DUK DAD'INKI DA MIJI
DUK DAD'INKI DA MIJI
episode 47
(BASED ON A TRUE LIFE STORY)
Hajiya jamila sunanta kenan, bazawara ce bata da yara, sai dai alokacin danaje aurenta saura wata hudu, haka nagama idda ta, alokacin nakoma ga Allah, Mammy har asibiti ta kwanta ciwo anma Abba yace duk wanda yakara masa maganata zai bar gidanshi, sometimes na kan zauna nayi tunani anya Abba mahaifina ne?, sai dai yazanyi mahaifin nawan kenan, taurin kai da kafiya uhm, ganin Abba bai da niyyan karbata yasa malam salisu yace nayi waec, da neco, hade da jamb, ina shirin yi hajiya jamila tayi aure, hakan yasa nakoma gidan malam salisu yakawo mai aiki shikuma yakoma kwana dakin abokinsa, haka na zauna har na gama waec kuma dama naci jamb, yasiya min waya nima nadan fara shiga gari, na dan saba da mutanen anguwan, dai dai kulawa ina samu haka zalika mammy na turamin kudi tagun malam salisu, banda damuwa daya wuce na mahaifina, haka result yafito nasamu admission a gwags, alokacin na koma asalin hafsat dita, don babu ma hanyan shaye shaye ba ruwana da kowa, inasamu malam salisu yace na wuce nakoma hostel, actually yayi kokari, tunda yakusa kai wata goma agun abokinsa yabar min gidanshi, nashirya nakoma hostel daga nan nake zuwa lectures nadawo, dakin da aka hadani ne nahadu da hanen, dafarko jinin mu bai hadu ba don haushin ta nakeji, naga taci wanka tafice bata dawowa sai asuba, tanada faraa da shigewa cikin mutane, nikuma kinsan yadda natashi yahadu da banson mutane, zaki ganni simi simi haka
DUK DAD'INKI DA MIJI
episode 48
(BASED ON A TRUE LIFE STORY).
Dakyar dai tasamu muka fara gaysawa, har muke dan cin abinci tare, har lokacin Abba na yaki kulani, Mammy kuwa turomin kudi take ba sassauci, na zama a kaf family dinmu ni ce mace tafarko da ta taba auren bare, ni ce mace tafarko data tabayin jamia, ashe Abba yayi niyyan sassauta min, jin naje jamia yasa yakara daukan dumi, donkuwa har wa malam salisu yadena yiwa magana, ko na kirashi baya dauka inya dauka kuwa maganganu marasa dadi ne, yarinka tur da halina kenan, wannan yasa na ajiye batunsa agefe nafara karatuna, ganin hanen yadda take rayuwa bata bari damuwa ya isheta, nan zata shirya tafice party, wataran tace muje na amsa, riga da wando nasa anma ban sababa donhaka duk a tsarge nake, dama kafunnan tasa naje nasa human hair, brazillian ma kuwa don ita tabiya, muka fice karfe goman dare acikin wani motan saurayinta, muna isa tashiga na bi bayanta sai dai karan wakan yamin yawa, bansaba ba, hakan yasa nafito nazauna awaje, har abokintan yace muje ya bude min mota, nabishi na zauna abaya shima yashiga ta dayan gefen yazauna, A gaskiya, a zahirin zance mace wacce ta taba aure tasan dadin aure, bi maana bazawara tanada kasada da saurin fadawa tarkon shaidan fiyeda budurwa, domin budurwa ta iya yiwuwa bata san mene ba, bazawara kuwa tasan namiji, shiyasa nake shawartar iyaye masu yaya zaurawa su tattara sukai makaranta can wani duniya, agaskiya sukara tunani domin mugun hatsari ne, kamar yadda yafaru dani zaman da mukayi mu biyu shaidan yazama na uku, na biye mishi don dama ina hannu ne. Abun kunya acikib mota na bada kaina, har muka kammala Hanen tafito muka wuce gida, tundaga ranan muka fara zuwa clybbing kullum tun bansaba da hayaniyan ba har na saba, haka zalika shigata ma tadawo ta karuwai, abokin hanen shi mukayi deal dashi yafara kawo min su cocaine, ranan da yakawo kaman na masa sujjada dan murna, haka bana zuwa lectures nake yin abuna hanen kuwa ina kallonta take kawo yanmata wani lokacin maza, kowa nata, ni am not that desperate once in a while dai haka, rayuwata taci gaba da tabarbarewa ne alokacin da malam salisu yawuce Malaysia yin wani course nadawo nikadai gatan kaina, babu mai takamin birki, wasa wasa sai gani nine da shan taba! Uhm waiyazubilah
DUK DAD'INKI DA MIJI
episode 49
(BASED ON A TRUE LIFE STORY)
Bariki na tayi nisa, banda Mafadi idan anyi hutu sai naje kano gun familyn mama na, anan nake nutsuwa tunda har lokacin Abba na yaki karba na, har na kammala aji biyu, a aji biyu aka kawo mana hamdiya don bazan manta ba, munyi niyyan renting gida toh bamu samu ba akusa da makaranta yasa muka hakura, duk da cewa ni da hanen ba wani shakuwa mukayiba, da hamdiya tazo sai suka fi shakuwa tare, nakanyi rayuwata ni kadai tym to tym muke zama dasu. Rayuwata babu abinda ya canju saima karuwa, nakanyi ciwo tym to tym da zaran nayi nakanyi quiting shaye shaye na for some time, donma kullum am on drugs da na dade da mutuwa hala, saboda abunda nake sha yayi min yawa,, second semestern mu sai Allah yasa a azumi ne, zamuyi axumi a skul, tuni na nutsu as usual kinsan duk wani dan bariki na kokarin nutsuwa a azumi, har nake sanya hijabi idan zani lectures, life challange dina started wata rana i think anyi goman farko ne, ina daki, hanen da hamdiya sunfice wata tayi knockn tace ana nemana a kofar hostel, jin haka kuma rigan baccine ajikina, dawowa na daga asham kenan kawai nasaka hijabin dana cire nafita, ganina yasa yafito daga motan, tun daga nesa nake kokarin ganeshi anma bansanshiba, dogo ne sosai, i dont even know yazan miki bayani, da taimakon hasken wuta na kalleshi, na kau da kai domin shima kallona yakeyi, kuma for the first time in my life tunda na bijirewa iyayena that na kalli idon namiji na kawar da ido, wani iri naji tundaga saman kai na izuwa yatsuna kafata yayi sallama yana murmushi, muryanshi sanyaya, kuma ahankali yake magana inba kin nutsu ba baxaki gane mai yake fada ba a kallo daya dana masa naga irin kyau da Allah yabashi, yana da gemu wanda ya hadu da sajensa, idonsa dara dara kaman na mai jin bacci, da dan dogon hancinsa, uhm alokacin don kar na yaudari kaina ne danace balarabe ne, sai dai i leta knew bafulatanin gombe ne, yana da dan haske anma ba can ba, ina wasa da yatsu na yayinda nake kallon motan da yazo da ita, joker ce, kuma ta tsufa sosai, ya katse min tunanina ta hanyan cewa "ina wuni hafsat?" I cnt actually remember wen last naji ankirani hafsat, tunda na koma ceecee, "Lafiya lao" na amsa mishi har lokacin kaina akasa.
"Zakiyi mamakin kiranki danayi kuma gashi harda sunanki, Sunana Jalal, and naganki ne jiya lokacin kinfito daga sisters forum, na sa aka nema min ke, gashi luckily enough nasameki" Nayi shiru gabana na fadi, wanda ni kaina na rasa dalili
"Na zo ne da kokon barata, na zo ne da alfarma ko zaki karbi bukatana, i believe keba yarinya ba haka zalika nima, donhaka let me cut the crap, naganki ne ina sonki, so kuma bana wasa ba na aure"

episode 50
(BASED ON A TRUE LIFE STORY)
Gabana yayi mummunan fadi domin tunda na shigo makarantannan babu wanda yataba zuwa min da magana shige irin nasa, duk da cewa zuciyata tafara sonshi d moment i saw him,kamar yadda tafara son A.j kar na maimaita similar kuskure yasa nace masa zanyi tunani, yace toh sannan mukayi sallama, na so yakarbi numban wayata anma bai tambaya ba, daya tafi naji wani iri, wat if bai kara nemana ba? Nace mishi yaban sati, duk na damu, ranan kwana nayi ina tunani harda sallolina saboda nafada sonshi, ina sonshi naji bazan iya hakura ba kuma, bai kara dawowa ba, gashi inbanda sunanshi bansan komi nashi ba, hatta joker sa nemanta nakeyi ko zangani anma shiru, na jigata domin har gizo yakemin sainaga kaman shi, randa nacika sati daya cur ina zaune a daki naga sabon num, da kamar bazan dauka ba jin ankira na biyu yasa na dauka, yayi sallama cikin muryarsa wacce ban manta dashi ba na amsa "Hajiya Hafsat kince sati daya, yau sati daya cur don haka nakira naji amsa ta" Nayi shiru sannan nace masa "inada matsaloli aba-" ban karasa ba ya katseni da cewa "ba past dinki nake nema ba, futurenki nake nema, nasan da past din naxo ahaka" wannan kalmomin suntaba min rai domin kuwa na tuna da maganan A.j dayake cewa wani mutum ne dan gidan mutunci mai neman mutunci zai auri mace irina bayan yasan halina, sai dai da dalili don haka naja numfashi nace "baka san komi ba" "Toh bana so nasani!, what i want is you" Nayi shiru sannan nace "anytime kaji bazaka iya zama dani ba, kabani heads up", yayi shiru sannan yace toh, Adda nan historyn soyayya ta da Jalal yafara, jalal mutum ne mai sanyi baida hayaniya, ko waya mukeyi magananshi daya biyu ne cikin sanyin murya, ga rikon addini da ibada kwata kwata social life bata gabansa, hakan yasa nake rayuwa ta aboye, don gudun bacin ransa duk da baitaba min magana ba alokacin anma nasan angayamasa halina, daga baya nake sanin yana da mata, duk da baikai talatin ba, sannan kuma daga baya nagane cewa ba karamin mai arziki bane, zuwan dayamin da joker yazo ya gwadani ne, Duk inda namiji yakai Adda jalal yakai, tausayi, sacrifice, kulawa, gudun magana, sanin yakamata, mutuntawa, har lokacin bantaba hadashi da hamdiya ko hanen ba, don kunya zanji tunda nasan ba shigan arziki zasuyi ba, Jalal kuma acikin maza kaso dari toh bazaa samu irin sa uku ba, the guy is super complete, i felt save, don alokacin naji kawai inaso nayi aure, har akayi sallah ina abj, mukayi exams muka koma gida, a can kano yake zuwa gidan sis din mammy dana ke zama, dukkansu bawanda ya kushe shi, kowa yabonsa akeyi gashi familynsa sannanu ne, nan nafara neglecting shaye shaye domin ina tsoron randa zai kamani cikin maye, dama taba bawani sha nakeyi sosai ba tuni shima na ajiye anan nasan cewa son dana ke masa bantaba yiwa wani da namiji ba, yanada mugun kyauta bantaba tambayarsa abu ba zakiga yasiya yakawo, did i tell u cewa all that while yatsana bai taba rikewa ba? Wanda hakan yakara masa daraja da mutunci a idona ,
DUK DAD'INKI DA MIJI
episode 51
(BASED ON A TRUE LIFE STORY)
A sannu sannu muka koma school , wannan karon munsami flat awaje, kowa da dakinta mu uku, muka fara lectures, duk da banisa hijabi nadawo sa kayan mutunci, don tsoron kar mu hadu da jalal ahanya, tun randa yafara ganina da riga da wando gurina yazo anma ganina da wannan shigan baimin magana ba yashiga mota yafice, kuma har yau baitaba min maganan ba, inya kamani ina laifi baya min magana, tafiya yake yabarni saidai yakiran daga baya muyi tadi kuma bazai taba kawo wannan topic dinba balle nasamu chance din bads hakuri, actions dinnan makes me feel guilty of myself, toh daga lokacin nadawo shigan kirki , su hamdiya ma inbaa gida ba bama haduwa kan hanya balle aganmu tare Kamar kullum nafito lectures, kowa na neman hanyan ficewa masaukinsa, nayi hostel zanshiga domin karban littafi nayi note wata mata da wata student wacce nagane fuskanta suka nufoni, fara ce tas matan, tana da kyau yar cas da ita, kallon da takemin yayin da suke karasowa shi yaja hankalina, student din tace mata "gata nan" sannan tafice, kallona tayi daga sama har kasa, sannan tasa hannu ta wanka min mari tana huci, marin shi yajawo attention din mutane gun yafara cika, ko batayi introduction ba yanzu nagane wacece, matar jalal, ta kalleni tanunani da yatsa
"Zan iya jura idan ke kamilalliya ce, kinada asali kinada kuma hankali da mutunci, anma bazan jura wata gidahuma, kilaki irinki ki makale wa jalal, for crying out loud who are you? Kina ma da hankali kuwa? Meya hadaki da jalal?" Nan da nan surutu yacika gun, idona akasa nayi murmushi sannan nace "Naji duk wannan batu naki, naga kuma gaskiya acikin maganarki, sai dai dani dake yazamuyi da kaddara?, ko kin manta DUK DAD'INKI DA MIJI sai ya miki kishiya!, ni dinnan dai ni zan shigo natayaki zama sai dai kiyi hakuri dani" Katseni tayi kaman zata haukace "karya kikeyi!!!!!! Nace miki karya kikeyi!! Mijina baya karuwanci, ke kinsan me kika mishi!, mijina kallon mata bayayi, mijina babu ruwansa duk kece makiran, toh wallahi kisani, gidana yafi karfinki, kitabbata inzakizo kitaho da shirin mutuwa, jaka banza dakikikiya irinki, toh ko bai gayamiki bane bai sanar dake mahaifyarsa bazata karbeki ba? Ni yar uwarsa ce, munanan jini da fata, a inuwa daya haka zaki ganmu ki barmu" gyra gyale na nayi wanda ke shirin fadi na juya nayi hanyan hostel inajinta sai zagi takeyi, ban kulata ba, shigana nasamu basu dakin donhaka nazauna agefen gadon ina tunani duk moments din da muke tare dashi, yadda yake lallabina, da furucin bakinsa masu dadin sauraro, wayata na dauko ina duba last text dinsa daya ke cewa " farkon haduwana dake kika shiga raina, kuma luckily enough na miki tayin kaunata, kika amsamin hannu bibiyu, wannan soyayyan bana tunanin zamu rabe infact babu rana saidai mutuwa ta rabamu, kullum kina barina cikin tunani da shaukin sonki," Nashiga wani hali, yanayina duk yacanja, sai nazari nake , idanu na duk sun juya, hawaye nata zubowa babu sassauci , duk sanadin soyayya, zan iya hakura dashi???? I blv you know that moment of love if kina tsananin son mutum ko tunaninsa kikayi sai gabanki yafadi

Post a Comment