DUK DADINKI DA MIJI
DUK DADINKI DA MIJI
episode 43
(BASED ON A TRUE LIFE STORY)
Ganin ban ce komi ba A.j yadawo dani baiwa acikin gida na, sai yadauko karuwarsa yadau abincin dana masa suci su kwanta, nakanje makaranta nadawo da yamma sai yadawo ruth ta mallake min gida, babu wanda yasan halin danake ciki hatta mammy na, ranan suna daki da ruth Addarsa tazo , nakarbeta hannu biyu anma a tsarge nake, yadda kikasan ni zaa kama ina laifi, tace yana ina nace barin kirashi, kwankwasa kofan nayi tayi bai bude ba, nadawo nace hala yana bacci, hankalina duk a tashe don kuwa insungama ba kunya tare suke fitowa, aikuwa tafara kallon film naji hannun kofa alamun zai bude, da sauri naje na tsaya, yana budewa na tunkudeshi muka koma ciki, hannu yadauka yakaimin mari, rike da kuncina na ce mar Addanka tana falo, inkuma zaka iya fita ahaka toh
DUK DAD'INKI DA MIJI
episode 44
(BASED ON A TRUE LIFE STORY)
Kallona yayi ya kauda kai, tare da umurtar ruth karta fita, yasa kaya muka fito, if kiga ganmu zakice we are the best couples ever, harta tafi yana makale da hannuna, tana fita ya wurgani kasa yafice, nayi kuka sosai, ruth tana tafiya nayi dakinsa, yana wanka, donhaka na zauna jiransa, wayansa na dauka nahau dubawa, bincike na yakaini facebook chatting din batsa sukeyi da yanmata kaf list dinsa mata ne, nayi nadaman auren A.j don nasan dan uwana na jini bazai yi garajen yin wannan taadar ba, yana fitowa yana goge ciki kaman baiga mutum ba, nashare hawaye na sannan nace " idan akwai abunda na maka kake sakamin da wannan wulakancin ka gayamin saboda nasani, zandena insha Allah" Baikulani ba harsai da yasaka kaya, sannan yace "luk, ki bude kunnenki kiji don bazan maimaita ba, ae ada ban soki ba, nasan ina sonki ne a kalma ta baki harna aureki don cimma buri na, anma yanzu adole nake zaune dake, bani da kwararran hujjan koranki ne, karkiji nace inasoki ki zata asalin SO, a a ko kadan, agabana keda yaruwarki naji kun zage wani, akan cewa baikai ya tsaya dakuba don kunfi karfinshi, wannan dinnan babban abokina ne, saidai bai da magana, baki san mutum ba karkiyi judging dinsa, don kin raina arzikinsa?, ki gode Allah nafito miki a asalita, bantaba sonki ba tunda nake son shaawa nake yi miki, kuma na kawar, wannan yazama darasi ga mata irinki masu wulakanta maza don sunga basu da arziki ko kin raina arzikinsa, kisani cewa namiji zai iya gwada miki yana sonki har na tsawon shekara ashirin batare da ya taba jin sonki ba, illa sai dai don ya cimma burinsa, kibar raina namiji, namiji zai iya kaskantar dake, ya wulakantaki ya cireki daga mutum yadawo dake tsumma idan yanaso saboda ku mata kunada rauni, kin raina abokina kin zageshi dalili kenan musababbi dayasa na lallabaki kika bijirewa iyayenki na aureki, sannan zan musguna miki na lalata miki rayuwanki na sallameki, inbanda jahilci irin naki, wani namiji nagari ne zakice masa kintaba shaye shaye, sannan wani banza acan yayaga miki budurci sannan ya aureki?, kin sha giyan wake ne kika yarda danace bakomi?, nima nazo kwasan rabona ne, don haka kibari nagama biyan bukatata sannan na sallameki kuma gashi Abbanki yace karki koma gida, ayya sai hakuri" saukan dutse naji, domin nayi nadaman tambayansa balle naji wadannan kalmomin, ai wannan gwara na yi ta ganinsa da matan akan yagayamin wannan kalman, A.j yacuceni ya yaudari Son danake mishi, Yaci Amanata, ina kuka na nufi dakina banyi bacci ba ranan, kuma tundaga ranan wulakanci yakaru, sai kawai nadena zuwa makaranta don kullum saina hadu da yan gidanmu, ni da nayi aure yadace suga ina kiba but sunga inata baki ina ramewa wasu sunzata ciki ne araina kuwa nasan damuwata, Ruth ta mallake min gida, agabana suke mashaa, na girka musu kuma suci, da zaran nayi taurin kai A.j yanemi bulalarsa yamin shegen dukan da babu mai cetona, saina kwana ina jinya, har dakina ruth take zuwa tayi abunda takeso tadibi abunda takeso hatta mammy na boyewa halin danake ciki yana daya daga cikin illan rashin yiwa iyaye biyayya, don da zaran kinsamu matsala bazaki iya fada musu ba balle su taimaka miki, Wata rana naji bazan iya ba don bana iya bacci, ga tashin hankali na sa uniform nace zani makaranta ban nufi ko ina ba sai shagon Amsad, nabashi kudi yaban cocaine namiko hanya nayi gida, na rufe kaina adaki na biya bukata ta , nan na koma yar gidan jiya
Post a Comment