0
DUK DAD'INKI DA MIJI





DUK DAD'INKI DA MIJI  


 episode 37

 (BASED ON A TRUE LIFE STORY).


"Yanzu don girman Allah hafsat sata kika fara?, yau nashiga uku na lalace" ta daura hannunta akai hawaye na bin idonta, riko kunnena tayi muka nufi falon abba, yana zaune rike da remote a hannunsa yana kallon cnn, ganin yadda mammy tariko ni yasan ba lafiya ba, ta wurgani gabansa sannan tace "Ga ta nan, jiya jiya nagama maka complain cewa ana min dauke dauke, kace nine bani kirge dakyau, gatanan agaban safe dina tana kirga kudi" daddy ya ajiye remote din sannan ya gyra zama yace " me kikeyi a safe dinta?" Na goge hawayen daya zubomin sannan nace "daddy abude fa nagani nake rufewa" wani naushi da Mammy takaimin sai danaji jiri ya kwasheni, Abba yace tabarni natashi natafi, nikuwa na koma, bankara shiga safe din mammy ba, washegari dasafe danazo gaydashi yamin waazi mai shiga jiki, ya gwadamim cewa mutum mafi muni shine marar wadatar zuci, kazama mai godiyan Allah aduk inda kake, ya min misali sosai yace idan kinada wadatar zuci kinfi kwanciyan hankali sannan yace idan ina bukatan wani abu nafada asiyamin, yace babu abinda zaifi karfinsa insha Allah, idan naga inason abu bai baniba, toh tabbas wannan abun ba alheri bane agareni sannan bai dace na mallaka ba, nayi kuka sosai nayita bawa Abbana hakuri haka zalika mammy. For the meantime nafara dan nutsuwa duk da wani iri danakeji tamkar zanyi hauka, don bansha garinnan ba, islamiya ma naki muhadu da amsad balle yakara ja na, nasa araina sai nasami kudi nabashi. Did i tell you cewa mu a gidanmu auren dangi muke, wannan zuriar toh haka ake aure yamu yamu, inzamuyi biki tsantsan yawan mu bama gayyata, sannan duk iyayinki kina gama secondry zaa hado wani acikin family daya gama skul Abba yabashi aiki sai dai kawai kiji an daura aure, sometimes ma idan akaga rawan kanki yafiye yawa yanzu saikiji antofa fatiha a masallaci, acikin tur (communtyn mu) zaa baki gida keda mijinki, ku hayayyafa kuma, tun tasawota ina tir da wannan halin, don nidai bazaa min ba.




DUK DAD'INKI DA MIJI 

episode 38

(BASED ON A TRUE LIFE STORY)


 Wata rana sistern Mammy na tana aurar da yarta, mammy bata zauna ba a gwammaja ake bikin don haka kullum muna hanyan zuwa, dani take zuwa as usual purse dinta, biki ne na masu fada aji, nasamu kudi nan da nan nabawa Amsad yakawomin gari na wanda har ranan bansan sunanshi ba, kuma banda wanda zan tambaya, yabani a kofar hotel din da ake dinnern inda nace mai zanje, don wayan mammy na sata na kira numbanshi, yana bani na dunkule ajikin rigana na wuce, gab na buge dawani kaina akasa na dago na kalleshi, dogo ne sosai, duk da dare ne na iya kallon fuskarshi ta wutan dake haskawa, cikin sanyin murya nace "yi hakuri" na wuce banyi nisa ba yace "baiwar Allah" kaman bazan juyo ba, juyowa ta naganshi da kullin ledan garin a hannunsa yana kokarin shinshinawa yagane meye, hamnunsa na murzawa, a tsorace na isa na kwace, kaina a kasa yace "sorry, kin yar ne, but anya naki ne?"


 Idona na zaro, nace "aika akaban" ina fada na wuce ciki, gabana sai fadi yake, yashigo sai anan naga ashe ma kanin angon ne, Adda ba exaggerating ba but duk inda namiji yake yakai, yahadu iya haduwa, a story books ina karanta about love at first sight bana yarda, anma wallahi wannan yasameni, tun daga lokacin gabana yafara fadi, sai naji inama a daura mana aure kawai gefe yaje yazauna some time to time mukan hada ido dasauri nake kawar da nawa, angama dinner mammy tace injirata a mota nida driver tana zuwa, ina tsaye sai juye juye nakeyi ina dubawa ko zanganshi, sai naji sallama, bazaki gane kina so ba sai wanda kike so yamiki magana kiga wani natural nutsuwa da yake ziyartarki, yace "Sunana Aliyu Jabir, ana kirana A.j am a brother to the groom, and heres my card" yamiko min card din a hankali nasa hannu na karba, dukkan jikina bari yakeyi bansan meyasa ba, nace "sunana Hafsat Tur" yayi murmushi sannan yace " i know" juyawa yayi yafice, wata cousin dina tagun mammy tazo da sauri "ke hafsy me yace miki?" "Bangane me yace min ba" " nayi mamaki ne, miskilin namiji ne baya magana, last week yadawo daga Malaysia yaje karatu, kin dai san ko sonshi kikeyi haka zaki barmin shi, familynku bakwa auren bare" gabana ne ya tsinke yafadi na harareta sannan nace " shegen sensitivity, tambayata yayi ba komi ba" wucewa tayi tana binshi da kallo kaman zata hadiyeshi nikuma nashiga mota ina tunani, tabbas kuwa zaayi rikici na gwammaci in kashe kaina ko inbar musu gidan da akan a auramin wani a dangi, as for me nasamu mijin aure.



DUK DAD'INKI DA MIJI


episode 39


(BASED ON A TRUE LIFE STORY)


 Muna isa gida nayi daki nayi wanka, card din na makale a hannuna, ina karanta sunan company din Jabir and sons limited sai alokacin kwanyata tadau caji tabbas nasan Jabir and sons bawan Allahn nan yana da gidan mai a kano sunfi a kirga, arashin fita na nasan sama da sha biyar shiru nayi ina tunani oho nima ai Abba na yana da kudi, dahaka nayi dakin mammy, ta tafi gun Abba donhaka nadau wayanta nakira numban, har ya tsinke bai dauka ba hakan yasa nakara kira, yana dauka yayi sallama na amsa sannan nace " dazu kabani contact dinka" yace "oh haka, kice min beauty ce" wani dadi naji araina da yace min beauty nan na kara narkewa muka shagala muna tadi sai da kudin mammy yakare nan yakira dana ga ba ranan gamawa na dau wayan nayi dakina, tun takwas muke waya har karfe sha daya kafin muka hakura, inda nace miki tsundumm toh ina nufin haka nafada son A.j, yanada daddada kalamai, kominshi daban, shine first love dina sannan inaji ajikina inbashiba toh sai rijiya, bacci nayi mai dadi wanda ban taba yiba, dama awayan nagaya mishi yadda gidanmu yake, nakuma ce mishi karya damu, da yace zai ganni na gwada masa saidai mu hadu a skul nan yace aa, zai jira har sai randa na nemi hanyan da agida zan ganshi yaxo muyi hira agaban kowa da kowa, uhmm rikici



DUK DAD'INKI DA MIJI 


 episode 40

 (BASED ON A TRUE LIFE STORY).



Satin mu biyu ahaka wayan mammy nake sata muyi waya, kullum tace na karar mata da kati nayi tsit, wayanta aguna yake kwana ranan muna waya yace yatambayeni na amsa "Ranan naganki rike da wani substance, nayi mamaki sosai don nagane menene, anma bari dai na tambayeki menene?" Gabana yayi mummunan fadi, nan nafara rawar baki yatareni tareda cewa zaifi jin dadi idan nagaya masa gaskiya nan da nan nafara kuka, na gaya masa farkon haduwana da Amsad har zuwa ranan, ya ji tausayina nikaina nayi mamakin yadda akayi nafada masa yace "shekarunki sunyi kankanta wa cocaine, its expensive i wonder how shima yake samu, yana damagin dinki internally from respiratory failure, stroke,bleading in the brain, heart attark dasauransu, ke ko mai ciki tasha danta ma haka zaizo atlast haka, the earlier you stop the better, at your age a nja bantaba ganin mace tana sha ba, just promise kindena" ina kuka har raina nake cemasa nadena, na masa alkawari ko magana da Amsad nadena, ranan bamuyi waya yadda muka saba ba saboda ya tsorata sosai musanman jin ss1 nake zanje ss2, inaso naganshi yazanyi nayi tunanin duniya narasa hanya a karshe kawai na yanke shawara, mikewa nayi naje nasami Abba a falo, Mammy ma nagefe, nagaysheshi sannan nace "Abba alfarma nake nema" " wani iri fa?" "Abba aure nake so kamin don Allah" mammy dake gefena tayi salati "ke mekika sani a aure?"

Kawai na fashe da kuka, tunda na daure nazo na sami Abba bayan tsoronsa da nakeji ya tabbatar dagaske nakeyi ba wasa ba, yace "acikin yayunkin wa kike so?" Nan na goge hawayeta na gyara zama sannan nace "ko daya Abba, na sami wani daban nakeso, ni bana son auren dangin nan" Mammy da ta kai min wani mari sai danaga taurari na kirgasu kaf, "Tashi ki fice mana anan yar rainin hankali" ina kuka na koma daki, ranan banyi bacci ba sai tunanin mafita nakeyi, wanda yake bin Abbana malam salisu shi naje nasamu washegari, na masa kuka sosai nace ya roki Abba na don Allah , yace "hafsa magananki mai karfi ce, kin san dai Abbanki ne yake daura auren nan, ba wanda yataba cewa

AA sai ke yar cikinsa zakizo ki ce AA, kin kuwa san bazai yadda ba" ina kuka nace " ka taimaka kayi magana da sauran inkunce kun yarda shikennan zai bari" haka nayita lallaba malam salisu daga baya ya amince zai gwada, dama shi baya zama weekends yake zuwa, a abuje yake lecturing acikin gwagwalada, ina zaune mammy tace inje conference room ana kirana,(gurin da iyaye suke meeting, muna yara mukan kira gun kotu, saboda ko laifi kikayi gun zaaje ayanke miki hukunci, agun ake hada auren yara ma), nan naje sun cika goma sha shida kowa na zaune idonsu akaina, nazauna ina jira naji mezasu ce,

Abba yace "Na yanke hukunci zaki auri Abdullahi gobe jumaa, nan sukayita bashi baki Amma Abba zuciyanshi a kafe, taurin kai kaman me kuka nake ina rokonsu, karshe kam ma cewa yayi "inhar yayan wasu zasu min biyyaya su danne damuwansu, ke kina yar cikina bazaki iya ba, toh ki tattara kibar min gidana babu ni babu ke" Ayadda nake jin zafin son A.j mikewa nayi nafice, daki na nufa nafara hada kan kayana, inason A.j zan iya komi akan shi kuma.

Post a Comment

 
Top