0
DUK DAD'INKI DA MIJI 






 DUK DAD'INKI DA MIJI 


episode 41
 

 (BASED ON A TRUE LIFE STORY)



 Mammy tashigo "Ina zakije?" "Zan bar masa gidansa, tunda baya son farin cikina" Mari mai kyau tasakar min a fuska, don saida yatsunta suka fito, taja tsaki "a jahilci irin naki, namiji zaki yiwa wannan sacrifice din?, angaya miki namiji ana masa haka ne?, inbanda hauka irin naki, har zaki bar gydan iyayenki akan namiji, toh ki sake tunani, gwara kije ki roki gafaran mahaifinki" tafice , kuka nayi sosai, sai shigowan Malam salisu nagani yace nasameshi a falo, inashiga yana zaune shida Abba nan yace "nasamu da taimakon yanuwanki mun roki mahaifinki, ina shi wanda kike so ki aura din? Kije yazo gyda in dagaske yakeyi a daura muku aure" ji nayi kaman ansani a aljanna, na mike dasauri na nufi dakin mammy wayanta nadauka nakira A.j nake sanar mishi cikin farin ciki ya amsa. Ran jumaa aka daura auren mu inda anan aka kaini gyda na dake sharada, duk da komi yazo ba shiri kudi na da daraja, familyn A.j cikin kudi suke haka zalika nima, nan fa surutu yafara zaga gari, Abba na yana auren dangi yanzu yakarya akaina, kowa ma zai iyayi da wanda yake so, mutuwa ne kawai abba na baiyiba tsantsan bakin ciki, ko walima baayi ba natare, kayan aure ma sai daga baya zasu iso,


DUK DAD'INKI DA MIJI


episode 42 


 (BASED ON A TRUE LIFE STORY)


 Duk wannan bai dameni ba, inbanda lalle babu abinda nayi don alokacin babu lokacin wani gyra, shekarana 17 a lokacin muna hutun ss1, zamu shiga ss2, komi yafito ajikina balle ace nayi karama, Daga nan kuma na shiga Rudin rayuwa, jarabawa wacce bana fatan ko wacce mace ta shiga, wanda ni nadauka a matsayin rashin bin zabin iyaye ne yajawo min, 

Daren farko na nuna zakewata akan gado, abunki da yarinta, gashi bandade da rasa budurcin ba balle ace nakara rufuwa, washe gari haka naga fuskan A.j babu walwala duk da nagaya masa labarina yasan da haka ban tsammace haka ba, nadai share nafara biyayyan aure, daga baya shima ya share, Muka shimfida soyayya, soyayya mai tsabta da abun kwatance, kullum yana makale dani, inzai fita gun aikinsa wanda a company din babansa ne, baya awa daya zaki ga yakirani, nashiga duniyan dadi da aljanna, inada son jiki hakan yasa kullum ina makale dashi, wataran inbai dawo ba a yarinta na direba nake sawa yakaini office dinshi nabashi abinci nadawo, mufita shopping tare so many memories, bacci bama taba raba shimfida, suddenly naje bikin wata cousin dina a gidansu mammy, alokacin wata na shida da aure, munyi da

 A.j zaizo yadaukeni naji shiru, nakira wayansa bai dauka ba nahau adaidai ta nawuce gida, nayi mamakin ganin motarsa a gida anma dai nashiga, karin farko naga kaya a falo nahau tattarewa na nufi daki, Adda haihuwar uwa na tsinci mijina da wata suna aikata alfasha, nayi salati naja jikin bango na fadi kasa, a gigice ta tashi tafara suturce jikinta tafice, abun mamaki ba musulma bace, daga gani inyamura ce, na ajiye kayan a saman gadon na nufi dakina, na cire kayan jikina nasa rigan bacci sannan nanufi kicin, ina girki ina kuka na dafa masa taliyan da yace zai ci na ajiye a dinning nafice, kuka nayi sosai a zatona 

A.j zai zo yafara rokona nan naga sabanin haka, don kuwa cin abincinsa yayi yashige daki, naje nasameshi tareda cewa inada magana, hannu yasaka min "Karki dameni, inkinga bazaki iya ba kiwuce gidanku" Anma me, Adda bazan iya zuwa gidanmu ba, Abba yace nasaka araina ko meya sameni karna dawo masa gida haka yanuwana, dawani ido zanje musu illa yawuce nayi hakuri? Toh mafarin matsalata kenan (Kuyi hkr, jiki da jini, zakuna jina dai insha Allah)

Post a Comment

 
Top