0
DUK DAD'INKI DA MIJI






DUK DAD'INKI DA MIJI
 

episode 65

 (BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


A kullum bana iya bacci kullum tunanina shine yadda zanrama meyamin, yana cikin daula shi da iyalansa, har lokacin bansan dangina ba, shiryawa nayi naroki feela, ita zata kwana dashi aranan da yayi wa karya wa matarsa cewa zasuyi meeting da shugaban kasa, alhali yana makale da karuwarsa, naroki da ta ciromin gashin kansa ma kadai ya isa, haka na hada nakai don ayi mana DNA test, luckily enough nasamu results dina as expected shine ubana, asamu evidence donhaka nashirya naje gidansa, amilah tayi farin cikin ganina sosai, munyi tadi sosai da mamar alokacin datake cemin bari tamika wa baban abinci, acewarta falon acike yake da baki, mutanensa yan siyasa, duk dacewa itama da dan kawayenta sai alokacin take fadamin yasami promotion, oh God!! Kenan haryanzu efcc basu nufo kanshi ba, tunda harda promotion, ba damuwa tana shiga nabita, kansa na nufa yana ganina ya shake daga milk shake din dayake kurba, nan guard dinshi suka fara kokarin rike ni, karan da nasaka babu shiri kowa hankalinsa yakawo kaina, cike da nutsuwa na fincike hannuna sannan nace

"Kana tunanin abunda kayi zaka boye wa Allah?, inka boyewa duniya?, meyasa bazaka gayawa duniya abunda kayiba, ko in sanar da matarka cewa ni yarka ce, wanda shine mafi munin kalman danakeji abakina, abun tur da Allah sauwaka" Na jefa mishi papern dasauri yadauka yana gani yafara yagawa zai hadiye, tuni matarsa tarike tabude, hawaye suka bi idonta, tana tambayarsa meye wannan? Bawan Allahn nan yarufe ido yace sharri nake masa, ga kiri kiri fa, tana tsaye nabasu labarina kaf, duk abun kunyan dayayi dakuma abunda ya aikata sani don zuwa matakin dayake, sumewa matar tayi, jin na ambaci HIV, araina nace kadan kika gani, fita nayi nabar musu gidan, bansan ya suka kare ba,anma dai naji labarin matar ma tana dashi sai alokacin tasan cutanta, yan jarida tuni suka fara nemana, yayinda shima yafara harin rayuwata, banda gurin zuwa, shine na tattara nakoma gombe, anan nayi hayan gida, bazance na nutsu ba anma nadena duk wani mumnunan harka danakeyi, natuba nakuma koma ga Allah nadai san cewa bazan taba aure ba, bazaa soni ba, idan alumma sunsan wayeni zaa kyankyame ni, gidana na maitama siyarwa nayi, aiki na nema anan gombe, bazan fadi gun ba saboda ina boye kaina ne kar duniya sugane wannan abun kunya, akullum ina addua Allah ya laanta mahaifina, ina kuma adduan ya bayyana min yanuwana duk da nasan bazaa soni ba, nazo bauchi ne don jin labarin abunda yasami hamdiya, wanda sai alokacin kowaccensu nasan labarinta, hakika duniya abun tsoro ne, muna zaune ne awani gefe bamusan meke faruwa ba, anma wanda suke wannan rayuwan sunsan gaskiyanta, wanda suke samu awannan hanyan sunsan gaskiyanta, kungiyanmu ma bance musu nabari ba gudun karsu bini sukashe, nadai cemusu zantafi garinmu, sun sararamin, domin suna ganin girmana, ina rokon Alumman musulmai dasu mana addua.



DUK DAD'INKI DA MIJI 


episode 66

(BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


 Bayan Addua ina roko don Girman Allah don darajan muhammadu SAW, idan kunga abu yasami wata yaruwa mace ko namiji kudena tir da halinsu, kudena tsine musu, kuna mana addua, ni na tabbata lalacewan mu yakaru da zagin da alumma suke mana, kowani dan Adam yana da tarihin rayuwansa, da kuma mummunan kaddararsa idan kunga munyi abu kubimu da Addua,n shiriya, Allah kadai ke shiryawa yakuma bata, mace don jin dadi bazata tagayyara ba bayan tasan zatayi nadama, kowa tanada dalili da jarabawanta, Sannn ga wanda kuke ganin ku bakwa yi, ku kwana kuna godewa Allah daya shiryar daku, ba baiwar ku bane, ba wayonku bane, sannan ba ilmin ku ko dabararku bane tasaku shiriya ikon Allah ne, ku gode masa, i just wished arayuwana ace anhaife ni ta sunna shine babban burina, nawa acikinku kuke nan haihuwar sunna? Shin kintaba daga hannu kin godewa Allah da wannan rahaman? Komin kashin arzikinki akwai wanda yake neman fiye da naki, toh yanzu ni ga ilmin, ga kwalin degreen, ga kudin wanda nanemoshi ta haram, gani da kyau amma ga matsalolina birjik, son bakida kudi kice zaki bijirewa Allah? Don bakida kyau ki bijirewa Allah? Mu koma ga Allah, ina rokon iyayenmu suna mana addua, karkice wayonki zai sa ki tarbiyantar da yarki, kinyi kuskure, yayin dakike sarkanki wani can yana kuncewa, babu abinda yafi wahala arayuwa irin tarbiyar ya mace, mukula musani, ya mace rahama ce, sannan ina rokon adduarku, kumin adduan cikawa da imani, nagode sosai Adda Allah bar zumunci"=

Toh nima dai benaxir na ajiye takardata nayi godiya sosai sannan na rakata ta tafi.

Anan na ajiye alkalamina, laifin danayi Allah yagafarta mana da inda nayi kuskure, sannan kunsani wannan labari its a true life, muyiwa hamdiya adduan Allah jikanta, hafsat Allah bata zaman lafiya, hanen kuma Allah ya kara shiryata yakuma rufa mata asiri yataimaketa, anan nake ce daku makaranta NAGODE NAGODE NAGODEE!!! UBANGIJI ALLAH YABAR ZUMUNCI **SAUDAKARWA** NA SAUDAKAR DA LABARINNAN GA DUKKAN WATA MACE DATAKE FADIN KASANNAN,

**JINJINA GAREKU***** MASOYA NA ADUK INDA KUKE, NAGODE ALLAH BAR ZUMUNCI ***SAKON GAISUWA*** Rufaida Omar Ybk Hauwa jabo Ummu abdul Bingel Adda jummai (umar bappah gombe) Adda farida usman Maryam dankama Juwy ,samha,fatsi,mimi Maryam maleka Queen miemie Hauwa mudi Da wadanda ban ambata ba kuna raina***** Both facebook and whatsapp groups i see you all, and i love u bunch! Saimun hadu nan gaba a littafina me suna

Post a Comment

 
Top