0
DUK DAD'INKI DA MIJI





DUK DAD'INKI DA MIJI  


 episode 20

 (BASED ON A TRUE LIFE STORY). 


A satin muka zo bauchi bikin cousin dina, abunku da family house, dakin kakata nida cousins dinane muke kwana sauran dakuna kuma iyayenmu, wata rana nafito da makeup kit dina Mac, full set ina make up, famma cousin dina sai kallona take, can dai tace '" yanzu ke inbanda asaran kudi meye zakiyi da kayan kwalliya? Wannan janbakin ma kanshi 7k ake siyarwa, na kalli jan janbaki da ta dauka tana shafawa sannan tana mita, hajiya dake gefe tace "mene, mene?" Famma dasauri ta dauki powder da janbakin takai mata sannan tace "umma asalin original desighner ne fa wannan, da kudin bata tasiya dakinje kawai tasiya supern ta mai kyau,wannan janbakin dubu bakwai, powder kuma dubu sha daya" umma ta kalleni, tuni na hango tsantsar bacin rai da alamomin tambaya daga fuskanta, nan da nan nafara neman karyan dazanyi, anma too late, don umma tashi tayi tarufe kofa, tasani bude akwatina idona tuni ya cicciko, tace famma ta nutsu ta duba, farko daya bayan daya ta ke ciro kayan kwaliyyan wasu batama san kudinsu ba sai datayi gooogling, a daddafe tahada dubu dari da hamsin akan kit din kwaliyya na, umma idonta ya cika fam da hawaye, atamfofi as usual dama a makaranta bansawa ba donhaka duk umma tasan kayan, har zata rufe akwatim ta kyallaro turare na, hannu ne kawai bansa akai nayi ihu ba, tun wanda na siya a dubai ne, ta karanta sunan Caron Poivre, tace wa umma bata gane turaren ba, gashi dan karami kaman tasa a baki ta hadiye, Umma tace "duba mana a wayanki nawa ne" ta kuwa shiga, salati tayi ta zare ido sannan tace "innalilahi umma, turaren nan ba wasa ba, dollar dubu daya per ounce, dollar dubu anan fa naira kusan dubu dari biyu ne umma, kuma anan yakusa kai 4 ounce" umma ta dafe kirjinta numfashinta yafara daukewa da gudu nasa kuka ina rikota, famma kuwa waje tayi takira su yaa umar, sai da aka bawa umma maganinta numfashi ya dai daita har lokacin bata dena zubar da hawaye ba, "Waya baki wadannan kaya masu tsadan?" Kaina akasa nace Alh.ilya, dasauri tace yaa umar yakirashi, bugu biyu yadauka aka tambayeshi could you imagine me mutumminnan yace? Yace yana min kyauta, anma baya wuce na dubu biyar zuwa dubu talatin, donhaka ba shi bane, wato na gayamiki Yaa umar ranshi yayi mummunan baci, ya kallen sannan yace kisameni a daki, wato dakin samari, bankawo komi araina ba illa bai wuce yamin waazi kamar yadda yasaba ba, naje ni harda yar chewn gum dita ina tattauna wa, nashiga, ina shiga ya sa key yarufe kofan anam gabana yafadi, belt dinsa yacire, idonsa jawur ya dura min ashar, kai ashar dinnan tunda nake banta ba ji ba,zagi yake kan zagi "kifadamun aina kika samu?,daga kayan kwaliyya zuwa turare kin hada abun miliyan daya, aina kika samu kudin? Waya baki? Hamdiya karkisa zuciyata ta kasance cikin zarginki" kyam naki tankawa 



DUK DAD'INKI DA MIJI


  episode 21

(BASED ON A TRUE LIFE STORY).




 Babu yadda baiyi ba naki, wato daya daga belt dinnan yafara dukana, karfinshi yake zagewa gaba daya ya daken, jina jina ya farfasa min fatan jikina, yasa hannu ya dauki wayata, ashe bawan Allah inbox yaje baisamu komi ba har zaifita yaga zenith bank message, a saninsa bai budemin account da zenith ba,dasauri yashiga ya dubatransaction, salati kawai yakeyi, hawaye na bin idonshi "innalilahi wainna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musibati, na shiga uku hamdiya mekika dawo? Karuwa? Wayyo Allah na nashiga uku" bazan iya misalta halin da yaa umar yashiga ba, bantaba ganinsa acikin wannan yanayin ba har rasuwan babanmu ma baiyi kuka ba, waya yasa yakira su yaa imran, duk sai gasu sun hallara, yana musu bayani hawaye na bin idonshi, suma dukkansu sun jigata, sai kunganni a lokacin kamar marainiyar Allah, Yaa aliyu ne da ya tashi yakaimin wani naushi wallahi ban bude idona ba sai a gadon asibiti, ina farkawa naga sudinne akaina, sai famma yana ganin na farka ya yo kaina zai shakeni ana rikeshi yana cewa "kubarni na kashe makira munafukar yarinya marar godiyar Allah, kinci amanan iyayenmu kinci amanan yan uwanki, kzakuma kiga sakamako gun Allah", keh kuka fa yaki zuwa idona a bushe, dakyar aka fice dashi famma duk ta tsargu, ga shi ta damu, tadamen na fada mata aina nasamo, alokacin duk sun watse sun barmu don bakin ciki, da raina ya baci nace mata "ke karuwanci nayi , Da namiji ne yabani, sai meye?";hannun kofan aka murda yaa umar ne yashigo a nutse alamun yaji duk abinda na fada, dasauri na sunkuyar da kaina, ina kallon calulan da aka samin a hannu inashan drip, famma tace " zaki kashe mahaifiyarki don yanzu haka hawan jini likita yace tana dashi, ga asthma ga hawan jini, ban ce komi ba, har aka sallamen acikin yayuna bawanda ya lekoni ana daura aure yaa umar yace mudawo abuja, har lokacin umma ko kallona batayi, muna isowa abj duk suka zauna a falo, umma ta kallen sannan tace "zantambayeki ki bani amsa dai dai " Na ce "toh umma"

 "Akwai abinda kika taba cewa a siya miki ni ko yayunki bamu siya miki ba?" "A'a" " akwai abinda kika nuna kinaso muka nuna bamaso bayan ba haram bane a addini ko abun zubar da mutunci?" "A'a" " acikin yayunki akwai wanda ya taba damunki ko takuraki ko tauye miki hakki?" "A'A" " nagode da amsa na, ki shirya kifito da miji nan da sati biyu, idan baki fitar ba, zaa aura miki ko waye" tana gama fada yaa imran yajata yakaita daki sannan yadawo, ya umar da yaa aliyu sai kallona suke, can suka tusa keyana mukaje dakina suka hau bincike, anan cikin kasada suka hango keyn mota da na boye a kasan gado, , kai bana son tuna ranan, anma

 Adda nasha duka, jikina duk ya fashe, idona daya yana jini, kafana ya gurde, gashina ma saida yaa aliyu ya aske, da ya binciko wayata yaga hotunan danayi wanda hakan ya tabbatar musu da rayuwan da nakeyi a makaranta, suka kwace wayan, da atm din dana ke ajiyan kudin, duk kayan suka dibe bansan ina sukayi dasu ba, yaa umar yace " hamdiya na yarda da tarbiyanki da amananki yasa na yarda kikaje jamia, ashe jamia bazata min rana ba, donhaka daga yau na soke, babu ke babu makaranta, ke kofar gida idan naganki wallahi wallahi bakya bina bashin rantsuwa saina cire miki kafafu, babu ke babu kawa, babu fita, kici kanki ke kadai har randa umma zata aurar dake" kai naga tashin hankali. 

Tun daga ranan ga jinya, ga zazzabi gashi ba wayana babu fita nadawo wacce iri, duk yayuna babu mai tausayina, acewarsu na tozarta su, na wulakantasu a bainar duniya, ni ba ma wannan bane damuwata, damuwata shine yadda zan nemo mijin, ni yaushe nakeda wani tsayayye, sai Raihan yafadomin arai, nikam raihan ba aji na bane, kwana da kwanaki ina tunani, watarana kawai nayi tunanin guduwa, yes shine kawai mafita ingudu tunda inada account num dina zan iya zuwa nayi withdrawn cash, nasan hanyan da zannemo wani keyn abude min motata nayi gaba, yes shine shawaran

Post a Comment

 
Top