0
GANGAR JIKINSA NA AURA




 GANGAR JIKINSA NA AURA


CHAPTER 3
 

*yar Baba
muje mu ajiye kayan. Suka juya
harda saurayin
wajen bencinda yake, Malam Habu
ya kama
akwatin dake kanHanne ya sauke mata ya juyo ya
kalli saurayin nandake zaune akan
benci ya ce
"Yaro bazan gaji da yimaka godiya
ba.Madalla
Allah Ya yi maka albarka zan tafi nabarku lafiya,
af kaga ko sunanka ban tambaya
ba.Saurayin nan
yayi murmushi ya ce "Sunana
Haisam,Baba.
Malam Habu ya ce "To madalla. Ya juya yakalli
Hanne wacce ke tsaye idonta ya
ciko da kwallaya
ce "*Yar Baba zan tafi na barki ga
Allah na barki
ga wannan bawan Allah. Sai ta rushe da kuka
takoma kan akwatinta ta zauna ta
kifa kai a
gwiwatana kuka. Hawaye ya
kecewa Malam Habu
ya ce"Nima ba'a san raina zan tafi na barki ba
Allah Yakaddara saduwarmu. Ya
juya ya kalli
Haisam ya ce"Yaro mai wuyar suna
har na manta
sunan(fatan Yayarmu ma Zee zata iya rike sunan,
kodayake ita 'yar birnice, loz) na
tafi, sai wata
rana. Haisam ya ce "To Baba Allah
Yakiyaye.
Malam Habu ya juya ya fara tafiya yana
facemajina yana goge hawaye da
gefen babbar
rigarsa,sai yaji muryar Hanne ta ce
"Baba ya juyo
ya ce"*Yar Baba. Ta taso da gudu ta karaso inda
yake takama gefen zaninta ta
kwance sai ta
dauko wasu cukurkudaddun *yan
Naira ashirin
guda hudu tace "Baba karka tafi da kafa gashi ka
hau mota.Haisam dake zaune har
yanzu akan
benci yanakallonsu sai da yaji kwalla
ta cika masa
ido dontausayin Uba da *yarsa. Malam Habu ya ce
"AllahuAkbar, *yar Baba Allah Yayi
miki albarka.
Allah Ya baki ilimi mai amfani, kinji?
Waye ya baki
harmurtala hudu? Hanne ta ce "Dana shiga
makwabtanayi musu sallama suka
babbani wasu,
saurankuma kudina ne da nake
tarawa tun na
yawonsalla. Malam Habu ya ce "Kya bani duka
ingomurtala biyu ni na dauki murtala
biyu, kema ki
rika siyan *yar gyada kya zauna
haka kina ganin
yarasuna siye-siye ke bakya siyan komai? Hanne
ta ce"A'a Baba murtala biyu baza ta
kai ka gida
ba, banaso ka shiga mota kudinka
bai cika ba,
kana rokonayi maka ragi irin na dazu. Malam Habu
ya sakekecewa da kuka ya ce "To
*yar Baba na
gode na tafi na barki ga Allah baki da
kowa, baki
da komai,ba ki san kowa ba, Ya juya ya tafi.
Hanne na tsayehawaye yana zuba
daga
idanuwanta tana kallonMahaifinta
yana tafiya yana
waiwayenta.Taji wani kululun bakin ciki marar
misali akirjinta da mummunan tashin
hankalin
rabuwa daMahaifinta, yaune ranar
da ta taba
rabuwa daMahaifinta daidai da rana daya basu
taba rabuwaba. Gashi a yau ya
kawota inda bata
san kowa baya juya ya tafi ya barta.
Hawaye ne
mai radadi yake zubo mata har sai da ta daina
hango fararenkayansa ya kure,
sannan ta yi ajiyar
zuciya tasagefen mayafinta ta goge
idanuwanta ta
juya tadawo kan akwatinta ta zauna. Haisam na
zauneakan benci yana kallonsu
zuciyarsa cike
datsananin tausayi ji yake wani abu
yana yawo a
cikin kansa, saboda wani abu guda daya daya
bashimamaki ya bashi al'ajabi, shine
ganin yadda
Hannetake da Mahaifinta suna cikin
tsananin
talauci ammasuna da wadatar zuci. Haisam yaci
gaba da kallonHanne wacce take
zaune akan
akwati a gabansa tasunkuyar da
kanta kasa tayi
shiru kamar mai tunani, amma hawaye na digowa
daga ganintahankalinta a tashe yake
tana cikin
damuwa. Yagyara zama gami da
zare farin
gilashin da yakefuskarsa. Ya ce "Hanne, kukan
mai kike yi ne?Bakya so ki zauna a
makaranta kiyi
karatu kamarsauran yara, kin fi so ki
koma gida ki
zauna da Baba? Hanne ta girgiza kai alamar a'a,
ya ce "Tomeye kike kuka? In kinsan
bakya son
makarantarnan yanzu nayi sauri na
tsayar da
Babanki kafinyayi nisa sai ku koma gida. Hanne
tayi sauri ta ce"A'a bana so na koma
gida, ya ce
"To ai kuka kikemeyasa kike kukan
tunda kina son
makarantar? Bakya son ki koma gida inda zaki yi
wasa kuyiwake-wake da kawayenki
a dandali?
Hanne tayidan murmushi ta sunkuyar
da kai.
Haisam ya cigaba da cewa "Ni kuwa na dauka
danmarar nan dakika ci ta zuwa
wake dandali ce.
Hanne tayi narai-narai da ido kamar
zata yi kuka
ta ce "Ni ba'a barina naje dandali wasa. Kullum
aiki nake yi sai daiinzo in wuce su in
zani debo
ruwa. Haisam ya sakegyara zama
ya ce "Ban
gane ba sai dai ki zo ki wucesu in zaki debo
ruwa? Ke kullum a debo ruwa
kikebakya zuwa
wasa? Hanne ta ce "Eh, sai dai
suSaude Yayyena
da kanne na ne suke fita wasa.Haisam ya ce "Ina
Mahaifiyarki take? Hanne tasake
saka gefen
gyalenta ta share hawaye ta ce"Tun
ina shekara
biyu ta rasu. Yaji gabansa yayanke ya fadi ras,
saboda yanzu ya gane Hanne
agidansu tana cikin
halin wahala
kasancewarMahaifiyarta ta rasu da
alama kishiyar Uwa tana wahalar da ita. Allah
Sarki Hanne ya fada a ransayayin
daya kura mata
ido. Hanne ta bashi tausayida, a
yanzu kuma ta
sake kara bashi tausayi akantausayi wanda badan
ya daure ba da zai iyarushewa da
kuka. Can bayan
sun dauki wani lokacimai dan tsawo
babu wanda
ya sake cewa komai. Dukkaninsu kansu a sunkuye
a kasa suna tunani,Haisam ya rike
kai da
hannuwansa guda biyu canya dago
ya kalli Hanne
ya ce "Yanzu dai a gidankuke kadai Babarki ta
haifa kenan baki da Yayye ko?
Hanne ta ce "Eh.
Ya ce "Shine kuma ake saki
deboruwa kullum.
Hanne ta ce "Ba debo ruwa kawai ba kullum ni
nake wanke-wanke, shara,
wankinsu, dakai
dabbobi kiwo daga can nayo musu
ciyawa.Haisam
ya buga kafa a kasa ya ce "Kai wannanwanne
rashin imani ne haka? To ya akai
kike
zuwamakaranta? Hanne ta ce "Sai
wajen sha
dayan ranakoma wataran bana zuwa, tun ana min
dukan makaranta har suka daina su
Malamai.
Shine waniMalami ya je ya sami mai
gari ya ce a
yiwa Babanamagana a dinga turoni makaranta da
wuri tundaina da kokari, Haisam ya
ce "Sai da
maigari ya kiraBabanki ya fada
masa sannan ake
turakimakarantar da wuri? Hanne ta ce "Cafdijan
shima Baban ya isa? Ya ce "Kamar
yaya bai isa
ba.Ta ce "Shima tsoron Iya Abu
yake, matar
tasazaginsa take,*ya*yanta suyi masa, sai dai in
ana dukana inakuka shima yadinga
yi. Hawaye ya
sake kece mata, shima ya jikwalla
ta cika masa
ido, ya dauko wani hankici fari kal a aljihunsaya
gogeidanunsa ya mika mata, ya ce
"Yi shiru
Hanne dainakukagoge hawayenki.
Ta karba ta
goge. Haisam ya ce"Bari na danyi miki tambayoyi
naji kina kokari? What is yourname?
Hanne ta ce
"My name is Hanne Habu,Ya ce
"Howold areyou?
Ta ce "I'm eleben years old. Wich school areyou?
Ta ce "I'm in Babban-mutum special
primary
school.Haisam yayidariya ya ce
"Hanne Habu haka
kike da kokari? Toke da bakyazuwa makarantar
sosai ya aka yi kika koyi
dukwannan? Hanne tayi
murmushi ta ce "Ai daga baya
maigariyasa
akakirawo ita iya Abu da kanta taje fada ya
sakashaidu ya ce"Duk ranar data
hanani zuwa
makaranta ko namakara sai ya kaita
kara local
goverment. Sannan take barina natafimakaranta
da wuri sai dai idan na dawo tayi
tadukana
tanacewa ga wanke-wankenta nan
harya bushe
natsaya a hanya ina wasa. Haisam yayi tsaki ya
girgiza kai alamartausayawa.Yayi
gyaran murya ya
ce "Hanne ina so kiyi minalkawarin
zakidage kiyi
karatu duk rintsi duk wuya. Kar ki zo kifara ayi
hutu ki koma gida kiga kawayenki da
yayyanki
sunagida basa zuwamakaranta
kema kiki dawowa.
Hanne ta ce"Kwarankwatsazan dawo.(hahah.
Inkikayimata dariya
bazancigabarmikiba,'Eh' dake
nake Zee )Haisam ya kece da dariya
(subhanallahi, tinda shima yayi to
kema danyi amma kadan),ya
ce"Kwarankwatsabarantsuwa
bace wallahi Allah za ki ce. Hanne
tayidariya ta
ce"Mantawa nayi Malamin
makarantar Islamiyya yahana mu cewa kwarankwatsa.
Haisam ya ce
"Kina zuwaIslamiyyakenan? Ta ce
"Eh, ada
makarantar allo muke zuwadaga
bayaaka bude makarantar Islamiyya da yamma
dakuma dare
duka ina zuwa. Haisam ya ce dakyau
Hanne
yanzuidan anyihutu kin koma gida sai
kici gaba da zuwa taIslamiyya karkifasa zuwafa
kinji? Hanne ta
ce "To. Haisam ya cigaba da
kallonta har sai da
Hanne ta fara jin kunyar kallonda
yakemata sannan yayi murmushi ya ce "Hanne
dukwannankwalliya ce kika yi a
fuskarki, ta zuwa
makarantace? Hanne tayi murmushi
ta sunkuyar
da kai kasa tana rurrufefuska dahannu ta ce "A'a
ba kwalliya bace. Ya ce "Gashi
nankinrambada
kwalli kinja wata doguwar jagira
kinyifashin goshi
da kwalli kinyi digo-digo duk fuskarki kice
bakwalliya bace. Gawannan
tsakiyoyi da kika jifga
a wuya da hannuhar kafarkima kin
daura, Yana
dubanta yana dariya. Hannan tace "Eh sarkar salla
tace Baba ya siya mun. Ya ce
"Kingananmakarantar an hana sawa
idan Malamai
suka ganizasu kwacesu tsittsinka
miki, ciro su ki bani in ajiye miki saianyi hutu in zaki
tafi gida na
baki. Cikin sauri taji
zancentsittsinkawa taciro ta
bashi, yadda take bala'in kaunar
sarkokinnan natabata son abun da zaisa ta rasa
su. Haisam ya
karbayana jujjuyasu yaga wasu irin
tsohon wuri ne
aka jera sucikin liloaka daura ya ce
a ransa "*Yan kauye suna gayu.Yayi murmushi ya
jawo jakar
kayansa ya budewanikaramin zip ya
zuba ya
mayar ya rufe. Ya juya yakalli
Hanneya ce "Kuma a cikin akwatin naki bude in gani
kokinzo da wani
abunda dokar makaranta ta hana.
Hanne tatashi
dagakan akwatin ta bude ya karkato
ya leka akwatinbabu abundaya hango sai
tsummokarai,
cikin sauri ya ce "Hanneme wancan
nake hangowa
kamar miciji a cikinakwatinki?
Hannetasa hannu ta zaro wani dan siririn gyale baki
yakanannadeya
kudindine ta ce "Gyale ne ba miciji
bane.
Haisamya kyalkyale da dariya ya ce
"Na dauka kofi kika yiminna miciji.Hanne ma
tayi dariya ta ce
"Gyale na ne dan bansaruwa bana
kadeshi shiyasa
ya cukuykuye, ya sake lekaakwatin
sai ya hango wani dan dogon karfe mai huda huda
ajikinsa,
jikinsakamar farar azurfa yana kyalli
ya ce
"Hannewannan fa, karfenmenene?
Dauko muga. Hanne ta yi murmushi tadauko
karfen ta mika
masa ya karba ya jujjuya bai san ko
meyeba ya
ce"Wannan kuma na maye. Hanne ta
ce "Idan najekiwo nakeyiwa dabbobi busa
dashi, abun busa
ne. Haisam yace abun busa kuma?
Hanne ta ce
"Eh kawo ka gani. Ta karbikarfen
tamayar da akwatin ta rufe ta koma kan
akwatinta tazauna
takaikaice ta fara busawa Haisam
wannan karfen
kaikace Sarkin busar Sarki ne yake
yi, karin busar mai dadi daalama daiwaka ce,
Haisam ya buda
kunnuwa yana sauraroya baza
idoyana kallon
yadda take yi.Can ta kyalkyale da
dariya ta ce "Haka nake yi.Haisam yayimurmushi
ya gyara
zama ya ce "To ni abunda bangane
ba,kamar yaya
sai kinje kiwo kike yi? Daman a
wajenkiwo ake yin busa? Waye ya koya miki kuma?
Nan da nanHanne
tacanja daga yanayin farin cikin da
fara'a da
sakinjikin da takejikinta yayi sanyi
ranta ya baci. Haisam ya ce "Yakika canja nan da
nan daga
tambayarki? Hanne ta rushe dakuka
ta kifakai da
gwiwa, Haisam yayi matukar
mamaki daganin wannanhali da Hanne ta fada yanzu-
yanzun nan
ya ce"Yaya kina dariya ki koma
kuka, Hanne dago
kanki. Ta dagoya ce
"Gogehawayenki. Ta goge. Ya ce "Fada min meye nakukan?
Hanneta ce "Wani
abu na tuna shine ya sani kuka.
Haisamya ce
"Meye abun da kika tuna? Hanne ta
sa hannu tasake gogehawayen da ke idonta
ta dauko abun
busar dakekan cinyartata rike a
hannunta tana
jujjuya shi.Tace kullum dasafe nake
fita kiwo da raguna da akuyoyin iya abucan
dawa. Bana
dawowa sai da yamma
musammanrabar asabar da
lahadi. To awajan kiwo ne
nakehaduwa da wani tsoho mai suna malam saleh. Wani
lokaci sai yazo
ya wuce ni ina kuka idan yunwa
tadameni don yini
nake anan kuma ba.a
kawominabinci. Har dai rannan ya zo ya sameni a
gingininuwa ina kuka.
Yayi ta tambayata dakyar dai
nagaya masa yunwa
nake ji. yace '' ba.a kawo minabinci
daga gida ? nace ba.a kawomun kuma bana
zuwa dashi. Ya ce
'' ina babata? Nace ta rasu'' shineya
ce min kullum
zai rinka bani abinci ina ci
dakekullum da rana daga gidansa ake kawo masaabinci
nan wajen
kiwon rigarsu tana nan kusakusa da
garinmu ,
shine kullum muke haduwadashi
yana waka harya koyamin nima nakoya. Sai ya ce ya
barmin abun
busar tunda na iya, ko bayanransa
dansa zai ringa
kawo shanunsa datumakinsa kiwo
na dinga yi musu busa. Bayan nannaga kwana
biyu naya zuwa
kiwo bana ganinshanunsa kuma.
Hankalina ya
tashi naji duk banajin dadin kiwon ni
kadai babu wanda muke zama muyi hira muyi
busa muyi waka
tare. Sai da akadade naga shanunsa
da
tumakansa an kawosuwajen kiwo
amma ba malam saleh bane wanisaurayi ne. Naji
gabana yana ta
faduwa ko lafiyaina malam saleh
yake? Naje na
tambayi yaron sai yace shi dansa ne
kuma babansa malam saleh satinsa biyu
da rasuwa
shine a duk sanda naje kiwo
nagadabbobinsa sai
suyi ta bani tausayi ina kuka''hanne
ta goge hawayen da yake zubo mata
haisamyayi ajiyar
zuciya. Zuciyarsa cike da tausayin
hanneya ce a
ransa'' hanne yarinya karama tasan
bacinrai, tasan tashin hankali ta rasa kowa da zai
tarairayeta
wanda zata gani taji dadi baya
gamahaifinta. Allah
sarki , na yiwa allah alkawaribazan
kyale yarinyarnan taci gaba d tagaiyara
ba''ya juyo ya
kalli hanne wacce har yanzu take
rike daabun
busarta a hannunta tana
jujjuyawa.Yacekawo abun busar shima na ajiye miki, idan ba
haka shima
malamai zasu kwace'' hanne tayi
murmushita mika
masa ya karba ya jujjuya ya bude
zip dinjakarsa inda ya saka tsakiyoyin nan nata ya
saka yamayar
da zip din ya zuge ya ce'' yanzu
abunda za.ayi
kije kicin gashi can ya nuna mata da
hannunsaya ce kice uwar biyu, tazo inji malam
haisam kinji ku
taho tare'' hanne ta mike cikin ladabi
tana
maiamsawa cikin ladabi ta nufi inda
ya nuna mata tanatafe tana kara tsuke damarar
data ci da gyale
akugunta.Haisam ya bita da kallo
har ta kure
yayimurmushi ya girgiza kai'' bayan
tafiyarta da kamarminti biyar sai ga hanne da
uwar biyu sun
taho tare bayan uwar biyu ta gaishe
da haisam
durkuso harkasa duk da ta haifeshi
tama yi jika dashi amma aidurkusama wada ba
gajiyawa bace
irin abunalherin da haisam yake yi
musu ita da
abokanaikinta na kicin sune masu
dafawa yan makarantaabinci. Duk ranar da yake
duty idan
yazo kicin duk sai ya bisu da kudi
dukkaninsu don
haka allahallah suke malam haisam
yazo kicin bayan sungaisa ya ce'' uwar biyu
wata alfarma
nake si kiyimin idan baza ki takura
ba '' uwar biyu
ta sakegyara gwiwoyinta da ta
durkusa tace'' haba malamhaisam menene ni kuwa a
duniya zaka
nema ina dashi na takura ai babu sai
dai ma nayi
murna yauharka nemi wani abu a
wajena , mai yi maka kansada kafarsa. Kana yi
mana alheri allah
ne zai sakamaka da alherinsa''
haisam yace '' amin
na gode .Ba wani abu bane daman
wannan yarinyar da kikagani kanwatace
amma daga
kauyenmu taci makarantar nan
babanta ya kawota
dazu. Tokasancewar acan basu iya
karatuba basu san ancea diko kayan makaranta ba
da sauran
saye saye .To shine naga dasu
koma gida gashi
garinbakusaba shine nace zan baki
ita ki tafi da itagidanki kamar kwana biyu haka
kafin na diko
mata kayan makaranta( uniform) da
sauransiyayya
sai tazo ta koma hostel. Uwar biyu
tace''allah sarki malam haisam ai wannan ba
wani aikibane
babu komai ai sai mu tafi daman na
gamadaure
ledata tafiya kawai zamu yi'' haisam
ya ce'' tona gode '' yasa hannu a aljihu ya dauko
kudi ba tare
daya kirda ba ya mikawa uwar biyu
yace '' toga
wannan don ku samu ku saisayi dan
abundababu'' uwar biyu ta karba zuciyarta cike da
farinciki da
mamaki irin wannan yawan kudin da
koalbashinta
na wata baikai wannan haka ba,
gashidaman wata yayi nisa. Tayi ta godiya da da shi
albarka har ya
gaji da amsawa. Ya kalli hanne
yace'' hanne inaga
yau duk a wunin nan baki ci abinciba
ko? Hanne ta sunkuyar da kai tayi
murmushitace'' na karya da
safe'' uwar biyu tayi caraf tacea.a.a
tin karin
kumallon safe kuna ta tafiya ko?
Haisam yace nisa , don haka uwar niyu kuje ki bata
abinci taci ta
koshi.Haisam yace ki siya mata
tsiren nan na
bakintasha dan alla '' uwar biyu tace
to in allah ya yardayanzu kuwa'' haisam yaci gaba
da cewa''
sannan kisai sabulun wanka da mai
me kamshi ki
bata tayiwanka , karki barta ta
sharba yanxu duk fuskartata kwabe da kwalli. Hanne ki
daina yin
wannan dige digen kinji ? Hanne tace
to uwar biyu
tayidariya tace'' ai da haka suma
zasu zamo 'yan matasu koyi yadda ake kwalliya me
kyau irin na
yanboko ko hanne? Haisam yace''
ina ganin har
kantasai an wanke , anyi mata
sabon kitso, ko kinyi kitsomuga kan? Hanne ta zame
dankwalinta
ta durkuso da kanta ta nuna musu
wayyo allah
kowa ya kallikan hanne zai san bata
da uwa a gidan ko wanitsayayyen mafadi ko
kuma kazamar
uwa allah yabata gashi ne irin
kanannadaddennan
na fulani kobuzaye ko larabawa mai
laushi mai santsin gaskebaki wullik mai tsawo
sosai wanda
yake taba doron bayanta. Amma
me ? Yayi datti.
Kura, amosalikai kace dambe tayi
aka tumurmusa kan a cikinyashi . Sai wani kitso tuma
tuma guda
biyu dagagani ita tayi da kanta. Uwar
biyu tace'' la
la hannehaka kanki yake ? Amma
kinyi wasa a yashi ko ?Gaki da gashi tubar kalla
baki san yan
mata yanzu ido rufe suke neman
gashi ba. Da
kudinsu ma siyasuke su kara yaya
kika bar kanki haka babugyara ? Hanne tayi shiru
kanta a
sunkuye a kasatana kokarin daura
dan kwalinta.
Haisam wandayake zaune yayi shiru
sai girgiza kai alamantausayi. Can ya nisa yace''
uwar biyu yanzu
dai abunda za.a yi ga wannan wasu
kudi ne ya
sakecunkusowa daga aljihunsa ya
mika mata tace'' nameye wannan kuma? Ya ce'' ina
ganin hanne
nabukatar abubuwa da yawa a
kwana biyu da
zatayigidanki . Ki tsaya a aishalle
super market kitattambayi masu wajen irin man
wanke gashi,
dana kitso da sabulun wanka, wanki,
abun goge
kafa kisiya mata silifas. Ki duba kan
idan akwaikwarkwata ki sayi shaltos duk
a fesa su
mutu. Kozaki taho aiki gobe to ki
sami wata ki
biya ta waccezata gyara mata
kannan tayi mata kitso. Kai harmawanka kuyi mata da
kanku ai bata
wuce ayi mata wankan bama'' uwar
biyu tace'' in
allah yaso yaudin nan kafin mu
kwanta da kaina zan gyaratagobe kuma ko zan taho
aiki da diyata
halima tananan auren ya mutu tana
gida sai in
barta da ita.Kuma ta iya kitso kala
kala sana'arta kenan ki agarin da tayi aure'' haisam
yace to nima
gobe wajen karfe biyu idan an tashi
a makaranta
akwai tela dazamu je dashi can
gidan naki ya auno ta zai dinkamata kayan
makaranta
(uniform)sai ki kwatantamin gidanki
don naje. A
kanti kike ko cikin gari ?Uwar biyu
tace'' ah a cikin gari nake. Idan kajefada, kofar
gidan sarki daga
hannunkan a dama zaka ga titi ya
mike to kabi shi
kace a nuna makagidan dalhatun
kazaure alhaji hamisu to lyngun mudaya ko a gidan
kace gidan
uwar biyu kake nemayaro karami zai
nuna maka
dan mu muke yi mususurfe, katangar
gidanmu daya'' haisam yace'' toshike nan
yanzu k dauki
wannan kayan ku kai store din kicin
ki ajiye su sai
nan da kwana biyuidan anyo siyayya
sai a dauko a zuba, sannankuma abinda nake so
dake bana son
ki gayawasauran abokan aikin ki ga
dalilin da yasa
zata jegidanki da sauransu. Ko a
cikin gari ma kiyi gum dabakinki kinsan jama.a da
surutu za.a yi ta
cewa an kawo yar kauye makaranta
babu komai
sai dauwar biyu takai gidanta wani
malami ne yayi matasiyayya da dai sauransu. Ba
wai nace kin
cikasurutu ba ko gulma a'a ko mutum
daya yaji
saidubu sunji. Kuma ai akwai matan
kicin da yawa damuke gaisawa amma dana ga
alamun suna da
yawan magana ai ban kira su na
basu amana
bako ? To yadda tasa nace ta kira
uwar biyu'' uwarbiyu ta kyalkyale da dariya dadi
ya lullubeta 



Post a Comment

 
Top