bi nan corridor direct zai kaiki d'aki na, dan nasan shima zaki ce baki san gurin ba" ya juyo da kanshi da kafad'arshi ya kalleta, idan kuma kin yarda game is over duka d'aya ne a gurina, ya wuce abin shi duk da bata san ina zancen shi ya nufa ba ta sami kanta da bashi amsa da cewa,
"d game is not over, yanxu aka fara ma" da k'arfi ta fad'a ta yanda zai jiyota. Murmushi kawai yayi ya wuce abinshi, ya shiga d'aki yana tunanin wannan yarinya, tama raina ma kanta wayo, dan ba shi ta rainawa wayo ba, ya cije yatsa, ya naushi iska, "miyasa ban biye mata bama? Da sai na bata amsa kamar yanda ta buk'ata, dan kuwa zata yi dadin playing, dan zan ta winning dinta ne, ko ba komai she's beautiful & she make me happy today, in fact she make my day, kan gado ya fad'a yana ta tunanin Suhaila da abinda ta mishi, yana ta murmushi, mata akwai fi'ili, yana ganin fuskarta kamar ya santa, musamman lokacin da ta mishi wannan shagwabar tata, amma ya kasa tuno ina yasan ta, shi duk ya d'auka da gaske game take dashi. Bai san seriously Suhaila tayi loosing memory dinta bane.
********
Can gidan su Suhaila kuwa da suka jita shiru, sai suka yi tunanin ko har yanzu bata huce bane game da irin auren da akai mata, tunda ta nuna bata so, k'arshe ma tak'i bari akaita ne, tayi fushi dasu, dan haka yasa ta kashe wayar ta, dan duk wanda ya buga baya samunta, idan aka tambayi Ahmad sai yace tana nan lafiya lau, mama ce ta damu akan sai tayi waya da autarta, ta kuwa dami Ahmad akan ya kira ya bata suyi magana! Ya kenan?
Post a Comment