0
MAGANA JARI CE LITTAFI NA DAYA

labari na goma sha uku


IN AJALI YAYI KIRA KO BABU CIWO AJE


In Ajali Ya Yi Kira, Ko Babu Ciwo A Je 
      Wata shekara mutanen kasar Suraida suka kai yaki kasar Niraini. Mutanen Suraida suka kori na Niraini suka kashe musu jama’a mai yawa. Suna murna za su shiga garin, ashe Sarkin Yakin Niraini ya shirya wadansu dakarai, suka biyo jama’ar Suraida suka yi musu zobe, suka hana su gaba, suka hana su baya. Da wani dakaren Suraida, wai shi Barde, ya ga za a halaka su nan tsaye da yunwa ma kadai, sai ya ce, wa ‘yan’uwansa, “Ya kamata mu yi kunar bakin wake. Kada mu mutu nan, mu bar wa na baya abin fadi.” Suka yarda, suka tasam ma mutanan Niraini. Barde ya fara kaiwa, ya soki wani dan saurayi, ya mace. Mutanen Niraini suka kashe yawancin mutanen Suraida, aka kama Barde, har an fara sassare shi za a kashe, Sarkin Yaki ya ce a kyale shi. Ya sa aka dauke shi aka kai shi gidansa, ya yi ta jiyyarsa ba dare ba rana, kamar dansa. Kullum safe, da ya fara iya magana, sai ya zo ya tambaye shi yaya ya kara ji.

Shi kuwa sai ya amsa masa, “Na gode Allah.”

Yana nan gidansa, ba ya iya tashi har wata guda, sa’an nan ya fara tashi da sanda yana doddogarawa. Sarkin Yaki na binsa, yana tare shi kada jiri ya kwashe shi ya fadi. Bayan ‘yan kwanaki, ya fara tafiya ba sanda. Ran nan yana tattakawa, ya dube shi, ya ce, “Yi tsalle mu gani, in ka iya.” Barde ya yunkura kamar zai yi tsalle, sai ya ji ba ya iyawa. Ya dubi Sarkin Yaki, ya ce, “Baba, ai ba na iyawa sai dai an kara kwana biyu.”

Bayan kamar kwana bakwai, da Sarkin Yaki ya ga lalle Barde ya warke, sai ya ce ya yi tsalle ya gani. Ya yunkura, ya yi tsalle, ya buga kafa, ya dube shi, ya durkusa ya ce, “Allah ya taimake ka yadda ka taimake ni.”

Sarkin Yaki ya ce, “Alhamdu lillahi, tun da ka warke!” Sai ya nufi cikin gida, ya dauko masu guda biyu, ya fito da su wajen Barde, ya ce, “Mu je bayan gari yawo, mu shawo iska.” Barde ya ce, “To.” Ya karbi masu ya rike, har suka isa bayan gari.

Da isarsu sai Sarkin Yaki ya ce masa, “Zabi daya.” Barde ya ce, “Me za mu yi da su?”

Sarkin Yaki ya ce, “Kai dai zabi daya, na ce.” Ya zabi guda gajere, ya mika masa dogon.

Ko da ya karba, sai ya ce masa ya tsaya nan, shi ya ja da baya kadan su yi yaki. Yaki ko na sosai, ba wasa ba, kowa ya sami dan’uwansa ya kashe.


Da Barde ya ji haka, sai ya yar da nasa mashin, ya ja ba baya, ya ce, “Subuhana lillahi, Allah ya sawwaka in yi yaki da kai!”

Sarkin Yaki ya ce, “Ko kana kasa kana dabo, sai ka yi. Cikin yakin da muka yi da ku watan jiya ina da a, kai ka sa mashi ka tsire shi. Na neme ka kasa da bisa lokacin nan, na rasa, sai daga baya har an yi maka raunuka za a kashe, na gan ka, na ga in na kashe ka sa’an nan ban huce ba, don lokacin nan kusa da matacce ka ke. Saboda haka na ce a kyale ka, na jiyyace ka, sai yanzu da na ga ka warware, ka iya jin zafin da dana ya ji, na ke so in rama masa, ko da ya ke ba shi da rai. Yana kan kokarinsa ka kashe shi, saboda haka ni kuma na ke so in kashe ka bisa kokarinka, ba sa’ad da ka ke ba wani makami a hannunka ba. Yanzu ko kana so, ko ba ka so, sai ka dauki mashin nan ka taso mini, sa’an nan ni ko in tsire ka.”

Barde ya yi tubar duniyan nan, ya ki ji, sai ya ce a ransa, “Da ma ni kusan cikin matattu na ke, shi ya kubutad da ni, to, tun da Allah ya nufa, don in kara shan ruwan wata guda ne kadai, aka nufe ni da tsira da fari, ai sai in yi godiya.” Ya dauki mashi ya rike.

Ko da Sarkin Yaki ya ga ya rika, sai ya zaburo zai tsire shi, yana tsaye yana Kalmar Shahada. Allah mai aikata abin da ya ke so, wallahi, yallabai, kafin ya kawo gare shi, sai kafarsa ta fada cikin wani ramin kurege, mashinsa ya kafe daga baya. Yunkurawan nan da ya ke yi da fushi, sai ya fadi da baya bisa mashin. Nan take ya tsire kansa, bai ko motsa ba. Da Barde ya ga haka, sai ya rungume shi yana kuka. Ya sa hannu a kai, ya shiga gari ya gaya wa Sarki yadda duk aka yi. Aka zo aka iske shi, aka yi ta mamaki, aka rufe shi.

To, tun daga ran nan Barde ya dauki alkawari yana kawo wa iyalin Sarkin Yaki abin da za su ci, har ya kan kawo musu awaki su sayar su sayi hatsi, duk dai wai saboda alherin da Sarkin Yaki ya yi masa.

Musa ya ce, “Wallahi in ni ne ko kasa ba na bada musu, tun da ya ke ba da niyyar gari ya yi mini alherin ba.”

Aku ya ce, “Ai ba kai kadai ba, kowa ma ya ji wannan labari haka zai ce.”

Musa ya yunkura zai tashi, sai ya ji an yi asalatu, ba damar ya fita, kowa ya farka. Da azahar tayi, Waziri ya ga ba zai sami Musa ba, ta ya rude shi da Mahmudu na can na abin kirki, sai ya sake dabara ya rubuto takarda kamar daga Mahmudu, ya aiko tsohuwan nan ta kawo wa Musa. Da ya karanta sai ya ga an ce, ‘Daga Mahmudu zuwa ga dan’uwana Musa, rabin ransa. Gaisuwa mai yawa da so da yarda. Bayan haka, Musa, yanzu kana da rai har ka yarda aka raba mu ko? To, ga shi jiya na fada wani barde cikin mutanen Sinari, ya yi mini raunuka abin ba ko masaka tsinke. Ga alamar da na ke ji a jikina, ni da ganinka kuma sai Darassalam. Tun da har ka manta da ni, ba ka iya kokarin da za ka zo mu nemi juna gafara ba, to, shi ke nan, ba kome, ni na roke ka gafara. Mutuwa dai ai kowa ka gani za shi ne. Musa! Musa! Tuna zumunci, Musa! Haza wassalam.”

Da Musa ya karanta wannan takarda sai hawaye. Tsohuwan nan kuma ta tsuguna ta yi ta yanka masa karya, wai gidansu (a ke jiyyar Mahmudu). Wannam takardar wai shi ya ba ta hannunsa da nata. Musa duk ya dimauta, mutanen gida suka rasa kansa, suka rasa gindinsa.

Da asubar fari, tun bayin nan ba su yi barci ba, sai ya kintsa, ya tafi wajen aku yana kuka, ya nuna masa takardan nan da tsohuwa ta kawo. Aku ya sa tabarau, ya karanta, sai shi kuma ya fashe da kukan karya, ko da ya ke ya san takardar ba Mahmudu ya yiwo ta ba, makirci ne. Sai ya ce wa Musa, “Sai ka yi shiri ka tafi.”

Musa ya ce, “Ina fa ka ga tafiya yanzu, ga bayi can ba su yi barci ba? Da ma abin da ya sa ka ga na zo tun da wuri haka, don in kawo maka takardan nan ne ka gani. In kuma kana da wani labari wanda zai dan faranta mini rai, ka gaya mini tun yanzu, ko na ji dan sanyi-sanyi a zuciya, kada in taho an jima in sun yi barci ka ce za ka tsai da ni, har in zo in makara.’

Aku ya ce, “Haba, ranka ya dade, in tsai da kai bayan na karanta wannantakarda, mahaukaci ne ni? Tun da dai ka ce kana son in gaya maka wani dan labari wanda zai sa bakin cikinka ya ragu, wannan shi ya fi kome sauki gare ni. Ga kujera nan, zauna, don tsayuwa ba ta da amfani.”

Mua ya haye kujera ya zauna zugudum. Aku ya yi kaki, ya tofad da yawu, ya fara.

Post a Comment

 
Top