0
AURE KO ZAMAN GIDA ?




 
AURE KO ZAMAN GIDA?


****PART 9****


Jikina a mace nayi sallah dan abin ya dauremin kai
jin cewa azeez yanada mata harda yaro, Muci abinci
sai muci gaba ko jabo nace ai ina azumi ta kwashe
da dariya, kinmanta kinsha fresh milk dazu nima
abin ya bani dariya dan kawai insha labari nace ina
azumi tamana girki indomie mukaci a gurguje taci
gaba da bani labari...
In gayamiki jabo kamar ance fito dan ba inda nake
zuwa sai wani park na bayan gidana shima mutane
suka fara damuna suna cemin (siya pust)Baqar fata
kenan nadaina zuwa ina gida abina ina fitowa
naganshi zaune dirshan cikin sanyi yana kuka wllhy
jabo ko kwaya zarra banji ya bani tausayiba
hasalima wani tsanarsa da nayi duk lokacin bansan
yanada mataba, Ina kallonsa miyaji sai naga ya daga
kai da qarfi ya kalloni hadi da wata irin kyakyawar
aziyar zuciya, Ya miqe tsaye ya bude qofar gidan ya
shiga kai tsaye na koma inda nake har magriba ban
shigo gunsaba nama manta dashi inachan gurin
makwabtana yar tsohuwa dai tagane akwai wani
abu (chi shod dokhtaram?) Miyake faruwa yata
( hech) ba komai (pas chira shoharat omada wali to
khushhal na shodi ?)To miyasa mijinki yazo bakiyi
murnaba(Hech momon alan miram pishash)Ba
komai mama yanzu zanje gurinsa(Affarein dokhtari
khub zud baro guna dore az rahi dur omade
istiqbalash ham na karde)Da kyau yata yi sauri kije,
Bazaiji dadiba ace yadawo daga tafiya amma kinqi
kije tarbarsa, (Boshe momon)To mama. Na fito sumi
sumi na shigo a parlour naganshi zaune yayi wujiga
wujiga dashi ya kalleni ina shigowa ya miqe tsaye
naja natsaya na dauka zai kwasheni da wani marine
kamar yanda yayimin a airport, Amma sai naga
sa6anin haka, Durqusawa yayi gabana yana kuka
kaman qaramin yaro yana bani haquri ya cutar dani
yayita surutansa har yagama bance masa komaiba,
Yatashi yagoge fuskarsa wai inshirya zai maidani
wurin aikinsa nanfa aka fara sabuwar rigima dan
bazan yarda yakaini wani sabon guri ya ajiyeniba
alhalin bansan kowa agurinba, Nan nashiga rera
kuka yazo yana lallashina amma naqiyin shiru, Yayi
yayi naqiyin shiru sai shima ya zauna ya fara kuka
lokacin abin ya bani mamaki ace kamarsa yana
kuka sai ya bani tausayi ahankali na daina kukan
natashi na bashi guri intaqaita miki jabo saida yayi
nasarar barin wannan gidan dani...
Kukasance tare dani a


 AURE KO ZAMAN GIDA ?


*****PART 10*****


Nayi kewar maman sumayyah maqociyata sosai
amma yana iya sai haquri, Zamana dasu na waye
sosai kuma nayi clean coz sumayya yarta yar
duniyace irin shigar datake agida da yanda take
hulda da mutane nima na koya dama nima ba
bayaba gurin shed'ana lokacin idan kika ganni sai
kince nayi karatu ne wata university jabo....
Mun isa gidan da zamu zauna, Gida qaton gaske
yanada part biyu a dayan gefe muka wuce da
kayana gidan yaci uban gidan da na zauna sau dubu,
A parlour na zauna fuskata a daure yaqare gyara
komai ya siyomin pizza inajin yunwa dole naci, Yazo
yazauna yaci gaba da bani haquri har ya gaba ban
ce mishi komaiba, Ina kwance ina game da wayata
najiyo hayaniya awaje kuma ga dukkan alamu da
hausa ake fadan hayiniyar tayi yawa kamar ma
gidana ake yinta ina fitowa nayi karo da wata mata
yar lukuta da ita dan takaiki jabo an, Ina zuwa abdul
azeez yachanza yare yakoma farsi yace (turu khuda
ba zabani khudamun juluyesh harf nazan namikhom
alan bi fahme)Dan Allah karkiyi magana da hausa
dan banason yanzu ta gane abinda muke ciki, Matar
itama da yaren tace (khub agyar nami khod bi fahme
y kari kun)Idan bakason ta gane kasan yanda zakayi
dani, Sukayi ta magan ganu da yare inajinsu basusan
adaqe nake kallonsuba dan duk inajin abinda suke
fadaba gashi batama iya yaren ba, Abin yabani
dariya sosai yanda take cewa sai ya maidani inda
yadau koni ita bazata zauna daniba, Araina nace
nima bari in ta6a nawa iskanci dana koya agurin
sumayyah, Na matso kusa dashi na rige hannunsa
yanda koda yayi qoqarin kwacewa bazai iyaba nace
masa eshqam (my dear ) Wannan matar da ka samo
tazo tana mana haushi agida kaman karyafa?? Ta
juyo da qarfi da daga hannu ta wankeni da wani
wawan mari, Kaji tassss itama ya wanketa da mari
nima na wanketa da mari sai tayi sololo tana
kallonmu dan gaskiya ta mata yawa nima nasan nayi
jarumta jabo, Dan matar agirme ta girmeni takai
34yrs fa nasaka hannuna na damana rungumeshi ta
baya na kwanta a qirjinsa, Nace mata duk iskanchin
da zakiyi karki kuskura kice zaki dagawa mijina
hankali najawoshi shiko solon sai ya biyoni nashiga
daki na kullu qofa ni na barta a parlour tana zage
zage ta fasa abunda zata iya fasawa ta gaji ta tafi,
Ingayamiki jabo tunda nashiga daki na wuce bayi na
kulle kaina shiru har yakirani na kunna ruwa yaji
qaran ruwa yasan dai cewa inajinsa yayi jira yayi
buga gofa har ya gaji nayi banza dashi, Kinsan
wannan matar wai matarsace ashe dama yayi aure
har sunada yaro, Ke wllhy jabo haka nasamu kaina
ina bala'een kishi da matarsa dukda nasan cewa
banasonsa, Amma matar ta bani haushi, Nayi kuka
har na nagaji, Nidai bansan bala'een da yake biye
daniba niba uwaba dasai ingayamata haka nayi ta
fama da baqin cikin kishiya amma duk da haka
tsorona take dan duk bala'een da zatayi bata zuwa
kusa dani saidai tayi nesa dani, Ataqaice ingayamiki
hauwa jabo, Matarnan maza takebi ke hatta yaron da
ta haifa ba na azeez bane kuma duk ni na ganesu,
Yanda akayi kuwa shine....

Post a Comment

 
Top