0
DUK DAD'INKI DA MIJI 






DUK DAD'INKI DA MIJI 


episode 52


 (BASED ON A TRUE LIFE STORY) 



Toh haka na gama kuka na basu dawo ba, namike nafice don zuwa gida, luckily naje bansamu su hanen ba nayi wanka kawai na kwanta, bacci anma ya gagara zuwa, ina zaune ina jiran wayansa anma shiru abunda bai taba yiba kenan, nan hankalina yatashi duk na rude, kar dai yarabu dani? Nadau wayata ina kiranshi bai dauka ba karshe naji switched off, Ranan haka na kwana idona biyu babu irin tunanin da banyiba, na jigata sosai, na dauko taba zansha nakasa, haka sauran cocaine shima sai naji wani iri bazan iyaba, gani nakeyi tamkar yana kallona na tattara naje na wurga a kwandon shara, nakoma na zauna, washegari ma nagagara fita lectures, ina makale a daki slightest karan waya naji zakiga na dauko da gudu thinking shine anma shiru, bugun zuciya ne kawai bansamu ba, sai karfe daya naji kira ina dauka naga shine dasauri nasa a kunnena ina wani irin numfashin wahala, tamkar zakanya tayi gudun samun abinci, ya yi sallama na amsa anan cikin sanyin murya yake cewa nafita ysna kofan hostel, hijabi na saka nafice yana sanye da shadda yayi balain kyau ga gemunsa akwance yasa hularshi tazauna akan gashin daya dan tara, na risina na gaysheshi sannan na tsaya agefe "Kiyi hakuri kinjini shiru, wallahi inna ta ce takwanta ciwo toh dake a gigice nabar gida nabar wayan a gida bankoma ba kuma sai yau" a zuciyata nan nagane cewa hala deena(matarsa) ce ta kashe wayan, cikin tausayi na tambayi jikin nata sannan nace muje na gaysheta, kamar yace a a yace "toh muje din" na koma ciki nayi wanka nasa atamfa ta riga da skirt sannann na saka hijabi ko powder bansaba inbanda turare dana fesa, dama sna zafi balle nasa wani mai ontop of oily skin dina,



 DUK DAD'INKI DA MIJI


episode  53


 (BASED ON A TRUE LIFE STORY)


 Nafito yana cikin motan nashiga muka fice, ahanya nace ya tsaya nasiya fruits, ina karba yabiya nayita godiya bai kulani ba, duk hankalinsa atashe nan nafara kokarin kwantar masa da hankali, muna isa national hospital dakin da aka kwantar da ita muka nufa, gabana ya tsananta fadi, ya bude dakin muka shiga dakin mutane hudu ne kaina akasa na tsuguna ina gayshesu, cikin sanyi suka amsa yayin da daga gefe naji muryar da bazan manta ba wato deena "Meya kawoki?, bin mijin nawa a gari bai isheki ba kinbiyosa asibitin?" Ta fada tana kokarin mikewa

"Ke banson yarinta meye haka, kibari ta gayshe ta mana kawai" yafada cikin bacin rai, jin haka yasa ta harareni ta koma tazauna hakan ya tabbatar min da cewa Yafi karfin gidansa, tana zaune akan kujera ta tsura min ido can cikin karamin murya tace "Deena ita kike fadamun?" "Itace inna"

"Toh ai batayi kama da mai shaye shaye ba"

"Inna duk burga ne" wani harara da ya sakar mata tayi shiru, yace "Tazo gaysheki ne fa inna"

"Da Allah kamin shiru kafin yanzu ranka ya baci, inbanda rashin godiyar Allah me deena ta rageka dashi? Da zakaje ka dauko mata karuwa a matsayin abokin zama, hala ma ba aurenka zatayi ba yaudaranka takeyi, toh wallahi bar ganin ina gadon asibiti ko bayan raina ban yarda ka auro wa deena wannan marar kamun kan ba" ayadda take maganan bazaka rantse marar lafiya bace, gabana yana fadi hawaye yafara zubomin a ido, yayinda yace "Inna bata karuwanci" "Anma tana shaye shaye ai" shiru yayi yace min "Taso mutafi" na goge hawayen idona na ajiye ledan nafito, deena cikin sauri ta dauko ledan ta biyoni dashi ta wurgamin

"Ba mu miki kama da matsiyata ba, " hawaye na bin idona, idona yayi jajur har muka shiga mota, bai iya magana ba sai da muka kusan isa makaranta "Kiyi hakuri zansan yadda zanyi na shawo kanta, mata na kuma kimata hakuri, duk kushi ne" nayi shiru domin har raina babu komi din, kowani wulakanci nagani arayuwata nina jawowa kaina!, Yana saukeni yatafi, nashiga ciki nayi kuka sosai, anan nasamu Hanen tana cemun Hamdiya bazata dawo skul ba iyayenta sunce aure zasu mata, abunda nafada yabawa hanen mamaki don ita cewa takeyi zata zuga hamdiya ta gudu nace mata "ko da wasa karki sata ta aikata kuskuren dana aikata, tayi biyayya wa iyayenta shine babban gata, koda kuwa zata fuskanci tashin hankali bazai kai yadda idan ta bijire musu ba, har yanzu ina ganin sakamakon rashin biyayya wa iyaye arayuwata" daki na nufa, ranan banyi bacci ba duk da munyi waya da Jalal anma yadda yakemin magana nasan ba dai dai yake ba, washegari yakirani yasanar dani mahaifiyarsa ta rasu nayi jimami sosai shima duk da tawakkalinsa ya girgiza, haka naje nayi gaysuwa wannan karon deena ko kallona batayiba uhm ashe tasan meta shuka, bayan kwana bakwai jalal yazo yake ban hakuri, akan nayi hakuri zai hakura da nemana, wasiyan mahaifiyarsa ta karshe shine ko zaiyi kishiya wa deena karya kuskura ya aureni, ba da yawunta ba, alokacin jikina yana bari anma haka na danne yabani hakuri yace zamuna waya yatafi, Adda bantaba sanin son danake wa jalal yayi tsauri ba,kuka nakeyi raina kaman zai fita, don inaga ko sanar dani mutuwarsa akayi iya kukan dazanyi kenan, har gadon asibiti na kwanta anan Hanen takira Mammy inda Mammy ba shiri ta taho abuja, abun dayafi komi ban mamaki shine tana tahowa abba yabiyota, asibiti sunce inada ciwon zuciya, DUK ADALALIN DA NAMIJI!, sunkuma ce inban dena tunani ba zan iya rasa raina, bude idona nafarko naga Abba na sainayi zaton mafarki nake, hakan yasa narufe nakara budewa, shidinne dai yana rike da hannuna bansan lokacin dana fara kuka inacewa "Abba, Abba kayi hakuri ka yafeni, Abba bazan kara bijire maka ba!" Shima hawayen ke zuba mishi anma baice komi ba, ganin hawayem Abba na ba abune mai sauki ba don innataba ganima toh na manta, Anma meyafi iyaye dadi?, da taimakonsu na samu karfin jikina cikin sati daya, aka sallamen, dama a gidan Abba na abuja suka sauka nan muka wuce gidan acikin gwarimpa, nayi sallah na zauna ina godewa Allah da yabarmin raina, sannan naroki Allah yakara shiryar dani, donkuwa Jalal duk da ban aureshi ba yazama darasi ga rayuwata

Post a Comment

 
Top