0
ASHE KAINE MIJINA? 1


 

Na HAUWA M. JABO...

Ke nazia kiyi sauri ki tattaro
kayanki kizo
mu tafi yayanki yana jiranmu, ko
walle mu tafi
mu barki!

ganinan zuwa inna! nazia ta
baiwa inna
amsa tana qoqarin fitowa daga
tadinka da dan
gunshin
kayanta a hannu, da yar
jakarta inna ta
kalleta a hantare, kekam kinji haushi
Kullum idan
za'afita
sai an barki, duk zumudin da
kike ya
zama na banza tunda har na rigaki
shiryawa, nazia
ta
kwashe da dariya, wallahi
inna kesan
kayana sunada yawa shi yasa ban
samu na fito da
wuriba, ke dan Allah wuce ki
bani guri ko
in
hantareki, mara kunya, dama haka kike
kullum da
baqar shiririta, ta qara
kwashewa da
daria, hadda
gyagyataWa, duk wanda yaga nazia a gida
idan ya
ganta a waje zai dauka ba ita
bace, yanda
take
daure fuska kamar bata taba murmushi
ba, zaka
dauka kamar ma bata taba
dariyaba a
rayuwarta,tafito da dan gudu
gudu tana kallon ko
ina idan basuyi Mantua ba ta
kalle ko ina
amma
komai babu tafito tana
murmushi, yayanta ya
kalleta, ke wallahi kinci
albarkacin inna
da sai mu
tafi mu barki kinfi kowa cewa
a koma birni amma
kuma kinfi kowa shiririta,
mtsww yayi tsaki, na
qyalqyale da dariya
abina
na fada jikinsa yi haquri yayana, yanzu ai
gashinan na fito mu tafi ko,
amma fa abu
daya ya
rage min, inna da yaya duk
suka juyo suna kallon
juna da mamaki, inna tace
dama baki
kammala ba
Nazia??? aah inna na qare
komai amma ai kince
inje gidan.......
ASHE KAINE MIJINA..??
Na HAUWA M. JABO....
Amma ai kince inje gidan su
abban fatin birni in
musu ban kwana,
Inna ta saka salati tana tafa
hannu, dama
nazia
da nace kije ki musu sallama bakije kin
musu
sallama ba, yar duniyar ta
qara
kyalkyalewa da
dariya, amma anyi shaqiyiyar yarinya inji
inna, ta
kawo min duka amma ina na
kauce, na
qara
kyalkyalewa da dariya, mutuniya banza,
sai ta
ishimutane da dariya sai
kace mai tabin
jinnu,
yaya ya gama qufula, baice komai ba.!!! Na
zabga
a guje ina ta dariya, ina shiga
dayar
kwanar na
daure fuska, kamar banice mai kyalkyala
dariyannan ba, na gyara
hijabina nashiga
gidansu
hafizun birni mamanshi tana
ganina ta hau washe
baki,tana min kirarin da ta
saba amma ko
ajikana
nasha magani abina tace
auta matar auta, badai
tafiyar ceta tashiba, kamar
banason
magana na
kebe baki nace, E, tace yar
nan Allah ya kaiku ya
lafiya gashi sameer baya nan
da sai in ce
ya baki
number yayan naki nura idan
kunje sai ku nemishi ku riqa qaisawa,
bance mata
komai ba, ta
qare surutanta, nace zamu
wuce su yaya
hafizu suna jirana, tace to yar nan
Allah ya miki
albarka,
ta bani kudi wai insha ruwa a
hanya
amma naqi in karba, nace ina fati take?
Allah sarki
bata
dawo makaranta ba idan ta
dawo xan
fada mata kun tafi, xatayi kewa Wallahi
xan wuce
yarnan
baxaki karbi kudin ba nagode
hajiya,
dama itama ta sanni da taurin kai aranta
take cewa
tauri da
tauri sai qaqa.. ......
ASHE KAINE MIJINA..3?
Na HAUWA M. JABO Sai qaqa, koda na qaraso na
tarar da an
kulle
gidan mu kuma ba motar
yaya ba
labarinta!!! Tuni hanjin cikina suka shiga
kadawa
idona suka
cika fall da hawaye sai kuka,
yanzu su
yaya da inna sun tafi barni, kuka
Sosai nakeyi na
zauna
dirshan a qofar gidan mu na
rufe ido ina
kuka,maimakon in dan xagaya amma
anan na
dabe ina kuka, sai ji nayi
ankwasheni da
mari ta
gefen fuskata ! Kutumar uba waye yake
dukana
duk da ina cikin qunci amma
da bala'e na
dago
kai inga wane dan iska ne yake dukana!!!
Daga
kan da zanyi sai kawai naga
yaya, fuskar
nan a
turnuqe kamar an aiko mishi mutuwa,
wallahi
idan baki tashi mun wuce ba
zan
babbalaki anan,
mamaki da tsoro ya cikani, araina nace su
tafi su
barni sannan kuma yaxo
yana dukana da
zagi,
araina na fara balaee na daure fuska, ashe
nice
banida kai mota gatachan
gaban gidan mu
kadan
kwana sukayi suna jirana, da yake ni idan
ina
tafiya bana qage sai ban
hango motar ba,
na
kuwa sha kunu na fuske abina, ya shiga
gaba ina
bin bayanshi saida muka isa
jikin mota
naja na
tsaya, kamin kace kwabo inna ta wankeni
da wani
marin,ta buda baki xatayi
magana na
rigata
nashiga uku, nace minayi muku kukeson
ku
kasheni,sai inna ta shige
mota ta barni,
naci gaba
dan kunga ina zumudin zuwa birnin ne
ake min
wulaqanci...!! to Wallahi na
fasa zuwa
birnin
banaso, bazanjeba asaukemin kayana...!!
ba inda
zanje, na qara fashewa da
wani kuka....
yaya ko kallona baiyiba
shima ya zagaya ya shiga
mota ya kunna yana jiran in
shiga amma
ina
taurin kai ya motsa, ko
ajikina, yayi horn alamar
in shiga amma ina sai ya fito
......,
ASHE KAINE MIJINA..4 ?
Na HAUWA M. JABO
sai ya fito, kinsan Allah nazia idan baki
wuce
muka tafi ba zan babbalaki
yanzu nan, ko
kallonsa banyiba, na kauda
kaina gefe, yaga da
gaske nake yakaimin duka,
ko in kauce
na tsaya
qiqam mugun halin ya mosta
hakan ya qara bashi
haushi, dama shima gwanine
a gun xuciya
amma
dai bai kaini ba, ya fara
dukana har na fadi yasa
qafa yayi ball dani, hankakin
Inna ya tashi
tasan
idan zai kasheni a gurinnan
ba tashi zanyiba,
kuma tunda nace bazan jeba
ba tafiyar
zanyiba,
tazo ta janye yaya hafeez
daga gareni, ba halin ta
mishi fada yanda taga ya
chanza har
fuskarshi
tayi jaa dan tsananin fushi
,da yake shi yaya
hafeez fari ne Sosai ko
kunya yaji sai kaga
yayi
ja, haka lokacin sanyi ma jaa
yakeyi, uwa uba
idan yayi fushi sai yayi jaa
kamar bature
haka
yake, tayi gefe dashi ta daura
hannunta akan
kafadar shi ta dama, haba
yaya!! Ya zaka
biyewa
nazia? Yarinyar da ba
hankali ya ishetaba, kuma
sam batasan ciwon kantaba,
wuce ka
shiga mota
bari in daukota, yayi mini
wani mugun kallo, rai a
bace ya shiga mota yana
huci "nima dai m.
jabo
da nake biye dasu ya bani
tsoro dan nayi niyyar
in gudu sai mun hadu birni
amma dai nayi
ta
maxa na tsaya" inna tazo ta
durqusa kusa dani,
tace ba tafiya mukayiba
kinsan haryar
qaramace
shine sai yayanki yace bari
muyi kwana kamin
kizo shi yasa baki hango
muba kuma ke
gashi
bakya kallon hanya kina
zuwa baki ganmu ba
maimakon ki duba gefenki
sai kawai kika
nemi
guri kika zauna kika fara
kuka, abin ya bani
haushi ne dan kada yayanki
yace na goyi
bayan
ki shi yasa nima na dakeke
amma nima raina
baiso ba....!! haba autan inna
kuka ba naki
bane
kinga kin bata wa yayanki
lokaci kusan awa biyu
fa muna jiran ki kuma ya
gayamana
yanada aiki
kuma duk ke kika janyo
araina ......, ASHE KAINE MIJINA..5 ?
Na HAUWA M. JABO
Araina naji dadi ko banza na
bata masa
Lokaci,
amma kuma naji jiki, Lallai nice banida
gaskiya
sabida ina zuwa kawai banga
motaba sai
na
zauna na fara kuka, kuma ni kaina nasan
ba
yanda za'ayi su tafi su barni,
wauta ce
take
damuna ko qauyanci? na bude baki cike
da yawu
da jini na zubar da yawun
gefen inna, inna
da
taga jini hankalinta ya qara tashi,
maimakon in
sassauto in lallaba in tashi
mutafi sai na
fuske,
"kamar jabo tayi rashin kunya ta fuske"
ina
sheshe kar kuna bace inna
ba inda zani na
fasa
tafiya,birnin banza, dan yaga inason inje
birni ne
shi isa yake min wulaqanci,
yanxu kuma
na fasa
zuwa asaukemin kayana, ashe yaya yana
jina, da
qarfi ya fito motar ya bude
bayan motar
motar ya
ciromin kayana ya jefini dasu kikaji jakar
timmn
akaina, tabbas wannan yafi
dukan da
yamin
qonan rai, inna ta kalleshi, ta daure fuska,
ashe
bakada hankali? Mi kayi
kenan? To sai ka
fito min
da nawa kayan nima ba zaniba, tunda abin
naku
rainin hankaline, hankalin
yaya ya tashi,
nima dai
naji tsoro kuma naji kunya, ya durqusa
inna....
kamin shiru ka fito min da
kayana nace ba
zaniba
ko dolene,!! Narasa yanda zanyi akaina
ake mishi
fada kuma nice banida
gaskiya ga uban
taurin
kai, ya juyo gurina nazia dan Allah kiyi
haquri??
na sunkuyar dakai, banji
dadin abinda na
masa
ba... Itama inna taga rashin
dacewar hakan abu
ya
hade masa biyu ta miqe
tsaye ke nazia
tashi ki shiga mota kaima wuce mu
tafi sumui
sumui
kamar munafuka na miqe zan
dauki jakar
kayana yaya ya karba inna tace sake
mata
kayanta ta
dauka da kanta, Lallai ban
kyautaba kuma
duk ni na janyo amma......
ASHE KAINE MIJINA..6 ?
Na HAUWA M. JABO
Amma ya zanyi fuskewa
kawai zan cigaba
dayi yaya yashiga mota nima
nashiga, nasani
sarai
idan akwai abinda ya tsana
baifi ashiga
bayan mota a barshi shi kadai a
gaba ba, na
kuwa fuske
nabi Inna baya, ya kalleni irin
kallon
tausayi muka hada ido amma na fuske
abina, na bude
baya
zan zauna, Inna tace nan
kika saba zama??
Sumui sumui naje gaba na zauna,
yaja mota sai
sakwato
birnin shehu, sokoto garin
dan fodiyyo
garin karamci qarin mutumci, garin
dattako,
garin
kashe kunya, na jinjina muku
sakwatawa,
Allah ya barmu da qaunar ma'aiki.!!
Tunda muka shigo nake raba
ido sabida
qarin
yamin, Gaskiya qarin yanada
kyau da tsabta, sai
kalle kalle nake sabida tunda
nake ban
taba zuwa
sokoto ba sai yau, rabona da
sokoto tun ina
shan nonon innata, haka
kawai naji
hawaye suna
saukomin, Lallai ban
kyautawa yayaba! Na mishi
butulci Sosai, shine wanda
Kullum burinsa
ganin
farin cikina! Shine Kullum
burinsa farantawa
mahaifiyata,! Muna qauye
amma ba wanda
zai
kirani da ba qauya! Ba wanda
zai rainani, a
qauyen mu nice gwana, nice
yar gayu,
nice kowa
yakeso, kuma duk albarkacin
yayanane, yanzu
haka da na shigo cikin birni
duk yan
matan da na
riqa hangowa a mota, ba ko
wacce na gani da
irin tufafinaba, sai daidaiku,
cox yaya yayi
ta
fadamin tufafin da yake min
ai na manyan matane
dinkin ma haka, tufafina
masu tsada na
yayan
masu kudi amma shine zan
yiwa butulci irin
wannan gaskiya dole in........,
ASHE KAINE
MIJINA 7 ?
Na HAUWA M. JABO
Dole in bashi haquri, na dan faki ido na
kalleshi,
sai ya qara bani
tausayi,matuqa narasa
irin
halina, tun bayan rasuwar mahaifin mu
munsha
wahalar duniya, wanda daga
baya yaya
yana
karatu yana bin motar daukar kayan
gwari irinsu
ayaba da lemo da mangoro,
duk dai wani
fruits
da ake yayi, haka zasu loda cikin mota
idan sun
isa gari sai su sauke, ana
biyansu, kuma
ahakan
yake karatu yana wannan sana'ar har ya
qare
secondary anan mai gari ya
dauki
nauyinsa da
yake mai qarin mu abokin marigayi
babane, ya
dauki nauyinsa yaje dan
fodiyyo sok anan
yayi
dgr na farko yana kammalawa ya fara
karantar wa
a sokoto cement primary
anan dai ya sami
kudin
shiga Sosai har ya ci gaba da karatunsa,
duk
albashinsa akan mu yake
qarewa sabida
yaya
mutum ne mai zuciyan yi kuma yanada
son
fitarda kanshi dama wani
nashi kunya shi
isa tun
yana qarami da yake dako kayan kwalliya
ina
dasu komai yana siyamin har
na tasa
nadan
girma, kuma sam bashida qyashi duk
abinda ya
samu inna da naxia,
Mu biyu muke a gurin
mahaifin mu ni da
yaya, mahaifin mu ma'aikacin
prison ne yana
gadi a
sokoto prison a wani rikici da
akayi a
gidan yari aka harbeshi anan Allah ya
karbi ranshi,
tun
daganan muka dawo qauyen
mahaifiyata
da zama tun ina shan nono ataqaice
dai bansan
mahaifinaba.....
ASHE KAINE MIJINA 8?
Na HAUWA M. JABO
Bansan mahaifinaba sai yaya da inna
stakanina
da yaya shekara takwas ne,
sabida inna
tace har
ta daina tunanin haihuwa sai ta sami
cikina ta
haifeni, yaya na matuqar
sona kamar
shine
babana, bansan wahalar rayuwaba sam,
Ki fito mun iso naji ya fada
cikin
sassanyar
murya, tausayinsa ya qara
kamani, ban san
lokacin da na masa
murmushiba, amma
sam
fuskar sa bata kaina, gidan
da na gani ya tsoratani, wani fakacecen
gidane, da gate
yaya ya
bude, muka shiga, naga ikon
Allah araina
nace a cikin wannan gidan zamu
zauna, sabida
ko a
mafarki ban taba ganina a
iran wannan
gidan ba, gidane bangare biyu ban gare
daya an
kammala
ginin dayan banqaren kuma
ba'a
kammalaba amma wanchan bangaren da
ba'a
kammalaba yafi
banqaren mu girma, muka
shiga, muna
shiga na tabbatar da yaya yamin gatan
da yake
fadar zai
mini, naga so da qaunar da
yace zai nuna
mini, tabbas nayi sa'ar dan uwa,
wasu hawaye
suka
sake zubomin, yaya ya shigo
da kayan
mu, ya nuna min dakina komai a
tsare hattana
kayan
make up an saka min toilet
dina sai
wanda ya gani dakin inna ma haka
komai tsab an
gyara, sai
dayan dakin da ya nuna
mana na baqi, ya
nuna ma inna kitchen da kayan
abinci da komai
a ciki
duk da tana daure masa
fuska yana mata
bayanin komai nima yamin bayanin
komai amma
yaqi bari
mu hada ido yayi waya
ya.........,

ASHE KAINE MIJINA 9? 

Na HAUWA M. JABO.

Yayi waya yace aturo yaron
sun iso,
almajiri ya
nema mana wanda zai riqa
mana cefane da sauransu, ya baiwa inna kudi
kamar
yanda ya
saba sai kawai yace sai
anjima ya fita,
nida inna mukayi jugum jugum sabon
gida sabuwar
rayuwa,
Lallai yaya ya cika min
alqawarina, sabida
ya kawo ni birni kamar yanda
kullum nake
cewa
inason akawoni birni gurin
mijina, yau
gani a birni a birnin ma sokoto birnin
shehu, gari
mai
kyau kuma gida mai kyau, in
kalli inna
ina tsoron in mata magana naga ta
daure fuska, sai
na tashi
nashige dakina, nayita kalle
kalle, komai a
tsare kuma tsab dai dai da buqatar
duk wani
dan birni,
hotona dana yaya da inna
munyi kyau
Sosai anyi babban frame dinsa an kafa
a dakina, nayi
kyau a
hoton yarinta na a fuska
qarara amma bai
hana kyauna fitowa ba, yar
qaramar fuskata
das da
manyan idanuwana das dasu,
hmmm
gaskiya nayi kyau a hoton, na zauna
jigum, sai na fara
tunanin
qawayena na qauye fatima
yarin yayar
nura ce duk qauyen mu ita kadai
tamu tazo da ita
sabida
itama yar gayuce iyayenta
suna birni
amma ita tana qauye abinta, nura shine
wanda tun
da
mahaifiyata ta sami cikina
yace idan mace
aka haifa matarshice, hak kuwa
akayi tunda
aka

haifeni ya ke sona ana cemin
matar nura,
mamanshi takance dani auta matar auta,
tun
inada shekara uku, ya koma
birni gurin
yayanshi
baban fatima qawata ban qara ganinsa ba
har
yanzu da nakeda shekera 14
a duniya....,

ASHE KAINE MIJINA.10??

Post a Comment

 
Top