MAGANA JARI CE LITTAFI NA DAYA
labari na ashirin da biyar
RAINA KAMA KAGA GAYYA
Raina Kama Ka Ga Gayya
Wata rana yautai yana kiwo a bayan gari sai tarko ya kama shi. Ya yi ya yi ya kubuce, ya kasa. Yana nan yana kuci-kuci sai ka wani tsohon kare ya zo. Da yautan nan ya gan shi sai ya ce masa, “Don Allah, wannan kare, ka dubi zumunci, ka ji kaina, ka sake ni, kai kuma Allah ya taimake ka.”
Kare ya tsaya kamar ya ki, ko kuwa ya dan cinye shi ne ya wuce. Ya ga dai kamar ko ya ci, shi, ba zai san inda ya nufa ba. Sai ya tafi kusa da shi, ya sa baki ya tattaune tarkon nan, yautai ya kubuta. Da yautai ya ga an kubutad da shi sai ya yi wa kare godiya, ya tambaye shi inda za shi. Ya ce za shi neman abinci ne.
Shi kuwa kafin ya zo nan a kama shi a tarko, ashe ya ga inda wata ‘yar akuya ta mutu, aka kai gindin wata itaciya aka yar. Saboda haka ya ce wa kare ya zo ya kai shi, kafin dare ya yi kuraye su cinye. Ya tashi, kare yana bin inuwarsa har suka isa wurin. Kare ya tsaya, ya sa hakori ya barke cikin akuya, ya ci ya tafi ka ga shekata, kullum in ka matsu da son abinci ka zo, ni kuwa in tashi in kewaya gari, inda na ga wani abin da za ka iya ci in zo in kira ka mu tafi.”
Ya ce, “To, madala! Mu tafi in gani.”
Da saka fara tafiya suka kai kan titi, sai ya ce, “Wallahi naman nan da na ci ya kusa ya kware ni, da za ka dan dakata mini in kwanta nan in huta kadan, da na so.”
Yautai ya ce, “Ai gaskiyarka. Kwanta ka huta, in kana son barci ma yi, ni kuwa zan hau nan in tsaya in na ga yara zan gaya maka ka tashi, don kada su buge ka.”
Kare ya ce, “To, madalla!” Kwantawarsa ke da wuya sai barci ya share shi. Can an jima kadan sai ga wani tafe da keken shanu, masa, “Kai mai keke, kai mai keke, yi kwana, don kada ka take mini dan’uwa, ga shi nan yana barci.
Mai keke ya Harare shi da fushi, ya ce, “Wane ne dan’uwanka da ka ke tsai da ni dominsa?”
Ya nuna masa kare da ke barci, ya ce, “Ga shi nan.” Mai keke ya dubi kare, ya yi tsaki, ya ce, “Da ma don saboda kare ka tsai da ni? karen me? Kai ar, Allah wadanka!” Sai ya kora shanunsa suka bi ta bias karen. Bai ko shura ba, ya mutu, hanji waje.
Yautai ya tashi ya bi shi yana kuka, yana cewa, “Wayyo ni, kaico kaina, ka kashe mini dan’uwa, bai ci ba bai sha ba. Na yi maka magana ka lura, ka ki, dona ka raina ni. To, yadda ka sa na zubad da hawayena yau, kai kuma sai na sa ka zubad da naka. A bar ma ta batun hawaye, yadda ka sa dan’uwana ya bar duniya yau, kai ma kana barinta, in Allah ya so.”
Mai keke ya yi dariya, ya ce, “Har kai nan dan tsuntsu, yadda ka ke za ka ce ka iya sa ni kuka? Duban ni da kyau fa ka gani.”
Yautai ya ce, “To, shi ke nan. Raina kama ka ga gayya!” Mai keken nan kuwa a gaba kamar ya wuce shi, sai ya dawo ya sauka bisa buhunan gero, mutumin nan bai sani ba. Ya yi ta yi musu huda, gero na tsiyayewa, mutumin nan bai sani ba. In ya ga kamar zai wajwayo sai ya boye tsakanin buhu. Zuwa can gero ya tsiyaye, sai ya ji keke na gwaram gwaram, kamar ba kaya. Ya tsai da shanu, ya sauka ya duba kaya, ya yi salati.
Yautai ya tashi, ya ce, “Kadan ke nan. Ai ban gaya maka ba, raina kama ka ga gayya?” Ya tashi ya sauka bisa idon sa guda, ya yi ta tsatsagewa, sa na tsalle-tsalle. Mai keke ya gan shi, ya dauki wani gatari nasa zai kwantara masa, sai ya tashi, ya sami kan san. Sa ya fadi nan take ya mimmike. Mai keke ya ce, “Wash!”
Yautai ya ce, “Tukuna. Ai na gaya maka, raina kama ka ga gayya.”
Mai keke ya ciji baki, ya sauka ya daura wa daya san keke, ya hau ya kora, ya nufi gida. Yautai ya komo ya sauka bisa idon sa dayan, ya fara tsattsaga, shi kuma ya yi ta tsalle-tsalle, yana harbe-harbe. Mai keke ya dube shi, ya ce, “Lalataccen nan ya dawo.” Ya dauki gatari, ya tsaya tsai, wai ya dube shi daidai ya sare sai ya tashi, ya sami kan sa. Sai ya fadi, nan ya sure. Ya sauka ya rasa abin da zai yi, sai ya saba gatarinsa, ya nufi gida yana cizon yatsa.
Yautai ya ce, “Mu tafi gidan, ai na gaya maka, raina kama ka ga gayya.”
Da matarsa ta gan shi ya shigo yana zage-zage sai ta ce masa, “Lafiya, babba da kai kana wannan irin mugun baki?”
Ya ce, “Ina fa lafiya, wani dan tsuntsu duk ya sa na kashe shanuna, wai don na taka wani kare a hanya?” Ya waiwaya sai ya ga yautai bisa tukwanensu, ya ce, “Kin gan shi ma ya biyo ni, lalatacce!” Matarsa ta ce, ‘Kai ar, sululun wofi, yaya dan tsuntsu kamar wannan, wanda bai fi a hadiye ba, zai ruda ka haka?” Sai ta fizge gatarin da fushi, ta wurgi yautai da shi. Yautai ya tashi, ta sami tukwanensu, duk suka fashe.
Yautai ya koma cikin dankin matar ya sauka, ya ce, “Raina kama ka ga gayya!”
Da matar ta waiwaa ta gan shi, sai ta sake daukar gatarin ta wurge shi da shi, ta sami korenta, duk suka fashe. Kai, in gajarce maka labari dai, suka yi ta yin haka har ta fasa kayan dakinta duka.
Yautai ya dube su, ya ce, “Tukuna dai. Raina kama ka ga gayya!”
Daga nan mijin ya tuna da wata dabara, ya matsa wurin matarsa, ya rada mata ya ce, “Rufe taga maza, ni kuwa in rufe kofa, mu rutsa shi, mu kama, mu yi masa irin kisan da mu ke so.”
Suka zabura waje gaba daya, suka rurrufe. Suka koma ciki, tarya nan tarya nan, har suka kama shi a hannu,Suka bude kofa da taga, suka fa tsaya gardamar yadda za su kashe shi. Mijin ya ce, “Hura wuta za ki yi ki jefa shi.”
Matar ta ce, “A’a, ba haka za mu yi ba. Fige shi za ka yi yanzu, ni kuwa in nika tosshi in kwaba shi, in tsoma shi ciki. Ko kuwa ma ba haka za mu yi ba, in mun fige shi in sa wuka in kwakule idandunansa yau, gobe in yanke kafa guda, jibi in yanke fiffike guda, mu bi shi da yanka haka gaba gaba har ya mutu, dan lalatacce!”
Da yautai ya ji haka sai ya ce, “Ta Allah ba taku ba. Raina kama ka ga gayya!”
Ko da suka ji haka duk sai suka fusata, matar ta zaro wani takobin mai gidan da ke nan, ta ce, “Bari in sare shi.” Mijin ya ga nawar ya bar matar ta sare shi, sai ya duka wai ya take shi, sai matar kuwa idonta duk ya rufe don fushi, ta kai wa yautai sara daidai da sa’ad da mijin ke dukawa ya take shi, sai ta sare kan mijin. Ya fadi, ya mutu. Yautai ya tashi ya fita, ya ce, “Alhamdu lillahi! Da ma hakin da ka raina shi ke tsone ma ido.”
Ganin wanan al’amari ya sa maatar ta haukace, ta dauki gatari ta shiga jeji. Kowane tsuntsu ga gani sai ta kaimasa jifa tana cewa, “Raina kama ka ga gayya!”
Da aku ya gama ba da wannan labari sai ya tashi fir ya koma fada.
Da Musa ya gan shi ya tambaye shi labarin da ya gaya wa Waziri, aku ya ki gaya masa hakikanin abin da aka yi sai ya ce, “Na gaya masa labarin Umaru Mu’alkamu ne da Shaihu dan Fodiyo ya nuna masa karama.”
Musa ya ce, “Wace karama ce Shaihu Mujaddadi ya nuna wa Umaru Mu’alkamu, wadda ban tuna da ita ba? Alhali kuwa labarun Shaihu da mu’ujizarsa sai mu gaya wa wani ba wani ya gaya mana ba.
Aku ya ce, “Ranka ya dade, ai ka san sani wuyar al’amari gare shi, kome abin mutum in ya san wani abu bai san wani ba.”
Musa ya ce, “To, fada mini wannan labari in ji,ko na tuna da shi.”

Post a Comment