ILIYA DA SARAUNIYA
ILIYA DA SARAUNIYA
Jim kadan sai ga Sarauniya ta fito,
Iliya
ya dube ta da kyau ya ga tun sa ya
ke yawo
cikin duniya bai taba ganin mai cikakkar kyaun
halitta kamar ta ba. Irin tufafin da ke
jikinta sai
wanda ya gani. Yam mata biyu suna
biyeda ita
daga baya suna gyara mata tufafinta da ke jan
kasa. Gashin kanta kuwa har bisa
dugduganta.
Da zuwa ta rungume Iliya da murna
ta sumbace
shi. Ta kama hannunsa suka nufi cikin gida, sai
ka ce wanda ta ga wani tsohon
masoyinta.
Aka kai Iliya cikin wani irin daki na
hutawa, shafaffe da zinari, kowace
kusurwa kuma an dafa mata sham a. Kasa
kuwa am bi
duk an shimfida dardumu da kilisai iri
iri, ga
kujeru wadanda in ka zauna su
zauna, idan kuma ka kwanta su kwanta. Akwai
tebur a
tsakar dakin n farin karfe, an rufe shi
da zane na
farin siliki, an jera abinci, da na sa iri
iri. Waje daya kuma ga wurin wanke hannu, ga
sabulu da
tawul a rataye. Suka zauna kan
kujera, ga
teburin a gabansu. Suka shiga
shaye-shaye da ciye-ciye wadanda Iliya bai taba
saninsu ba.
Tana yi masa gaisuwar maraba da
murya mai taushi. Duk abin nann Iliya
sai
kallonta kawai ya ke, yana lura da irin abin da
ta ke nufin kulla masa.
Gaskiyar Iliya ashe matar hila ta ke
yi
masa don ta zambacee shi. Yam
fashin nan ne shuka ajiye ta, suka gina mata
wannan
katafaren gida, suka samo yam
mata don su
rika yi mata aike-aike, suna kuma
taya ta zama. Duk fadin gidan kuwa ba
namiji ko
daya. An shirya shi sosai yadda duk
wanda ya
zo gidan nan, ko Sarki, ko tajiri, ko
malami, ko jarumi, lalle zai halaka. Abin da ya
bari kuma
ya zama ganimar matar, da yam
fashin.
Akwai wani daki wanda aka shirya
musamman wanda nan a ke halaka duk wadanda
suka je. An kawata dakin kwarai da
gaske, an
sa kayayyaki iri iri masu tsada.
Akwai gadon
karfe wanda aka yi wa shafen zinari, ga kilisai
da barguna ko ina an cika dakin da
su. Matasan
kai kuwa ko ina an jingine. Akwai
kwalaban
turare wardi daga kololuwar dakin a rataye, an
hudar bakinta, tana diga kadan
kadan kan
gadon. Kuma ga fitilu masu haske a
kowace
kusurwa. Gadon nan yana bisa wani katon
shisshike ne na karfe wanda ke juya
shi ko ina,
ga zannuwan gado masu tsada an
rufe
shisshiken yadda ba za a gan shi ba. To, dabarar kashe mutanen duk a
wurin
gadon ta ke. Akwai katuwar rijiya
daga
karkashinsa, kamar girman daki,
daga can ciki, zurfinta kuma ya fi gaba dari uku. An
rufe
bakinta rif da shimfidu. An shirya
gadon yadda
idan mutum ya kwanta, har gadon ya
rabu da bangon dakin, to, sai ya kife, mutum
ya fada
cikin rijiyar. Sa an nan kuma gadon
ys koma
yadda ya ke. Duk abin nan Iliya
kamar ya sani. Da su Iliya suka kare cin abinci suka
shiga hira, tana ba shi labarin duniya,
shi kuma
yana fada mata wadansu labaru irin
wadanda ya
kamata ya fada mata. Sai ya rika yin gyangyadi
da gangan, kamar yana jin barci. Sai
ta ce da
Iliya ya kamata su tafi ya kwanta
don ga alama
ya gaji. Iliya ya ce, To, da kuwa na so. Ta
shige gaba ya bi ta har suka shiga
dakin nan
inda rijiyar ta ke. Ta ce masa, Ga
gado kwanta
ka huta, ai ka wahala. Har za ta fita sai ta ce
masa, Af, yau kuwa ana sanyi-
sanyi. Sai ka
matsa daga can kusa da bango,
akwai muhun
wuta daga cikin wancan dakin da ke game da
wannan, za ka ji dumin wutar, ka
gasa jikinka,
don ka ji dadin harci!
Iliya ya ce, Ai ba na so in cika barci,
saboda kullum dare na kan kita waje in duba
dokina. Kafin ta juya sai ya yi wuf ya
fizgo ta,
ya jefa bisa gadon, ya danna wajen
bangon, inda
ta ce shi ya kwanta. Ko kafin ta yi kara, gadon
ya bintsire ya kifar da ita, ta fada
cikinn
rijiyar. Shi kuwa sai ya yi tsalle waje
daya,
gadon ya koma inda ya ke. Da ya ga haka sai
ya koma waje daya ya kwanta, ya yi
ta sharar
barcinsa.
Da gari ya waye Iliya ya fito ya kira
yam matan nan da fuska murtuke, ya ce, Ku
kawo mini makullan dakin nan na
kasa.
Saboda tsoro da rudewa ba su
tsaya wata-wata
ba, sai suka kawo masa. Ya ce su nuna masa
wurin da a ke budewa, suka nuna
masa. Ya ga
ashe wadansu irin manyan karafa ne
kamar
azaru da su aka yi kyauren. Ya husata ya
watsad da makullan, ya sa kafa ya
balle kyauren
ya shiga. Ya tarad da mutane jingim
suna zaune
a cikin rijiyar ba ko shinfida. Wadansu suna
kuka, wadansu suna ta salati.
Wadanda suka
dade kwarai suka saba, suna ta
wake-wake.
Kuma kusa da su ga gawar wadanda suka mutu,
wadansu sun bushe wadansu kuma
danyu suna
ta wari. Iliya ya daka musu tsawa ya
ce, Ku
fita, kowa ya san inda ya yi! Nan da nan sai
wuri ya rude, suka tashi a gigice da
rawar jiki,
wannan ya ture wannan, wannan ya
ture wancan
suna ta fita. Ko wanne ya fita waje ya ga
hasken rana ko waiwayawa ba shi
yi, balle ya
tsaya ya dubi inda zai nufa. Sai ya
bazama
kawai, ya nufi inda ya sa gaba. Sai ka ga Sarki
ya tattara buje ya soke, ya sheka
da gudu bai
san ko wajen da ya ke rufa ba.
Jarumai ran nan
babu ko ta da hannu, balle a tuna da kayan fada.
Daga nan sai Iliya ya samo wadansu
kosassun dawaki guda uku, ba su
kome a turke
sai harbin iska, ya kamo matan nan
ya sa sarka ya daure hannayenta, ya daura wa
doki guda.
Ya kuma daure ko wacce kafa da
sarka, ya daura
ga doki guda, kana ya buge su suka
watse gaba daya, ko wanne ya nufi wurinsa
dabam. Shi
kuwa sai ya kau da kai don kada ya
ga irin
mutuwar da za ta yi. Sa an nan ya
shiga gidan ya kwashe duk dukiyar da ke ciki, da
duk
abubuwan da ke da amfani, ya rabe,
ya aike wa
kowane mutum da aka yi makirci ya
fada cikin ramin nan. Amma shi ko allura bai
dauka ba.
Ya kuma watsa duk yam matan da
ke cikin
gidan, ya sa wa gidan wuta ya kone.
Ya kama dokinsa ya hau ya koma wurin
dutsen nsn na
mararrabe ya sake rubuta: Ni Iliya-
dam-mai-
Karfi, na bi hanyar da ta nufi hagu
amma ban sami mace ba, Daga nan ya tsaya
lokaci mai
tsawo, sa an nan ya ce, Duk na bi
hanyorin
nan biyu, amma ban sami abubuwan
nan da aka ce ana samu ba, bari kuma in nufi
wadda ta nufi
wajen dama, ko kila na sami abin da
aka ce.
Iliya ya kama hanyar da ta nufi
wajen dama ya yi ta tafiya har ya iske wani
kurmi.
Bayan shi kuma ya ketare wani
kwari mai zurfi.
Da ya wuce wannan kwarin, sai ya
iske wadansu ramuka manya manya kamar rijiya
wajen guda
dari, duk ciccike da zinari da azurfa
da jauhari
da lu ulu u, sai saukar ido su ke yi,
tal, tal, tal! Daga gefe guda sai ya ga an
rubuta:
Wannan dukiyan duk ta Iliya ce.
Shikenan sai
ya sauka ya bi ramun nan da dai dai
ya ga irin tarin dukiyar da ke cikin ko wanne,
ya yi
mamaki matuka, ya kuma rasa
yadda zai yi da
ita. Ya ga ko mutum dubu suka
kwana dubu suna aiki a wurin, ba za su iya debe
rabin
dukiyar ba. Ya tsaya ya yi tunanin
abin da zai
yi, sa an nan ya hau dokinsa ya koma
Birnin Kib, ya fada wa Waldima. Ya ce
kuma yana son
mutane dubu wadanda za su yi ta
aikin tonar
wannan dukiya. Nan da nan aka
shirya masa su, suka tafi wurin suka kama tonar
dukiya. Suka yi
ta aiki ba dare ba rana har kamar
wata uku,
amma ko rabin rabi ba su debe ba.
Iliya ya sake komawa wurin Waldima ya samo
wadansu
mutum dubu, suka hadu suka shiga
aiki. Da
suka kwana kamar hamsin gaba
daya suna aikin ba su kare ba, sai suka kwashe
iyakar abin da
suka hako, suka kai Birnin Kib. Iliya
ya danka
duk dukiyar ga Waldima, ya ce ga ta
nan a diba a yi masallaci, sauran kuma a raba
wa gajiyayyu,
shi
Post a Comment