0
DUK DAD'INKI DA MIJI


DUK DAD'INKI DA MIJI

 


DUK DAD'INKI DA MIJI


episode 54


(BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


Ko ba komi A dalilin shi na shiryu , kuma na soshi, fitowa falo nayi inda Mammy tace Abba na nemana, ya kalleni sannan yace "Dafarko ima godewa Allah da ya ankarar dani acikin kuskuren dana aikata, Tabbas na yarda cewa duk da yaran mu suna bijire mana, mu ma iyaye muna taimakawa gun lalacewan yaran, dakika gwadamin ga yadda kikeso da ban miki dole ba bai dace ace na tsame hannuna daga alamarinki ba, duk da yanamin ciwo, inyi ciwo intashi anma inason ganin gudun ruwanki, gashi nakai yata ga hallaka da kaina, kiyi hakuri, kiyi hakuri yata" kuka nakeyi sosai nace "Abba nine da rokon gafara, bayan ka tufatar dani ka ilmantar dani, ka tarbiyantar dani, ns bijire maka, nabi son zuciya karshe nafada ga hallaka, ka gafarceni abbana, ashirye nake ka aura min kowaye acikin ranka" ysyi murmushi sannan yace "hafsat ai ko ni nakawo son zuciya bazan aura miki danuwa ba yanzu, akwai son zuciya aciki, bayan nabarki kinyi yawan duniya kuma nazo nahadaki da wani? Ai sai sun yarda dakansu" na gyada kai nace "Na yarda ahakan Abba" Nan nabar falon, washegari muka koma kano, Abba yace tunda nafara zai nemamin transfer zuwa kano kawai, na yi mamakin yadda yanuwana suka karbeni hannu bibbiyu ko dayake ba abun mamaki bane, sunaci da sha da zama akasan arzikinsa bazasu butulce masa ba, nan Abba yakira meeting akan duk wanda zai iya sacrificing zai badani, aciki akayi saa Abdullahi ya amince, ashe dana guje shi an aura mishi wata again, tazo ta rasu gun haihuwa, uhm abun mamaki ko? Da ace nazauna nayi ladabi da muna zaune tare lafiya hala ma na haihu, anma na bijire masa gashi nadawo back to square one, yanzu anyi fixing aurenmu nan da one month, dakyar akabari nazo bauchinnan, saboda case din hamdiya yasa mammy taroki Abba, for now am born again nabar shaye shaye nabar komi, thanks to jalal wanda suna zaune da matarsa right now, My lesson of life shine ina gargadin yanuwa na mata karki sake ki bijirewa iyayenki, ko da wuta sukace kishiga my dear sister jeki shiga, yafi balai da matsifa da zaki tarar, nd to parents don Allah kurinka daga kafa wa yaranku, kudena tur da yaranku ko kumusu baki bakusan halin da zasu fada ba, nagode sosai Da nasamu wannan daman don na fadi darasin rayuwata Allah sa masuyi ko masu shirin yi zasu dena!" Nima benaxir danake rubutawa nace "ameen, Anma hanen fa yaushe zatazo tabada nata?" Ta yi murmushi sannan tace "inaga hanen sai gobe ko jibi"


DUK DAD'INKI DA MIJI 



episode  55

(BASED ON A TRUE LIFE STORY) 

Hanen ce zaune tana murmushi "Adda bena ba karamin dadi naji ba da zaki rubuta labarina" na kalleta sannan nace "kinga kece ta karshe, Da ni da yan makaranta na muna nan munzuba kunne don jin labarinki, sannan kuma mekikeson ki fada mana?" Ta gyra zama sannan tace

"Wato Adda nasan kashi casain acikin dari na yan makarantanki suna min kallon ballagaza, tunda a labarin da hamdiya ta bayar ni na tsoma ta a mummunan hanya, labarin hafsat ma duk da tafara a gidansu zama dani yasa takoma ruwa tsundum, sannan nasan kowa na son jin nawa fannin labarin, tunda ni nayi sanadin kawayena, ni waye nawa sanadin?, uhm!, iyayena sune sanadina na duk lalacewata, banyi sa'an iyaye ba, da ba don annabi muhammadu SAW ya umurce mu da muyi biyayya wa iyayenmu ba sannan don da bazai iya tsinewa iyayensa ba dani na tsinewa nawa, iyayena su suka ja ni cikin hallaka, mahaifiyata tajani, mahaifina kuma ya tsunduma ni, iyayena su suka lalatani, suka janyomin wulakanta, tozarta a idon duniya, da ace zan iya hakura dasu dana dade da hakura dasu, sai dai yazanyi? Su suka haifen, bana fata kowacce mace a fadin duniyannan, tasamu iyaye irin nawa, Musamman UBA, sanadinshi na zagi Da Namiji, Namiji abun tsoro ne, sannan Abun jigata ne, Allah yarabamu da sharrin maza"

"Kin daure min kai, nasan bani kadai ba hatta kowa dake karanta wannan labarin kin daure masa kai, meye haka iyayenki suka miki kike ambatonsu haka kike kaskantar dasu haka?, shin ko kin manta babban laifi kike aikatawa ne?"

"Adda Bena!, ae laifi ne agunki anma nasan agun Allah bazan samu zunubi akan wannan kalmar dana fada ba, saboda abunda sukamin yaci ace na dau wuka na dabbara wa kowanne acikinsu"

"Waiyazubillah, Allah yarabamu da sharrin zuciya, ina mai rokonki da ki gaggauta sanar damu waccece ke? Sannan meya sameki? Wani irin jarabawa kika fuskanta?


DUK DAD'INKI DA MIJI


episode 56

(BASED ON A TRUE LIFE STORY)


 " Sunana Hanifa lawal, Haifaffiyar cikin gwagwalada, bansan meya faru abaya ba, anma natashi ne ni kadai agun mahaifiyata bani da wa banida kani, sannan ni kadai mahaifiyata take riko, banda mahaifi, idan na tambayeta ina mahaifi na, takance min ya rasu, sai dana shiga primary 5 a surutun duniya naji labarin cewa , mahaifiyata tayi soyayya da mahaifina ne, kuma sun bukaci suyi aure anma iyaye sun hana, ayadda naji labari iyayen mahaifina sunada karfi wanda suke kyankyamin iyayen mahaifiyata, sunso suyi aure amma aka hana agarin haka suka yanke shawarar su gudu su bar garin, cikin ikon Allah suka gudu daga gombe suka koma abuja cikin gwagwalada, wuya, talauci haka suka rayu alokacin ana marmarin juna, har rabo ya gifta, karki manta baa daura musu aure ba, mahaifiyata tana samun ciki, babana yace sai ta zubar itakuwa tace babu wanda zai sata zubar wa, sanadin haka yatafi yabarta, tahaifeni, tana zuwa gidan masu kudi tayi aiki ahaka take ciyar dani, abuja gidan bariki bawanda yadamu yasan metake ciki, babana ko ince miki lawal bai kara waiwayo mu ba, har nagama primary din, don ni danasan gaskiya ma bantaba gwadawa mama nasani ba, sai ta zamto tana bani tausayi, anma fa talauci na cin mu, gashi taki komawa gombe tushenta, inda iyayenta suke, nagama na shiga js1 nagama naje 2, anan nafara fuskantan tashin hankali, domin ko ashirin nace inaso mama saita kallen tacemin nashiga duniya na nema karna kuskura na dameta, in takaita miki yazamo mama tazauna agida tadena fita saita cemin naje nanemo kudi duk inda yashiga yafita, tun ina bi gida gida ina neman aiki, kawai nahadu da wata mary a anguwan tafara kaini shago ayi romancing dina aban dari ko dari biyu, wata rana ina zaune wani yazo shi yasamen nine Hanifa? 

Nace ae, sunan mahaifiyata fa duk nafada masa sainaga yakoma gun motan daya fito, wata mota ce wanda azamanin mallakata sai wane da wane, can kuma saiya dawo yace min nazo inji maigidansa, naje ciki a sanyaye nashiga, mutumin yadan manyanta kadan bazai wuce 38 haka ba, yanata faraa yana min tambayoyi ina amsawa, can saiyaje muje yasiyamin abubuwa, nikuwa murna nakeyi, yau zansami abun kaiwa mamana, mukaje yazuba min shopping din hauka sannan yawuce dani hotel, bandamu ba tunda naga yanada kudi nan fa ya lallabani yayi disvirgining dina, tsabar gigicewa kaini anguwanmu sukayi suka ajiyeni da kayan suka fice, Adda guess waye? Lawal! Mahaifina dai, ya sadu dani, don siyasa, don yaje gun malaminsa ko ince boka sukace yaje yasadu da yarsa, ya bincikoni yayi aikinsa yayi gaba,

Post a Comment

 
Top