NAMANTA KOMAI
By yasima Suleiman
NAMANTA KOMAI
Episode 16 to 17
Amadadin Marubuciya Hauwa M. Jabo
CHIGABAN LABARI.
Haka take bacci a palo tana jiran mijinta, sai dai ta farka ta ganta a d'akinta, tare da yaranta yau kwana biyu kenan. Cikin dare ta farka ta kasa bacci ta tashi ta zauna, tana ta kama tasha, ta dai rasa abunda ke mata dad'i, ta rasa gane kan komai "to wai haka ake aure dama?" tambayar da ke ta yi mata yawo ke nan cikin kanta, ta k'ara d'auko d'an littafin nan data gani a kayanta ta k'ara karantawa, taga yanda ake soyayyyah ake tarbar miji, a masa girki, kwalliya, uwa uba kwanciya, amma ita ko k'eyarshi bata gani bare ta mishi wani abu, a zuciyarta ta na ganin hadda laifinta, da take bacci da wuri, kuma take tashi letti, dole ta dage ta rik'a jiranshi har ya dawo komin tsawon dare, amma ace baka magana da miji, ko ganinsa ma bakayi ta na ganin kamar hakan ba dai dai bane,. Kodai akwai wani abu da bata sani ba bayan wanda aka rubuta a littafin? Wata zuciyar ta raya mata ta kwashi yaranta yau su kwana a dakin shi kawai, amma kuma sai ta fasa, "to wai dama haka muke dashi, ni kuma miyasa bana iya tuna komai ne? Mi yake shirin faruwa dani ne? Kamar akwai abinda ya faru amma na kasa tuna komai WAI MA YA SUNANA?" A haka tayi ta tunaninta ta k'are tayi kukanta sannan bacci yayi gaba da ita.
A haka sai da Suhaila tayi sati d'aya bata ga mijinta ba, kullun itace hidima da yaranta, gashi wani sonsu ta ke ji a ranta kamar me, ta saba da su kamar hauka. Rannar da gari ya waye suka shirya kamar kullun sai Surayya ta kama hannunta tace "Mumy miyasa bakya son kaka Rabi?" A ranta tace waye kaka Rabi kuma?" Ta tambaya, " To yau kizo muje ki gaishe da, kullum ita take gaya mana ranar da zakizo har kikazo, ko bakya sonta ne? Rukayyah ta tambaya" da sauri Suhaila ta gyada kai, "ina sonta mana, nama fiku sonta" oya muje ku rakani, "amma ku tsaya, a cikinku wa zai gaya min idan naje gaidata da safe ya nake ce mata?" Yaran suka kalli juna, suna murmushi su kace "Mumy ai baki taba zuwa gurinta ba" nan ma kanta ya k'ara kullewa, a ranta tace" ban taba zuwa gurinta ba? To ko bata dad'e gidannan ba" yamutsa fuska tayi ta basar, "oya to ku zo muje" ta rik'e hannun ko wacce suka tafi gun kaka Rabi. Da yake sassan gidanta daban yake amma a jikin babban gidan gonar ne, dan tace ita bata son bene, ina ruwan yar tsohuwa Rabis. Suna shiga suka ruga suka rungumeta suna kaka Rabi oyoyo suna dariya, tace "ni dai to kuyi a hankali dai karku k'arasa ni kun sami Momy kun manta da kaka ko?" ta fada tare da rungumesu, tana "fadin lale marhabin da Momy, tare kuka zo? Shigo ciki mana keda gidanki, bisimilla zauna ga kujera nan" haka kurum sai Suhailah taji tana jin kunyar kaka Rabi, a ranta kuwa sai sak'e-sak'e takeyi, "ko waye wannan kuma oho?" Tunda tazo take jin sunanta, tama taba hangota sau d'aya amma bata tab'a ganinta ba sai yau, sai kame kame take sabida kayan jikinta, Kamar dai ya dace ace tasa kayan traditional irin na jikin kaka Rabi, "to waima in dai nan take zaune ai ya kamata ace ta tab'a zuwa gaisheta, kai tabbas akwai wani abunda bata sani ba, to menene wannan abun?" Dama ba wando da riga ta saba, ta mayar dasu kayanta koda yaushe su take sawa, tsaki tayi a ranta tace "da ba tazo dasuba, tun da dai tana kyautata zaton uwar mijinta ce tunda 'ya'yanta suke ce mata kaka, " nikam na shiga uku, na kasa gane komai! Ko mijin nawa ina yake oho? Kamar ta tambayi kaka ina yake, sai ta tuna a littafin da ta karanta ance a rik'a boye sirrin miji, wannan ma sirri ne sai ta fasa. Haka ta zauna ta gaisheta cikin ladabi, "kaka tace Suhailah ya jikin naki,kin samu sauk'i ko?" nan take gabanta ya fadi, "ashe bani da lafiya ma?" Ta cigaba "Ahmad yace min kin fadi ne baki ji dadi ba" shiyasa ma baki zo ba, kuma nace zan lek'oki yace wai kina jin kunya ne da kin wartsake zaki shigo, shi yasa baki ganni ba nima, jikin da sauk'i ko?" tayi murmushi ta rufe fuska, cikin jin kunya tace "eh da sauk'i sosai," ta dad'e a duk'e dago kan da zata yi sai taga kaka ta d'auki waya ta kara a kunne tana magana, tashi tayi da sauri ta fita, kaka tayi murmushi "ko ta d'auka sirri zanyi yarinya mai kunya" Suhaila kuwa tana tafe tana sak'e sak'e, lallai bata da lafiya, shi yasa take jinta kamar ba itaba, ta tuna ko sunanta ta manta, idanuwanta suka cika da kwalla ta shiga d'akinta ta k'ara bincike yan kayan da ke cikin jakunkunanta biyu, nan ma bata ga komai ba da zai sa ta tuna wani abu, ta k'ara bubbud'e duk wani wuri da take tunanin zata ga wani abu sam bata ga komai ba, anan ta k'ara fashewa da kuka, kuka sosai take har da sheshsheka, to me ya Sameta? Tana nan zaune tana kukanta taji yaranta na hawowa sama, suna ta surutu, tayi sauri ta goge fuskarta, kamar zata shige bayi ta wanke fuska, sai ta fasa, koda suka shigo tare da Dady suka shigo, shima bata san sunanshi ba, in ba dan taji kaka Rabi ta fada ba, idanunta suka k'ara cika da kwalla ta mike tsaye, taso taje ta rungume shi, kamar yanda ta gani a littafin data karanta, (kada yara su hanaka yiwa mijinka soyayya) amma ta kasa, sai kawai tace "sannu da zuwa" ya kalleta a karon farko tun bayan zuwanta gidanshi, sabida a palo ma idan ya ganta tayi bacci d'aukar ta kawai yakeyi ya kaita d'aki ya shinfidar dama wutar palo a kashe take, baya wani kallon ta, gata da nauyi kuwa, amma haka yake tallabota ya kawo daki, ta k'ara ramewa, ga idonta cike da kwalla yayi jajir dashi, murmushi kawai yayi, a ranshi yace "zaki k'are felek'en ki ne yarinya" amma da mamaki wacce yaji labarinta shez always happy and active, amma yanzu duk ta canja cikin sati d'aya, idan ma saukowa tayi ai ya dace ta kawo kanta ne kawai, bawai ta tsaya jan aji ba. Ya amsa ta sama sama "yauwa sannunki " Matsowa tayi maimakon ta rungume mijin sai ta rungume yaranta "Mumy wa ya dakeki kike kuka? Ko kaka Rabi ce?" Tace, "
no abune ya shige min ido yanzu, amma na hureshi" ta dago ta kalli mijinta a karon farko bayan sati d'aya, kamewa yayi, yace" kunga na kawoku gunta dama wasu files nazo dauka, bye d'inku" suna murmushi suka d'aga mai hannu "bye Dady" ya juya zai fita kenan tace "ina son magana da kai" ya juyo ya kalleta, sai kuma ya cigaba da tafiya sai da yakai k'ofa har ya fice sanan " yace ina zuwa" Ko mi zata gaya mishií
Fitarshi da kamar minti biyar Nanny dinsu Auntie 'yar bak'a tazo ta lallabasu, da k'yar suka yarda suka bar ta, 'yar bak'a ta tafi dasu dan tayi masu wanka da shirin bacci dama dare yayi, ga dukkan alamu Ahmad shi ya turo ta. Fitarsu da kusan minti goma, sai ga Ahmad ya shigo d'akin cikin k'ananan kaya bak'in wando da farar shirt, duk da hankalinta a tashe yake, dan jinta take a rude, a ranta ta yaba da shigarshi, da alama daga wanka ya fito, sai k'amshi yake, ta dago kai ta dube shi tayi mashi murmushi wanda ya kasa gane mi yake nufi, sai ya basar dai-dai lokacin da yake shirin zama saman wata kujera da ya jawo daga gaban mirror ya kawota gab da bakin gado kusa da inda take zaune ya zauna, ya k'ura mata fararen idonsa, bakinshi kamar ya shafa lipstick sai maik'o yake, sai ya burgeta har cikin ranta, yace "miye maganarki?" yana tsotsa minti a hankali, ta kauda kanta daga dubanshi ta tunzuro baki kadan, wai ita ala dole shagwaba, dan a littafin data karanta ance shagwaba tana sanya mace ta saye zuciyar mijinta lokaci daya,namiji zai ga yanda kika k'ask'antar da kanki gabanshi kina harkar yara, bare kuma shi dama namiji kamar rak'umi yake a gun mace, idan baki iya sarrafashi ba to kuwa zai zame miki kamar ingarmar doki da zai zo yafi k'arfinki, dole sai ana hadawa da shagwaba da lallabawa, a book din an kawo misalin yanda za'a rik'e miji a nuna mishi fushi, ba wai da daure fuska da kunbure kunbure ba, da su gaba ba, no da kissa da kisisina irin ta mata, an kawo misalan yanda ake yiwa miji shagwaba da tasirin shagwaba a gun miji, wanda sune Suhailah take jarrabawa. A sanyaye a shagwabe take maganar, tace "nasan bani da lafiya, amma ya kamata ai kayi mani bayani," yanda ta mishi magana cikin sanyin murya, da yanda ta shagwabe masa ya burgeshi, wanda yake ganin kamar gaba d'aya ta sauko ta barwa Rabbana komai. Yace
"wane irin bayani zan miki kuma? Bayan kin san baki da lafiya mi zan miki?" Ido ta dago ta mai wani kallof,, saida yawu suka sark'eshi, saida yayi guntun tari, a ranshi yace "wato yarinyar nan ba k'aramar 'yar rainin hankali bace" duk suka yi shiru na wani lokaci sanna ta cigaba da cewa, "dama haka muke zama tuntuni baka zama gida? Kuma bama magana?" Dariya yayi sosai, ya kalleta, sama har k'asa ya girgiza kansa, sai kuma ya d'aure "Please kada ki nemi ki bata min lokacina, inada ayyukan da ya dace nayi, idan kin hada wani plan sai ki nemo ni, but now, game is over for you" ya mik'e zai wuce da sauri ta rik'e hannunsa, sokoko yayi yana kallon ta, ta zaunar dashi ya kuwa zauna. "Zan maka tambaya uku zuwa biyar duk lokacin da kake free sai ka bani amsa" " please wacece ni? Miye sunana? Ina iyayena? Kuma inane naje da yarana suke murnar dawowata?" Ta kalleshi sosai, taci gaba "nifa ba abinda na sani a kan kaina, bare wani nawa kai kanka ban san sunanka ba, amma nasan kai mijina ne, tunda ga yaranmu nan da nake tunanin yan biyu ne, suma da ace banga gashin kaina da nasu iri daya bane wallhy da nace ba yaran mu bane, dan Allah duk lokacin da kayi free ina jiran amsoshi na" ta mik'e da sauri zata nufi hanyar bayi, dan kuka na neman subuce mata, rik'o hannun ta yayi ya juyo fuskarta suka fuskanci juna "Thank God da kika san cewa I am your husband, yanda kika gane cewa ni mijinki ne, wannan ma ya zame miki assignment kije ki gane amsar sauran tambayoyin ki" ya nunata da hannu,"shame on u da kika yi failing game dinki ranar farko, kin kasa winning duk zamanki smart girl," sauke kafada yayi, but still you try, u can go on, may be next episode u can win, but now u fail Zeroooo" ya fadi zero din yana zare ido, yanzu muna 1-0. Ya kalleta kallon kinyi missing yace, "zaki zama fa gud player but u need more & more training" tsaye tayi tana kallon sa, gabaki daya ya k'ara batar da ita, ya k'ara dagula mata lissafi, ya k'ara sata wani duhu bayan wanda take ciki, ta yanda bata ma san ta inda zata kamo lamarin ba. "kina iya wucewarki, ina jiran next episode" ya fada yana murmushi juyawa yayi ya wuce abinshi, har ya kai bakin k'ofa sai kuma ya tsaya yace "idan kin shirya wani din ina d'aki na ki kirani, da kin bi nan corridor direct zai kaiki d'aki na, dan nasan shima zaki ce baki san gurin ba" ya juyo da kanshi da kafad'arshi ya kalleta, idan kuma kin yarda game is over duka d'aya ne a gurina, ya wuce abin shi duk da bata san ina zancen shi ya nufa ba ta sami kanta da bashi amsa da cewa, "d game is not over, yanxu aka fara ma" da k'arfi ta fad'a ta yanda zai jiyota.
Murmushi kawai yayi ya wuce abinshi, ya shiga d'aki yana tunanin wannan yarinya, tama raina ma kanta wayo, dan ba shi ta rainawa wayo ba, ya cije yatsa, ya naushi iska, "miyasa ban biye mata bama? Da sai na bata amsa kamar yanda ta buk'ata, dan kuwa zata yi dadin playing, dan zan ta winning dinta ne, ko ba komai she's beautiful & she make me happy today, in fact she make my day, kan gado ya fad'a yana ta tunanin Suhaila da abinda ta mishi, yana ta murmushi, mata akwai fi'ili, yana ganin fuskarta kamar ya santa, musamman lokacin da ta mishi wannan shagwabar tata, amma ya kasa tuno ina yasan ta, shi duk ya d'auka da gaske game take dashi. Bai san seriously Suhaila tayi loosing memory dinta bane.
********
Can gidan su Suhaila kuwa da suka jita shiru, sai suka yi tunanin ko har yanzu bata huce bane game da irin auren da akai mata, tunda ta nuna bata so, k'arshe ma tak'i bari akaita ne, tayi fushi dasu, dan haka yasa ta kashe wayar ta, dan duk wanda ya buga baya samunta, idan aka tambayi Ahmad sai yace tana nan lafiya lau, mama ce ta damu akan sai tayi waya da autarta, ta kuwa dami Ahmad akan ya kira ya bata suyi magana! Ya kenan?
Post a Comment