0
LITTAFIN JIKI MAGAYI






LITTAFIN JIKI MAGAYI 

part  1

daga taskar john tafida umaru zaria Da rupert east

A CIKIN Birnin galma akwai wani mai arziki sunan sa malam shehu yana da jakunkunan kudi da tufafi da hajjoji da kekunan dinki da
da na hawa da barori da shanu a garkuna da dawakai uku masu kyau suna harbin iska a barga tasa,
kullum da la'asar yakan tafi barga ya zauna barorinsa da mutanen gari masu son kwabon sa su kewaye shi,ana ta nishadi
fadi banza, fadi wofi
sabo da tajirincinsa ba inda sunansa bai kai ba yana aikar yaran sa fatauci ko ina wadansu a jirgi wadan su a mota wadansu ya labta wa jakuna ko takarkari ko rakuma
hajjjoji da goro su shiga cikin kasa suna ciniki shi ma da kansa da wuya ya san iya kar dukiyarsa

BAI HAIHU BA

shekara ashirin da yin aure amma bai taba haihuwa ba yayi aure da yawa gidansa ba a rasa matan aure hudu ya batad da dukiya ba iyaka wajen
malamai da bokaye da yan bori garin neman maganin haihuwa amma cikin matansa babu wadda ta taba ko batan wata ko yaushe idan ya tuna da wannan babbbar hasara
ta rashin da sai ransa ya dugunzuma ya dami dukkan mutanen gidansa da fade_fade wani lokaciin ma ba mai ganinsa a waje tun safe har wajen la'asar yana can cikin dakinsa
yana rokon ubangiji ka jikaina ka bani da ko da wannne iri ne"

YAYI MAFARKI

ana nan wata rana yayi mafarki ya ga wata god'iya a gidan malam audu an kai ta kasuwa wani mutum kuwa yana sonta kwarai da gaske har yayi cinkin ta
sai shi kuma da ya gan ta ya so ta kwarai kamar me ya kara kudi aka sallama masa ya biya aka kawo masa gida ya daure wancan kuwa ya hakura tilas god'ya tana gidansa har ta
haifa masa dan dukushi kyakkyawa wanda duk wanda ya gani yana sha'awar sa  da ya yi girma ya isa hawa rannan sai yace ayi masa sirdi
aka yi ya hau ya fita kilisa  daga can doki ya abauce ya kada shi ya tsere yabar shi cikin ciwo kwarai
da haka ya farka daga barci duk jikin sa yana rawa yayi ta waswasin wannan abu cikin ransa har gari ya waye da asalatun fari ya tura aka kira masa wani malamin kasa
ya buga yace masa naga kuwaa maganar aure da haihuwa a tsakani na ga wani kuma ya kwace gabanka amma idan ka maida hankali zaka ture shi kuma naga wahala a
cikin wannan aure in kayi watarana zaka yi nadama in ka bi shawarata kada ka saka yatsa cikin wannan al amari
ka bar shi yadda annabi ya bar duniya saura allah ya sani

YANA SHAKKAR BAYANIN

bayan da ya  tashi malam shaihu ya zauna yana bimbini a ransa a kan mafarkin da abin da malamin ya gaya masa sai a rai malam audu yana da ya sunanta zainabu yace
lallai ita ce aka nuna masa a mafarki,in kuwa haka ne in ya aure ta ya sami abin da yake bukata sai kuma ya tuna da sauran abin da ke cikin mafarkin da shawarar
da malamin ya yi masa Amma don tsananin son da ya maida duk wannan ba a bakin komai ba idan dai bukatarsa ta biya wata kila ba gaskiya bane
maganar matsibbata ce sanin gaibu sai allah da haka ya kwantad da hankalin sa ya gama shawara daga na sai ya aika aka kira masa ,malam audu da yazo suka shiga waje daya yace
masa abin da ya sa na i kiran ka na ga wani abu ne a wurinka wanda nake so ban sani ba watakila zan samu sa'an nan ya buda masa

YARINYA DA WANDA TAKE SO

sai malam audu yace masa wannan magana tana da wuya domin kuwa ita zainabu tun  suna kanana akwai wani yaro sunansa abubakar tare suka taso tana sonsa shi kuma yana sonta har kuwa
kowa ya sani ita zai aura mutane da yawa da samarida wanda bai zaburo yana sonta ba amma taki sai shi
shi kuwa abubakar duk duniyar nan bashi da wadda yake so sai ita ka sani kuma yaro ne mai zafin zuciya kwarai idan har bai auri zainabu ba babu wanda abunda zai yi ni kaina bazan shara ba
malam shehu ya ce masa idan ka bani izini in aika a kirawo ta domin in yi magana da ita dukkan abin da mukia shirya in sanad da kai
malam audu yace wannan fa ai ba magana ta bace sai wadda kayi domin kuwa ina tsammanin ko aika wa kayi bazata zo ba balle kuyi magana
saura ni bani da tacewa cikin wannan sha'ani
da ya koma gida ya shaidawa uwar yarinya maganar da suka yi da malam shehu akan zainabu uwar tace haba malam wannan magana ma ya za'a yi ta ?
idan muka yi haka ai a maida mu shashashai kada a ko fara yinta


YA SA AN KIRA TA

da la'asar tayi attajirin ya aika a kirawo zainabu da aka shaida mata malam shehu yana kiranta ta ce a koma a shaida masa bazata zo ba aka koma aka fada masa sai ya aika a shaida mata jawabi daya[1] ya ke so suyio
shine jawabin aure
ta sake ita ta rigaya tayi miji ba kuwa da niyyar sake wani da aka zo aka fada masa ransa kuwa ya baci yace ashe akwaai sauran mace a wannan sarari wadda zan aika ince tazo ta kekasa kasa tace3 bazata zo ba ?
sai yaronsa da ya aika yace haba mai gida kai kaso ina kamarka mai kiran dubu daga wata kasa su amsa sa[an nan ka bata kanka a wajen irin wadan nan yara ko da yake tana da kyau dai
ai bai kamata irin ka ba aci masa zarafi


RAN SAURAYI YA BACI

Ana cikin haka kwaram wani cikin yaran malam shehu ya tafi ya fadawa abubakar ai malam shehu ya aika an kira uban yarinyar da take tashi ya kuma aika a kira ta amma taki zuwa
nan da nan sai ran abubakar ya baci da jin wannan magana ya rasa abin da yake ciki yayi ta dokin yamma tayi ya tafi
wajen zainabu da yin yamma sai ya nufi gidansu ya aika kaninta ya fada mata ta fito suka tafi wajen da suka sab azama suna zance suka shiga cikin zancen duniya sai abubakar yace mata matar mai kudi
tace wacce irin magana ce wannan da kake yi yau ?
dama na ganka yau duk harhar kake ji yace abin da yasa na fadi haka domn naji ance malam shehu mai arzikin garimmu ya aiko ki tafi
tace masa shi wanda ya baka labarin bai gaya maka jawabin da mayar masa ba ?

MATA HALINKU NA DA WUYA

ya fada mini amma duk da haka raina ya tashi kwarai da gaske domin na sani ku mata halinku na da wuya kin ji ance da doki da kogi da mace ba a basu amana har ni ma watakon ba ka yarda da ni ba ?
ai mata duk halinsu daya [1] ne, to sai ka bani dalili da ka ce haka yace abin da ya sa nace miki haka domin doki in kana sonsa babu irin wahalar da baka yi masa amma wata rana sai ya harbe ka kogi kuma
sai ka wuce yanzu lafiya ba ruwa amma sa'ad da ka nufi komowa sai ka iske ruwa ya kawo ba dama mace kuma an ce alkawarinta na kwana arba'in ne idan ya wuce haka idan ta samu wani duk son da take maka
sai ta bar ka malam shehu atajiri ne in ba ki son shi don kome ba zaki so shi domin dukiyarsa.....

ALHAMDULILLAH KARSHEN PART [1]

Post a Comment

 
Top