ASHE KAINE MIJINA.?
ASHE KAINE MIJINA.? 56
Na hauwa m. jabo.
Ya kalleta ya marairaice haba hul....
ta katseshi da sheeeeee....!!!
yimin shiru munafuki macucu mayaudari lokaci daya ta kirashi da sunayen ta bude marfin motar da qarfi ta fita abinta...
yafito yabita a baya har xata shiga taxi yaja ya tsaya yabita da kallo hadi da kallon cikinta lokaci daya Allah ya sakamar qaunar cikinta fiye da yanda yake tunani...
nihal nason tayi magana amma kuma yanda taga ya daure fuska ya wani chanxa sai tayi shiru...
chan kuma sun kama hanya tace uncle nifa bangane wannan abunba nakuba naga..
bakuma xaki ganeba...
ya bata amsa a taqaice, ta kalleshi ta gefe, har xata qara magana ya katseta..
kuma banason inji wannan abinda ya faru gurin kowa...!!
hmmmm..! nihal taci gaba da driving dinta,
uncle ina xamu tafi yanxu..
gidana!!
nanma amsar a taqaice ya bata..
To ai..
to ai me? look nihal kindameni da magana kibarni inji abinda nakeje pleaseeeeeeeee...! har suka isa bata qara mai maganaba...
nazia direct gidan su ta wuce tana xuwa ta fada jikin innarta tana kuka,
inna tana tambayarta abinda ya faru dagyar ta iya bude baki tace nurane ya sakeni .!!!
Inna tasaka salati..! sakifa kikace!!! eh wallahi inna ya sakeni!!
inna tana ganin abin kamar bada gaskeba ko kuma mafarki,
to Ina takarda, nazia tadan taqaita kukan nata tace takarda tana gida namanta da ita, hankalin inna inyayi dubu ya tashi,
inna ta kalleta rai a bace kinga yanda kika dawo lokaci daya kamar mai jego!!?
qirjin nazia ya qara bugawa..
waima miya hadaku ne da har ya sakeki??
naci gaba da kukana ban bata amsaba inajinta tayi waya da yaya ta gaya mar abinda yake faruwa.
bansan abinda yace mataba kawai sai naji tace to sai ka iso ta kashe wayar...
taxo taxauna kusa dani, tayi tagumi chan kuma tace,
Allah dai ya saukeki lafiya amma wallahi yaronan baiyi halin iyayensaba, amma dai bari muji miya hadaku kamin ince wani abu. !!
Wani rasss naji dama inna tasan inada ciki kenan ?? to ya akayi suka gane inada ciki?
yanxu idan ma nace baitaba kusantanaba ba yarda xasuyiba lallai da sake....
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA.? 57
na hauwa m. jabo.
Lallai da sake dole insan yanda xan bulloma lamarin "xancen xuci takeyi" Allah nagode ma da ka xubar da cikinnan..
na tashi xan shiga dakin inna kenan, sai sallamar yaya mukaji yashigi kamar an turo shi yayi jaaa kamar qauta?? sai huci yake kamar wani kasa...
wallahi inna tun farko nasan xa'ayi haka.!! nurr bayason nazia itama bata sonsa amma muka rufe ido muka ce sai anyi auren nan kuma na gaya miki haka tun farko yanxu ga wulaqancin da yayi mana nan yasokota dan ma cikarshi dan iska baitashi sakintaba saida ya mata ciki yanxu dan Allah inna abinda yayi ya kyauta kenan??
Ya mata adalci kenan??
yanxu ki.....
inna ta katseshi kai wai wane irin mutunne kai bakasan miye ya hadasuba kawai xakaxo kana ma mutane rigimar banxa, Ai ka bari ta mana bayanin miye ya hadasu har ya saketa sannan ka fara rigama rigimamme kawai.!
dan taxo tace yasaketa haka kawai ba fada ba komai xai saketa?? dukansu basason juna to katabbata akwai laifin kowanne su aciki kabari tayi bayani da bakinta, ta kuma nuna takardar sakin sai aji yanda xa'abullowa abin..
yaya yayi ajiyar xuciya ya nemi guri ya xauna, amma fuskar nan har yanxu a turnuqe,
ya kalleni cike da tausayi kiyi haquri nazia kidaina kuka Allah xai saka miki idan ya yaudareki ina takardar sakin naki,??
Nazia ta bude baki dagyar muryanta duk ya dushe..
yana gidan!
miyasa bakixo dashiba,
mantawa nayi dashi.
gobe xamuje ki dauko kayanki da kuma takardar Allah ya sakamiki!!, ana cewa ya natsu ashe da sauransa, ni da ganin idinsa nasan baida kirki mutum banxa ay dama nasan xaiyi fiye da haka....!!
Inna ta kalleshi rai a bace waikai lafiyanka?
waya gayamaka ana shiga tsakajin mata da miji.?? wallahi xasu baka kunya daga baya ana ma magana kamaida ni mutuniyar banxa...!
ai inna duk ke kika janyo tun farko ni banso auren nan ba amma kika nace sai anyi sannan yanxu ga wulaqncinda yaI mata kina cewa abari sai anga takarda, kawai inna kisa mana ido dan ba qara bari xamuyi mu maimaita kuskuren farkoba dole in nemawa qanwata yanci dan anga bamuda uba..!!
Karo na farko da yaya yaqi sauraren inna idan tana magana, haka idan tana magana ya maida mata amsa..
mamakin duniya yacika inna tasaki baki sululu tana kallonsa,
Lallai baitaba mata hakaba, kawai bari ta barshi har ya sauko sannan su fahimci juna....
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA ? 58
na hauwa m. jabo.
har ya sauko sannan suyi magana su fahimci juna.
ya tashi fauuuu... har yakai qofar fita ya juyo ke nazia xo muje,
na kalli inna naga ta dauke mana kai na fuske abina nabi yaya ina dan dingishina.
part din yaya muka wuce da yake an gyarashi tunda yaya ya kusa aure da zainb khalifa.!
mukaje sashensa muka xauna a parlour yaya yaso yamin magana amma ganin fuskata yanda na harqitse yasa yaja bakinsa ya dinke, amma ransa a bace,
ki shiga dakina ki kwanta ni xan kwana anan kamin gobe muga yanda xa'ayi..
ba musu na amince dan bayana kamar ya bude dan xafi gashi na jiqe sharaf da jini, ina buqatar xagayawa in kimtsa jikina...
na tashi naje dakinsa..
direct bayi na wuce dan in gyara jikina saidai kuma ba pad sai da tissue nayi amfani na watsa ruwa na fito..
ina fitowa na nemi guri na baje.
abinka da mara lafiya ga gajiya nandanan bacci yayi awon gaba dani...
A bangarennura ko kuma muce deen,
ya gama rudewa ya zare kamar wani dan gwaya..
dama hulwarsace matarsa??
dama itace a gidansa bai saniba??
yanxu tana dauke da cikinsa!
waima ya xaman cikin yake shege ko mai uba.!??
dana ba shege bane!
dana dan halal ne koda bada sanin junan mu muka sameshiba.! dayan bangaren xuciyarshi ya bashi amsa,
ina qaunar dana fiye da raina!
lokaci daya qirjinsa yayi wani mummunan bugawa daya tuna cewa ya saketa!!
ya tuna wulaqancin da yamata. anya xata yafemin kuwa??
bangaren xuciyarshi ya bashi amsa da xata yafe masa tunda tana sonsa!!
amma yana tunanin baxata taba yafe marba.....
yafi yarda da cewa baxata yafemar ba.
kuka ya saki kamar qaramin yaro ya durqushe qasa lallai na yaudari kaina na yaudari soyayyar da hulwaty ta nunamin...
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA ?? 59
Na hauwa m. jabo..
ta nunamin, ya rasa yanda xai yi da rayuwarsa, xuciyansa kamar ta fito dan baqin ciki da damuwa babban burinsa ta isa gida lafiya..!
waima da wane ido xai kalli iyayenta dama nashi iyaye iyayenta sun mai karamci tun tana jinjira ya nemi a bashi ita kuma aka bashi aka ijiyemasa ita tun lokacin har ta isa aure lallai ya xalunceta, koda baya sonta baidace ya mata abinda ya mataba, kodan karamcin da iyayen ta suka mai , mixaicewa iyayensa idan sukaji cewa ya saketa.!?
yanxu yake tuna maman nihal ta taba cemar nazia nada cikii yana kallonsu wani iri har yake ce musu shi ko ganinta yayi baxai ganeta, ashe da gaske hulwarsa tana dauke da cikinsa..!!
Lallai ya tsuke tunaninsa ya akayi bai ganetaba? ya akayi bai gane sunantaba..!? Ta taba gayamin sunanta nazia amma tace babanta yana kiranta da hulwa, so tafison sunan shi yasa bai gane sunanta na asali ba.
ya tuna lokacinda xai siyamata ticket daga abuja xuwa sokoto yaga sunanta Nazia muhammad amma baiganetaba.!
duk tunanin daya dauko baya kaiwa qarshensa, yaga ba yanda xa'ayi ya ganeta, amma hadda jahilci yayi mai yawa .
yanxu yatuna ya kirata hulwarsa da jahila ashe nine jahilin nine daqiqin nine axxalumin yaci gaba da kuka hadda gunji kamar qaramin yaro....
nihal tana parlour tayi jigum tajiyo kamar ana kuka ta leqo taga lallai uncle dintane yake kuka..!!
itakam ta rasa gane komai duk tunaninta bata samun amsa, lokacinda xata iso Mamanta tace kada ta riqa barin antin nata da aiki dan tanada juna biyi (ciki)
lokacin da taxo uncle da aunty nazia sun nuna basu ma san juna ba.!!
duk tunanin ta bata sami amsaba.
taja ta tsaya qofar dakinsa. tana tsoron ta shiga dakin ya balbaleta da masifa gashi ya gargadeta..
ganin kukan da yake ya tsananta da wani gunji da yake yasa bata tsaya wata wataba ta fada dakin taje gunsa cikin tsoro,
uncle miyake faruwa??
kamar baijitaba
ta qara maimaita tambayar har saida ta tabashi da qarfi sannan ya dago ya kalleta yanda taga ya chanxa ya hargitse lokaci daya abin ya bata mamaki da tsoro..
kodai yanada aljanune??
ta kalleshi uncle mi yake faruwa ??
ya kasa magana amma dai ya daina kukan da yakeyi,
ya dago ya kalleta abin tausayi dashi " koda ni jabo bancika jin tausayin maxaba dan basuda kirki amma yadan bani tausayi kadan??" ya bude baki nihal xaki timakeni???.
Eh uncle xan taimakeka..!!
kinyi alqawari!??
Eh nayi..!
Duk wahala???
Eh.!!
nihal talk tome ina cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali kimin alqawari idan kowa ya gujeni ke xaki tsaya tare dani xaki rufamin asiri..!!?
Uncle na maka alqawari duk wuya duk wahala xan kasance tare dakai har qarshen rayuwata...!!!
___________________
kuyi haquri kun jini shiru wallahi nayi busy ne da yawa wannan ma a train na rubuto mukushi
idan na dawo xan kammala.
Auntie M. Jabo:
ASHE KAINE MIJINA 60?
Na hauwa m. Jabo.
Har qarshen rayuwata.
Yaji dadin alqawarin da nihal ta daukar masa yasan kuma akwai ta da jajircewa akan abinda takeso idan har ba wulaqanci a ciki. ta yarda dashi saidai tunaninsa daya ya xasu bullowa abin., ? Dolene ya gayawa nihal gaskiyar abinda ya faru anya zai iya kuwa? tabbas baxai iyaba zai tonawa kansu asirine kawai wannab sirrine tsakaninsu baidace kowa yajiba. zaidai san yanda zai bullowa abin. Nihal dai tana zaune tana kallon uncle dinta duk da ya daina kuka amma yana wani gunguni gunguni dukkan alamu dai ya zautu ta kira sunansa uncle ya dago ya kalleta, au kinanan? Ai
Kina iya tafiya, tace to, ta tashi ta tafi cike da saqe saqe a ranta haka yaci gaba da tunane tunanensa yana kuka har barci yayi awon gaba dashi..
Bai farka ba sai guraren asuba ya tashi idonsa sunyi hulu hulu ba kyan gani. Maimakon yayi sallah sai ya wuce dakin hulwarsa yana shiga ya dauki turarenta yana shinshinawa hadi da hugging din kwalbar turaren yana kwalla kamar wani xararre ya tashi yana yan tabe tabe tabensa har yakai gun wayarta battery low ta mutu ya jona chaji komi yake nema oho ya dauko hand bag tinda yana lakube anan yayi karo da takardar sakinta da magungunab.! vai duba maganin kona miye ba tunda yasan tanada ciki xai xama maganin masu cikine. Aranshi Wato bata tafi da takardar ba "yama manta da cewa suma tayi a hanyar hosptl ta farfado tace a kaita gida" lokaci daya baqin cikinsa ya dawo farin ciki yayi wani murmushi bada bata lokaciba ya shiga bayinta ya yayyaga takardar yayi xuba a bayi yayi bayan gida akai?? ya kora rowa yayo alwula yaje yayi sallah... Allah kadai yasan abinda yake saqawa a ranshi har gari ya waye yana laximi akan Allah yasa ta yafe masa su dawo normal...
Yaxo ya sami nihal ta hada mai break fast bai iya ci sosai ba yadan taba dai kawai duk dahaka nihal tayi mamakin sakewar da yayi akan jiya. Nan xarginta ya qara tabbata akan uncle dinta yanada jinnu dan su suke haka one time kuma kamar ba'ayiba
Taso suyi magana sai kuma ta basar tunda jinnu ne baxai tuna komai ba....!!
Naxia bata farka ba sai guraren 8 na safe duk jikinta ya qara ciwo sabida batasamu tasha maganiba, ta rarrafo taxo palo ta sami yayan ta bayanan tasan ba gurin aiki yaje ba dan sai 10 yake tafiya aiki?, tayi tunanin bari taje kitchen ta hada tea ta kora tana xuwa taga yayanta tana fere dankali abin ya bata dariya dan bata taba ganin yaya a kitchen ba. duk ya xubar da rabi garin ferewar aranta tace lallai zainb khalifa xatayi fama ko irin mata bataji dadiba miji ya tayata girki da dan ayuka yaya kam ba abinda xai tabuka. Ta kalleshi ta gaidashi ya amsa cike da fara'arsa hadi da tausayin yar marainiyar qanwarsa!!! kin tashi tace eh.! Ka kawo In qarasa yace aah ki barshi xan qarasa kina baquwar tawa sukayi dariya... AI yaya a wannan duk ka xubar da rabin dankalin yayi murmushi ina practice ne kamin maaadam taxo dariya ta kamani amma na fuske wato zainb khalifa ce maaadam. lallai rayuwa mai juyi da yanda yaya ya tsani xainb khalifa amma yanxu itace wacce yake burin ta xama uwar yayansa....
Kije ki shirya muje gidan wancan yaro ki dauko takardar sakinki da kayan buqatarki.
No yaya muje a haka kayana duk suna chan gidan.
Kije ki duba wardrobe dina zaki ga kaya ki xabi daya ki saka
Naje dakin abin ya bani mamaki ganin kayan mata kamar wani qaramin store ta dauki wani dogon riga baqi ta saka duk da ta rame amma kayan su. Karbeta sosai.
Koda ta fito harya qare hada musu break fast ta xauna suka ci lallai taji yunwa rabonta da abinci tun jiya da safee.!!
Suka fito sukaje sashen inna suka gaisheta ta amsa ba yabo ba fallasa suka gaya mata zasuje gida nura in dauko takardar sakinna da kayana har sunkai bakin qofa inna tace ban yarda kuyi chin mutunci da kowaba yaya ya amsa da insha Allah..!
Suka isa unguwar tunda suka isa unguwar qirjinta yake dukan uku uku har suka isa gidan suka iske gidan a bude suka shiga nihal "sis khadee" sukayi karo da ita a palo tana chatting fuskarta cike da fara'a da gani ita da ammar suke soyewa koda bansan still suna tareba.
Tana ganin mu tayi shock xunbur ta miqe ta gaidamu cike da fargaba yaya ya amsa mata rai a sake direct dakina na wuce abu na farko danayi karo dashi yasa nasan an mini bincike dakin cike da qamshin turarena kamar anyi wanka dashi hand bag dina komai an juye a saman gado waya a chagi haka dai ta tattare kayanta na buqata amma ta nemi takardar sama da qasa bata ba labatinta.! wayarta ma dagyar ta ganta dan a chaji take ta fito a sanyaye tacewa yaya bataga letter dinba da kuma yanda ta sami dakin anan suka gane yayi bincike ne kuma shi yadauke takardar ran yaya ya baci matuqa ya kalli sista khadee ke ina nura?? Bakinta na rawa tace Yaje office ya dauko wasu takardu har suka gama xaman jira bai dawoba an kira wayar a kashe suka tafi gida sunje sun ma inna bayani tayi tagumi batace komai ba.
Post a Comment