0
 GANGAR JIKINSA NA AURA



GANGAR JIKINSA NA AURA CHAPTER 1



Gangarjikinsa ta Aura

GANGAR JIKINSA NA AURA


 JAMILA UMAR  TANKO {JUT} ?

 CHAPTER 1

Wata
kwarababbiyar mota kirar bus
mai kararfatattakekkiyar salansa ce ta tsaya a
bakin get dinmakarantar 'yan mata
ta gwamnatin
tarayya dakegarin Kazaure, wato
F.G.G.C.
Kazaure. Tana tsayawakondastan motar ya ja
kofar ya bude "Barararaa"saboda
kwankwatsewar
da kofar motar ta yi sakamakon cin
ruwa da gafje-
gafje da tsabar tsufa.Wani dattijo mai kimanin
shekaru saba'in da doriyane ya fito,
da wata *yar
yarinya tana biye dashiwacce
shekarunta basu
wuce shekaru goma shadaya ba, Bayan sun furfito
kondastan motar yazagaya baya
wato but ya
dauko wata katuwar akwatin karfe
irin ta *yan
makarantar wacce akadafka sunan mai akwatin
garza-garza da fenti bakiHANNE
HABU IMAMU. Ya
ajiye gefe ya sake janyowata
karamar katifa
wacce take daure ya doraakan akwatin, sannan ya
dauko wani bokitin karfesabo dal
yana sheki shima
an fenteshi da sunan mai bokitin
wato HANNE
HABU IMAMU. Daga karsheya mayar da kofar but
din ya rufe ya juyo ya kallidattijon
wato Malam
Habu ya ce "Baba baka fa cikamana
kudin
motarmu bafa, gashi har kun sauka"Malam Habu
ya sake marairaicewa ya ce "Dana
daAllah fa
nake hadaka kuyi hakuri kudin da
yayi saura a
aljihuna ko gida bazai mayar dani ba, sai nanemi
ciko kayi hakuri dan Allah, dan haka
nemanace ta
zauna a maleji yanzu baza ka
tausayawatsoho ba,
karbi arba'in din?" Kondasta ya sakefusata ya ce
"Dalla Baba kana bata mana lokaci
gafasinjoji har
sun fara tsaki sun kagu suma a kaisu
inda zasu.
Ka zauna kana mana magiya tun dazumuma fa
ba'a bati muke shan man motar da
mukejigilar nan
bafa, da kasan kudin motar taka bai
cikaba me
yasa ka hau? Har zaka ce wai yarinyar amaleji ta
zauna, maleji ba cikin mota bane?
Bakasan har a
sittin muke daukar na maleji ba daga
inda muka
dauko ku zuwa nan nayi maka ragi nace kakawo
hamsin dinma gashi kaki biya sai
wataarba'in ka
bani, kai wallahi Baba saika ciko
managomarmu
kaji ko? Direban motar dake zaune awajen tuki
wanda yake jin duk abinda suke yi,
saiyanzu ya
waigo inda suke yayi magana ya ce
"K.b wai
yane? K.b ya ce "Har yanzu wannan tsohon
baidaina magiya ba wai shi ayi masa
ragin goma
kudinyarinyar nan data zauna a
maleji, Hamsin
nace yabiya, ya wani bani arba'in. Kuma ma dan
raininhankali harda cewa kudin
aljihunsa bazai
mayardashi gida ba, wato yana da
kudin, cikawa
ne bazai yi ba.din aljihunsa bazai mayar dashi gida
ba, watoyana da kudin, cikawa ne
bazai yi ba.
Malam Habuya danji dadi ganin
direban yayi
magana ko zaice abar masa amma sai yaji
kalamansa sabanintunaninsa gara
ma abinda
kondastan ya fada masa,cewa yayi
in har bazai
biya ta dadin rai ba to zasu farka aljihunsa su
dauki gomarsu, Malam Habu yarike
baki don
mamakin irin wannan rashinmutunci,
can ya nisa
ya ce "Allah Ya kyauta, bari nabaku kudinku abin
duk bai kai ga haka ba, yasahannu a
alhihunsa na
dama ya dauko
watacukurkudaddiyar naira biyar
ya sake saka hannu a aljihunsa na bangaren hagu
ya dauko gudar nairaashirin da
kwandaloli guda
biyar, ya hadakwandalolin nan guda
biyar da
cukurkudaddiyarnaira biyar din nan ya mikawa
kondosta ya ce"Gashi dana Allah Ya
kiyaye. Ba
kunya ba tausayintsohon nan yasa
hannu ya karbe
yana gunani "Daman kana dashi ka tsaya kana
bata mana lokaciduk fasinjoji sun
kagu, direba ya
juyo ya ce "YayaK.b ya baka, sun
cika? K.b ya ce
"Eh sun cika jamujeJ.J.C. Malam Habu da *yarsa
Hanne suka bi motar dakallo har ta
hau titi ta kure
sannan hankalinsu yadawo kan
kayansu. Malam
Habu ya kalli *yarsa Hanne wacce hawaye ya
gauraye idanuwanta dakumatunta,
abin ya bashi
mamaki ganin Hanne nakuka alhali
kuma ita take
son karatu take murna dazasu taho, ya sake
juyowa sosai ya kalleta
yagahawaye ne ke zubowa
daga idanuwanta dayanabin daya,
ya ce "*Yar
Baba, kukan me kike yi? Karki cemin yanzu bakya
son makaranta bayan keaka kira
fadar mai gari
aka tambayeki kika ce kinaso. Ba'a
son raina ba
nima na kawo ki makarantarnan ke kika amsa
musu. Shine kuma yanzu kikekuka?
Idan kinsan
bakya so to ni a wajena tafinono fari
sai mu juya
kafin mu shiga ciki. Kansila da mai gari su suka
tilastamin in kawo ki amma
badanhaka ba nima
bazan rabu dake ba na kawo ki
nanuwa duniya,
babu wanda kika sani. Hanne tagirgiza kai cikin
shesshekar kuka ta ce "Baba
bamakarantar bace
bana so, rashin kunyar da
masumotar can suke yi
maka shine ya sani kuka. Malam Habu yaji
hawaye ya cika masa ido amma sai
yajure yayi
murmushin karfin hali ya ce "Allah
Sarki*yar Baba,
babu komai duniya ce. Duk wanda yagagirman
tsohon wani, za'a ga girman nasa.
Hakakuma duk
wanda ya raina tsohon wani sai an
rainanasa,
zamani ne ya canja babu sanin girman Allah, ko
an hada mutum da Allah kamar an
hadashi
dasa'ansa, wani cewa zaiyi daina
hadani da
Allahkarka cuceni Wa'iyazubillah. Ya ci gaba da
cewa"goge hawayenki 'yar Baba
kizo in dora
mikiakwatin mu shiga ciki kada dare
yayi min
kinga harla'asar tayi. Tasa gefen gyalen da taci
damara dashi ta goge idanuwanta
kana ta matso
ya ciccibiakwatin karfen nan ya dora
mata a kai
shi kuma yadauki bokiti da katifa a daya hannun
sa'annansuka juya suka doshi cikin
babbar kofar
shigamakarantar, yaci gaba da yi
mata nasihohi
masuratsa jiki yana nuna mata wannan abin da
aka yi masa a gabanta ya zama
darasi a wajenta
duklalacewar tsoho koma ba tsoho
bane na gaba
da itakada tayi masa fitsara. Ta zamana ko a ina
takekuma kome ta zama ta girmama
na gaba da
ita.Ta zama mai taimakawa
mabukata,
kasancewartasan talauci ta kuma dandanashi tana
kandandanashi. Masu gadi uku suka
iske a bakin
kofarshiga cikin makarantar, suna
zazzaune,
MalamHabu yayi musu sallama gami da mimmika
musuhannu, Hanne ma ta duka ta
gaishesu, bayan
sun amsa, Malam Habu ya ce
"Yarinya na
kawomakarantar nan, ta ina zanbi mu shiga ciki?
Dayadaga cikinsu ya ce "Mikewa
zakuyi sosai
zaku tararda ofishin Malamai dana
shugaban
makarantar.Malam Habu yayi godiya suka wuce,
har sun danyonisa suka ji masu gadin
nan sun
kwalla musu kira bayan sun dawo,
sai daya daga
cikinsu ya kallesusama da kasa ya ce "Dan Allah
Malam muna datambaya sai bayan
da ku ka wuce
tambayar ta fadomana. Malam
Habu ya gyara
kayan dake hannunsagami da yin murmushi ya ce
"To Allah Yasa na sani.Ya ce "Wai
shin me kake
tambaya ne? *Yar makaranta ka
kawo daliba ko
kuma mai aiki kakawo gidan Malamai a nuna
maka gidan Malamai(staff quaters)?
Malam Habu
ya ce "A'a daliba nakawo 'yar
makaranta ce. Su
duka suka kyalkyaleda dariya suna tafawa wani
harda buga kafa akasa. Abun ya
daurewa Hanne
da Mahaifinta kai. Menene abun
dariya?Konan ba
ita bacemakarantar 'yan mata ta gwamnatin
tarayya dakeKazaure? Malam Habu
ya tambaya
suka ce "Nan cemakarantar daka
ambata amma
watakila kayibatan kai ko baka ji dai-daiba. Malam
Habu ya ce"Batan kai kamar yaya?
Daya ya ce
"Nan makaranta ce ta 'ya'yan masu
hannu da
shuni,'yan birnimasu kokari, ba haka kawai dan
ance 'yarka tacimakaranta ba kaje
ka suyo akwati
da katifa kazoka zabi makarantar
da ranka yake
so ka shiga kacega daliba. Daya ya ce "Ko dai
waccan makarantar ceta gwamnatin
jiha suka rasa
suka shigo nan. Koda yake ko can
dinma dakyar
su kwashi wannan.Sannan na karshe ya ce "Ku dai
ku tsaya babumamaki nan din taci
abun ai na
Allah ne, Malam inatakardar shaidar
taci nan
makarantar? Malam Habuya ce "Mu babu wata
takardar shaidar cinmakaranta a
tare damu, ni dai
kansilan garinmu yazo har gida ya ce
jarabawar
da *yata tayi a birnita fito kuma duk karkararmu
ita kadai taci, maigarinmu ma ya turo
inje ya
shaida min ya ce lallai-lallai nan taci
in kawota, ya
ce min makarantun'yan mata a Kazaure guda biyu
ne data gwamnatintarayya data
gwamnatin jiha, ta
gwamnatin tarayya taci in kawota.
Amma ni babu
wanda yayi minzancen takarda. Suka sake kecewa
da dariya. Dayaya ce "Malam sai
kuyi waje don
baza ku shiga bababu takardar
shaida, ku koma ku
sami kansila komaigarin naku su baku takardar
shaida sai kuzo kununa sannan mu
barku ku
wuce. Yau gashi kusan wata daya ke
nan da aka
riga aka gamakawo yara har sunyi nisa da fara
karatu, kai saiyanzu kake kawo
'yarka. Malam
Habu ya ja 'yarsaa sanyaye suka yi
waje,
zuciyarsu cike damummunar damuwa.Hakika
Nigeria muna cikin wani hali lokacin
da yake ajiye
kayan dake hannunsa a
waje,yakamawa 'yarsa
akwatin dake kanta suka saukekasa. Suka tsaya
suka yi cirko-cirko suna kallon masu
gadinnan,wadanda har yanzu basu
daina yabo
musubakakenmaganganu ba. Malam
Habu ya nisa ya ce "AllahSarki rayuwa, Allah Ka
fimu sanin halin
da muke ciki kaizaka fitardamu, 'yar
Baba zauna a
gefen akwatinki kinjikafin
mugayadda Allah zai yi damu. Isa kansila da maigarisuka ja
mana wannan
wulakancin. Ni nasan a rina, shi yasa
dafarko
nakifur da akace za'a kaiki birni
daukar jarabawa,kuma kema daakayi
kiranki me yasa ki
amsa musu? Kika ce kinason
karatun, ga irinta
nan ai. Hanne ta zauna a hankali
jikintayayi sanyi,wanda ko yatsanta wuyar
dagawa yake yi
mata.Zuciyarta cikeda damuwa,
babu abin da take
tunawa illakomawarta gida
haduwarta da iya Abu kishiyar uwarta da'ya'yanta.Irin
tsananin azabar
da suke gallaza mata dabautar ta
din daake
tamkar baiwa alokacin cinikin bayi.
Ta ce aranta "Da inamurna zanzo makaranta
nabar gidan da
banahutawa kuma ban taba hutawa
ba sai yanzu.
Gashi yanzumakarantar masun koro
mu dole mu koma gida. Taci gaba da
tunairintataburzar da aka
sha da Mahaifinta kafin Iya
Abutabar su suka fito
daga gida zuwa makarantar nan.
Wai itaidan Hanneta tafi babu mai yi mata
aikace-aikace su
sharawanke-wanke,debo ruwa a rafi
ko tuka-tuka.
Saboda haka nemataki fur wai baza
a kawo Hanne makaranta ba. 'Ya'yantakuma
garda-garda maza
da mata suna zaune ko tsinke
basadaukewa
saiHanne wacce bata da uwa a
gidan. Allah Sarkihawaye ne ya kecewa Hanne
yayi ta zuba
daga idanuwanta.Maganar dadaya
daga cikin
masu gadin keyi ita ta katse tadaga
tunanindata dulmiya tana yi. Taji kamar daga
sama yanacewa
"Kai kauyawa ma da rashin tunani
suke dan kawai
ance'yarka tacimakaranta sai ka
taho ka zabi makarantar data yimaka kawaika
sako kai, dubi
yarinyar daya kawo sai kace
maizuwa tallar kalwa
riga a cukurkude, zanin daga kasa ya
nadekamar annade tabarma. Takalmin kafarta
harda leda
tadaure waye zaice daliba ce. Daya
ya ce
"Danmarar data ci kai kacedandali
zata, ta daure kugu tamau. Ina jin ma basu san
anadinkakayan
makaranta ba (Uniform) balle
takalmikambas da
safa.Hanne tayi ajiyar zuciya ta
hadiye yawun da ya cikamata bakinta tayi shiru,
kanta a sunkuye a
kasa.Tace a ranta "Lallai ko nafi
maye kwakwa
dole nahakura damakarantar nan
harda kayan makaranta akedinkawa. Wayezai
dinka min? Ta
sake kallon kayan jikinta tace
aranta "Kayan sallar
tawa shine suke cewa duk a
cukurkude? Niina ganinnayi ado kowa a garinmu da
muka zo
wucewayana cewaHanne yau kuma
ina zaki kika
ci ado haka? Su anankazan- kazan
suke ganina ashe, dole mu koma gida asheban
rabu dawahalar
Iya Abu ba. Kuka ya sake kece mata
hardashessheka. Malam Habu ya
kalleta fuskarsa
cike dadamuwa ya ce "Yi shiru 'yar Baba bari
zamu san yadda zamuyi mukoma
gida. Ni yanzu
ke nake ji gashi kudin da yarage mun
aaljihuna
saura Naira ashirin kacal. Da niyyatainnakai ki
makarantar in zan koma gida sai in
hau mota
daganan zuwatashar Kazaure daga
can kuma sai
in kama hanyada kafa harBabban- mutum (garinsu)
idan dare yayi mun insami waje in
kwanta washe
gari na tashi naci gaba. Har dai
inkarasa kokwana
nawa zanyi a hanya. To yanzu ba zai yuwuba
tundagaki, sai dai kawai mu shiga
mota muje
tasharKazauren, ko a bakin tashar
sai in siyar da
akwatin nan ko katifarkoma dukamu samu muyi
kudin motar komawa gida. Hanne
tazabura tace
"Ka siyar da akwati da katifa fa
kace? Kansila
aisai yasa a kamaka, cewa yayi fa gwamnati ce ta
siya ta bani.MalamHabu yayi kasake
yana tunani
na wani lokaci maitsawo can yace
"To laifin
waye? Shi kansila da maigari basu sanda kudi za'a
zo makarantar ba, babu wanda ya
bamu
kosisinsa,kansila kullum yana min
alkawarin zai je
ya karbokudin da zaayi miki siyayya da kayan
makaranta da komai dakomai, har
cewa yayi
motar gwamnati ce zata zo ta
kawoki..Daga
karshe ya zo ya fara hanya tun dagagwangwarmarakwatin nan da
katifa da bokiti
babu abunda yakara
kawowa.Bansan wacce
shawara suka yi da maigari ba
kumadaga karshe suka ce inzo in kawoki haka za'a
aiko
mikikayayyakindaga baya. To yanzu
gashi takardar
makarantar cebabu aka yimana
korar kare ina ga idan muka shiga ciki aka cemu kawo
kudi, muka
ce babu ai sai a rakomu da duka.
CikinsauriHanne
ta ce "Lah Baba na tuna jiya maigari
ya aikoda watatakarda da yamma ya ce ta
makaranta tace,
bakanan. Na karba nasa a akwatina
ko itace suke
tambaya?Malam Habucike da
mamaki da zumudin dauko takardar ya ce"Haba
'yarBaba kina 'yar
karamarki kike mantuwa, tun dazufa
ake maganar
takardar duk baki tuna ba. Yi maza
kidaukotakardar in nuna musu ko itace takardar.
Hanne tadagaakwatin da sauri ta
bude, babu
komai a ciki saikayan sawarta kala
biyu a
cukurkude suke kamar anyi sukuwardoki a
kansu.Ta binciko can kasan akwatin
ta dauko
watadoguwar takardafara ta
mikawa Babanta.
Malam Habu ya karba dasauri ya doshi wajen
masu gadin nan yana cewa "Ga
daiwata takarda a
cikinakwatinta saiyanzu ta tuna
ashe mai gari ya
aiko da ita jiya kudai ku duba ku gani ko ita ce. A
yatsune daya daga cikinsu yakarba
yaduba yana
dubawa kuwa yaga takardar shaidar
andaukiHanne
Habu Imamu a F.G.G.C Kazaure ce wato
(Admission letter) Sun sha mamaki
kwarai da
ganin nanmakarantar kuwataci ba
batan kai suka
yi ba. Cikin sakin fuska sukayi musuizinin su
kwaso kayansu suzo su wuce.
Cikinmurna Hanne
da Mahaifinta suka kwashi kayansu
suka wuce
izuwacikinmakaranta. Basu tsaya a ko'ina ba sai a
bakin wanibabbangini wanda ya
kunshi doguwar
baranda da ofishinMalamai.Babu
kowa a wajen
hatta leburori masu share-share da goge-goge duk
basa nan, wajen tsit kamar
babubil'adama.
Sukasami gindin wata bishiya suka
sauke
kayansu.Hanne ta hau kan akwatinta ta zauna
Malam Habu ya ce "To
fawannanshine ko in kula,
yanzu kuma ina zamu dosa kokuma
wazamu
tambaya? Ni wallahi abun nan na makarantarbokon nan ya ishe ni
daga nan sai can
ana tsattsare ka datambayakamar
a lahira mun
gama da masu gadi yanzukuma Allah
nekadai Ya san wa zamu hadu dashi, kai Allah
Yakyauta,
wannan shine ake cewa ba shiga ba
fita wai
anbawamahaukaci gadin kofa.
Shigowar wata dalleliyarmota ce Jeeplaunin koriya
(dark green)
wacce ta tunkaro indasuke, ita ta
katsewa Malam
Habu surutun da yake yi. Ta zo
dafda su tatsaya babu abinda yake tashi a cikinta sai
sautinkida
dasanyin A.C maza ne samari guda
biyu suka
fitodaga gani wa ne da kaninsa,
kanin yana sanye da kayan bautarkasa ajikinsa wato
(N.Y.S.C)

Post a Comment

 
Top