Anan aka xauna ake tambayata da wane dalili ya sakeni yaya yake cewa kodai da nihal kuka sami sabani nace aah na rasa abinda xan fada.......
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA
ASHE KAINE MIJINA 61 ?
Na Hauwa m. Jabo.
Na rasa abinda zan fada na sake fashewa da kuka, shikam yaya ya rasa abin fada sai kawai ya tashi ya fita abinshi nayi kukana, inna dai taga kukan bamai qarewa bane tazo tana rarrashina har nayi shiru.
Guraren maqreeb yaya ya dawo ya sameni nadan saki jikina baicemin komaiba har zai fita inna ta kirashi ta tashi ta shige daki ya bita baya bansan mi suka tattaunaba naga sun fito abinsu.
Ya qara wuta inna bata min magana nima bance musu komai ba har nayi Kwana biyu a gida. Ina duba wayata da yake na dan saki jikina kadan kuma na warware rashin lafiyarda nayi dan inashan magani akan kari. Ina karanta wani hausa novel a group din hauwa m jabo sai wata tace amata sending din wani pic ina dubawa kawai naci karo da hoton takardar sakina dana dauka zan nunawa deen lokacin dan inason inyi surprise dinsa.. sai yacimin mutunci yace bani bashi "dama na nuna mai tun lokacin zai gane tunda rubutunsane" sai naji maganar yaya da inna da guduna na fito na na nunawa yaya hoton takardar sakina yana dubawa baice komai ba ya ma inna bayanin takardar inna tace saina fadi dalilin sakina naga dai boye boye ba nawa bane sai kawai na bayyane musu komai na gaya musu bai taba kusanta naba yaya ya kalli inna inna ta kalli yaya cike da mamakin maganata sai inna tayi qarfin hali ke dan mijin ki ya sakeki kada ki maida mu mutanen banza, kinason kice cikin da kike dashi ina kika sameshi?? Ko kin dauka dan baki gaya mana kinada cikiba mu ba zamu ganeba ki chanza wata qaryar ba wannan ba.!!!! Inna ta karkade zaninta ta qara gaba ta barmu da yaya ya juyo ya kalleni yazo kusa dani ya zauna.
Ya dafa kafadata nazia kiyi magana ki fadi gaskiyar abinda ya hadaki da mijinki wani ki mai sharri ko qire ko qage duk bai taso ba ki fadamin gaskiya kinji autar inna! Na fara rantse rantse akan ba abinda ya taba shiga tsakanin mu dashi iya abinda na fada shikenan ba wani ciki da nake dashi kawai dai nayi jikine hatta honey moon da mukaje kowa da ban ya tafi abinsha haka dai nayita tona asirin zaman mu amma ban fadi yanda muke dashiba....
Yaya kam ya gamsu dan bai sanni da qarya ba dama shi baiga ciki ba inna ta bashi labarin cikin wacce akace tanada tace ba haka bane miye nasu na qarya tawa.
Ya shiga sukayi magana da inna ya fito ana maimaita maganar cike da jimami....
Zamu jirasu zuwa qarshen sati idan har danginsa basuce mana komai ba zamuje mu kwaso kayanki dan ba komawa zakiyi gidannan ba..
nura da nihal sun rasa yanda zasu bullowa lamarin nura daikam ya dawo kamar wani almajiri sai tarin qasun ba dayatara duk wanda yaganshi ada yaganshi yanxu yasan yana cikin wani hali, su kitsa su warware duk yanda zasu bijirowa iyayen zancen saki ba tare da tonon asirinsa ba a maida nazia sun kasa samun mafita nura ya rasa yanda zaiyi, ba wata mafita da yake da ita idan yace baitaba kusantar ba to cikin na uban waye waye?? Ga son duniya ya dauka ya gwallafawa cikin nan hawaye ne suke gangaro mai na nadamar abinda ya aikata nihal har ta saba da ganin kuka uncle dinta tuntana mai kallon mai jinnu har ta gane tsabar son da yake yiwa nazia ne da damuwar da yake ciki. A qarshe sun yanke shawarar kada su gayawa iyayensu ita nihal qarshen wannan satin zataje gidansu nazia suyi magana.
"kaji wauta irinta yara wai nihal zataje biko"
Nazia dai kam inna ta yarda ba tada ciki tunda bataga cikin ba yanxu kuma alamomi sun nuna haka tunda lokacin kullum idan sunyi waya da nura daga yace baya gida sai yace yana kan hanya sai yace tana bacci ko tana sallah hakadai bai taba baiwa nazia sun gaisaba kullum kwana kwana yake mata shima yaya ya yarda dan shima kusan haka ta faru ya kira nazia ina nura tace baya gida ya kira nura ya nazia yace tayi bacci bayan daidai likacin suka qare waya yayi tunanin wani abu saidai bainkawo komai a ransa ba haka dai kowa ya riqa fadin albarkacin bakinsa..
Nazia baqin cikin wulaqancin da deen ya mata yana damunta amma ba halin fada dan ita ta janyowa kanta sonsa ya rufe mata ido yanxu ga abinda ya mata tasha alwashin duk ya kuskura yazo gidansu sai tamai kaca kaca.
Yau suka shirya kwaso kayanta da la'asar guraren biyu saI ga nihal a gidan inna dai kam bata ganeta ba tace gun nazia tazo.
Inna ta kira mata nazia ta shige dakinta.
Nazia ta fito da fara'a wa zata gani maqiyarta sista khadee. Nazia Ta wani daure fuska tasha magani ta zauna akan hannun kujera ta dora qafa daya akan daya tana girgizawa tana shan sweet..... sis khade ta gaisheta ta amsa da lfy a taqaice.
Gunki nazo, aunty nazia idan zaiyiwu mu shiga daga ciki..
No.. Nan ma is ok nazia ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba.
Ta hadiye yawu tayi qasa qasa da murya. Dama aunty akan maganar.......
Ta dakatar da ita da hannu...
Don't ever called me your aunty, am not & i will never be the one. I can hear you go ahead.! Ta qara kawar da kanta gefe..
Nihal Tayi ajiyar zuciya dama akan maganar uncle ne naxo dan Allah...... nanma ta qara katseta..
Shot your mouth up! you thinkless, do to most disgraced embrassemented matter you already done to me & your inrespective your mannerless, uncle do! But your came with another ovios alonatic thinking?.
to let me tell you, kije ki fada ashawon uncle dinki idan ya isa yazo da kanshi ke banida lokacinki wawaye kawai, ran sis khade ya bala'en baci taji maganar har cikin ranta tasosu kuma taji haushin maganganun nazia amma ba yanda ta iya tazo gyara tayi barna.??
Ta dago ta kalli nazia taga yanda ta daure fuska tasha jinin jikinta ta rasa abin fada chan nazia ta juyo.
Get out of this abode.! before I disgraced your personality now! Think less, stupid people haved to go and find an approach of manners & valuable of any mankind has wasing to you.
Oya ga hanya ta nuna qofa get out.!! Ta fada da tsawa.!
Sis khade ta gama qulewa tasan idan har taci gaba da zama faruwa naci ba nata bane mutuncinta yafi mata komai ta dauki jakarta ta fita kamin ta fita ta jiyo tsakin nazia think less kawai..!
Nazia tasani sarai sis khade batason tsaki tasha fada da mutane a secondary skull akan tsaki dan kuwa da kamata tsaki gara ka waska mata mari... har ta tsaya sai kawai ta wuce rai a bace...
Ta fada mota taja daqarfi tana fotowa gidan taja ta tsaya tana kwalla, lallai nazia taci mata mutunci da yake tasan weak point dinta shi yasa ta mata haka anya zata iya cika alqawarin da tayiwa uncle dinta kuwa da wuya dan bata daukar raini gun kowa wallahi. ta share kwallarta taci gaba da driving kamar zuciyarta ta fito dan baqin ciki ita zata cire hannunta dan tasan nazia da bala'en tsiwa komai zata iyayi..
Idan kuma ta juyawa uncle dinta baya wazai taimakeshi.?? Dayan xuciyarta tace wanda yasa ya saketa ya taimaketa..
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA 62?
Na Hauwa M. Jabo.
Sis khadee Tana tafe tana tunani yanda zatayi. qarshe ta yanke shawarar zame hannunta daga lamarin baki daya. ko banxa batasan abinda ya hadasu, ga rainin wsyo irin na nazia da bazata daukeshiba tayi tayi uncle ya fada mata abinda ya hadasu, saidai yace just help me nihal.!! a hakan zatayi helping dinsa batasan abinda ya hadasuba?? kawai zan koma gidane bana ganinsa ma bare ya bani tausayi...!!
Da wannan tunanin ya isa gidansa koda taje ta tarar baya gidan ta tattara kayanta tayi gidan su, mamanta na ganinta taji tsoro kardai kun saida hali da matar uncle din naki?? Da yake ke nihal bakida hali ga zuciya kamar ta kasheki naga fuska duk a turbune...
Sis khade tayi murmushi ta nemi guri ta zauna to umma yau baki chankaba, ta kwashe duk abinda idonta ya gano mata ta fada musu kuma lallai alamu sun nuna baima taba ganinta ba itama haka.
Maman nihal tayi dariya.! kefa har yanxu yarinyace wata qila sabani ya hadasu amma mace hadda ciki kice basu taba ganin junaba. Nihal dai tayi qoqarin yiwa umna bayani har saida umma ta gamsu da dalilan da ta kawo mata dan kuwa taji har ya saketa da kuma ta fada mata da bakinsa ya fadi ya saketa din. amma kuma nihal din tace abinsa harda aljanu kam. Amma bari baban fati "abbansu nihal kenan" ya dawo muji yanda abin yake.
Ran nazia yayi fari sol ko banxa ta gaya mata magana kuma tasan ranta zai sosu, taso taqi fita ta hadata da karen gidansu amma sai ta tafi. Ta shiga daki cike da farin ciki tasha maganinta ta shirya tana jiran yayanta. Bada jimawaba yazo suka je gidan mai gadi ya bude musu gidan suka tattara duk wani abu da sukasan nasune suka qara qaba....
Bayan isha saiga nura yazo gidan yana neman nihal yaga gida wayam!! Ba nihal ba kayan naxia abin ya bashi mamaki wato ya tura nihal gyara ta maibarna ko?? Zai kuwa chi ubanta.!! ( kaji wawa) yaje gun maigadi a firgice yana tambayarshi ya haka maigadi yamai bayani daga zuwan nihal har zuwan su nazia yana qarewa nura ya wankeshi da mari kaji taaasssssss!!! kuma yace sai ya dawo da kayan da suka diba dan bai bashi umurnin barin kowa ya dauki komai a gidan ba! ((kaji hauka ina ruwan maigadi ai sai yace sai ya dawo mai da matarsa bawai kayan matarsaba??))
Magadi yayi tsuru tsuru ya riqe kumce yana bada haquri nura ko saurarensa baiyiba yace yabar mai gidansa ya sallameshi ya wuce cikin gida a fusace. Dama su nura an iya kuka ya zauna tsakiyar palo ya fara kuka ba mai rarrashinsa cikin kuka ya jiyo magana sama sama koda ya duba sai yaga abban nihal tsaye yaxo gabansa yaja ya tsaya yamai kallon banxa ganin gidan ba kayan nazia ya qara tabbatar mai da cewa lallai ya saketa. Bai tausayawa halinda yaje cikiba ya haushi da masifa. Qarshe yace yadauka yazama mutum ashe har yanxu da sauransa! Sabida haka ya tattara kayansa ya bar wannan gidan dama albarkar nazia aka bashi wannan gidan nura ya tsananta kukansa basu barshi da baqin ciki rabuwa da mataraaba suna qara mai wani baqin ciki.
Yayan nura yayi waya gida ya fadawa mamansu da babansu abinda yaronsu yayi itadai kam maman nura da taji abin kasa magana tayi dan tsananin bacin rai... nura baiyi halacciba sai kallo kallon suke itada mai gari "baban nura" maman nura tace a kira inna amma mai gari yace wannan mugun abin ya wuce waya saidai su tafi. da kanmu har gidan. tun da asuba iyayen nura suka baro qauye sukaxo birnin sokoto. Bayan sun dan huta suka kwashi jiki sukaje gidansu nazia bawai biko sukaje sunje bada haqurine.
Koda Inna batasan zuwansuba ta musu tarba cikin mutunci da sakin fuska kamar ma ba abinda ya faru amma maman nura ta kasa koda hada ido da ita. Inna kam Sai neman ayi hirar bayan rabo takeyi amma duk sun kasa kunyar abinda dansu yayi ya ishesu. Chan dai maman nura ta fashe da kuka ta rungume inna tana bata haquri. Nura vai kyautaba! Baiyi halacciba.! Yaci amanar nazia.hakadai tayi ta sunbatu. inna nafadin babu komai har dai itama ta fashe..!! dan abin ya dade yana cinta inna kuka maman nura kuka dagyar dai mai gari ya samu ya rarrashesu sukayi shiru cike da kunya shima.....!!
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA 63 ?
Na Hauwa M. Jabo.
Mai gari (mahaifin nura) yaci gaba da maga. dukan mu bamusan abinda ya faruba jiya ake gaya mana abinda ya faru, dan Allah kuyi haquri yaron ne basu da hankali kwata kwata, basu san halacci ba da nura yasan halacci da nura ko bayason nazia ai dan darajar halaccin da kuka masa yaci ace ya zauna da yarinyar nan, maigari dai yayi maganganu na ban haquri qarshe yake tambayar lafiyar nazia da lafiyar cikin ta. Inna ta musu bayanin da nazia tayi na cewa basu taba hada shinfidaba mamaki ya kama kowa ganin yanda ake fadar tanada ciki duk dangi sun sani amma yanxu ace ba ciki. Basu isa su qaryataba. Ana nan mai gari yaci gaba da cewa yanxu sai ayi haquri a maida auren inna batace komaiba sukayi ta bata baki har tace Allah yasa hakan yafi zama alkhairi ana haka saiga yaya hafez ya shigo shida zainb khalifa su zainb ana wani iyayi an sami saurayi dan gayu , suna zuwa suka ga baqi a gidan sama sama suka gaisa zainb ta wuce gun nazia, yaya ya zauna ayi dashi anan mai gari ya fadawa yaya buqatar su ta da amincewar inna akan maida auren. zunbur ya miqe. Baxata yiwuba.!! Akan me kuke playing dinmu? Ko dan kunga mahaifin mu ya rasu?? to nine gatan nazia kuma nice mahaifinta.!! idan har kukaga ta koma gidan wannan yaron to ita ta buqaci hakan. amma baxa'a qara wulaqantamin yar uwaba ya buga rigarsa zai fita. Inna ta miqe zata cimai mutunci akan rashin kunyar da take ganin yayi. mai gari ya takatar da ita yaje ya janyo hannun yaya hafez ya zaunar dashi. Hafizu bazamu taba tursasa nazai akan ta koma gidan nuru ba abinda kawai mukeso shine kada wannan zumunci namu ya lalace. idan har basu shirya kansuba zan turo Dr mustafa yaron qanina wataqila su daidaita kansu banason abinda zaisa zumuncin mu ya bace , maman nura bataji dadin hadin da mai gari yake shirin yiba tace insha Allah ma zasu daidaita kansu haka dai zaman ya kasance har guraren azzahar.
Suka kwashi jiki sai gidan su sister khadee mai gari yasa aka kirawo masa nura bai bata lakociba yaxo ganin yanda ya zama lokaci daya abin ya basu mamaki da tausayi.!!
Jikinsu yayi la'asar maman nura ta kalli autanta tama manta da aika aikar da yayi ta taso ta riqeshi tana tambayar lafitar shi. Ran yayan nura ya baci ganin yanda mamansu ta rude ganin halinda danta yake ciki ya daka mai tsawa hadi da cemai munafuki wallahi mama kuk kuke kulashi iskancine kawai.!! mama ta dalla ma abban nihal harara ta zaunar da shi. Palon yadau shiru chan mai gari ya fara yiwa nura bayanin abinda suka sani hankalin nura yayi mugun tashin dajin cewa tace basu taba hada shinfidaba, kuma batada ciki kenan ta zubar mai da ciki?? Cikin da ya daura ma son duniya.! Cikin da yake tunanin shine zai taimaka masa su gyara auren su. Ya saki wata irin qara saida kowa ya firgita a gurin yace.........
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA 64 ?
Na Hauwa M Jabo.
wallahi ni ban saki nazai ba!! kuma qaryane tace bamu hada shinfidaba har cikina tana dashi wallahi.!!! kenan ta zubar mun da ciki?? Kowa yayi tsit....
sai kukan nura ke tashi a palon jikinsu yayi sanyi yayan nura yace dama nihal tace aljannu ne suka shafeka, inaga yafi kyau a bari sai yaji sauqi sannan ayi maganar. nura ya dallama yayan sa wata muguwar harara idonsa cike da hawaye sunyi jaa cike da fushi yace kaine mai aljannu baniba dama ka tsaneni baka sona daaga yau kai ba yayana bane..!! Duk palon saida kowa ya yayi dariya da maganar malam nura autan mamanshi... suka qara tabbatar da cewa yanada rashin lafiyar jinnu. dan kuwa ko musu bai taba hadasu da yayan saba kuma yana tsoronsa fiye da yanda yake tsoron iyayensa. Amma yana mai irin wayannan maganganu. kowa sai ya gasganta maganar abban nihal. Ya taso yaxo ya rungume qaninsa yana rarrashi cike da tausayi shi kuwa sai wani qace jikinsa yakeyi.!! Haka dai zaman ya qare ba wata natija.
Da dare maman nura ta bi nura dakinsa suna magana ya qara jadda dama abinda ya fada farko cewa bai saki nazia ba idan ya saketa kuma ina takardar saki?? Nan fa duk da cewa tana mai kallon mara lafiya ta gasganta maganar sa. Bayan ta fito ta samesu a palo suna tattauna maganar akan a nemowa nura magani anan maman nura tace idan har da gaske ya saki nazia ina takardar sakin take?? yaka mata fa idan za'ayi abinnan ayi adalci bai yuwa ace autana ne kawai bashida gaskiya
itama da laifinta. Sukayi shiru lallau yakamata ace ga takardar saki bawai kamar yan da inna ta musu bayaniba wai sakin a waya ne. Haka dai aka qare akan za'a nema mishi magani idan yaji sauqi sai a hadasu su biyu a aji gaskiyar maganar.!
Haka kuwa akayi an kai nura gun mai ruquya aka danna mai maganguna da hayaqi kala kala. kamar gaske bayan kwana uku yadan da normal amma fa bai daina hararan yayansaba kuma baya gaidashi ba yace duk ya hadu da nihal sai ya kakkaryata dan gani yake zuwanta gidan su nazia yasa komai ya qara lalacewa bayan tace zata taima keshi.....
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA? 65
Na Hauwa M. Jabo.
*********************
An shirya zama kowa yazo hadda su nihal an hallara.
Aka fara maganar kowa ya fadi albarkacin bakinsa amma nura yaqi saukowa akan cewa ya saketa. Akayi sama akayi qasa amma yaqi yarda yace idan har da gaskene to ta kawo shaida a rubuce dan ba zasu yarda da waya ba, wannan zamanin komai ana iyayi. qarshe nazia taga ba nasara a gunta ta miqe taje daki ta dauko qur'ani tazo gabansa ta tsuguna ta miqa mai qur'anin tace idan har yayi rantsuwa da wannan qur'anin akan cewa bai saketa ba, zata koma gidansa yau dinnan.!!
Nura ya rasa yanda zaiyi sai zufa ke keto masa.!! Chan dabara ta fado masa ya karbi qur'ani yace zaiyi rantsuwa amma itama tayi alqawarin cewa zatayi rantsuwa akan cewa basu taba hada shinfidaba kuma bata dauki cikinsa wata huduba.
Qaqaqara qaqa....
Suka fara kallon kallo tsakaninsu palon yayi tsit ana sauraren wannan lamari nasu.! Nazia ta karbi qur'ani jiki a sanyaye tace kamin ka rantse ni zan rantse. ta riqe qur'ani hannu bibbiyu ta rufe ido tana hawaye...
Tace Ni nazia muhammad na rantse da darajar wannan qur'anin!! A matsayina na matar nura ta sunna bai taba kusantana da sunan raya wannan sunnar aure ba daidai da second daya saidai ya......... tuni nura ya taso yarufe mata baki ganin zata fallasa sa dayan mugun aikin da suka aikata.! wanda baya fatar hakan ta kasance har qarshen rayuwarsa.!! Bayason Iyayensa susan halinda ake ciki. Tausayin nazia ya kama kowa yayan nura ya haushi da fada akan me xaka hanata fadar gaskiya? ? Ta tabbata kenan bakada gaskiya.!! kamaida mutane sha sha shai. Yayan nura yazo gaban nazia yace mata nazia ci gaba saidaime???
Nura baisan lokacinda ya juye bakiba da harshen farisanci da suka koya tare da nazia tun kamin suyi aureba yace mata (( nazia turo khuda asrari moro pakhsh nakun na bi khatiri man bi khatiri khuda.....)) ta dago ta kalleshi harga Allah ya bata tausayib yanda ya hargitse da kuma yanayjn sautinsa ko banza tana sonsa ta kalli yayan nura tace mai ba komai. Nura yayi ajiyan zuciya yayansa ya kalleshi ya rasa bakin magana tunda baisan mi yace mataba.!! (( nima hauwa jabo saida na tambaya aka fassaramin abinda yace kuma bazan fassara mukuba ??)) nihal ta taso taxo ta qarbi qur'ani itama tayi rantsuwa akan cewa lokacinda tana gidan uncle ya fada mata da bakinsa ya saki nazia yakai sau 50. Ta fadi yana yawan maimaita cewa ya yaudari nazia ta taimaka masa..... Mai gari yace kada ku maida qur'ani abin wasanku mana. Ya karbi qur'ani hannunun nihal ya koma ya zauna kowa yayi shiru ana jiran gogan naku nura mayaudari yayi magana amma kamar ruwa yacishi yayi tseeeeet....
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA ?? 66
Na Hauwa M. Jabo.
Nura mayaudari yaqi magana kamar ruwa ya cishi yayi tseeeet.! Palo ya dauki shiru kusan minti uku ba wanda yayi magana ana sauraren nura mayaudari. Chan ya dago kai ya kalli hulwarsa yaga yanda take zaune a natse amma da gani a kwai damuwa tattare da ita tausayinta hadi da wani qaunarta da yakeji ya qara kamashi, ya tuna maganganunda ya fada mata lokacinda tace tana da ciki wato zafin maganar ne suka sakata ta zubar da cikinsa kenan? miye laifinta ma tunda shi yace ta zubar ba ruwansa.! Idonsa sun cika da kwalla ya sunkuyar da kai yace....
Baba lallai na saki nazia saki daya!! Lokacinda na saketa bansan cewa itace matar tawaba! Kuma ni dauke takardar sakin dana mata na yaga dana fahimci itace matar tawa, dan wallahi inason nazia baba fiye da yanda nakeson raina bazan iya ruyuwa ba itaba yana magana murya na sarqewa.!
Maigari yace alhamdulillahi dama munason muji gaskiyar magana, kuma gashi kun fada da bakinku. amma cikin maganganunku akwai abubuwan da ban ganeba.!
Kace lokacinda ka saketa bakasan itace matarkaba!!
Kenan kasanta tun farko kenan??
Itama tace baku taba saduwa da sunan aureba saidai....
sai ka hanata qarasa magana wanda yake nuna kamar kunsan juna kamin aure ko makamancin haka
Sai maganar ciki da kakeyi wanda kowa ya shaidi tanada ciki kuma akazo aka rasa cikin yanxu.
Ka nuna baka taba saninta ba baka ma taba ganinta ba ya akayi kasan tanada ciki?? Hakan ya nuna akwai wani boyayyen lamari da mu bamu saniba yanada kyau muma a mana bayani.!
Lokaci daya nazia da nura suka kalli juna kamar hadin baki sukace wallahi baba!!! sai dukansu sukayi shiru,, babu kom.....
Sai maganar ciki da kakeyi wanda kowa ya shaidi tanada ciki kuma akazo aka rasa cikin yanxu.
Ka nuna baka taba saninta ba baka ma taba ganinta ba ya akayi kasan tanada ciki?? Hakan ya nuna akwai wani boyayyen lamari da mu bamu saniba yanada kyau muma a mana bayani.!
Lokaci daya nazia da nura suka kalli juna kamar hadin baki sukace wallahi baba!!! sai dukansu sukayi shiru,, babu kom.....
nan ma hada baki sukayi suka qara yin shiru nura ya qarasa maganar da cewa baba ba komai tsakaninmu baba!
Maigari dai bai gamsu ba sauran mutane ma tambayar maigari ta sakasu cikin tunani yanda suka hada baki ma ya nuna rashin gaskiyarsu a bayyane, yaya nura yace tunda dai munji haqiqan abin shikenan wani bincike bai tasoba baba koma miye wannan tsakaninsu ne rashin kyautawa ne dai nura ya riga yayi muna dada bada haquri. inaga shikenan kawai. anan dai akayita bada haquri akan qara abinda nura yayi aka shigo da maganar komawar nazia, yayan nazia yace abarta ta huta daga baya ayi wannan zancen, nazia da qarfin hali tace ni na bazan koma gidansa ba na amince idan na qare idda xan zamu daidaita da Dr mustafa idan mun shiryasai muyi aure.
Ke hulwaty..!!! Kinada hankali kuwa?? Kinsan abinda kike fada?? Da aurenki kina tunanin wani namiji ko?? Ta dalla mai harara da murguda baki aure kuma?? Ai yanzuu hulwa ta mai raboce haka suka fara musanyar magana sun ma manta akwai mutane tare dasu kowanne cike da kishi da bakin cikin rabuwa da dan uwansa!!
Harga Allah naxia dan ta bata masa rai tace zata aminta da Dr mustafa bawai dan tanasonsaba. Dukansu abin ya basu dariya yayan nura yace shikenan ya isa! Nura ya kalli yayansa cikin kwalla yace yaya kanajin abinda take cewa ko?? Nura yama manta da baya ma yayan nashi magana!! Tausayin qaninsa ya kamashi yace kayi haquri ta bari zamuyi magana daga baya.!
Haka dai abu ya qare, zaman baiwa nura dadiba idan ya tafi ina zai qara ganin hulwarsa. Kowa ya watse aka qara qaba....
**************************
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah yau wata shida abubuwa sun faru na baqin ciki da farin ciki nura ya zautu kamar bashiba ya dawo ustaz baya magana sosai abinci kadan yakeci ba wanda yake ganin walwalarshi yayi yayi akan hulwarsa ta haqura ammabina tqqi haqura. yayi kamun qafa gun yayanta sai yace ya nemeta su daidaita ta chanxa layi baya samunta. Jin dadinsa daya qin yuwar aurendu da Dr mustafa yanaga da mutuwa kawai zaiyi.
Naxooo tun kan ta qare idda yayanta ya samo mata admtn a dan fodiyo ta fara karatun ta amma soyayyar mijinta tana mata yawo akai ta tabbata har abada ba zaata daina son deen ba saidai tana barwa cikintane tunda ba yanda zatayi.....!
Kaji sona gaskiya.
Post a Comment