HASKEN IDANIYA
HASKEN IDANIYA
parts 33
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Lokaci daya Kamar wacce aka zabura ta durkusa da sauri ta kwashe takalman ta da suka fado tasa su cikin leda,ta dago cikin hanzari ta na Mallam na gode,ba ta ma tsaya jin amsar shi ba ta fice ta na cilla kafa tanajan takalmin kafar ta. Mallam ya bi ta da kallo ya na jinjina kai,Allah da iko ya ke,shi kuma Muhammad wannan ce ta ma sa kenan,lalle Allah daya gari bam bam,kowa da kiwan da ya karbe sa.!
Ita kuwa Sumayya burin ta ta cinma Moh kan ya tafi,amma ina bakin alkalamin ya riga ya bushe,dan ko kurar sa ba ta tarar ba sai shatin tayar su da ta gani,hannu ta sa ta dafe kai,ta dade ba ta yi dana sani kamar na yau ba,ji ta yi kafafun ta sun kasa daukan ta,a hankali ta ja kaffafun ta da Dan tsinkakken takalminta tana cilla yar qafa,ta je wani dan dakali bakin dpment ta zauna,idanu cike da kwall,lalle ni Sumayya na cika butulu!duk kokarin bawan Allah nan dan ya mutumtani ji yanda na sa ka ma sa,ol his efforts ashe na yaban takalmi da zan sa a kafa ta ne......abun da ta ke fada kenan yayin da ta sa hannu cikin leda ta fito da takalmin da Moh ya siya ma ta. Hill ne jikin sa an bi an masa ado da white stones,gashi silver ba kayan da ba zai shiga da shi ba. Huhhw!ta saki ajiyar zuciya ya Allah ka kara hada ni da shi koda sau daya ne na gode ma sa.....ta mayar cikin leda,ta tashi za ta tafi kenan,takalmin ta ya karasa tsinkewa yanda kwata kwata ba za ta iya tafiya da shi ba,ba a san ranta ba ta fiddo da na Moh,abun mamaki ya ma ta daidai,abun ku da farar kafa,ya ma ta kyau kuwa. Ita kadai kunyar kan ta da kanta ya lullube ta,ita dai kam ba ta san irin Moh ba,da ba ya shaye shaye da an yi cikakken mutum. Zuciya cike da dana sani,bini bini sai ta kalle kafar ta,haka ta tafi gida da burin sake ganin Moh.
********
Da isar ta gida bayan ta gaisa da Gwaggo da ke zaune tsakar gida ita da lelen ta da tin shigowar Sumayya ta tsurawa kafar ta ido. Sumayya ta cire hijab din ta,zuciya daya ta cire takalmin da niyar sa slippers ta shiga toilet. Ganin takalmin da ta cire ya sa Lele daka tsalle cikin ihu ta ce Wooooow!!!Wayyo Adda wannan ajin fa!!!ba Sumayya da ta saki butar hannun ta dan tsoratar da ta yi ba hatta Gwaggo sai da ta tsorata ta zabura ta na kalu innalillahi wainnailaihir raji'un!!!hannu biyu bisa kirjin ta da ke dukan uku uku Sumayya ta ce Auzubillah,wai ke Lele yaushe za ki yi hankali ne dan Allah!!!!Lele kuwa ina hankali yayi gaba,takalman ne a hannun ta,fadi ta ke car uban nan!Aldo ne wlh!!!Gwaggo kin san tsadar takalmin nan kuwa? Dubi ki ga......ta matsa kusa da Gwaggo ta na nuna ma ta. Hankalin Gwaggo ya rude ta ji batun kudi,fadi ta ke kai haba Lele,mu gani,ta karbi takalmin,har nawa ya ke?zai kai nawa.......?
HASKEN IDANIYA
parts 34
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Tch!!!!!sautin da ya fito daga bakin Sumayya kenan ganin yanda Lele ta sa Gwaggo ta rude,ta dau butar ta ta shige bayi ta na jiyo Lele ta na ce ma Gwaggo wlh Gwaggo wannan takalmin sai dai dubu ishirin.....dubu ishirin?Gwaggo ta maimai ta,ita kuwa ina ta samo shi?ko aro aka ba ta?Lele ta ce bari ta fito ki tambaye ta Gwaggo.
Gwaggo sai shafar takalmin ta ke taji kudi tana girgiza kai,cafdi dubu shirin kidin buhun shinkafa da buhun masara kila ma har gero.....Lele ta sa dayan takalmin a kafar ta sai juya kafar ta ke, kinga daidai gafata kuwa tana juyawa....ganin fitowar Sumayya,Lele ta yi saurin cewa yauwa Adda,dan Allah za ki bani aro na sa ranar dinner din sch?Gwaggo ta kara da ke yar nan ina ki ka sami takalmin nan haka?butar ta aje,ta dawo kusa da Gwaggo ta nemi wajan zama sannan ta ce takalmi na ne ya tsinke shi ne wani ya bani wannan.....
Kai dan Allah Adda?Lele ta dawo kusa da ita ta zauna,kawai sai ya baki?wa ye haka san ki ya ke? Me ne tsakanin ku? Gwaggo ta kara da in ce dai ba ki ma sa wannan fuskar shanu da ki ke wa mutane ba?kin mai kwatancen nan ko?cike da kokawa Sumayya ta tashi ta na fadin shikenan ba a isa a yi taimako kawai a duniya ba?kai jama'a,babu abun da ke tsakani na da shi,babu abun da ya hada mu,tazarar da ke tsakani na da shi kamar tazarar da ke tsakanin sararin samaniya da kasa ne.....ta shige daki a fusace.
Gwaggo da Lele su ka kalli juna,Lele ta ce ikon Allah da magana sai cibi ya zama kari?Gwaggo ta ce kyale ta wa za ta nunawa zafin zuciya,wacce ba ta gaji arziki ba.......
Ta na shiga daki kan katifa ta fada,ta na jiyo su Gwaggo suna sunbatun takalmi,filo ta dauka ta danna kan ta karkashi,ita kan ta ta kasa gane me ke sa zuciyar ta tafasa haka,ko duk cikin dana sanin yanda ta yi wa Moh ne? Yau kam Moh na matuqar barazana cikin zuciyar Sumayya,gaba daya ta kasa dena tunanin sa,fuskarsa sanda ya sakar ma ta murmushin nan nashi kan ya aje ma ta ledar takalmin ke ma ta gizo cikin ranta,karo na daya da ta wuni da tunanin wani cikin ran ta a tarihin rayuwarya Huhhw!ta saki ajiyar zuciya,lalle sai ta nemi Moh ta ba shi hakuri,amma dai har yanzu ba ta ma san yanda za ta yi ta same shi ba. Sam wata yunwa Sumayya ba ta jin shi yau,nan ta kwanta kan ta karkashin filo idanun ta runtse,tin ta na jiwo surutan Gwaggo da lele,har baccin takaici ya yi gaba da ita.....
HASKEN IDANIYA
parts 35
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
***********
Gidan su Muhammad kuwa kannan sa ne Fatima da Zainab zaune a falo,Zainab ke bawa Fatima labarin yau sai ga Big bro a makarantar mu,da ke ba makaranta daya su ke ba. Fatima ta ruke baki,ke da gaske Zainab?Zainab ta ce wlh fa,da fari ni da aka ce yaya na ya zo kin yarda na yi, dan big bro din da ko hanyar makarantar mu be taba nunawa ya sani ba, ke banma san cewa yasan koda sunan skull dinmuba, ashe wai yasani, da kuwa na gan sa office din principle, na tabbatarda shine, tsorata ma na yi,na yi zatan ko wani abu ne ya faru,musammam da na ji ya ce zo mu tafi,gaba na be dena faduwa ba sai da na ji ya ce ba sai na dauko jaka ta ba yanzu za mu dawo.....habaa?ina kuma ku ka je?Fatima ta tambaya cikin zumudi. Zainab ta ce cewa ya yi na kai shi in da zai sami takalmin mata....M-A-T-A.....?Fatima ta maimaita hannu a haba cike da mamaki, . Zainab ta daga gira,yes mata sis,ke ma ba rannan ya gama tambayar ki kayan kwaliyya ba. Fatima ta dara eh kam,ki ce big bro an shiga yanayi....
Zainab ta jinjina kai,Hmmm yarinya sai ga Zainab kan bike din big bro,kin ji yanda ya ke gudu kamar walkiya ko ina kallonmu akeyi,,bike din ga dadi ga fargaba,ke wlh ban San sanda na kamkame shi ba dan na yi zaton zan fadi!Fatima dariya har da kwalla,ta ce matsoraciya,ina ku ka je kuma?......Boysenberry mu ka je,mun yi sa'a Innasco da Adda Zainab suna nan,su su ka taya mu zaba,tin da shi kan shi be san size din da ya ke so ba, amma kuma takalmin ya hadu wlh. Bayan ya maida ni sch ya sinna min rabo na. Fatima ta ce nawa ya baki?za ki bani rabo na ni ma?Zainab ta ce ina ruwan ki,je ki karbi na ki mana..ba ki da baki...Fatima ta ce uhum,ni kaza,na hakura,shi ya sa be zo da wuri ba,Dad ya karaci jiran sa wlh har ya yi fushi ya tafi....jin motsin kofa su ka yi shiru su ka nutsu,dan sun tabbatar Moh ne,ileko sai gashi ya shigo hannun sa ruke da hamlet. Welcome big bro...su ka fada a tare. Hannu kawai ya daga mu su ba tare da ya kalli in da su ke ba, kai tsaye ya nufi hanyar bangaran sa,kan ya kai ga kofar da zai sada shi da bangaran na sa Zainab ta tashi da sauri ta dan biyo sa ta na big bro.......jin ta kira shi ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Ganin haka Zainab ta gama tattaro nutsuwar ta,ta ce big bro dama so na ke na tambaya,wannan ummm amm wannan, as in ya yi sizing din ta kuwa......?ta karasa cikin sanyin murya da tsoro......shirun da ta ji yayi ya sa gwiwar ta sanyi,dama Moh ba a ma sa gwanin ta su dangin gidan maza. Ta na shirin juyawa sai ta ga ya juyo,ya na murmushi ya ce yes i guess........thank you precious......ya juya ya shige ciki ya bar Zainab da ta yi mutuwar tsaye jin dadin amsar ta shi,su dai su na son yayan su,su na so ya kula su, amma sam basa samun kulawar, da gudun ta koma wajan Fatima ta fada jikin ta.....Fatima ta tura ta na yau anci gari,ko ke ce wacce aka kaiwa sai haka,kin san me?tinda yarinyar nan ta iya Jan hankalin big bro,am sure she must be very classy,higly stylish,tall nd elegant.........Zainab ta dan yi kasa da ido kamar me day dreaming, ta kara da kuma fara ce siririya kamar ni.....Fatima ta ce ina......baka ce mai dan jiki kamar ni.........nan fa musu ya kaure,kowa so ya ke ta zama kamar ita, snan kuwa ba su san Sumayya ta wuce tunanin su ba.....
HASKEN IDANIYA
parts 36
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Moh sam ba ya jin dadin ran sa,ga abun da Sumayya ta fada ma sa na ya fita daga rayuwar ta, yana bala'en motsa ran sa,gashi Dad ya tafi ya na fushi da shi......nd d worst part of it shi ne Sumayya da ta ce ya fita daga rayuwar ta ta,hez a honourable guy,be da wani choice da ya wuce ya ma ta yanda ta ke so.....ba tare da bata lokaci ba ya shiga sana'ar da ba riba,wato shakar farar powder..........
*******
Washagari Sumayya da shirin ganin Moh ta shiga sch,amma ina ko kurar sa ba ta gani,haka ta karaci zuba ido har ta hakura.
Sanyi ake sama sama,kusan sati daya ya rage su fara exam,kai yayi zafi sosai. Sumayya ta fito daga library za ta masallaci,ta hangi Moh tare da abokan sa. Yau ga wanda ta ke fatan gani,duk da ba ta da wani kwarin gwiwa ta yi saurin nufar su.
Sam be lura da ita ba,duk da shi ma idaniyar shi na kyewar ganin hasken fuskar ta, kuma wani lokaci idan xatabi hanya ta wuce ya naji a jikinsa, cewa xatabi hanyar, Fita za su yi dan haka duka sun dora hamlet din su kenan,Moh ya gan ta gaban sa,Shamo ya ce ga kayan Moh.....Sumayya ta yi kasa da idanun ta,ta na shirin magana ta ji karar tashin bike,da sauri ta daga ido,wayam ba kowa gaban ta sai kura,Moh ya yi gaba abun sa haka ma gang din sa....guiwar Sumayya ta yi sanyi,ba ta ga laifin Moh ba,jiki ba dadi Allah ma ya so ba kowa wajan, da tafijin kunya, ta wuce masallaci.
Shi kuwa Moh sai da ya cije ya jajirje ya iya tafiya ba tare da ya kula Sumayya ba,ba yanda zai yi ne amma it is killing him inside,su na fita maimakon ya bi hanyar da su ka saba bi,sai su ka ga ya baude,gudu ya ke kamar walkiya,duk yanda su ka so su cimma ma sa sai da su ka hakura,lalle ran sa ya baci kenan,dama idan ransa ya baci yakanyi irin haka, amma kuma sukan kamoshi, wannan yayi worst, ya riga ya wuce, su ka juyo su ka rabu da shi tare da fatan Allah ya tsare....
HASKEN IDANIYA
parts 37
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo
*******
Kwanci tashi,yau Sumayya ta gama exam,sam burin ganin Moh ya fita ran ta duk da de ta kan hange shi daga nesa nesa,deep inside her she missed him. Kuma sanadin sa ana ba ta girma da mutumci sosai ba kamar da da ko wani kare da biri ke iya taka ta ba.!
Bayan komawar ta gida ne Gwaggo ke fada ma ta watan haihuwar kanwar ta Bilkisu ya kama,gobe za tafi London in da ta saba zuwa haihuwa. Sumayya ta ce Allah sarki,Allah ya raba lfy. Gwaggo ta ce ameen,shi ne ta yi waya,ta na neman wanda zai zauna ma ta da yara tun da su na makaranta kuma Baban na su shi ma ba ya gari......ba tare da ta kawo komai cikin ran ta ba ta ce dandai yara biyu ita ma dai ai da nan ta kawo su.... Nan?Gwaggo ta kame baki,yaran da su ka saba da gidan hutu ina za su iya zama gidan nan,ki na gani ko wuni da kyar su ke iya ma na...mstw!Sumayya ta ja tsaki,dan iyayen Nada kudi su ba nan uwar ta su ta tashi ba? toh kam sai su ta zama,a samo mai zama da su lfy.....Gwaggo ta ce ai an ma samu,dazu na nemi alfarmar Baban ku,kin ga tinda kin gama jarabawa sai ki dan zauna ma ta........ni kuma Gwaggo? Sumayya ta nuna kan ta,Gwaggo Bilkisu fa kanwa ta ce,ina ma lefi a tura mata Lele ya xanje gidan qanwata tsoron yayaaa.......
Ungu nan!!Gwaggo ta ma ta dakuwa,sokuwa kawai!!!ba za a tura Lelen ba,ke in ki ka zauna me za ki tsinana min a gidan?ke ba manema ba kamar Lele bare ace kar a zo a ta neman ki ba dadi,ita Lelen ba jarabawa ta ke ba,kai ko da manema aka bar ta sun isa a ce ta zauna a gida!!har wani kanwar ki ce Bilkisun!!!!kanwar ta ki din ai ita da auren ta dan haka ta zama gaba da ke,in hakan ya mi ki ciwo ki fidda mijin aure a mi ki ma na!dan haka ki shirya za ta aiko gobe da safe a dauke ki.....ta na kare maganar ta shige ciki ta bar Sumayya zaune kwalla cike idanun ta,oh ni Sumayya,sai ka ce ni na hana a aure ni ya Allah ka kamin sauki,abun da ke fita daga bakin ta kenan ta na share hawayen baqin ciki,

parts 38
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Kamar yanda Gwaggo ta fada da safe driver ya zo ya dauki Sumayya,ba a san ran ta ba ta koma Sulemanu crescent renon 'ya'yan kanwar ta,dan ko haduwa da kanwar ta ta ba su yi ba,sai dai magana a waya,gashi yaran sam ba sa ji,an bata su da yawa, shegen sangarta da rashin kunya,,babban ke da shekara shida wanda ake kira Amir,sai karamin mai shekara hudu wanda su ke kira Sadiq.!
*********
Satin Sumayya daya a Sulemanu crescent,yau asabar an wayi gari cikin sanyin hunturu,sanyi ake na gaske. Da sassafe Sumayya ta bi gidan ko ina ta kunna room heather,tuni dumi ya game ko ina,da ke ana sanyin sosai ma su aikin gidan ba su zo da wuri ba.
Dakin su Amir ta shiga,dan duba yanda su ke. Lullube ta gan su cikin bargo,sai baccin su su ke,ta gyara Mu su kwanciya sannan ta dawo dakin ta da tuni ya yi dumi to the extend dat har ta fara dan zufa da ke sanye ta ke cikin rigar barci mara hannu sai ta dora rigar sanyi a sama. Ganin haka sai ta cire rigar sanyin,ta na kokarin bin lfyar gado ta ji kamar karar wayar falo,cikin zuciyar ta ta ce ba mamaki Bilkisu ce,wayar ta ta dauka ta duba,misscals din Bilkisu ne ba adadi,da ke ita Sumayya mantawa ma ta ke ta na da waya,ta ce uhum i tot as much,bara na kira ta,ta na kokarin kira wayar falon ta ji ta ci gaba da kara,dan haka sai ta aje na ta,zuciyar ta daya dan ta san daga ita sai yara ta fito abun ta ba tare da ta damu ta mayar da rigar sanyin na ta ba koma ta sa hijabinta na gadoba....!!

parts 39
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Kan ta kai ga wayar ta tsinke,ta dan tsaya jim gaban wayar,kamar saukan aradu ta ji muryar shi cikin kunnan ta ya na ashe kin tashi......a razane ta juyo,wa za ta gani?Dawud ne mijin Bilkisu tsaye daga shi sai singlt da boxers, ganin sa da kuma irin shigar da ke jikin sa Sumayya ta dan dada gigicewa,mutum ne jibgegen gaske ga tsayi ga jiki,bam da ma Bilkisu ta ga kudi ina ita ina Dauda. Kan ta a kasa Sumayya ta fara shirin barin wajan,da kyar ta iya furta cea ashe ka dawo....!? dan kuwa ganin na shi ya ma ta bazata,bare ita gidan su ba namiji ko daya dan haka ba ta saba ganin namiji da shiga irin ta sa ba......
Maimakon ya ba ta hanya sai me?sai bin in da ta yi za ta wuce yayi babakere ya tsaya ya na fadin jiya wajan dayan dare na dawo ai,ko kanwar ta ki ba ta san da sauka ta ba Adda...cikin rashin fahimtar komai Sumayya ta tsaya cak kan ta a kasa,duk da ta kasa daga kai ta kalle shi tabbas kellon ta ya ke tin daga sama har kasa.....shirun da ta ji ya sa jikin ta ya ba ta hakan,kamar wacce aka kwararawa ruwan kankara haka ta ji yayin da ta farga ta tuna da na ta yanayin shigar,ba suturar ta ba mutuncin ta ba hijabin ta jikin ta,da sauri ta dada yunkurawa za ta kauce dan nemowa kan ta sutura......amma da ke Dauda numba daya ne sai ya kara tare ta ya na saurin me ki ke haka ne,ai na ga in da kara ko nima kanin ki ne,ashe haka ki ke a dire amma ki ke boyewa cikin hijabi, ai kinfi bilkin diri mai kyau adda......A fusace Sumayya ta ce dallah Mallam matsa min na shige,ka na hauka ne?amma sai me?maimakon ya bata waje ta wuce sai ma fara motsowa kusa da ita da ya fara......ya na ma ta murmushi mai ban takaici......
Hankali tashe Sumayya ta fara ja da baya tin da masifar da jan ido ba zai yi ba,ta fara rarrashi,fadi ta ke Dauda ba ka gane ni ba ne,Sumayya ce fa Addar matar ka,yayar matar ka ce Dauda,ta ga matsowa dai ya ke,ta yi hagu yayi hagu,ta yi dama yayi dama,ya ce tsaya ki ji Adda,ki manta da ni mijin kanwar ki ne,kin san dai a haife dai na haife ta,ke kuma na girme mi ki nesa ba kusa ba,so kimanta da wani batun auren kanwar ki mu huta abinmu.......

parts 40
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Innalillahi wainna ilaihir rajiun......Sumayya ta fasa kuka.....lokaci guda waya ta shiga ringing ta na sowa Bilkisu ce ta sake kira,amma Inaaaa daga Sumayya da hankalin ta ya gama tashi har Dauda da ya gama zurfi cikin tunanin mugun nufin sa ba wanda ya lura da hakan...........
Sumayya na ja da baya ta na kuka ta yi tuntube da tinti da ke aje falon,ta fadi kasa,ganin haka Dauda ya saki wani murmushi ya ce ki hakura Adda ki bani hadin kai, kema kiji yanayen system din......da sauri ta tashi ta na dan Allah Dauda ka duba mutuncin addinin ka da ya haramta ma ka taba matar da ba ta ka ba,kar ka manta Allah subahanahuwata'ala ya fada cikin alqur'ani mai girma kar mu kusanci Zina,kasani Manzo(S.A.W) ya ce idan mace da namiji su ka kyebe na ukun su shedan ne,na san shedan ke maka huduba mafi muni a rayuwar ka,wlh da ka taba ni gwara na mutu,wlh da ka taba ni gwara ka sanya hannun ka cikin wuta..........a haka har ta kai bango ya kure,kuka ta ke wiwi daya na bin daya,waya ba ta dai na ringing ba,da ta katse sai ta cigaba....
Dauda ya yi nisa,ba ya ji ba ya gani,burin shi ya taba Sumayya,ganin Sumayya jikin bango yayo kanta gadan gadan,ganin haka Sumayya ta runtse ido ta kurma ihun da shi kan sa Dauda sai da ya yi baya da sauri,dama Sumayya ba daga nan ba wajan ihu.......a gigice ganin Amir da Sadiq sun fito a guje Dauda ya wayence ta hanyar fadin ni?ni ki ke zagi Sumayya?Amir ya na Dady menene wai?Dawud ya ce wannan Yayar uwar ta ku ce daga kawai na ce ta doran ruwan zafi sai ta hau zagiba da ihu kamar mai iska......
Idanu cike da hawaye Sumayya ta dago ta na kallan Dauda,ba kunya bare tsoran Allah ya sa yara a tsakiya ya na shirga mu su karya, ai dole tarbiyarsu ta gurbata, dan takaici Sumayya ba ta san sanda ta rufe shi da zagi ba,fadi ta ke mugu azzalimi,wallahi abun da ka min sai ka gani a kwayar cin tuwan ka,tir da miji irin ka.......wayar ta fara ringing da gudu Amir ya je ya dauka ya na wlh sai na fadawa Mommy ki na zagin Dady,ya daga ya na hello Mommy Anty Sumayya ke zagin Dady......ina Sumayya ko bin ta kan su ba ta yi ba,Bilkisu na ji ta cewa Amir ka bawa Auntyn na ce!!Amir ya dauko wayar ya na mi ka ma ta,ta bike wayar ta fadi kasa,Bilkisu na Hello,Adda kar ki kashe min aure wlh idan wani abu ya sami aurena ba zan yafe mi ki ba.......

parts 41
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Shi kuwa Dauda da ya riga ya san tarkon da ya dana fadi ya ke ba laifin ki ba ne,ba laifin ki bane laifin mata ta ne tin da sanadin ta mai nakasa kamar ki ta sami lasisin ci mun mutunci......Sumayya ta harzuga ta ce nakasa gare ni a zahirance amma a zuci kafi kowa nakasa,shashasah mara mutunci,dabba na tausayawa Bilkisu,in har haka maza su ke gwara na mutu ba aure....ta na gama fadan haka ta shige ciki da saurin ta,Bilkisu hauka ne kawai ba ta yi ba,kawai yayar ta na zagin mijin ta,ta kashe wayar ta sake kira,Dauda ya daga ya shiga shirya ma ta karyar yanda aka yi.!
Sumayya kuwa ta na shiga daki hijab da zani kawai ta iya dauka ta sa,silifas ne kafar ta,ta fito ba ta ma san inda ta dosa ba,ta na ji Sadik na fadin laa Aunty Sumayya ta fita,Dauda ya ce kin ji ma ta fita ko?me Bilkisu ta ce oho......
Tafiya ta ke tana kuka,wani irin sanyi ke busa ta gashi hijab kawai ta sa ba ta maida rigar sanyin ta ba. Da sanyi yayi sanyi,iska na kada ta gashi ba ta da ko sisi dole ta ja gefe,ta na kakkaura,ta na rawan sanyi.
Ba kamar kullum ba,dan yawan na su yau ya sha bambam,dan a kalla mun dirga bikes kusan ishirin,sai da su ka cika sannan su ka tsaya kofar gidan su Moh,ba tare da bata lokaci ba ya fito da shigar sa cikin bakaken kaya tin daga sama har kasa,hatta hamlet din sa baki ne,ga katan jacket da ya rufe shi ruf ba a kanin fatar jikin shi ko kadan. !
Kai tsaye su ka dauki hanya,Abuja su ka nufa,Ba su kai ga nisa ba ya hange ta sai rawar dari ta ke,kuma da alama kamar kuka ta ke,ya so ya dake ya wucewar sa,amma ina ya kasa,kawai sai ganin shi su ka yi ya ja ya tsaya gaban ta dan haka dole kowa ya tsaya...

parts 42
Na Khadija Sidi & Hauwa M. Jabo.
Kuka ta ke ba kakkautawa,sai jin karar bike ta yi gaban ta,ta dago a hankali ta bi su da kallo,ganin yawan su da shigar su gashi duk fuskokin su rufe cikin hamlet ya firgita ta...ta dan yi baya,Moh ne ya sauko daga na sa bike din,ya cire hamlet din sa ya na duban ta,tuni ta waye shi,hankalin ta ya dan kwanta.....haka sauran ma duka su ka ciro na su,daya daga cikin su dake groups din bike riders ne ba su Shamo kadai ba, cikin rashin fahimta ya ce me ya kawo tsayuwar mu?Shamo ya nuna ma sa Sumayya ta tare da fading if am nt mistaking kayan Moh ce.........daya ya ce ka na nufin..kan ya karasa Moh da idanun sa ke kan fuskar Sumayya, a hankali muryansa a sanyaye, ya ce ku wuce kawai,zan biyo ku. Ba musu dan su Shamo sun san za a yi haka,su ka maida hamlet din su su ka yi gaba...
Gaban ta ya tsaya ya na nazartar ta,daga bisani ya ce what is wrong?me ki ke yi a nan?maimakon ta bashi amsa sai ta dada fashewa da kuka,mutane da ke wucewa sai kallon su suke,bare Moh unguwar su ce ba wanda be San shi ba. Ganin haka Moh ya aje hamlet din sa kan bike,ya matso kusa da ita ya na shhhhhsh!!!kar ki tara min jama'a mana,kamar wacce aka zuga,sai ma dada rera kukan ta ta ke.
Moh ya daga kafada ya sauke tare da fadin shikenan cry all you want.....cry ur hrt out. Ya sa hannu a aljihu ya fidda hanky ya mi ka ma ta. Ta karba ta na kokarin goge hawayen,amma ta kasa tsada su. Sai da su ka kai kusan minti goma sha biyar ta na sharbar hawaye,ya jingina jikin bike din sa kafafun sa harde hannu cikin aljihu ya na kallan ta. Sai da ta yi mai isar ta,ta koma sai ajiyar zuciya kawai ta ke. Moh ya taso ya na cire Jacket din jikin sa,wani irin iska mai sanyi ce ta buso su,sai da Sumayya ta girgiza,idanun sa kan ta,ya karasa gare ta,Jacket din sa da ya ciro ya rage da ga shi sai rigar sa ta ciki lng slip ya daura kafadar Sumayya ta hagu,ya zagayar da ita ta bayan ta,ta sauka bisa kafadar ta na hagu,ya ma ta kamar mayafi,a hankali Sumayya ta dago idanun ta da ke cike da kwalla su ka shiga na sa yayin da ya sakar ma ta murmushin da ta ji shi har ran ta,ya ce even when you are crying you are beautiful too....

Post a Comment