0
JIKI MAGAYI PART 3


 JIKI MAGAYI PART 3
 

JIKI MAGAYI PART 3


KANA SO KA KASHE TA NE ?


da uwar zainabu taji kukan da yar ta take yi sa'ad da ke dukanta sai ta leko tace mai ya faru da zafi haka?kana so ka kashe ta ne ? malam audu yace mata akan maganar auran su ne da abubakar,kin san dai bashi yiyuwa ace na amsa zan bashi auran zainabu sa'an nan yanzu tazo ta dauko wani wai shi zata aura, tace shi take so da aure kinga idan nabi maganar ta kin sani naji kunya
kenan nan gaba babu wanda sake mai da ni dattijo, kowa sai yayi ta yi dani, ace sabili da kudinsa ne yasa na aurar masa da yata.daga nan uwar tace ai kasani abin duniya ba'ayin sa da karfi sai da rarrrashi da ban magana, abinda nake so da kai kayi hakuri a rarrashe ta watakila ta koma cikin hankalinta, amma yanzu idan kace zaka yi mata na karfi kasan halin yaran zamani watakila wannan ya zamashine sanadin da zamu rasa ta
dungum, babu rai babu girma  sa'an nan ya kwance ta yamma fari sai gidan malam shehu tace masa tun da ya ke abubakar yayi zafin zuciyar sa ina so ka fito maganar neman aure,


AN YI JAYAYYA


da gari ya waye malam shehu ya aika wurin malam audu a fada masa yana nan yana aikowa akan maganar da suka yi malam audu ya aiko a fada masa ba dai shi ba dai, sai ko alkali ya daura musu aka yi jayayya kwanaki da yawa, sa'an nan yan uwa suka taru kan malam audu tilas ya amsa ba don son ransa ba ko kadan
malam shehu ya fito zance aure aka yi masa baiwa, ya biya wadansu ramuwa wan da yarinya taci a ran nan aka sa ranar biki duk gari suna yi da malam audu don rashin dattakun da yayi,ran da za'a daura aure ya saki mata tasa daya 1 da yamma aka kawo amarya kashe gari aka yi kasaitaccen biki wanda ko sarkin galma bazai yoi irin sa ba, abokansa da ko ina suka zo, babu irn abin da ba'ayi kowa sai cewa yake yi tubarkallah lallai mai arziki yana  biki
sai facaka ake yi da kudi aka kwana uku 3 ana wasa sa'an nan aka yi budar kai aka kawo gara sannan kowa ya watse


SAURAYI YA SHIGA DUNIYA


abubakar ya fita gida bai san inda zashi ba yana ta yawo har yazo wani gari wanda ake kiransa zauna da shirinka garin kuwa na wadan da suka yi ko sata ko abun kunya ne, suka gudo daga garinsu suka zo suka kafa tasu tunga, basu yin komai sai masha'a duk garin daga yan bori sai kasaitattun barayi sai matsibbata da karuwai mata, abubakar ya iso garin sai ya rinka jin yizga tana tashi da wake_wake sai zauna gindin wata bishiya yana hutun gajiya har bacci ya dauke shi n
sai wani mutum ya zo ya ganshi kwance sai ya tashe shi yace samari daga ina ka fito ? sai ya farka suka yi gaisuwa sai ya tambaye shi a garin nan ko akwai wani shahararren malami? mutumin nan yace masa balka ji sunan garin nan ba ? yace naji, yace to kaga wanne malamin kirki zai zauna cikin wannan gari ? mu nan bamu sha'anin komai da malamai sai bori, sai yace to dakyau nuna min gidan babban matsafi


ZAN WAR WARE MAKA ZAREN DA ABAWA


sai ya tafi dashi gidan wani wai sunan sa tausayinka da sauki, da aka kai shi gidan bashi nan ya tafi wani garin al'ada kwanan su uku3 amma ana tsammanin da yamma zai dawo ya zauna yana jiran sa bai komo ba sai da tsakad dare da ya shiga gida ya kintsa sai wani daga cikin yaransa ya shiga ya fada masa yayi bako, tunm da hantsi da can sai ya fito ya sa aka yi kiran abubakar suka kadaice da dai abubakar ya ganshi sai jikin sa ya dauki rawa saboda kwarjinin da ke gareshi
suka gaisa ya tambaye shi abinda ya kawo shi, abubakar yace magana ta na da yawa sai allah ya kaimu gobe na warware maka zare da abawa
da gari ya abubakar ya tafi ya gaida tausayin ka da sauki da suka gama gaisawa yace abin da ya kawo ni gareka bacin rai ne, ni ke da wata yarinya wadda nake so kuma ta ke so na fiye da kima, tun muna yara har muka girma ina nan ina tashinta zamu yi aure ina cikin shawara kenan zan sa uwata taje ayi mini baiwa sai wani attajiri a garin mu ana kiran sa malam shehu yaji labarin ta domin kwadayi kawai ya kangarar da ita, ko da yake yana da matansa hudu 4 wannan mutum bai kamata ya zauna
lafiya ba, bashi yiyuwa a gareni na zauna cikin garin nan in ji ya aure ta saboda haka ne na rasa abin da zanyi in fanshewa kaina, sai na shiga cikin duniya ina yawace_yawace har allah ya kawo ni garin nan ina cikin tambaya har aka gaya mini babu wanda ya fika magani cikin dukkan kasar nan, saboda haka na zo gareka in ka yadda ka taimake ni in dauki fansa kansu in huce haushi,

tausayin ka da sauki ya ce ka ko kawo kuka inda za'a share maka hawaye, dukkan abin nan da ya kawo ka kafin ka fadi na riga na sani, domin jiya da muka rabu doguwa ta zo ta fayyace mini komai da ke tafe da kai, ammma yadda kake tsammani ba haka bane ba kwadayi kadai attajirin nan yayi maka wannan abu ba
dalili kuwa dai yana son da ne an kwa gaya masa idan ya auroi yarinyar nan zai samu  sa'an nan abubakar yace ashe haka ne ? yace eh, abubakar yace zai kuwa samu, yace lallai kuwa zai samu domin wannan magana ba nufin mutum bace ikon allah ne, sai abubakar yayi shiru ya nitsa cikin zurfin tunani sa'an nan yace to tun da yake kwadayin da ne ya sa yayi min wannnan abu, abu daya 1 kadai zai faranbta mini rai shine albarkar nan da yake nema ta zamar masa la'anta.

Alhamdulillah karshen part 3 kenan

Post a Comment

 
Top