0
MAGANA JARI CE LITTAFI NA DAYA

labari na ashirin da hudu



SAURIN FUSHI SHIKE KAWO DA NASANI


Saurin Fushi Shi Ke Kawo Da Na Sani

      Wata rana Sarki yana kilisa, sai ya tarad da wani dan kwikwiyo yana kwance, duk kiyashi sun cika bakinsa nishi ya ke yi dai dai, kansa. Ko yaya aka yi ya rabu da uwarsa, Allah kadai ya sani.

Da Sarki da dube shi sai tausayi ya kama shi, ya ja linzami ya tsaya, ya dubi mutanen da ke biye da shi, ya ce, “A, kakkabe wa Sarkin Babanni ya lura da shi da kyau yana ba shi abinci, in yana da sauran kwana gaba ya tashi.”

Nan da nan, kafin Sarki ya rufe baki, bayi sun dira sun kama karen, sun shafe masa baki da hannanyen rigunansu. Wani ya sa shi kan kwacciya, ya tafi da shi gida ya kai wa Sarkin Babanni, ya Sarki. Da rana ta yi sanyi suka komo.

Bayan kamar kwana uku sai dan kare ya farfade, har ya fara tafiya, Da ya sami kamar wata biyu sai ya zama kamar ba shi ba. Ya yi bulbul, duk inda Sarki za shi yana biye. Da ya girma sai kullum dare in Sarki ya shiga barci, shi kuwa sai ya zo kofar Saboda haka Sarki ya rika sonsa kwarai da gaske. Ba mai ikon ya buge shi, ko ya yi masa wata katuwar tsawa, don tsoron Sarki.

Ana nan, ran nan safiyar Salla Sarki ya yi shiri zai fito ya hau zuwa idi, sai karen nan ya biyo. Sarki ya waiwaya ya gan shi, ya buga masa tsawa, ya koma daki ya kwanta, don ya san haka a kan yi masa in ba a son ya bi.

Yana nan kwance dakin Sarki, can an kusa saukowa daga idi, sai aka kare toye-toyen Salla. Wata sadaka ta fara dauko kwano guda ta kawo cikin dakin nan ta aijye. Amma maimakon ta rufe abincin yadda ya kamata sai ta bar shi a bude, don ta san ko da zai rube karen nan ba shi tabawa.

Karen nan yana kwance, sai ya ga wani kumurci ya biyo matakin soro, ya sauko daga kan azara, ya sa baki cikin abincin yana ci. Kare ya fita wage yana haushi don mutane su zo. Ba wanda ya kula da shi.

Da mata suka ji ya dame su da hausahi, sai suka dauki dutse suna jifarsa, don sun ga Sarki ba ya nan. Da karen nan ya ga ba su gane abin da ya ke nufi ba, sai ka kyale ya shiga daki ya kwanta. Maciji kuma da ya ga ya koshi, sai ya sulale ya koma cikin azara abinsa ya shige.

Can an jima Sarki ya dawo. Da shigowarsa iyali suka yi masa barka da sauka. Bayan sun tashi, ya nufi wajen abincin nan zai ci. Kare ya bi shi yana kada wutsiya kamar ya ce, “Kada ka ci, maciji ya zuba dafi a ciki.” Allah bai ba shi ikon magana ba.

Sarki ya wanke hannu ya sa cikin abinci abinci, ya yanko. Kare kuwa sai ya kai nan ya kai na, Sarki na tsammanin son abinci ya ke yi. Ya jefa masa ya ki ci, sai haushi ya ke yi wa Sarki.

Sarki ya bude baki zai sa wannan lomar sa’an nan ya dauki sanda ya kore shi, sai karen ya yi farat ya buge hannun Sarki, loma ta fadi kasa. Sarki ya dunkula hannu ya shiga dimar kare, amma kare sai gurnani ya ke, bai kula ba. Ya sa baki ya cinye loman nan da ta fadi daga hannun Sarki, ya kuma hau wa sauran abincin duk ya cinye sarai. Tun Sarki na dukansa, har haushi ya kama shi, ya gaji ya bari. Ya tsaya kurum ya ga ikon Allah.

Ko da kare ya cinye abincin nan, sai ya koma gefe guda ya kwanta. Kafin Sarki ya kare ciccika, kare ya mimmike nan ya mutu.

Ganin wanan abu fa ya kara ta da hankalin Sarki, ya ce, “Lalle akwai wani abu game da abincin nan. Watakila sadakar da ta kawo ta yi mini sammu ne in ci in mutu.”

Sai sarki ya fito ya kira ta, ya tambaye ta, tarantse da abin da zai kasha ta ba ta sa kome ba ciki. Ya tantambayeta ko ta bari garin sauran kishiyoyin, ta ce a’a, da karewa sai ta zuba cikin wannan kwano ta kawo.

Sarki ya ce, “To, da kika fita ba wadda ta shigo bayanki?”

Sadaka ta ce, “Mts, bayana ba wadda ta shigo. Ba na daukan akhakin wani, ni kadai na dawo na bude, don ya sha iska da na ji kuna tafe.”

Sarki ya yi shiru, ya ce, “Lalle karya ku ke yi. Munafincinku na mata wane ne bai san shi ba? Ba shakka ki gaya mini abin da kuka zuba, in ba haka ba kuwa in sa a yanka ki.”

Sadaka ta fadi tana ahi, tana rantse-rantse tana cewa ba ta sa kome ba ciki. Ya dube ta, ya ce, “Ke ar, munafuka!” Ya aika a kira bayi su zo su yanka ta. Nan da nan suka shigo, aka cafĂ© ta tana kuka, aka yi waje da ita.

Sarki ya yi zugun cikin daki, yana mamakin abin da ya yi wa sadakan nan har da ta ke so ta kasha shi, ya rasa. Can sai ya ji sadakan nan har da ta ke so ta kasha shi, ya rasa. Can sai ya ji dakin ya gume da wani wari kamar na gwano. Ya tashi ya inda ya ke zaune, bai ga gwano ba. Yana kakkabe rigarsa ko ya shiga ciki, sai ya ji ka-ka-ka-ka-ka a bias rufin daki. Ko da ya daga kansa sai ya ga wani katon kumurci a cikin azara. Da ya gan shi sai ya san lalle barin abincin nan da ta yi a bude ne, macijin nan ya zo ya ci. Saboda haka ya tashi da sauri, ya tafi inda bayin dandanne za su yanka, sai kuka ta ke tana salati. Sai ya ce, “Kai, ku tsaya, ku tsaya!”

Bayi suka tsaya suna kaduwa, suna tsammani Sarki ya raina saurinsu ne. Sarki ya ce, a sake ta. Ya kira bayin, ya tafi da su turakarsa, ya nuna musu kumurcin. Ya gaya musu kuma da abin kumurcin kasa, aka fid da shi wage aka yar.

Sarki ya tara dukan iyalinsa, ya gaya musu wannan al’amari, ya kuma gargade su kada su sake barinabinci a bude. Nan gabansu kuma ya gafartra wa sadakan nan, suka koma sha’aninsu.

Ya sa aka fita da Karen nan zaure, ya gaya wa fadawa da Sarakunansa abin da ya auku cikin gida duka. Ya sa aka gina dan daki a kofar gidansa, aka yi wa karen nan kabari a ciki aka sa shi. Ya yi bakin ciki kwarai saboda mutuwar Karen nan. Ya kuma gargadi mutanensa da abu biyu. Na daya, ya ce kada su rika saurin fushi, kowane a’amari ya auku, kafin su zartad da hukunci su tsaya sai sun bi cikin al’amari ya auku, kafin su zartad da nan sun yi saurin cika umurin da ya bayar a yanka sadakan nan da ya yi da na sani daga baya. Na biyu, ya ce su kyautata tausayi da jin kai ga dabbobi da tsuntsaye, ko da ba su da dabara kamaru, ba a san inda rana za ta fadi ba. Kowa ku ka gani a duniya, yana da ranarsa. Ko ba don wannan, ma ba, ai an ce aikata alheri ga kowa, sakayyarka tana wurin Allah.

Da Waziri ya ji haka sai ya ce a rana, “A’a! Me ya ke nufi da wannan labari? Dan tsuntsun nan fa rigima gare shi! Yana tsammani ni yaro ne, balle ya ce ya yi mini wa’azi?” Sai ya hadiye fushinsa, ya yi murmushi, ya ce, “Wannan labari naka iyaka ne. Bari in yi maka kyauta.” Sai ya zaro wani zobe na zinariya ya rike a hannun hagu,ya nufo aku wai zai ba shi, hannunsa na dama ko na cikin riga. Aku ya rika tsalle yana ja da baya, Waziri na binsa yana cewa, “Tsaya mana ka karba!”

Aku na ja da baya dai yana cewa, “Ai sadaka na yi maka labarin, ban don ka biya ba.”

Da Waziri ya lura aku ya gane shi, sai ya zabura gaba daya ya kai masa bugu, aku ya goce, buje ya tadiye Waziri ya fadi, ya daushe baki har hakorinsa guda ya fita. Ya tashi ja wur cikin jinni, nan da nan baki ya haye.

Da aku ya ga haka sai ya haye cediyar kofar gidan, ya kaikaici idon Waziri ya yi ta dariya. Da ya ga Waziri da dubo, sai ya kanne, ya ce, “Sannu bawan Allah! Ba ka sani ba, Waziri, ni kuwa ban ji zafin ba. Da ka taba jin labarin yautai da wani mai keke, da ba ka kulla wannan niyya ba game da ni. Kana so in kare ka da shi?”

Wzairi dai bai ce uffan ba, yana can yana fama da abin da ya same shi. Aku ya faki idonsa ya yi masa gwalo, ya ce, “Ko ba ka so ina gaya maka, aimu abimmu muna yi don Allah ne. Sai ya soma.

Post a Comment

 
Top