0
DUK DAD'INKI DA MIJI






DUK DAD'INKI DA MIJI


episode 22

 (BASED ON A TRUE LIFE STORY)


Sai dana tabbatar cewa Umma ta kwanta, sannan duk sun shiga dakinsu bacci, na dau katon hijabi na saka na nufi hanyan gate, nasaka kafata kenan sai naci karo da yaa umar, wani fizgoni dayayi sai dana jigata, yaa aliyu dake bayansa ya damkoni, wato adda ko ana cewa mutum in ya mareka kana ganin stars, bantaba yadda ba, anma a zuciya irina ya aliyu daya rikoni wani saukan mari danaji, wallahi taurari nafara gani, wurgani cikin gida sukayi, yaa aliyu yazauna yayinda yaa muar yabani jikina, nasha duka don wannan karon ba da dorina ba, akwai igiyan injin markade, wlh dashi ya zage karfinsa yashigeni, jikina duk ya faffashe sai dana sume yabarni, farkawata dai naganni gefen umma wacce take ta zubar da hawaye tana magana "ashe hamdiya bazaki tuba kikoma ga Allah ba?, hamdiya mekikeso a duniyannan da baki dashi?" Umma kuka take sosai yaa imran yajanyeta suka fice, nikuwa rufoni akayi a daki, abinci a wurgomin ta window, bayan haka har ummana bana gani, pain reliever ma sai yaa imran ne yake jefomin inbasa kusa, duk tausayina yakeji yafisu rauni don har kuka yakeyi kuma dama shi nake bi, nayi wata acikin gun alokacin nafara dawowa hankalina, wata rana ina zaune yaa umar yaleko yaganni nayi wanka dogon riga bakine ajikina yace nafito, nabi sawunsa sannan yace naje falon ana jirana, babban falon naje, nayi sallama na bude kofan, at dat tym bazan iya gaya miki kalan bakin danayi na rame ba, gabana ne yafadi ganin Alh.umar aliyu, babban dan siyasa ne wanda nja ansanshi.



DUK DAD'INKI DA MIJI


episode 23

(BASED ON A TRUE LIFE STORY)

 Na tsuguna na gaysheshi ya amsa, sannan yace "baki sanni ba ko?" Na dai gyada kai tunda dama asalin ba abunda yataba hadani dashi, ganinshi a zahiri bantaba yi ba, sai a tv ko labarai, sannan nasan frnd dina ne a facebook bamu dai taba magana ba saikuma a jarida, yace "kiyi hakuri idan nazo miki wani iri, anma ni friend dinki ne a facebook ,donhaka ranan naduba profile dinki kuma naji hankalina ya kwanta dake, nasan bazai yiwu muyi magana online ba yasa nasa aka nemo min komi akanki dalilin zuwana kenan, kuma yin hakan bawai dawani manufa ba sai alheri, inasonki ne da aure, nayi magana da bappaninki da yayunki sunbani izini nafara zuwa gunki inkin amince toh" kai na akasa gabana nafadi, ai babu wani tunani, dama nema nake nabar musu gidan kafim su kasheni, kuma da in auri raihan gwara na auri wannan atleast nasan halinshi kamili ne sosai, kuma mutunceccen mutum, kwata kwata baida matsalan sauran yan siyasan nan, nan da nan nace "zanyi tunani, zakaci daga gun yayuna" nayi hakanne kar yayi tunanin neman kai nakeyi,; yayita min bayanin kansa inda yace yana da mata biyu, yayansa hudu, dukka maza, nadai ji bayani sosai akansa, harya tafi, shigowana gida akafara meeting, yaa aliyu yarufe ido yace shi raihan zan aura, bayason kananu kananun yaudara, nikuwa kif nace da in auri raihan gwara na mutu ahaka, "Umma raihan abincin safe fa nema yakeyi, yaushe yagama service din kwata kwata babu aiki, inkuma zaku aurar dani naje na wahala ne toh" " zan dura miki ashar, yar'iskan yarinya da kika fara soyayya dashi kinsan da cewa bai da kudinne? Saida kikaje jamia idonki ya bude?"

 Cewar yaa umar, nan dai suna tayi nikuwa na kafe nace sai Alh.Umar washegari da bappaninmu sukazo ma, abinda na maimaita kenan aikuwa dole suka yarda acewarsu ni marainiya ce bazasu kuntata min ba, atakaice aka kira shi aka nuna masa an amince, kasancewarshi babba ba'a wani bata lokaci ba aka kawo gaisuwa aka sa rana, yayuna suka sani yin istibrai lokacin har ankoma makaranta anma kif yayuna suka hanani, wayana ma basu bani ba, aka kawo kayan aure na gani nafada, don nasami biyan bukata, duk kawayena yan kungiyanmu ne, aikuwa dai su yaa umar sunga bariki a bikinnsn, aka dauramin aure bayan nashaa waazi kaman zaiyi tsiro ajikina aka kaini, umma hankalinta ya kwanta, ba ita ba nakowa ma, anma fa na sha gyra , nine tsumi, matse nan tamke can, kukke can, shanye can, sunyi tunanin tunda nayi aure kam sun dauka na nutsu kenan, basu san cewa nan ne asalin bala'in take ba, basusan cewa zasuyi nadama har karshen rayuwansa, zasu gwammaci da sun barni nayi barikina ban yi auren ba, zasuyi babban nadama, wanda akarshe umma sai datayi tur da haihuwata innalilahi wainna ilaihi rajiun, 

Adda nashiga wani hali, bana fatan kowacce musulma tashiga ciki, inkuma akwai masu halina don wlh yanzu haka suna nan dayawa, don Allah sudena, alokacin famma mamaki ya isheta tana cewa "duniya abun tsoro, kiga yadda kikayi barikinki, kika zubar da ciki, at the end kinsamu miji kinyi aure, ankashe kudi a bikinki, kinsami gida mansion, inba mutum mai tunani ba wasu zasu yi sha'awar yin rayuwanki" anma duniya bazasu san mena fuskanta daga ciki ba, zahiri akwai mu dayawa, da Allah yana sonmu yana ja mana lokaci don muyi nadama, anma bama sani, mugama iskancinmu muzo musami innocent miji muyi aure, did i tell u saida raihan ya kwanta a asibiti?, while nikuma barikina alokacin nafara

Post a Comment

 
Top