MAGANA JARI CE LITTAFI NA DAYA
labari na ashirin da shida
LABARIN SHEHU MUJADDADI DAN HODIYO DA UMARU MU ALKAMU
Labarin Shaihu Mujaddadi Dan Hodiyo Da Umaru Mu’alkamu
Wata rana, sa’ad da Shaihu dan Hodiyo na Sifawa, sahabbansa suka taru ana tadi, daga nan sai wani daga cikin sahabban Shaihu wanda a ke kira Umaru Mu’alkamu, ya dubi mutane, ya ce, “Kai, ina ko son goro, ko akwai wani mai dan tsalli ya ba ni in ciza?” Mutane suka ce duk ba mai saura.
Shaihu na kallonsu, ya yi kamar bai ji ba, sai can, har an saki wannan magana, ya dubi Umaru Mu’alkamu, ya ce, “Tashi mu je shan iska bayan gari.”
Umaru Mu’alkamu ya ce, “To.” Ya tashi, suka tafi, Shaihu na gaba, yana biye. A lokacin nan ko la’asar ta yi sakaliya. Da fitarsu kofar gari, sun dan taba tafiya kadan sai suka kai ga wani dan rafi, suka sa kafa suka tsallake, sai suka isa wani daji, Umaru Mu’alkamu ya duba, bai ga kome ba sai itatuwan goro ko’ina.
Shaihu ya dube shi, ya ce, “ka ce kana kawar goro, to, ga su nan, debi iyakar abin da ke isarka.”
Umaru Mu’alkamu ya shiga diba yana mamaki, ashe akwai dawan goro kusa da Sifawa ba a sani ba? Ya cika aljihunsa, ya ce wa Shaihu dan Hodiyo, “Ai wannan ya ishe ni, Allah ya gafarta malam.” Nan da nan suka tsallako dan rafin nan suka komo gida.
Ana nan, bayan ‘yan kwanaki kadan goron da Umaru Mu’alkamu ya debo tare da Shaihu ya kare. Da ya ga dai dawan goron nan ba nisa gare shi ba, sai ya tashi shi kadai ya kama hanyar da suka bi da Shaihu, yana sauri ya je ya debo kafin hantsi ya yi zafi. Ya yi ta tafiya, ya yi ta tafiya har rana ta take tsaka cur bai ga ko alamar ya kusa da wurin ba. Sai ya yanke kauna, ya juyo. Kafin kuma ya iso sai da la’asar ta yi sansanya. Da isowarsa bai zame ba sai wajen Shaihu. Suka gaisa, ya dubi Shaihu, ya ce, “kai, yau na ga tasku!”
Shaihu ya ce, “Me ya same ka haka, har ka ke yaba wahalar da ka sha?”
Umaru Mu’alkamu ya ce, “Ai tashi na yi tun da safe, wai in tafi dawan nan na goro da muka je da kai shan iska kwanan baya na debo, in sake karowa. Na yi tafiya har Allah ya gajishe ni, ban ga na kai ko dan rafin na ba. Da na ga rana ta yi tsaka dai, sai na rufa wa kaina asiri na dawo. Ka ga tun sa’an nan isowata ke nan, ko ruwa ban biya gida na sha ba.”
Shaihu dan Hodiyo ya dube shi, ya yi murmushi ya ce, “Da ka san inda muka tafi fitarmu ran nan, da ba ka ce za ka bi ba. Ai cikin dawan Gwanja na kai ka ka samo goron.” Umaru Mu’alkamu ya rike baki. Shaihu ya ce, “Ka ga dan rafin nan da muka sa kafa muka tsallake kafin mu shiga dawan goron?”
Umaru Mu’alkamu ya ce, “Na gani.”
Shaihu ya ce, “Wannan ai kogin Kwara ne ka ga ya tsulance hakanan.”
Umaru Mu’alkamu bai sami ta cewa ba, sai ya kada kai kawai, ya ce, “Allah ya ba mu albarkacinku!”
Da Musa ya ji haka sai ya ce, “Af, wannan ai ina tsammani ma shi na fara ji cikin mu’ujizozin Shaihu dan Hodiyo. In dai za ka ba ni wani labari, na yarda ka ba ni, amma na Shaihu wannan namu ne, sai mu ba wani, muddin dai an yi shi. Gama ko labarin jihadin da ya yi, da biranen da ya gina, da wadanda ya ba tutoci, duk a kaina su ke.”
Aku ya gyara fiffike, ya ce, “Ai, ni ma hakanan, Allah ya ba ka nasara, ko da na ke tsuntsu sai dai in ba wani labarin Shaihu dan Hodiyo, ba wani ya ba ni ba.”
Da Musa ya ga aku ya tsunke da surutai yana yabon kansa, sai ya ce, “Tsaya! Mene ne na yabon kai? Yabon kai jahilci. Ni ba wani surutu na ja ka ba, balle ka cika mini kunne haka. Cikin labarin mu’ujizozin Shaihu dan Hodiyo yanzu zan gaya maka wanda ba ka sani ba, in kura ka. Ba na ma takalo labarin jihadi ko labarin asalinsa balle ka ce na yi zurfi shi ya sa ka kasa. Shiga kidaya, sai na gaya maka uku wadanda a ka sani ba, sa’an nan in shiga in yi azahar, na ji an yi kira.”
Aku ya ce, “to, ba sai ka fara ba mu ji? In dai lalle an yi shi, ai sai na gani.”
Musa ya ce, “Da fari ma ba ka san wanna ba. Wata rana sa’an nan Shaihu dan Hodiyo na yaro, suna zaune a Dagel da shi da ubansa Hodiyo. Ran nan Hodiyo ya shiga ya yi alwala su yi azahar, sai ya kira Shaihu ya ce, “Zo in aike ka Murnona—“
Aku ya yi farat ya karbe ya ce, “Wanda Shaihu ya tafi ya dauko littafi har ya dawo uban bai gama alwala ba? Shaihu ya yi alwala ya bi shi aka yi sallar da shi? Alhali kuwa daga Dagel zuwa Murnona zango guda ne ga mai kaya?”
Musa ya ce, “Me ka ke faranniya haka don ka gane na fari? In ka san wani ka san wani ne?”
Aku ya ce, “To, fadi mana ju ji, Allah ya ba ka nasara.”
Musa ya ce, “Wata rana Sarkin Gobir Wuro Nafata ya aika a kira Shaihu dan Hodiy9o kamar abin girma—“
Aku ya karbe ya ce, “—ashe ko nan ya sa an gina rami mai zurfi, ya kafa wukake da masu ciki, ya sa an rufe ramin da tabarma, don in Shaihu ya zo ya ce ya zauna nan ya fada ciki ko? Shaihu kuwa ya zo ya zauna, bai fada ba. Sarkin Gobir ya daga wata bindiga da ke gare shi nana boye zai harbi Shaihu, bindigar ta fashe. Sarkin Gobir duk ya kokkone. In ko ba wannan mu’ujizar ba, wata ka ke nufi ka fadi mu ji, Allah ya ba ka nasara.”
Musa ya ce, “A’a! Ashe dan tsuntsun nan a yi da shi. Ya dubi aku, ya ce, “Ka san labarin Shaihu da madugu?”
Aku ya ce, “Shaihu da madugu? Wane labari ne kuwa na Shaihu da madugu wanda ba sani ba? An ko yi shi? Allah ya ba ka nasara, sai ka fadi mu ji.”

Post a Comment