0
ILIYA YA GAMU DA GOGAJI


 


ILIYA YA GAMU DA GOGAJI


by yasima suleiman

Duk irin wadannan labarai na ban
tsoro, ba su
firgita Iliya ba, sai ma suka kara
masa karfin
tafiya. Ya ce, Ni dai ku nuna mini hanya
kawai. Idan na halaka, Allah ya hada
mu da
alheri a ranar kiyama. In kuma na
kubuta, to
Allah ya sa ina da halin dawowa garinku in sake
taimakonku fiye da wanda na yi
muku a yanzu.
Suka hakura dai suka kyale Iliya,
suka sa
shi a hanyar Birnin Kib, suka yi masa rakiya,
suka yi ban kwana ya tafi. Ya yi
kwana da
kwanaki cikin kungurmin daji, babu
kome, daga
tsaunuka sai duwatsu; sai kwazazzabai da
kurama. Wani lokaci ma ruwan sama
ya ba shi
kashi. A wadansu wuraren ma kamar
Allah bai
taba sa wata halitta ta bi ta wurin ba. Kwance
tashi, ran nan sai Iliya ya shiga dajin
da Gogaji
ya ke. Yana ta tafiya har ya kai
ainihim inda
aka ce yana zama. Tun daga nesa Gogaji ya habgu Iliya
tafe.
Abin da ya rabu da gani shekara da
shekaru! Sai
ya yi maza ya zaro kulkinsa, ya shiga
shiri, yana lashe-lashen baki. Ya nufi wajen
Iliya, yana tafe
yana kuwwa, hayaki nan fita daga
bakinsa.
Saboda tsananin gaza da kururuwa,
har Kwalele ya firgita, ya yi sassarfa, ya
durkushe. Iliya ya
husata, ya buge shi, sa an nan ya
mike. Gogaji
ya taso wa Iliya haikan zai kashe
shi. Amma Iliya ya tuna da alkawarinsa, ba zai
yi fada da
makami ba. Sai ya ballo wani itace
ya gyara,
ya dana a bakansa maimakon
kibiya. Ya auni Gogaji da kyau, a kahon zuci, ya
sakar masa.
Maimakon ya same shi a kirji, sai ya
same shi
cikin kunnen hagu, ya bullo ta kunnen
dama. Gogaji ya yi sama ya fado, ya tashi
ya yi wata
irin kara, ya sake faduwa rim! Sai ka
ce giwa ce
ta fadi.
Nan da nan Iliya ya sauka ya kukunce
Gogaji, ya daure shi da asalwayin
dokinsa, ya
kada shi gaba suka nufi wurin
kwanansa, watau
wurin da ya yansa su ke. Suna tafiya, har suka ketare wani
kwazazzabo, suka isa wata korama
mai kurmi, a
tsakanin duwatsu. Wurin kuwa wani
katon
lambu-lambu ne, an shafe tsakiyarsa da duwatsu
kamr sumunti. An kakkafa wadansu
manyan
karafa kamar azaru, an yi babban
daki.
Da ya yan Gogaji suka hango su Iliya tafe,
tun daga nesa suka fara murna suna
tsalle, suna
cewa, Alo, ga baba can tafe, ya
kawo mana
nama. Ashe yau muna da shagali! Wannan ya
ce ni ke da kai, wannan ya ce shi ke
da ido. Sai
Malel, wanda ta iya shirin nan ta ce
musu, Kai
sakarkaru, ku duba sosai, yau ubanmu ne aka
kmo, ba shi ne ya kamo ba. Sai suka
yi kuri da
ido, suna jiran su Iliya su iso. Tun
daga nesa
Gogaji ya ce wa ya yansa kada su sake su
taba Iliya. Amma duk da haka sai da
Malele ta
ciro daya daga cikin azarun nan na
karfe, ta
kwada wa Iliya a kai. Iliya ko dubanta bai yi
ba. Ta sake dagawa za ta kara, sai
Iliya ya
husata, ya sa hannu ya fizgo ta, ya
jefa ta
sama, ta fado, ta ragwargwaje. Gogaji ya ce,
Ai na fada muku. Ga irinta nan. Ya ce
wa ya
yan su kawo birgmanin zinariya dari,
da birgamin
azurfa metan, da na lu ulu u hamsin, su ba
Iliya, don ya sake shi. Iliya ya ce,
Bari
kayanka, ba ni son ko anini. Bukata
ta in tafi da
kai Birnin Kib. Ya tura keyar Gogaji, suka
kama hanyar Birnin Kib. Ya bar ya
yan Gogaji
suna ta kuka.
Ana nan kwance tashi, suna tafiya,
har ran nan suka kai Birnin Kib. Iliya bai nufi
ko ina ba,
sai ya tafi masallacin garin. Ya daure
dokinsa,
yskum daure Gogaji, ya ce masa
kada ya sake ya ce zai gudu. Gogaji yace wane shi
da zai iya
gudu. Nan da nan Iliya ya tafi fada,
ya aika a
fada wa Waldima, Sarkin garin
cewa, ga shi ya sauka. Ya fito daga Kanifo ne, ya
biyo kuwa ta
hanyan nan da ba ta biyuwa.
Waldima ya yi
mamaki kwarai, har bai yarda da dan
sakon ba. Ya sa aka isa da Iliya wurinsa. Ya
tambayi Iliya
garinsu, da labarinsa. Iliya ya fadi
duk abin da
ya gudana tun daga farko har
karshe. Amma duk da haka Waldima bai gaskata shi
ba sosai
cewa ya biyo ta wannan hanya.
Wadansu a nan
wurin ma sai suka rika ce wa Iliya,
Karya ka ke yi. Hanyar da manyan barade da
dakaru suka
kasa bi, sai kai za ka ce ka biyo ta
kai kadai!
Daga nan ran Iliya ya baci, ya ce, Ku
tashi mu tafi babban masallaci, zan gwada
muku shaida.
Sarki da Sarauniya, da mutanen gari,
suka
dunguma sai masallaci. Kowa ya yi
arba da Gogaji daure, sai ya yi baya kamar
bera ya ga
kyanwa. Duk wuri ya rude, sai
mutane ke ta
gudu suna komawa gida. Da Iliya ya
ga haka sai ya daka wa mutane tsawa, suka
kara razana fiye
da ganin Gogaji, suka rasa inda za
su nufa. Duk
suka yi dabur. Wadansu suka fadi
kwance, wadansu suka shiga cikin kwaruruka
suka buya.
Waldima shi da kansa ya firgita, ya
ce wa Iliya,
Mun yarda, lalle ta wannan hanya ka
biyo, don kuwa mun ga shaida ta sosai. Yanzu
sai mu tafi
gidana ka huta, ka ci abinci sa an nan
da
marece, mutane za su taru, mu sake
zuwa kallon Gogaji. Muna so ka sa ya yi irin
gazan nan da
ya kan yi wa taron mutane, idan ya
tare su.
Iliya ya ce, To, yanzu yana jin
yunwa, sai a kai masa abinci, da giya, don ya cika
cikinsa, ya ji
dadin yin gazar. Waldima ya sa aka
kai masa
tulunan giya wajen metan, da
kabukan abinci masu yawa. Gogaji ya ci ya koshi.
Kafin marece, duk labari ya watsu
cikin gari,
kowa ya kosa lokaci ya yi, ya zo
kallo. Sarki da
Sarauniya suka ci ado, suka wuce gaba jama a
ta bi su, tuu, sai wurin Gogaji, Iliya
ya ce, Kai
Gogaji Sarki Waldima yana so ya ji
irin gazan
nan da ka ke yi wa mutane idan ka tare su a
hanya.
Gogaji ya bude ido ya ga mutane
jigim. Ya
yi dam murmushi, sa an nan ya kafa
bakinsa kasa, ya tattake ya yi wani irin ruri,
wanda bai
taba yin irinsa ba. Kamar aradu
goma suka fadi
gaba daya. Kasa dai kamar za ta
tsage a lokacin. Mutane don tsananin firgita
har suka
kasa gudu, suna zato duk inda suka
nufa za su
hadu da shi ne. Wadansu suka some
a nan, wadansu suka fadi kwance wai suna
jira mutuwa
ta zo ta dauke su. Makarrabai don
razana har
suka kade Sarki da Saruniya, ba su
sani ba don firgita. Daga nan Iliya ya daka wa
Gogaji tsawa
don ya yi shiru. Wohoho! Iliya-dam-
mai-Karfi
Tsawar da ya yi har ta fi gazar
Gogaji ban tsoro. Mutanen da ke da dan saauran motsi
sai suka
katse sosai suna zato ko Gogaji ne
ya taso zai
halaka su. Gogaji shi ma kuma can
ya firgita ya raasa wajen da zai nufa. Ya fadi
gaban Iliya a
gigice, yana hurwa, ya na cewa, Na
ba ka
dukan dukiyar da ke gidana, ni dai
kada ka halaka ni. Iliya yace was Gogaji Ba
ni son
kome naka. Kashe ka zan yi, wannan
shi ne
sakamakon abin da ka yi wa mutane
shekara da shekaru.
To, alkawarin da Iliya ya yi ya cika,
tun da
ya kawo Birnin Kib bai zubad da jini
ba. Daga
nan ya tafi da Gogaji bayan gari, ya ciro
kibiyarsa guda ya dana ya sakam
masa a
makogwaro. Gogaji ya yi tsalle
sama, ya fadi
matacce. Iliya ya koma fada, ya fada wa Sarki.
Jama a duk suka yi ta murna. Shi
kuma Sarki
don nuna farin cikinsa ga Iliya, sai ya
tara dukan
manyan garin da attajirai, ya shirya biki
kasaitacce. Bayan Iliya ya huta
kwana kadan,
sai yayi ban kwana da Sarki, ya ce
zai ci gaba.

Post a Comment

 
Top