0
 DOLE KISONI


DOLE KISONI



Episode 51 DOLE KISONI  


 Sai bayan isha Amir yace ta shirya
sukoma gida simra najin haka
tadinga kuka wai wlh bazai
tafinmata da itaba yabarta anan
taje tasamu dady tana kuka dad
yace to kibisu amma ranan friday zai dawo dake saboda school kin
yarda da sauri tace eh aiko taje
taja hanun Aiman wai suje dakinta
tajada kaya suka tafi Aiman ta
tayata hada kayan itama murna
take akalla zata samu mai debe mata keya …muce ta aika maid
akirata tabar simra tatafi wajen
dakin mum..tana zuwa mum ta
miko mata wani abu a kofi kaman
madara tace yata shanye wanan
takarba tasha dan ita batasan meba…mum ta dauko wasu
abubuwa chocolate ne tabata tace
gashi kullum kidinga shan daya tai
murmushi tace nagode mum
daganan tasa ajaka mum tarakosu
har mota dad ma haka suka shiga suka tafi…sai kallonta yake amota
amma taki bari su hada ido wani
murna yake yanda bata tona mishi
asiriba suna shiga gida yana
parking suka fito taja hanun simra
sai dakinta shikuma ya tsaya dauko musu jakan simra….
Yakawo musu jakan yama Aiman
alamu da ido tazo ta murguda mai
baki ta tashi ta shiga bayi shikuma
ya wuce dakinshi da haushiiii
Maman shakur 


Episode  52 DOLE KISONI



 Washe gari bayan sunyi sallan
asuba tace ma simra jeki gaida
yayanki tako tafi shiru shiru taji
simra bata dawoba har karfe 7
shine ta sauka tana kaiwa bakin
kofan taji muryan Amir yana koyama simra karatun Al Qur’an
suratul rumm …muryarshi dadi
kaman na sudaies mamakine ya
cika mata ciki dama mutumin nan
nada ilimin addini yake iskanshi da
neman mata haka motsin dataji za’a bude kofan ne yasa tai maza
tajuya ta wayance kaman tana
neman abu simra takarso tace
matar brother mekikeyi anan??
tace bakomi tajata suka shiga
kitchen ta dafa musu egg pizza da hot tea kamshi duk ya cika gidan
suna cikin ci a dining Amir yafito
yataho ya zauna kusa da ita yace
baby ina nawa ta daure fuska
kawai gani tayi yasa hannu yafara
cin nata simra tace brother karka cinye mata mana ya daure fuska
taja bakinta tai shiru saida yaci
yay nak sanan ya mike ya manna
mata kiss abaki yace baby natafi
clinic take care jitayi kaman ta
kasheshi tai banza dashi shikuma yawuce yatafi…
Maman shakur 


Episode  53 DOLE KISONI 


Haka suka cigaba da rayuwa
simra nadebe ma Aiman kewan
iyayenta sosai tana bala’in son
yarinyar dan tanada shiga rai ga
surutu daban dariya yayinda Amir
najin dadin yanda tarage damuwa.. yanzu kullum da safe sai ya cinye
mata abincin yana jin dadin girkinta
sosai saida yanzu ko kallo bai
ishetaba dan kullum kara tsanarshi
takeyi..
******yaune takama friday randa simra zata tafi tun safe Aiman take
kuka amma a boye dan batason
simra tagane tai wani zuru zuru
yanda Amir yaga tayi yasa tabashi
tausayi yaki kaita harsai karfe 3 da
dady yakira yace yadawo da simra shine yaje yace tafito Aiman kuka
take sosai itama simra kuka da
kyar ya babbare simra daga jikin
Aiman yasata amota itakuma
Aiman takoma daki tana kuka daga
baya tamike tai wanka tasa wani three quarter iya guiwa yakamata
sosai dawata yar shimi mai v neck
shima yakamata tazauna tai shiru
har karfe biyar..tana zaune kawai
taji tana sha’awan zuwa tsakar
gida tako fito tana fitowa kawai ta hango gate abude kuma ba
securities din dukansu basa wurin
ai batai tunanin kayan dake
jikintaba da gudu tayi gate tafita
daga gidan gudu take iya karfinta


The End

Post a Comment

 
Top