NAMANTA KOMAI
By Yasima Suleiman
NAMANTA KOMAI
Amadadin Marubuciya Hauwa M Jabo
Episode 21 to 26
Yana office amma tunani yake yi, ya zai tunkare ta, ko kawai yaje ma ta da sunan game d'in ne shi ma? Idan ta ce ba ta sani ba sai ya gaya mata, dan yana kunyar Mama, "No I will not do that. Zanje kawai na ce mamanta za ta yi waya da ita, duk shirmenta ai tasan maman ko?" jeeeem ya yi, a ranshi ya ce "yarinyar nan fa ba k'aramar shedaniya bace," tsaki ya ja "zanga dai yanda za ta bullo wa abin, sai ni ma na san yanda zan bullo ma ta," ya tattara files ya fito, ya kama hanyar gida yana yan sak'e-sak'e a hanya har ya isa gida. Palo ya tarar da su ita da 'yar bak'a, ana koya ma ta girki, dan black duk wani abu na chi to ta na gurin, sabida tsabar kwad'ayinta, baiko kalle ta ba, ba ta ma san ya shigo ba, sai ji ta yi ya ce "ki sameni a d'aki yanzux" taji mi ya fada, haushin ta d'aya kar 'yar bak'a ta ji ta rainata, dan akwaita da iyayin banza, bayan kamar minti biyar ta mik'e ta wuce, d'akin ta shiga ta wuce toilet ta wanke hannuwanta, ta fito da har zata chanza kaya, dan wani 3quarter na Jeans ne a jikinta, sai kuma 'yar figigiyar best, gata 'yar lukuta da ita, ta tuna a book din nan ance "ba kullum bane zaka rik'a budewa namiji jiki ba," tsaki tayi "bayan ya gama gani na ma, miye ya rage wanda bai gani ba tunda muna da yara har biyu," Turare ta fesa, mai sanyi sosai, ta bude wardrobe za ta ciro riga sai kawai ta gan shi ya shigo, ta juyo ta kalleshi, sai ta rufe wardrobe d'in, ta fuske abinta, da sauri ya kauda kanshi, a ranshi yace "'yar lukuta kawai amma ta had'u fa , a bayyane ya ce "dama mama ce takeson magana dake, zaki iya tuna ta?"
Gyada masa kai tayi alamar NO, dariya taso kubce masa sai ya dake, okay, " mama itace mamarki, gaisheta zakiyi cikin tarbiya", " ya ake gaisuwa cikin tarbiya?, " ta tambaya, dariya yayi amma badan yaso ba, dariyar ce taci k'arfinsa, ya kuwa zauna kamar gaske, ya gaya mata yanda zata ce , ita ko harda maimaitawa tayi irin haka kake nufi ko? Gyada mata kai kawai yayi, a ranshi yace " 'yar rainin wayo kawai," ya kira mama bayan sun gaisa yace mama ga autar ki, but still fushi take dake, ya mik'a mata wayar, tayi d'an gefe da kan wayar tace dashi "nice auta?" Yace "Eh, " " to kuma kace na gaidata cikin ladabi, kuma kace mata ina fushi ya zanyi?" Karbar wayar yayi ya kashe haushi ta bashi sosai, "malama idan bazakiyi magana ba ki bari! Mahaifiyar kice kike yiwa wannan shirmen ! Ke idan baki san darajarta ba ni na sani, kada Allah yasa kiyi mata magana," a fusace ya mik'e, rik'e masa hannu tayi, a shagwabe tace "kayi hak'uri zanyi magana da ita kaji" tsaki yayi mara sauti ya dawo ya zauna, ya fara dannawa,
Wait Wait,ta dakatar dashi, " normal zanyi magana da ita ko kuma cikin fushi? " ya kalleta rai a bace" cikin fushi da ladabi" "yaya kenan?"" ban sani ba " mik'a mata wayar yayi, ta kara a kunne, sun gaisa fushi fushi take maganar amma da ladabi kamar yanda oganta ya umurceta, chan mama tace " ga suhail zaku gaisa " zare ido tayi ta kalli Ahmad, a hankali tace "waye suhail dan Allah " banza yayi da ita, suhail kuwa yana chan yana zuba kamar kanya, matsowa tayi daf dashi ta d'an bubbugashi, waye suhail, baiko motsaba yace "mata d'an uwanki ne" sannan ta fara masa magana yanata complain ta sharesu duk fushin ne takeyi dasu har yanzu, ita kuwa sai aikin bada hak'uri takeyi ba tare da tasan miye laifin nata ba suka k'are ya baiwa mama, nan mama ta shiga mata nasiha akan tabi mijinta, ta na ta In sha Allah ba abinda ta gane sai d'an yak'e da ta ke muvsu ta na cewa sorry, Mama ba taji dad'in yanda 'yar tata take mata magana ba, amma tasan su suka mata laifi, sun yi sallama ta mik'a masa wayarsa " ki ijiye min a nan " ta ijiye har takai k'ofa za ta fita saita waigo shi, karaf idonsa akanta yana mata kallon kamar mayunwachin zakin da ya hango nama, sauri ya yi ya janye idonsa, murmushi ta masa ba tare da ya gani ba, ta fice abinta, a ranta tace ashe ma har yanzu yana sona, kawai dan bani da lafiya ne. Chan ta sami 'yar bak'a ta kusa kammala wa, sorry black na ijiyeki ke kadai...
"No ba komai ai kin je gun mijinki ne" kallon ta kawai tayi, aranta tace "wannan black akwai bala'in shishshigi a gunta, suka k'are aikin, ta fito zata d'aki kichibis suka yi da shi , " Sorry " ta fad'a fuska a sake, bai kula taba ya gangara k'asa ya wuce gun aikinsa.
*********
Alhaji Ibrahim ya shirya tafiya wani aiki a morocco, amma yaga bazai iya tafiya baiga yarshi ba, musamman yanda take fushi dashi, shiryawa yayi ya kamo hanya, saida ya iso Abuja sannan ya kira Ahmad ya shaida mishi, yana gari, Ahmdy cike da farin ciki ya tarbo Dady su ka wuce gida, sun tarar da Suhaila, 'yar bak'a na koya mata yanda ake sinasir, gidan ya had'e da k'amshi, Dady cike da farin ciki yau zai had'u da 'yar autarsa, sunyi sallama, ta fito da sauri jin maganar Ahmdy da rana tsaka. Sannu da dawowa, ta fad'a ta kalli mutumin, lokaci d'aya ta gane shi, da yake ta tuna wasu abubuwan da suka faru lokacin da take 'yar shekara takwas haka, so ta gane Dady, cikin girmamawa ta gaidashi, Dady yana ta jin d'ad'i, Ahmdy ya sami gu ya zauna, a ranshi yace "wato yarinyar nan ta raina min wayo ko?. Zaki gane Dady d'inki, dama ni nasan duk kissa ce ta mata" Dady bari na shiga ciki, Ahmad ya barta da Dady d'inta, nan fa ya fara mata maganar da sam bata san ina ya nufaba, sai rudar da ita yakeyi yana bata hak'uri, "wai mi suka min da suke bani hak'ur'i?". Haka ta k'are zaman ta da rashin sanin kan zance na Dady har sukayi sallama, Dady zai tafi, ta haura sama ta kira Ahmad sai kuma taji olooo, dan ba zata iya shiga d'akinsa ba, sai ta dawo, "Dady ka mishi waya inaga baya gida" "ke Ina wayar ki ?", "ta b'ace ne Dady ", "ok". Ya kira Ahmad ya sauko suka yi sallama ya wuce. Za ta haura sama ya janyota da k'arfi saida ta fad'a jikinshi, " kin raina ma kanki wayo ko? Wato ni ne baki sani ba, amma kin san iyayenki, miyasa baki iya playing game ba?", kallon ta ya yi ido cikin ido sai kuma ya saketa ya juya ya wuce dakinsa tsaye ta yi ta na kallon sa...
************
Yau da gobe Suhaila tayi wata daya a gidan Ahmdy, bata ganinsa sam bare suyi game d'in da ya ke ce wa su yi, duk tabi ta damu, komai na ta a hankali ta ke yinsa sabida ta fahimci kamar ta MANTA KOMAI ne, abin duniya ya isheta, ta yi kuka har ta barwa Allah, tun ta na shiga hanyarsa ya na disgata har ta daina kula sa, harkar gabanta data yaranta ta saka gaba, ba abinda ta rasa a gidan komai normal. Ahmad kuwa a hankali sai yake ganin kamar abinnan da gaske takeyi, sabida ya aunata a hanyoyi daban- daban ba tareda ta sani ba kuma ya na ganin lallai kamar da gaske ta manta komai, sai ya tuna lokacin da "sa" ya wurgar da ita kanta ya fara bugun k'asa, may be kan ya sami matsala ne tadan yi missing din wasu abubuwan, yana son ya kaita asibiti gashi ta d'auke masa k'afa gaba d'aya, d'an gaidashi da take duk ta daina, duk yabi ya damu, shima k'arshe ya yanke shawarar zai kaita asibiti kawai a duba ta. Da wuri ya dawo gida ya tarar da su ita da yara su na wasan 'yar b'oye idan aka kama mutum shi kenan, idan ba'a kama shi ba sai aje a goyashi, to kullun in su ka yi, idan ita ta ci sai su ce 'Dady zai goyata", ana ta tara goyon har yakai tara.
" yeeee Dady zo ka goya Mumy, tana bina bashin goyo hudu, Rukayyah kuma tana binta biyar, dama munce kai za ka biya ta," Surayya tace " Mumy zo Dady ya biyaki", "na yafee" kawai tace musu ta wuce d'akin ta. Tana zaune bakin gado ta tallabe kumatunta da kanta, sai ta ji shigowarsa, k'in d'agawo tayi bare tamar magana, yazo kusa da ita, ya dad'e yana kallon ta, sannan yayi magana "Suhailah, ki shirya gobe muje hospital a miki check up," kamar bata ji shiba haka tayi, tayi baya da kanta ta kwanta idonta a rufe, ya tsura mata ido sosai, har cikin ransa yake jin yasan ta amma ya kasa tunawa, ya gaji da tsayuwa sai kawai ya wuce dakinsa, haka ya kwana yana addu'ar Allah yasa abinda yake tunani bashi bane. Da safee bayan ya k'are shiri yazo gunta, "ba nace zamu hospital ba?", "Bazan jeba" , haka kawai ta fad'a" murmushi yayi "haba maman twins"... tun kamin ya fadi abinda zai fad'a ta karbeshi,
"da gaske yarana twins ne?", Fuskanta a washe, "idan mun dawo zan miki bayani", ta turo baki" kaine Dady tun yaushe kasan bani da lafiya amma kak'i kaini hospital", "kiyi hak'uri yanzu zamu tafi", haka ya mata wayo ya lallab'a ta suka tafi, bayan bincike da kwaje kwaje aka gano cewa ta sami matsala a brain d'inta. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.! Hankalinsa ya tashi matuk'a gashi iyayen ta satin nan zasu zo gunta kuma zasuyi kwana biyu, tabbas baya son suzo su sameta haka, za su ga sakacinsa, na rashin kula da lafiyarta, har fiye da wata daya, kuma duk sanadiyar sa hakan ta faru. Likita ya tabbatar masa da cewa idan ta sami natsuwa da kwanciyar hankali a hankali komai zai dawo, daga asibiti direct gun abokinsa ya wuce ya ce ya masa bucking zai kai madam waje a dubata...
Post a Comment