ILIYA DA YAM FASHI
ILIYA DA YAM FASHI
Wata rana Iliya na zaune yana shan
iska ya wani
katon lambu a bakin kogi, yana
kallon yadda
kwalekwale ke ta yawo bisa ruwa, ga tsuntsaye
iri iri suna kiwo, sai ya tuna da yaki.
Ya tuna
irin hadarin da ya shiga, da kuma
wanda zai
shiga. Ya ce, Allah Sarki, tsufa ne, Na tsufa,
dokina ya tsufa, amma ga shi
zuciyata ba ta
gaza ba. Ya yi farat ya tashi ya ce,
Zama
wuri daya tsautsayi in ji kifi. Ya kamata mu
shiga duniya mu ga abin da ta ke ciki.
Da isarsa gida, sai ya jefa wa
Kwalele sirdi, ya
yi shiri ya kama hanya ya yi ta tafiya.
Tun yana ganin alamar karkara, har ya zama
ba ya ganin
kome sai daji. Ya yi ta tafiya har ya
tarad da
wani wuri inda hanya ta kasu uku.
Daya ta nufi dama, daya hagu, dayar kuwa ta
mike gaba
totar. A daidai wurin da hanyoyin nan
suka
hadu, an yi rubutu bisa wani dutse
mai fadi an ce --- Wanda ya bi hanyar hannun
dama, zai
sami isasshiyar dukiya. Wanda ya bi
hanyar
hagu, zai sami mata wadda ba
kamarta, Wanda ya mike totar kuwa zai gamu da
mutuwarsa.
Iliya ya tsaya, ya karanta ya yi shiru
yana
tunani, sa an nan ya ce, Ni da na ke
tsoho, me zan yi da dukiya? Me kuma zan yi
da
mace? Bari im bi hanyar da zan
gamu da
mutuwar tawa in gani. Na sani dai
kushewar badi sai badi. Mai rabon gain badi
kuwa sai ya
gani.
Iliya ya sakam ma Kwalele linzami,
ya zarce
sosai ta tafi. Can ya shiga cikin wani surkukin
daji mai duhu. Ba zato sai ga shi
gaban taron
yam fashi, mutum dubu hudu, da
babbansu
guda. Ko wanne yana rike da kayan fada iri iri.
Suna jira ne kawai wani ya fado, ya
bakunci
lahira. Ba su ankara ba sai ga Iliya
gab da su.
Suka yi mamaki, don sun tabbata ba mahalukin
da ke iya shiga dajin nan. Suka daka
masa
tsawa suka ce, Kai mai dokin nan
tsaya!
Iliya ya tsaya cif, har suka zo wurin da ya ke.
Suka ga dokin ba irinsa duk cikin
yakin kasar.
Suka ce, Ina za ka? Me ya kawo ka
nan
wurin? Iliya yace, Na biyo hanya ne zan
wuce, ban san zan gamu da ku ba.
Sai
babbansu yace, Ba ku gani har wani
kallon
hadarin kaji ya ke yi mana? Kila yana wani dan
gani-gani ne gare mu ko?
Iliya kuwa lalle a kaikaice ba a ya ke
musu. Ya
sunkuyad da kansa ya ce, Haba
samari, tsofai- tsofai da ni, gani-ganin me zan
muku? Ba ni da
kome sai yan kudin guzuri fam dari.
Wannan
damarar ta zinariya da du ke gani,
duka duka kudina bai fi fam dari biyar ba.
Rigara kuwa
tsofuwa ce, kudinsa ba zai shige fam
dubu uku
ba, takalmana da hulata kudinsu da
kyar zai yi fam goma. Wadannan likkafun da ku
ke kallo
tsofuwar azurfa ce, jauharin da aka
lillika musu
shi ke sa ku ke ganinsu kamar wani
abin kwarai, kudinsu fam dubu ne kawai. Sirdina,
ko da ya
ke na karfe ne, ba zai wuce fam
metan ba.
Dutsen nan da ke bisa kan dokina
kuwa, kun dai san darajarsa. Ba shi da wani
amfani, sai don
ya kara wa dokin gani idan dare ya
yi. Dokin
kuwa ba shi da wani amfani im ba
wurina ba. To, me zai sa ku tare ni? Ni ba ni da
kome, ina
rokonku ku kyale ni in wuce.
Yam fashi su ka ce wa Iliya, Tun da
mu ke
tare mutane, ba mu taba samun sakarai,
mahaukaci, kamarka ba. Babbansu
ya ce su
kama Iliya. To, a kusa da wani katon
itace
kuwa su ke tsaye, wanda ba kamarsa duk wurin.
Da ganin jama an nan ta yunkuro za
su kama
shi, sai ya yi wuf ya zaro kibiya ya
dubi katon
icn nan ya sakam masa. Itacen nan ya ratattake
ya fadi ricaa! Kamar dai tsawa ce ta
fada
masa. Karfin iskar faduwar itacen
nan da karar
fasuwarsa, ta sa yam fashin nan duk suka fadi
kas somammu. Da suka farka, sai
babbansu ya
ce wa Iliya, Mun yarda kai ne
shugabanmu.
Muna rokonka, ka zauna tare da mu, ka zama
babbammu. Muna da dukiya, zinari
da azurfa da
lu ulu u da jauhari da tufafi iri iri, ga
kuma
dabbobi. Duk yawammu im muka taru ko mun
shekara goma ba za mu iya gama
kidayar zinari
da ke gare mu ba. Mun yarda ka debi
duk abin
da ka ke bukata, mu dai ka zama shugabanmu.
Iliya ya yi dariya, ya yi wakar
nasara, irin ta
mayaka. Sa an nan ya ce, Yan
uwana, ba
ni so in wahalad da kaina don tsaron dukiya, ko
kiwon dabbobi. Ni bukatata in yi yiwo
cikin
duniya, in yi yaki. Dukiya kuma da
dabbobi,
tajirai da makiyaya su tsare. Na gode muku
kwarai, sai wata rana. Suka yi ban
kwana, ya
karya linzami ya koma da baya, ya
zo wurin
dutsen nan na mararraba mai rubutu. Daga
gefen inda aka rubuta, Wanda ya bi
hanyar da
ta mike total zai hadu da mutuwarsa,
sai ya
rubuta: Ni Iliya-dam-mai-Karfi, na bi hanyar
nan da ta mike, amma ban gamu da
mutuwa ba.
Daga nan ya karya linzami ya bi
hanyar da ta
nufi hagu, inda aka rubuta za a sami mace, ya yi
ta tafita. Bayan kamar kwana biyu
yana tafiya,
ran nan sai ga shi ya tinkari wani irin
gida mai
ban mamaki. Shi dai ya fi girman gida, amma
bai kai gari ba. Ginin gidan duk an yi
shi be da
wani irin farin karfe, sai kyalli ya ke
kamar
madubi. Rufin gidan kuma kansa da zinari aka
yi, ga tagogi kuma na madubi, ko
wacce an sa
mata labule iri dabam. Akwai furanni
iri iri
kewaye da gidan, akwai kuma lambu cike da
kayan marmari. Iliya bai tsaya ba,
sai ya tasam
ma kofar gidan. Tun kafin ya kai, sai
ga yam
mata arba in, ko wacce ta ce ado, daga kayan
gwal, sai tufafin farin siliki, sai
alharini, sun fito
taryarsa. Suka kewaye shi suna yi
masa
maraba, har suka iso kofar Sarauniya. Yam
mata nan su uka rike masa sirdi ya
sauka. Aka
fada wa Sarauniya
Post a Comment