0
DUK DAD'INKI DA MIJI






DUK DAD'INKI DA MIJI



 episode 33

(BASED ON A TRUE LIFE STORY)


 Bude kofan nayi ta shigo rike da leda a hannunta "oyoyo Adda! Hope ban tasheki daga bacci ba?" Naduba agogon bango nayi murmushi nace "ohhh ni benaxiratu, ai na dawo yar jarida, tunda labari yakawoki zauna, dama bawani bacci bane" Ta murmusa sannan tazauna, ta ajiye ledan agefe sannan tace "mufara?" Na gyada kai alokacin da na rike biro na da takardata nace "mufara" Tacire hijabin jikinta sannan tafara "Sunana Hafsat Aliyu Tur Haifaffiyar kano, anan aka haifeni har girmana, Mahaifina yanada balain arziki, idan nace arziki i mean Arziki irin tsoffin hannun kanawa kingane? Almost shekara goma iyayena basu sami haihuwa ba don har mammy tafara samun problem da dangin Abba, kafin tazo tasami daman haihuwa akaina kuma tun daga kaina ta tsaya, bata lokaci ne idan nace miki ga irin gatan da nake sha, kome nakeso anamin, Abba na yanada zafi shiyasa nake balain tsoronshi, Ummata kuwa batamin fada shiyasa tarbiyata tasami tangarde, gidan mu babban gida ne a full mansion, agefe baba yayi gini kaman estate,duk yan uwansa ya ajiyesu agun, sai yayi circulating ginin, sai gun yadawo kaman community don akwai shago, masallaci, islamiya, dakuma chemist duk aciki no need mutum yafita,.Abba yadauki nauyin basu gida dakuma kai yaransu makaranta,sannan munada katon makapolo, dukka yaran tare ake kaimu makaranta, akalla munkai 70, idan aka tashi kaimu haka muke loduwa muje, tun daga nursery one na makarantan har zuwa ss3 na makarantan, toh akwai yan gidanmu, mu muka mamaye makarantan, familyn Tur, ko ina kaje Tur, ko wa katabo Tur, gamu da balain ilmi, baataba competition a makarantanmu agama babu dan gidan Tur ba, haka zalika duk wanda ya tabo mu Abban nanan yatakeshi, Abba nada son yanuwa, hatta kayan sallah yadda zaimin haka yake wa sauran yaran , still a cikin gidan akwai orchard din Abba, yana da fruits sosai bamu muke aikin ba yanada masu aiki, Mammy saita dawo oganniya komi ta hannunta yake, daidai gwargwado tana kyautata musu, kuma zamansu Alhamdulilah. Now back to myself, I know inada kyau daidai gwargado, inada tsayi, sannan bakina mai kyau ne saboda mutane dayawa suna dauka ta black american bana kama da fulani ko hausa yaren iyayena, tsantsan hutu fatata zatamaki bayanin wacece ni, kofsi daya nasan inadashi banda gashi, toh hakan yasa kullum nake kitson zare a gidanmu




DUK DAD'INKI DA MIJI

  episode 34

(BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


Don mammy ko da wasa bata bari nafara sa attarchment ba, Ina da girman kai, da raina talaka, ba rainawa ba inada kyankyamin talaka da talauci, don ill not forget idan muka fita nida mammy mukaje gidan da basu da karfi, narinka tofar da yawu kenan kokuma nayita toshe toshe hanci, duka kam nasha gun mammy tace tozarta nakeyi anma naki bari, hakan yasa tadena fita dani anguwa, bayan haka banda son shiga hayaniyan mutane, ko daga labarin da Hamdy tabaki zaki lura cewa duk da muna zama tare bancika shiga cikinsu ba, rayuwa akebe dashi na saba, yanuwana ma gun dangin baba damuke gida daya sainayi shekara banleka fanninsu ba idan bawai mammy ce ta aikeni ba, bana fita ko ina daga makaranta sai gida, acikin gida i have all i need, inzaki sheni a kano cikin anguwanmu ma bansan suwaye makwabtanmu ba, 

Wata rana wata classmate dina tazo gidanmu tasha tambayoyi kafin aka barta tashigo kam, assighnment dina namanta agunta hakan yasa takawo min, naji dadi sosai saboda if not duka zansha washegari a class, mukazo zan rakata maigadi yace saidai na koma, nakira mammy tace yabarni tukunna yabarni na fita, muna tafiya a titn anguwanmu muna tadi, don har wani iska mai dadi nakeji, wani farin ciki nakeji danaji naganni awaje, haba mutum yayita zama acikin gida a prison, na rakata tasamu adaidaita ta hau sannan na juyo, alokacin ina ss1, kinsan wannan fallin da mutum yakeyi feeling ontop erhn, ina taku wani yazo ya tsaya agabana, kallo daya namasa na kauda kai, "Yi hakuri baiwar Allah ki saurareni" 

Tsaki na ja nakalleshi araina baikai wanda zan iya saurara ba kaman wani almajiri chap, ba yanda bayiba danayi zuciya najuyo na kalleshi sannan nace "ka matsamin warin talauci kakeyi, kuma kaima kasan nafi karfin na saurareka" ayadda nake maganan har cikin raina dagaske nakeyi, ya tsaya cak harna fara tafiya yace "insha Allah, wannan jikin dakikace shine jikin talauci, shine same jikin dazaki zo kibukata" tsaki naja nashige gida, naci gaba da rayuwata, in lokacin islamiya yayi muje, dama akwai yan cikin gari dasuke shigowa islamiyan gidanmu in antashi sitafi mukuma mu shige gida, har lokacin banda kawa bankuma saba da yanuwana ba, duk wanda kanmu daya bana shiga cikinsu kullum ina makale a daki, 

Wata rana nashirya naje islamiya kenan nashiga aji, ankawo mana sabbin dalibai su uku, biyu mata daya namiji, duk dacewa ajin manya ne, anma wannan daga gani yakai ashirin da biyar, haka yake zamaa acikinmu, layin sit din maza daban na mata ma daban,, kasancewar rayuwata nake bana lura dashi, saidai ko tambaya zaayi in nadago ido sai naga yana kallona, duk da fiskarshi tamin kaman na sanshi, kuma aduk lokacin dana ganshi gabana yakan fadi, wata rana anfita break na zauna kasan bishiya ina duba jakata yazauna agefena a tsorace nace "meye kakeyi anan, katashimin kafin ranka ya baci" zanci gaba da magana anma muna hada ido naji nakasa, yayi wani fari da ido sannan yacemin "sonki nakeyi, kuma inaso daga yau muyi soyayya" gyada kai nayi alamun na amince, karki manta wannan same guy dinne da yatareni a bakin titi banganeba, muka koma aji, nan muka fara exchanging letters, Tun daga ranan kiri kiri na fara son asmad, don kyau kam yahadu, saidai takaka ne sosai futuk fa, idan nazauna nakanyi tunani menake so ajikinshi amma babu, ke i dont even have time to think,

 wani matsanancin sonshi nake kaman babu gobe, kuma ko meyakeso ina masa, inyace yana son abu ko zaa mutu sai na nemo namishi, sannan idan yabude baki yace Hafsat karki yi kaza, toh ba mammy ba ko Abba ne yace nayi sai dai nasha duka anma bazanyiba, ranan yacemun yana son naje gidansa, nafara tunanin hanyan guduwa naje, cikin ikon Allah na lallaba cousin dita Nadra, tabani liqab dinta, da yan makaranta zasu tafi na bi cikinsu nafice, , bazaa gane bana nanba saboda bawanda zaiyi tunanin nafita, bantaba ba, dakinsa yakaini single room, yarufo kofan, mukaci abinci alokacin ba abunda yakai wannan farin ciki, jina nakeyi complete human being, aranan ya ketamin haddi, ina ss1 shekarana sha biyar , tundaga ranan na koyi guduwa, baataba ganewa ba, don idan anshiga sallah masallaci na magrib nake shiga sainaje wa mammy kamar na fito lambu, banda waya alokacin, Abba yace sai nagama secondry school,

 Amsad yadena zuwa islamiya, dama shagon wanki da guga suke, haka zanje na tsaya masa wataran acikin shagon yake danneni, its not like inajin dadi, a a wallah wahala nake sha anma tsoro nakeyi nabata masa rai, alokaacin kullum yakan sa abu inyazo yi, i never knew it was condom, ranan da zaimin yaga jikina duk ya kumbura yadauko wani allura yace "inna miki wannan alluran zai daina" nazauna yamin, sannan yaban wani abu gari na shaka nan da nan na bugu yayi abunda zaiyi sannan yafice, karfe tara nakoma gyda ranan alokacin mammy ta ankara bananan harta baza cikiyata, daidai kofar gida yajuya nashiga, ina shiga na fadi summamiya

Post a Comment

 
Top