0
DUK DAD'INKI DA MIJI 





 DUK DAD'INKI DA MIJI


 episode 35

(BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


Farkawa nayi naganni a gadon mamy, ga Abba agefe sai bappanina kowa hankalinsa atashe, ga drip ansamin, hakan ya tabbatar min da likitan mu yazo, kokarin tashi nayi mammy tarikeni idonta duk ya kumbura alamun tasha kuka, Abba kuwa cewa yayi "ta ina kika fita? Meya faru? Likita yanzu yagama cemana akwai garin dakikayi inhaling" Sai alokacin karya tayi clicking kai na, nasaka wani kukan sannan nace "daga islamiyanmu wata mai liqab ta sakamin a hanci, bansan kuma ya akayi ba" duk hankalinsu yatashi mammy kuka kaman ranta zai fita, Abba yakara kiran likitan yace yadubani yagani ko akwai matsala, bayan gwaje gwaje likitan ya gwada musu akwai alamun raping ajikina, duk da bai tantance lokaci ba yace tabbas ansamin karfi, don jikina a kumbure yake, bawanda jikinsa baiyi sanyi ba, Abba atake yabada ordern kar akara bari bare yashigo masa gida, nan aka fara binciken masu liqab kuma aka fara bincikosu don aga wayene yamin wannan tabargazan,.



 DUK DAD'INKI DA MIJI 


 episode 36

(BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


A lokacin hardasu saukan Al-qur'ani anmin don babban limaminmu yacewa Mammy akwai mummunan asiri da akamin, Mammy takara gigicewa "Oh ni me mukayi wa mutane, bayan taimakon da mukeyi anaso aga bayan yar'mu, bata zauna ba sai da aka karya asirinnan(asirin da Amsad yamin, na insoshi don ya bata ni), sai danayi jinya sosai na warke, asiri kuma ansamu dakyar aka karya sannan naci gaba da rayuwata, saidai wannan alluran danayin dakuma abinda na shaka wanda har yau bansan menene ba kwadayinsa ya tsaya min arai, da kyar aka bari yan cikin gari suka dawo shigowa sai dai anhana sa liqab, kuma daddy yasa tsaro sosai, alokacin Amsad yadawo, ganinshi na farko haushinshi nakeji duk da bakomi nake tunawa ba, ba yanda baiyi mu hada ido naki tsabar kyankyami, ban canja hali ba, alokacin bazan manta ba munshiga ss2 second term, na tsareshi nace masa "Ka tuna wannan alluran daka taba bani nayi? 

Dakuma wannan garin ? Meye sunansu? Inaso!, sannan inbaka fadamun ba zangayawa kowa abunda kamin, kasan daga kai har danginka bawanda zai tsira" Ba musu yace "basai nafada miki sunan ba, anma zanna kawo miki, kudi kawai zaki na kawowa yarinya" cikin azama na haura sama na bude wardrobe na kwaso asusuna dubu sha shida na sauko na bashi yakalli kudin sannan yace " Allah kaimu" Washegari sai gashi da garin a lungun ajinmu yamikamin a karamar leda na bude naga ko cikin cokali baikai ba, yacemin "da tsada fa inkinaso dayawa kisake kudi, sannan shaka zakiyi, anma ki tabbata lokacin da babu wanda zai ganki" aikuwa da murna nahau sama, karfe taran dare na ciroshi a kasan gado na rufe dakina da key sannan na shaka, babu!, kaf duniya babu! 

Alokacin abunda yakaimin wannan yanayin dadi, wani niima nakeji inajina a sama namanta kowani damuwata, dasafe bantashi da wuri ba saida mammy ta tasheni wani matsanancin ciwon kai yarikeni haka harnaje makaranta a rinka tikan bacci Tun daga ranan nadawo sanaa da Amsad,asiri kuma baisan takarye ba, azatonsa juyani yakeyi, baisan Addiction dina da farin garin da yake bani bane, haka kuwa saina bashi kudi, danazo banda kudi dakin mammy nake zuwa naje safe dinta naciro kudi kuma ba kadan ba, tun bata ganewa harta fara ganewa tana mitan wayake mata dauke dauke, ciwon kai kuma kaman nasiya da kudina kullum ciwon kai, a makaranta kuma kullum bacci, wata rana nashiga dakin mammy na bude safe a hankali na kirgo dubu ashirin ina kirgawa naji tana salati, innalilahi wainnailaihirajiun

Post a Comment

 
Top