DUK DAD'INKI DA MIJI
DUK DAD'INKI DA MIJI
episode 16
(BASED ON A TRUE LIFE STORY)
Na dago fuskata ina kallon nasa, shima kallon nawa yakeyi, ko me ya tuna? Kawai ya tunkudani gefe "subhanallah, auzubillahi" ji nayi kamar na bishi da duka, dasauri ya mike tare dacewa "tarin yadena?" Ban amsa shi ba, rike wuyata nayi alamun inajin jiki, hanyar kofa yayi tareda cewa "barin nemo students mata su taimaka miki" yana fita na mike na karkade hijabina na dau jakata na fice, zuciyata cike da takaici, ai wlh ko cikin mamansa yakoma saina bishi,yadda nasaka rai dinnan bai isa ya hanani ba, ko da na isa gida hijaban na dauka na jefa a akwatin kayan da nazo dasu daga gida, wanda zan iyacewa bana sawa sai zanje weekend,, banyi bacci mai kyau ranan ba, sai danasa aka bani full address din malam ustaz, baida mata, but yakama one bedroom flat a wuse, Allah Allah nake gari ya waye na je, kasancewar ranan weekends ne, ranan kam a asalita hamdy naje masa, na yi balain matsewa kaina yasha mai na yi parking tabaya, duk gani acike,daga manchester(mazauni), har arsenal(kirgen dangi) duk sun cika sun zauna dam, knocking nayi bugun farko wani yaro yaleko, saina kara duba address dina don intabbatar ko gidan ne, tabbas nanne, yaron yabude daga gani mai aiki ne, nace "ina mai gidan?" "Yaje asibiti nan baya anma yanzu zai dawo", ya amsani yana kare min kallo, rike kofan nayi alamun yaban hanya na shige, sai dayayi dum sannan yace "wakike nema ma?" "Ko ba nan bane gidan malam ustaz?" Yakara kallona sannan ya gyada kai yabudemin, nasan bazai wuce mamakin hala malam baitaba kai mace gida ba, but shaa mazan yanzu dukkansu burga ne, dont trust dem,
DUK DAD'INKI DA MIJI
episode17
(BASED ON A TRUE LIFE STORY)
Falon dan dai dai na kare mai kallo tas, daidai gidan gauro, ko ince tuzuru, mai aikin yashige ya dauko min ruwa da juice, hankalina yana kan tv da ake kallo, buga kofa naji anyi dasauri yaron yaje yabude sannan ustaz yashige, mamaki kaman zata kai shi lahira daya kyallaroni, inagani yamikawa yaron kudi yana masa bayanin kasuwa, daya fice shikuma ya wangale kofan, araina nayi dariya nace dakanka zakaje ka rufe, ko yau kaga yadda mace take fyade wa namiji, ya cire takalmimsa sannan yakaraso tana ajiye ledan maganin asaman fridge yace "meya kawoki?" "Naji malam baida lafiya ne na zo?"
"Agunwa kikaji, bawanda yasani" "Jikina ne yabani hardasu mafarkina" dariya tabashi sannan yace "yau kinyi niyyan fitowa a asalinki na hamdy kenan" gabana yafadi ras, anma na danne nace "ae!, tunda wanda na nutsu dominsa bai nuna yanason naci gaba da nutsuwa ba" "Baki dai yi niyya ba" yafada yayinda yazauna akan kujeran dake can gefe da nawa, "Bingo" nafada ina murmushi, "Kinzo gidan gauro meza'a kawo miki?" "Ni banajin yunwa, mayb anjima"
Yakallen alamun tambaya "Yau wuni nazo maka" "Ba'a gidan nan ba, kindai san cewa mace da namiji da ba muharraman juna ba idan suka kebe toh na ukunsu shaidan ne, donhaka yanzu zaki tafi" rigan sama nacire yazama daga ni sai bra, dasauri yakalli kofa sannan yace "kina hauka ne?,in wani daga waje yaganki yace me? Tashi ki fice, nagode da ziyara" yana fada yana tattaramin jakata, dakarfi yake maganan alamun har ransa, dana ga no go kawai mutuminnan dagaske yakeyi nafara kukan kissa ina cewa "yanzu don kaga ina sonka, shine zakamin wulakanci, don kaga na damu dakai, kadubi irin rayuwar da nakeyi anma saboda kai nadena kanuna ko inkula, yakakeso nayi da radadi da tsantsan son da nake maka?"
Yadda nake maganan ko macece yar uwata agun sai taji ajikinta balle namiji, shiru yayi yakoma yazauna yana dafa kansa "kinga ba haka bane, kema kinsan duk namiji dai mai hankali da lafiya bazai ki mace irin ki ba ai ko" nan fa na jajirce ganin yafara saukowa na ringa rikici ke saida yazama ya zauna kusa dani, ahankaki najawo hannunsa ya gagara kwacewa na rungumeshi naji nanma shiru, habawa sai sanaa kawai, nafita hayyacina alokacin da yamike yarufe kofa mukayi daki, toh dai anan nagane wani abu, kwata kwata malam ustaz dan koyo ne, alamun inya taba wannan abunma toh ba sosai ba, aranan na kauda shaawata, tuni naji yaficemin akai, muna fitowa yace in tsaya dare yakaini nace da mota naje haka nafice nabarsa har lokacin yaro boy dinsa baikoma ba,
DUK DAD'INKI DA MIJI
episode 18
(BASED ON A TRUE LIFE STORY).
Ina zuwa gida nayi wanka, did i tell you cewa alokacin sallahn asuba kawai nakeyi?,sai wataran nayi magrib?, toh bacci nayi don dama the previous day banyi ba, inata tunanin ustaz gashi na dandana naji meyene. Tun daga ranan ustaaz kullum kira, text shi tsakani da Allah sona yake, anma bazamu kara zina ba sai munyi aure, lyk serious ranan i laughed hard daya cemin aure, Aure?!, ai baya agenda na, Allah alokacin ko kallonsa nayi wani sabon kiyayya ke ziyartar raina, dahaka muka fara exams danaga bazai daina damuna ba, na canja number, luckily enough harna gama exams ban hadu dashi ba, nan nafara shirye shiryen komawa gida, babu tunanin da banyiba mezan ce agida akan alh.ilya daga karshe a dole nafara daukan wayan raihan shine kadai last option dina, nagama planning komi set, randa zankoma yaa umar yazo yakaini, duk kayana suna cikin gidan, motan kuma gidansu wata frnd dinmu hanen takai, ranan na shiga gida ina murnan ganin ummata, wacce tsufa yakara kamata
DUK DAD'INKI DA MIJI
episode 19
(BASED ON A TRUE LIFE STORY).
Nan fa umma tayita samin albarka, yaa umar kuwa mita yakeyi yace tun da naje makaranta ban taba kiranshi yaban kudi ko yaturamin ba, duk da kowani wata yanasamin dubu goma, a zuciyata kuwa cewa nakeyi yaa umar dubu goma ai a kwana daya zan nikata, a zahiri kuwa cewa nayi "ai har yanzu sunanan ina ajiyewa, bantaba ba, in ina da bukata zan yi amfani dashi, kullum ummata wa'azi game da rayuwar duniya, adduoi rike ibada duk ta dage nayisu, komawa na gida yasa nafara sallolina, da suka tikeni maganan alh.ilya kuwa kuka nafara yi nace ai yace sai ya taba hannuna da naki yarda shine bai kara kirana ba, ransu yaa umar ya baci ranan har dare mita sukeyi a gidannan, nikuwa na samu sake umma sai wa'azi takeyi "karki kuskura namiji ya rike miki hannu kinji ai, duk wayo zasu miki" nayi murmushi alokacin dana tuna muna yara idan zamuje biki family house dinmu hajiya sai tace karna bari kowa ya rikeni duk wanda ya tabani toh zanyi ciki, yanzu bata ambaci hakan ba sanin cewa nayi wayo, batasan cewa har maza na san dadinsu bama namiji daya ba.
A gida nazauna nayi full welcome back din raihan, muka dawo kamar da, sai dai shi kanshi ranan sai da ya tambayen meyasa yanzu banajin kunyarsa? Alokacin nagane cewa kunyana yagudu, nadawo tankareriyar mara kunya, don da agida bana iya zama ba kaya kullum a suturce, anma yanzu har bra da underwer ina yawo, yaa umar yayi mita umma ma tayi anma duk a banza, kuma kaina na saba da rashin dankwali alokacin while a da kullum a kulle don banaso a ga gashina, har nagama secondry scholl frnds dina nason bude kaina don suga gashi anma kif nake rufewa.
Daya daga cikin illan bariki kenan, rashin kunya karara. Wata rana ina zaune yaa umar yashigo yana farin ciki, ko da umma ta tambayeshi yace Dahar ne zai dawo, anan natuna shi, Dahar abokin yaa umar ne kut da kut sai dai tun banyi wayo ba yabar kasan yaje karatun likita acan kansas dake u.s toh sai lokacin zai dawo, randa zai dawo hardani a yan zuwa daukoshi don kaishi gida, tundaga saukowanshi daga jirgi da na daga ido na kalleshi, as usual kingane ai, nan da nan hankalina yatashi, yana karaskwa suka rungumi juna da yaa umar, yana tambayanshi hope bai fada wa yan gidansu ba?
Don yana son musu surprise, yaa umar yace ae, na gaysheshi cikin shakeken muryata, ya juyo ya kalleni yana murmushi dimple dinshi ta lotsa, ga idanuwanshi very sexy kaman mai jin bacci, God!, nan fa na hadiye yawu, mu shige saida muka kaishi gida sannan muka dawo, ranan banyi bacci ba, sai juyi nake akan gado, gashi dama nayi kwana biyu banji dumin wani agefena ba, toh dole na san yadda zanyi Dahar ya shigo hannuna, he's so tall, daga nan ma zaki gane cewa na fi ganewa tall guys, i dont go for the short ones, a satin ya zagayo meeting din kungiyarmu, nafara tunanin hanyoyin da zan hallata, karshe karya nayi da sunan hanen akan batada lafiya, yaa umar ya saukeni a gidansu, nan muka wuce meeting, sukayi hidimar su yayinda aranan aka hadani da wani Alh.tanko, na bashi jikina ya damka min kudina
Post a Comment