AURE KO ZAMAN GIDA ?
AURE KO ZAMAN GIDA ?
:::::::PART 7::::::
…Ban waigibo hasalima banjishiba saboda na tafi
duniyar tunani, zainab ce.??
Na waigo sai naga wani kyakyawan mutum dogo fari
tareda yan sanda guda biyu, Sukayi yare sai naga
sun juya suntafi, Ina dago kaina ya kwasheni da
wani wawan mari saida na fadi qasa, Anan nace
Lallai ma mutuminnan dan iskane ya aureni ya
ajiyeni gidan ubana shekara biyar, Sannan yakawoni
gidansa wata tara, Ba kulawa, Yaturoni daga qasa
zuwa qasa ni kadai saida na hau mutuwa(jirgi) sau
shida sannan inyi kwana hudu ina garari qasa da
qasa inzo ya rasa mizai sakamin dashi sai mari
gashi banida lafiya , za'ayi ta kuwa dan wllhy sai ya
sakeni yanzu kuma ya maidani gidan ubana nagaji
da Wannan bala'een tun banida wayo nake hadiyar
baqin cikin sa har yanzu na tashi na dauki wayata
naja kujera na zauna, Bai min maganaba yaja hand
lgt dina ya tafi yana jiran in biyoshi nayi banza dashi,
Shiru sai da yakai gate din fita yaga bani ya dawo,
Na daura kaina akan table din gurin ina kuka yazo
ya ta6ani ban motsaba ya girgizani ya matso kusa
dani yace kizo muje gida, Wani dum naji, Araina nace
dan yasan muryarsa tanada dadine shiyasa baya
magana, Ashe duk abinda mukeyi a police din gurin
suna kallonmu a cameran dakinsu yazauna bai sake
maganaba sai ga yan sanda sunzo suka ja shi gefe
suka tattauna suka dawo police yacemin (he is ur
husband?) Araina nace inaga mutanen wannan qasar
basu iya turanciba sai yarensu, Nace masa (no he is
nt my husband ) Ya zare ido ya kalleni da idonsa,
Nasaukar da nawa idon, Suka sakeyin yare police ya
qara tambayata mijinkine nace musu a'ah, Suka
jamu mukaje wani daki suka fara masa question wai
idan matarsace ina certificate din auren mu? Nan
yayi turus baisan nigeria basa wani certificate ba
nan nafahinci bayason magana sosai duk yarasa
mezai musu, Suka kar6i passport dina sukaga
sunana da sunansa suka kar6i passport dina da
nashi sukace mutafi kamin suyi bincike,Intashi muje
na sake fashewa da kuka, Yayi bala'een daure fuska
yayi musu yare sosai sai ya miqa min hannu na kalli
yanda ya daure fuska na saduda na miqa masa
yamatse sosai ya jawo jikinsa ya rungumeni na
natsu sosai ban ji komai a rungumar da yamunba
saboda ina masa kallon azzalumine kuma ga
tsoronsa da ya kamani sai qamshin turarensa da
yake dukan hanchina, Mukaje yatari taxi muka shiga
munyi tafiya sosai sannan muka isa inda zamuje
muna isa ya bani key yace ga gidanki nan. Tofa…
Kukasance tare danu a
AURE KO ZAMAN GIDA ?
°PART 8°
Miyake nufi da ga gidananan yana nufin ya tafi
kenan wani sabon kuka nafarayi ga sanyi inaji harna
tashin hankali amma ba yanda zanyi naduba gabas
da yamma ba wani mutum na lalla6a na bude gidan
nashiga gidan qaramine zaman mutum daya na
zauna nayi kuka har na gode Allah ga sanyi kamar
me saboda anyi snow sosai gashi ni bansan yanda
ake kunna heater room ba danaga zan mutu da
sanyi natare kitchen da zama, Wato ya raboni da
iyayena yakawoninan dan yaudara garama nigeria
ina ganin iyayena idan naso ganinsu amma yanzu
idan naso ganinsu sai na kashe over half million
sannan zangansu, Lallai ina cikin tashin hankali
mara iyaaka, Satina uku bansakashi a idonaba
narame nadaina chin abinchi ranar naji hayaniya
ashe maqociyatace mijinta ya rasu naje sunata kuka
sun bani tausayi talakawane ba laifi yar budurwar
yarta tana gane English kadan kadan shima idan ta
kwa6a sai cikin mutum yayi ciwo kan dariya,
Ahankali nasaba dasu sosai suna koyamin yare
kadan cikin sati biyu nafara fahimta Abdul azeez
kullum sai yamun sms ya nake amma bana bashi
amsa wai ashe akwai camera a gidan wacce duk
wani motsina yana gani a gidanshi shiyasa
yashareni watana uku bansakashi a idoba na yanke
hukuncin komawa gidan su makwabciyarmu da
zama tunda yanzu nasaba dasu sosai kuma batada
yaro namiji a yaranta mata biyune. Na kashe wutar
gidan gaba daya na tafi abina yare kam alhamdu
lillah nagama iyashi tsab, Nagayawa mai kawomin
kayan abinci idan ya kawo min kayan abinci nan
gidan zai kawowa komai nawa nan nake yinsa
arayuwa kwata kwata namanta da abdul azeez
hankalina kwance nakashe banzar wayar da
yakemin sms, Ashe yayi tafiyane shima shiyasa bayi
gane bana gidanba yaje Turkey wani aiki na wata
daya yadawo ya kunna cameransa yaga wayam
basa aiki anma kasheshe gaba daya yayi forwarding
din karsheb zamanta gidan yaga tana hada kaya da
komai dakomai ta kashe wuta yaji tsoron ko ta gudu
ya tuna passport dinta na hannunsa hankalinsa yayi
bala'een tashi bashiri ya dawo gida qofa a gargame
nan ya zauna ya fara danasanin abinda ya aikata
tabbas bai yiwa zainab adalciba koda yasan shi
yayiwa matarsa alqawarin bazai kula wata maceba
matsawar tana raye, Zainab itace za6insa tun tana
yar shekara 9 yanemi aurenta aka bashi ita, Itace
za6insa, Ita yakeso, Dan yanasonta ya aureta, Ya
auretane dan kar wani ya gwace masa ita yasata
zaman kulli shekara hudu ya ajiyeta gidansa a naija
wata tara ya kawota qasar da batada kowa batasan
kowaba ya tafi ya barta yana ganin halinda take ciki
amma dan kar ya batawa matarsa uwar yayansa rai
yaqi za6insa wacce sonta yake neman kasheshi,
Yamanta itama zata haifamasa yarane, Yanzu ina
zai sameta..? Ina zuwa zainab kina nufin Abdul
azeez mijinki yanada wata mata?? Kibari kawai wllhy
mata harda yaro daya inna lillahi wa inna ilaihi
rajiun... Hauwa jabo muje muyi sallah mudawo in
qarasa miki.…
Post a Comment