0
MAGANA JARI CE LITTAFI NA DAYA

labari na goma sha hudu

magana jarice na daya

LABARIN WASU ABOKAI SU UKU


Labarin Wadansu Abokai Su Uku 

      Wata rana wadansu samari su uku, abokan juna suka tashi daga garinsu za su wani gari neman aure. Kowane ya yi wankin kayansa, suka yi ado, suka kama hanya. Suna cikin tafiya, sai karamin ya ce, “Ku ci gaba, na iske ku ni zan ratse.

Suka wuce, shi kuwa ya ratse, ya rabu da hanya kadan sai ya tarad da wani dan akwati, barayi sun sato ya fadi. Ya duba gabas, ya duba yamma, bai ga kowa ba, ya duka ya dauki akwatin, ya ji da nauyi, ya nemo wani dutse ya fasa. Da hannun rigarsa ya kunshe, ya fito da gudu ya bi ‘yan’uwansa yana kira. Da suka ji kira, suka tsaya. Ya ce, “Albishirinku!”

Suka ce, “Goro.”

Ya ce, “Kun ga abin da na tsinta.” Kowane da ya kyalla ido ya ga duki, duk suka yi ta murna, suka koma gefen hanya suka kidaya, suka ga fam ashirin da hudu ne da sisi. Wanda ya tsinto kudin na kirki ne, saboda haka ya ce, “Sai a raba, kowa ya sami fam takwas takwas, sisin nan kuwa mu sayi abinci da shi mu ci.”

Da babbansu ya ji haka sai ya ce, “To, madalla, mn gode, Allah ya bar mu tare! Amma abin da ya fi, sai ka tafi gari maza kudin, in ka dawo sa’an nan mu raba.”

Yaron da ya tsinci kudin ya tashi, ya nufi gari da gudu. Da bacewarsa sai babban ya ce, “Abin da ya fi sai mu yi dabara mu karbe kudin nan, mu raba mu biyu, watau fam goma sha biyu biyu ke nan.”

Daya abokinsa ya ce, “Lalle gaskiyarka. To, yaya za mu yi ke nan?”

Babban ya ce, “Ina da dabara. Ga wani maharbi can, mu kirawo shi mu ce ya shiga kogon itacen nan, in an yi magana ya rika amsawa.”

Suka kira maharbi, suka gaya masa duk abin da su ke so ya yi musu, da abin da su ke so su karbe wa dan’uwansu, har suka ce sa ba shi lada. Da maharbi ya ji batun kudi haka ya yarda. Ya shiga kogon ke nan sai yaron ya komo. Da hango shi, sai suka fara kuka. Ya ce, “Lafiya?”

Suka ce, “Ina fa lafiya, itacen nan ya kwace kudi duka!”

Yaron ya dubi itace, ya ce, “A’a karya ne, itace da ba ya magana ma, ina ya kai ga sata? Ku dai ku sake shawara.”

Daga nan sai mutumin da ke cikin itace ya ce, “Wace shawara za a sake? Ni na dauke. Kuma in kana tsammani kai ka fi ‘yan’uwanka jaruntaka, to, zo karbi. Matsiyata ‘ya’yan zamani, wadanda ko iyayensu ma ba su san girmansu ba, balle wani!”

Ko da yaro ya ji haka sai ya garzaya, bai zame ba sai gidan Sarki. Ya gaya masa duk abin da ya faru tun daga farko har karshe.

Sarki ya ce, “An tasam ma munafunci. Yaya za a ce itaciya ta yi magana? Ina ‘yan’uwanka?”

Yaro ya ce, “Suna can gindin itaciya.”

Waziri ya dubi Sarki, ya ce, “Ranka ya dade, ai sai ka sa ni in tafi in ji in gaskiya ne. Ka san ikon Allah ya fi da haka.

Sarki ya ce, “To, sai ka tafi ka gani.”

Yaro ya shige gaba har gindin itaciyan nan, suka tarad da ‘yan’uwansa can suna ‘yan koke-koke kamar da gaske. Da ganin Waziri suka ce, “Alhamdu lillahi!” Suka fadi suka yi gaisuwa. Waziri ya dube su, ya ce, “Ku ne itaciya ta kwace muku kudi?”

Suka ce, “I, mu ne, ranka ya dade. Daga mun zauna nan gindinta muna kidayawa, sai muka ga guguwa ta tashi ta murtuke wurin, duk kura ta buce mu, muka rasa inda mu ke. Can an jima sai ta natsa, muka duba kudin da ke gabammu, suka ce dauke mu. Muka shiga tonon kasa, don muna tsammani kura ce ta rufe su, ba mu ga ko kwabo ba. Muka tashi za mu yi fada da juna, don ta kammu yayin da guguwa ta buce mu. Da muka fara zage-zage, sai muka ji kamar daga sama an ce, “Kada ku zargi junanku, ni na dauki kudin. In kuwa kuna jin wata-wata ne ku zo ku kwata. Muka duba babu kowa, sai dai magana mu ke ji na fitowa daga itaciyan nan.”

Da maharbin nan na cikin itace ya ji haka, sai ya nisa, ya ce, “M, wannan dahir ne.”

Waziri ya dube su, ya ce, “A’a! Ai kuwa ashe da gaske ne.”

Itaciya ta ce, “Af, da kana tsammani karya ne” Sai ka zo ka kwatam musu.”

Ko da Waziri ya ji haka sai ya rike baki, ya ce, “Ki yi mini gafara, ni ba ruwana, aiko ni aka yi.”

Nan da nan sai ya aika aka fada wa Sarki ya zo da kansa ya gani, domin a ce gani ya kori ji. Can an jima ya tinkaro duk da mutanensa. Da isowarsa Waziri ya ce, “Ranka ya dade, ka ga ‘yar itaciyar da a ke markabu kanta.”

Da maharbi ya ji haka sai ya ce, “Wai, wai, wai, ni ce ‘yar itaciya! Kai ne wa tukun da ka ce mini ‘yar itaciya? Har dan tsugunin nan naka ka isa zagina? Daga yau ba ka sake duban kamata ka ce mata ‘yar itaciya ba!”

Da jin haka fa, sai hantar Waziri ta kada,ya fadi ya yi sujada yana ta ahi, yana rokon gafara. Sarki ya tsaya tsayin daka, ya dubi kogon itaciyan nan, ya ga lalle mutum na iya shiga. Ya lura da gindinta kuma ya ga sawun mutum kamar ya hau ta, ya dubi takon nan ya ga dai bai yi daidai da na ko daya daga cikin samarin nan masu kudi ba. Ya tuna tun da ya ke bai taba jin ma wanda ya ji maganar aljannu haka a fili ba. Kai, karewa ma dai tun da Annabi ya kaura aka bar jin irin wannan al’amari. Ko da ya lura da haka sai ya hakikance makirici dai aka kulla, don a cuci yaron nan da ya tsinci kudi. Sai ya dubi Waziri da ke ahi, ya ce, “Kai, tashi! Kwaure ka ke wa sujada?” Ya juya wa itaciyar, ya ce, “Yanzu dai ko ki ba su kudinsu tun da girma da arziki, ko kuwa in sa a kone ki. Da mutum da aljani ni duk wanda ya tasam ma zalunci cikin kasata sai na ga iyakarsa!”

Sai itaciyar ta ce, “Kai dai tsaya kan mutane. In ka fada aljannu sai kai a ga iyakarka.”

Sarki ya dubi mutanen da ke nan, ya ce, “Duk ku saro kirare.” Suka ruga nan da nan suka cika gidin itaciyan nan da itatuwa da kirare.

Ya ce, “A kawo ashana.” Aka mika masa. Ya tasam ma itaciyar zai kunna mata wuta, duk kowa ya rike baki. Maharbi ya ga dai in ya kyale minti biuy, lalle zai halaka. Sai ya yi kara ya ce, “Don Allah, ranka ya dade, kada ka sa wutan nan. Ni ba kowa ba ne, mutum ne. Bari in sauko don Allah!”

Nan da nan sai mutum ya tsirgo daga kogo, da kudin rike a hannunsa. Ya fadi ya gai da Sarki, ya tsunguna nan, ya fede masa biri har wutsiya.

Sarki da mutanensa suka yi mamakin wannan al’amari. Mutane suka ya ta cewa, “Lalle Sarki shi ma aljani ne.” Nan take Sarki ya sa aka yi wa yaran nan biyu azzalumai, da maharbi, bulala hamsin hamsin, ya sa aka kai su gidan kurkuku su yi wata shida shida, ran da za su fito kuma a kewaya da su gari, kowa ya gan su. Ya dauki kudin duka ya ba yaron abinsa. Yaro ya fadi ya yi gaisuwa, ya tashi ya koma gidansu. Sarki kuma ya koma gida. Kullum I an ta da tadi, in ya dubi Waziri, ya tuna da yadda ya yi goho da katon bujensa, sai ya yi ta dariya.

Musa ya yi murmushi ya ce, “Ai ba Sarkin nan kadai ba, kowa ya ji wannan labari ya yi dariya. Munafunci dai ba shi da amfani.”

Aku ya ce, “Ina ka san munafunci ba shi da amfani, tun da ba ka ji labarin Kado ba, da wadansu ‘yam fashi guda uku?”

Musa ya ce, “Har ya fi wannan dadi? Ban yi tsammani ba. To, yaya suka yi? Fada mini mu ji.”

Aku ya ce, “Wannan din me? Kasa kunne ka ji.”

Post a Comment

 
Top