0
DUK DAD'INKI DA MIJI 






 DUK DAD'INKI DA MIJI 

 episode 61

 (BASED ON A TRUE LIFE STORY)

Kallon shi nayi domin alokacin babu tsoro daidai da kwayan zarra kuma bana tunaninsa a matsayin mahaifina, ficewa nayi nabarsa, takaici yaji sosai yayi asara miliyan biyar tunda bai isa yace na mayar masa ba domin kuwa zan iya tona masa asiri, ba karamin mamaki nayi ba ganin yadda yafitar da wannan makudan kudin, koda yake banga laifinsa ba, dan siyasa wannan kudon chicken change ne, mune muke ganinsa wani babbana kudi, tuni nayi hayan gida a gwarimpa nadauko mamana na ajiyeta, duk da albarkan data samin bai damen ba, don ba tausayinta nakeji ba, ina so tayi tsawon rai itada mahaifina suka sakayya a doron kasa, sakayyan abunda sukamin, nasamu admission nashiga gwags naso zuwa nile sai dai banda uban da zanyi gadara dashi lyk most of the children do, ahankali nazama exposed to campus life, anan muje meeting mudawo, wani sirri da bakowa yasaniba shine kungiyar madugu ba karamin kudi ake samu ba, akwai mata manyan mata, matan masu kudi, wanda mazajensu basu zama, zakiga sundau yarinya chick batasan me duniya take ciki ba, su kaita ayi abunda zaayi abata kudi, ni bansan ma meye ni ba, as far as zan kwanta da namiji na kwanta da mace i dont care, kudi ne damuwana, abu daya kuma nasa araina ban yarda nafara son wani araina ba, bana yarda da close relationships, muyi abaje kar mukara haduwa, inkasamu kyautan aids toh inba ka samu ba barkanka



DUK DAD'INKI DA MIJI


episode 62


 (BASED ON A TRUE LIFE STORY)



 Ko da aka kawo hafsat naji ina sonta da kawa ba da mummunan nufi ba, nan najata ajiki don naga kaman bakin ciki da ciwon so na neman zauta ta, ga rashin kulawar iyaye, as time goes by naganta da cocaine, at first nayi mugun mamaki, not even weed but cocaine, ba karamin abu bane domin kuwa nasan illarsa, kuma tayi kankanta wa wannan stuffs din, bama wannan ba yadda take samun kudin shine damuwa na, mai shan cocaine ba karamin mai kudi bane its damn too expensive anmma nayi noticing rayuwa kowa da tarihinsa, labarinsa da alamarinsa kowa da kaddararsa donhaka ban shige mata nayi judging dinta ba illa nabarta tayi rayuwarta yadda take so, ita bata damu da harkan dana keyi ba, ita damuwanta tasha cocaine sometimes taba, nikuma banayi haka muka cigaba da zamanmu da runsa har hamdiya tazo, itakuma namu yazo daya, saboda she seems interested a harkan danakeyi don haka najata, nasiya mota nakuma saya gida a maitama duk wanda yake garin abuja yakuma san maitama yasan how much it worth and kuma nawa nakashe, nazama mai balain kudi, inada yan siyasa sun mara min baya, gyran mata nafarayi don kinsan ance in kana da kyau ka kara da wanka, hanen nazama tauraro a tsakanin magidanta yazama harka da kananun yara baya gabana, hamdiya ce mai yi, tahada babba da yaro, nikuwa a manyanma saikaji kudi kake ganin takalmina, gani da sharadi sai hotel din danace kai namiji sai addua, just saboda jikina yadda nake juyasu kaman yayana,


 DUK DAD'INKI DA MIJI 


 episode 63

 (BASED ON A TRUE LIFE STORY) 



Saidai kinsan duniya juyi juyi ce, cutan jikina yanakan cinyewa duk da shan magani danakeyi, nazama very weak, kuma abunda yake damuna, har lokacin babu acikin yan siyasan danaji sunyi mitan sunada HIV basu sani bane? Ko basu kamu bane? Ko kuma tun asali sunadashi? Tunda bana yarda nasa condom sai daddayan lokuta!, toh mahaifiyata tafara ciwo banso ba, nan nasan yadda nayi nafitar da ita mukaje india, dont think fa soyayyar uwa yasa na kaita a a, so nake tazauna da rai suga sakayya tun a duniya, munje anmata treatment din heart problem din datake dashi, ko da muka dawo babu yanda batayi dani akan nazauna tagayamin abu ba, nasan tarihinta takeson bani yadda akayi ta kasance cikin wannan rayuwan, anma banaso tagayamin alokacin saboda zanju tausayinta sannan na hakura, donhaka nace ta ajiye magananta with time zata fadamun, bincike nayi gidan lawal, na gano yanada mata daya yaransa uku, biyu maza daya mace, mazan yan biyu ne, anma na girmesu, sai alokacin suke gama secondry school, macen kuma tana js3, 


DUK DAD'INKI DA MIJI


episode 64

(BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


Nayi iya tunanina wa zan bata acikinsu domin naji relief na karasa conclusion dina akan nabata ya macen, itace har abada zaiji zafin abunda namasa, nayi tracing makarantan dasuke, haka nake zuwa akai akai, dake secondry school ne babu wani tsaro sosai akan waye mai ziyartar yara, insun tashi kafin azo daukarsu muyita tadi da ita, amilah kenan, yarinyan was soo innocent, ji nayi bazan iya abunda na kudurta ba, nakan zubar da hawaye idan nagansu ganin irin rayuwan dasukeyi, cikin jin dadi da tarbiya da kulawa, wato maza haka suke, yamanta wacce ya hurewa kunne yazo yamata ciki yazo yayi aurensa yanzu da yara, yana dirty work dinsa duk cikin kwanciyan hankali, and how on earth duniya zaayi adalci? Muna makaranta mukazo bikin Hamdiya muka koma, exams dina hamdiya tagayamiki yadda muke ci, biyan kudi mukeyi muwuce, tuni muka fara exams din gamawa nan na nutsu sosai, mukayi muka gama, na tattara nakoma gida naji dadi sosai, don alokacin har mahaifiyar Amilah munsaba da ita, sai dai har lokacin batasan ni waye ba, duk da shirye shiryen ruguza mata gida danakeyi bata sani ba, ran asabar bazan manta ba 26 dec 2015, mahaifiyata tarasu da safe, sakamakon bugawa da zuciyanta yayi, banda yanuwa bansansu ba, balle nanemesu, haka dai mutanen unguwa suka yi mana makoki, naji takaicin rasuwarta ba don tausayinta ko sonta ba sai don bataga abunda nakeson tagani ba, sannan bata gayamun labarinta ba, tamutu tana rokona na yafe mata, oho bansan ko na yafe ba anma dai nasan naji mutuwan, naji mutuwan yadda tuni nakara tunzura domin daukan fansa gun lawal!, zan ruguza masa iyalansa, na ruguza masa gidansa yayansa da matarsa, anan zai tuna abunda yamin,

Post a Comment

 
Top