0
JIKI MAGAYI PART 2






JIKI MAGAYI PART 2

YARINYA TA SHA ALWASHI


na dai hayaniya ta kaure tsakanin sa da ita,tace dukkan abin da ka shikenan suka yi sallam ya tafi gida ya kwana yana bacin rai
da attajirin ya samu labarin yadda suka yi da abubakar sai yace bari in nuna wa yaron nan kowa ya ja dani ya fadi
sai ya aika aka kirawo masa wani mutum sunan sa malam sambo wanda duk mutanan garin suna tsoron sa harda ma sarki da yazo watsa masa kudi masu yawa
ya fada masa abinda ke tsakanin sa da abubakar


AN JUYE ZUCIYARTA


malam sambo yace wannan magana mai sauki ce wani ma yayi rawa balle dan makada  idan ma ka bukaci yaron ya mutu ai allah ya bamu wannan ikon da zamu yi wannan taimako
malam shehu yace mutuwa kan bana bukata abinda nake so ka juye zuciyar yarinyar da ta iyayenta daga gareshi
malaminsa yace to shikenan idan na koma gida yanzu ka aiko yaronka zan baka wani taimako idan yamma tayi kayi abinda na aiko maka dashi ka aika
idan ba ta zo ba ka aske mini gemu,kuma zan aiko maka wani magani kasan yadda zaka yi ka kwaba shi cikin juda ka bata idan dai har ta karba ta kai hancin ta shaqa
lalle m,agana ta kare idan iyayen ta na so ko ba sa so dole ne ka aure ta,"malam shehu yayi farin ciki ya kawo kudi masu yawa ya bashi


YA HADA MAGANI


da maraice ya yi ya aika aka karbo masa maganin daya 1 ya kwabe shi da juda dayan 1 kuwa ya yi turaren sa sa'an nan ya aika a kirawo zainabu da yaro ya je sai iske ta
suna zance da abubakar,yayi sallama abubakar ya amsa yace me kake nema ?
yaro yace malam shehu ne ya aiko ni wajen zainabu yana son ganinta sai abubakar yace koma ka gaya masa bata zuwa
har yaron yayi nisa ta zabura ta tsinka da gudu ta kirawo shi a gaban abubakar tace ya gaya wa maigidansa tana zuwa amma wannan magana da ya aiko da farko sam babu ta tsakaninsu
daga nan abubakar yace to ai gashi nan ko jiya ban fada miki ba ? tace masa haba abubakar ai wannan ba komai bane gani ba ci ba,tafiyar ta kuwa ba itace aurensa ba
na rantse maka da gaskiyar zamani bani auran kowa nan duniya idan ba kai ba watau fadin ina zuwa domin ransa yayi dadi ne kawai ka yace na wulakanta shi sau biyu 2 domin kuwa
kasan halinku maza idan aka yi muku gantsi akan sha wuya wataran
yace shikenan duk abinda kika yi dai_dai ne suka yi sallama tayi masa rakiya


SUN SADU A SORO NA UKU 3


da komowarta gida sai tayi wanka tayi shiri tace wa uwarta zata tafi wajen abubakar yanzu tana komowa da fitar ta bata zame ko ina ba sai gidan malam shehu
ta iske zaure tinjim ana ta hira sai ta wuce ciki ta jira shi a soro na uku 3 jim kadan sai malam shehu ya shuri takalman sa ya shiga cikin gida duk wuri ya gume da kanshin turare
da jin sa yana zuwa sai ta rufe kai da shigowarsa sai yace zainabu kin zo ?
don me na aika sau biyu 2 ayi kiranki kika ki zuwa zan ci namanki ne ?
tace masa ai dama ce ban samu ba, suka yi gaisuwa sannan yace mata abin da yasa na kira ki naji labarinki ne na kuwa ji akwai wani wanda kike son sa amma ni na sani ba ayi masa baiwa da ke
amma ko anyi ni ina so sai na ga abinda zai kore ni, mai zai kore ka kai ba mutum ? bane mutum na kin mutun ne ?to ina son ki da aure, nima ina sonka saura ba da aure ba,saboda me ba da aure ba ?


HAR YANZU INA KAUNARSA


domin kuwa tun ina yarinya babu wanda nake so tamkar abubakar,har yanzu kuwa ina kaunarsa duk garin nan dai dai ne basu neme ni ba, amma duk sun ga ba dama sun watsar
kuma bari na gaya maka gaskiya kaga dai na sani kai mai arziki ne abubakar kuwa talaka ne danuwana, idan aure ka babu yunwa babu kishirwa saura da abu daya 1 kai mutum ne mai zara
da yau zaka ga wadda ta fi ni kyau sai kace ita kake so, kuma ka cika aure_aure da yawa duk wadda ka aura kuwa da kaga kunyi yan shekaru bata haihu sai ka sake ta da cin zarafi
kuma kana da matanka hudu 4 babu wadda bata girme min ba, ni ba zan iya kishi da su ba, ka sani kuwa ba'a yin mata biyar balle kace zaka aure ni, yace wannan ba magana bace tunda ya ke nace ina sonki da
aure idan kina sona ki amsa mini ni nasan yadda zanyi, Ba'a saki ? tace tunda sakin wata zaka yi ka uare ni nima watarana saki na zaka yi  idan ka ga wata wadda tafi ni kyau ka auro ta


KINA SONA ?


ba haka bane zainabu, abu daya 1 nake so a gare ki idan dai kin amsa kina sona shikenan, babu dama,
na baki damar kwana bakwai dukkan abinda kika shawarta ki dawo ki shaida min, domin in san abinda nake ciki,
wacce shawara zanyi ? a'a ke dai kiyi shawara
suka yi sallama zata fita yace ta dakata masa ya shiga gida ya debo kudi da goro ya kawo mata tace a'a wallahi ba ni karbar kome naka idan aka gani a gida za'a doke ni kuma duk wanda yaji tun yanzu na fara karbar abu
daga hannunka sai ya tabbatar mana da halinmu na mata, yace kwashe kin sani ko ba dan wannan magana ba ni mai baki abinda yafi wannan ne


NASAN HAKA


tace nasan da haka, amma yau muke da kai da ba ka bani ba ?
yayi yayi ta karba ta ki'tayi wuf zata tashi sa ya kame zaninta yace to idan ba zaki karbi wannan ba ga wani abu dan kankani kiyi maganin rana, dom in kuwa bai kamata tsakani na da ke ki shigo gaishe ni kuma ki fita hannu wofi ba
watau baki darajtani ya zura hannu cikin aljihu ya dauko tuaren nan da ya cude da magani ya bata, ta karba da kyar ta  tafi da ta shiga gida ta dauki turaren ta ba uwarta tace abubakar ne ya bani
karbi ki ajiye mini, da zata bata ta lakuta kadan tayi bille dashi
da gari ya waye malam shehu ya aika aka kira masa malam sambo ya fada masa duk abinda suka yi da zainabu, sai malam sambo yace tun da yake ka bata turaren shikenan kada ka kara neman ganinta su da kansu zasu aiko a neme ka, malam shehu
yayi masa godiya ya koma kawo kudi ya bashi


SAURAYI YA DAMU


Amma abubakar ya tafi gidan su zainabu ya aika aka kira ta ya tambaye ta gaskiya ne kuwa jiya bayan rabuwar mu kinje gidan malam shehu
tace eh, yace yanzu nasan tsakanin mu rufa_rufa ce ina so ki fada min a sarari in baki sona, tace ai ka sani budurwa haja ce kowa ya gani yana so kuma kowa da irin tayin sa amma mai siye daya 1 ne,
ko da ba ayi mana baiwa da kai ba kai dai kana tashina, sai ya tashi da fushi ya tafi abinsa
da ya tafi gida ya gaya wa uwa tasa abinda ke tsakanin sa da zainabu, uwar tace ai ko ni da na sani ba zaka auri zainabu ba, domin kuwa tana da masoya masu arziki kasan komai na duniyan nan ba duka ake yi domin allah ba, sai don kudi kayi hakuri ka nemi
dai_dai kai


SAI NA RAMA


yace mata haba iya idan dai ni dan mutum biyu ne sai na rama zan shiga duniya da ko wanne hali na sani allah zai taimake ni amma kada ki damu
ga audu nan da kanwata da kakarmu sun ishe ki zaman duniya ni kuwa idan da rai watarana zaki ga na komo
da taji haka ranta ya baci sosai ta rasa abinda zata ce masa domin ta sani idan halin abubakar ya tashi babu wanda ya isa ya hane shi
damaraice sai ya tafi wajen uban zainabu yace masa abinda ya kawo ni na nagi tsakanina da yarka babu maganar aure ko ka sani ? dama naga yanzu dukiya ta bude mata ido har ta manta da alkawarin mu ina so ka kirawo ta a gabana in gaya mata magana


MAGANA BIYU 2


yace masa a ina kaji wannan maganar banzar ? dattijo iri na zai yi magana biyu 2? idan nine na haifi zainabu bata da miji sai kai
abubakar yace masa a'a kada kace nayi jayayya da kai a bata wanda tace tana so ai yan mata da yawa
malam audu ya kira ta yayi mata fada sosai har yace nan gaba ba zata kara fita ba sai dai ran da aka rufa ta za'a kai ta gidan abubakar
ita kuwa tace ko an daure mata abubakar a kafa sai ta tsinke shi da ta aure shi gwara ta shiga duniya
uban ya tashi da fushi ya buge ta ya taka ya daure ta yace wa abubakar koma gida allah ya huci zuciyar ka nayi maganin abina
abubakar yace to baba ba komai sai anjima

Alhamdulillah karshen part 2 kenan

Post a Comment

 
Top