0
NAMANTA KOMAI 

By Yasima Suleiman

NAMANTA KOMAI


 NAMANTA KOMAI 

Amadadin Marubuciya Hauwa M Jabo

   Episode 33 to 40


Ta janyo shi ta zaunar dashi, ta matso kusa dashi, " bakayi bacci ba?" " yad'an sosa kai baccin ne yak'i zuwa" " anan za ka yi baccin kenan,? Bari na maka massage sai kayi bacci ta dad'i," "no no ki barshi kawai yanzu zan yi bacci" ta kyaleshi su ka kwanta, ta matso jikinsa sosai, ita ala dole kissar cikin littafi ta ke so tayi, ha ka bacci ya d'auketa, sannan ya samu ya matsa jikinsa daga nata, Da safee kamar yanda suka shirya zata kira gida ta musu bankwana haka akayi, fuskarshi a sake ya kira wayar Abban ta karb'a bayan Ahmad ya gama gaisheshi, Yace ga Suhailah, ta karb'a ta ce "Dady ina wuni!" "Dady yayi fushi,tunda kin manta dashi ko waya koma ki kira kiji ya na dawo daga tafiya amma shiru," "Dady kayi hak'uri wayarce tawa ta lalace kasan ba yadda za'ai Suhaila ta manta dakai" batason tayi doguwar maganar da za'a gane ta manta komai, kamar yanda tamasa shirme lokacin da yazo, ta ce "Dady ka hak'ura ko!? Yace "Suhaila ai ba kya laifi," tasa dariya" tnx Dady ina Maama,!?" "gata" ya mik'a mata wayar

 " Mama ina wuni" lafiya k'alau Suhailah ya yaran,!? Tace "sunanan k'alau Mama suna wajen kaka Rabi" " Aah Suhails kar in k'ara jin Rabi abakinki, ki kirata hajiya kin ji ko, "to Mama" aranta tace ta kwafsa, ashe hajiya take kiranta, Mama tace" su Rukayya su na ta kiran wayarki shiru," Eah wallahi ta samu matsala ne amma zan kirasu in sha Allah," " to ga Suhail ta mik'a mashi waya, "yar k'anwata ya gida ya maigida," "Hummm..!! K'anwarka ko, to Sannu yayana, in gaya maka ai ko k'anwarka nake na girme maka yanzu tunda yayana biyu" ya kwashe da dariya "to Sannu mai 'ya'ya biyu" haka suka d'an taba hira Ahmad yana ta kaffa-kaffa kar ta kwafsa masu, har tayi masu sallama akan zasuyi tafiya gobe, "kenan ba zamu haduba, mama zamuyi tafiya gashi munso muzo mu ganki kamin mu tafi, amma ba komai sai kundawo" inji Mama. Tace "sai dai idan mun dawo ni zanzo da kaina gurinku" ta mik'a masa Mama tace" to sai kun dawo, Allah ya yi maku albarka," duk sun ji dad'in jin muryarta cike da farin ciki, kamar ba wadda ta guduba dan batason auren suna ta murna ta saki jikinta.

 ********


 Haj mairo kuwa Ahmad ya gaya mata cewa lallai Suhaila bata da lafiya, dan ta manta wani shafi na rayuwarta, bata iya tuna hatta sadda sukayi aure kuma ta d'auka su Surayya 'ya'yanta ne, wannan yasa zai fitar da ita amma kada ta gayawa kowa, sukai sallama Suka tafi, ita da yara harda kukan rabuwa, ita kuka yara kuka, âââ Sun isa Holland A airport wata yarinya baturiya mai kyau sosai, ta taresu mai suna Angelin, a cewar ta wai tayi missing dinshi sosai ya yi introducing d'in Suhaila as matarshi ita kuma Angelin as k'anwarshi, amma yadda ta rungumeshi ya sosa mata rai ba kad'anba, a ranta tace " Dan fa NA MANTA KOMAI ba shi zaisa a mayar dani mahaukaciya ba, ya za'ayi baturiya ta zama k'anwarsa" hakanan take ta yak'e mata fuska, tunda tasan ba k'anwar tashi bace amma sai ta basar, ita ta kaisu hotel d'insu bayan tayi-tayi su je gidansu su sauka yak'i koda zata tafi sai da ta k'ara rungumeshi tayi kissing d'inshi a kumatu sannan. Sukayi sallama, suhaila ta shak'a ba kadan ba, ko ita dai tinda akace batada lafiya bata taba kissing dinshi ba, sai wannan mai kamar da junan rana, tana fita ta dalla mashi harara ya lura da fuskarta ta chanza tun da suka had'u da Angelin, murmushi ya mata ya basar shima. Toilet ya shiga yayi wanka ya yi alwala yayi sallah, ya yi ma su order abinci. Itama haka ta yi wanka tayi alwala tayi Sallah tavsa yan kayan baccinta Sannan suka ci abincin, bayan sun gama ta koma bakin gado ta zauna da littafinta na qur'ani tana karantawa, ya isa inda take zaune ya zauna gab da ita ta mik'e tare da aje littafin a dan stool din gefen gado ya jawo hannunta ya zaunar da ita a kan k'afarshi, "me ya faru ne kike fushi yana kallon idonta.?" Tace" "ba Komai," yace "to me ya b'ata maki rai," "bakomai" " tell me mana yana wasa da yanyatsun hannunta, ya ce "are you jelous ?" ta harareshi tadan turo baki, kallon sa tayi taga yana murmushi yayi mata kyau, sai itama tayi murmushi ta girgiza kanta tace "i'm not" Tana k'ok'arin tashi ya gungumeta yayi kissing d'inta a kumatunta dama da hagu, na k'arshen a wuya, wanda ya aika mata sako a kowane lungu na jikinta, toilet ta shiga tana maida numfashi mai cike da farin ciki, itakam itada mijinta amma sai ta rikajin komai kamar sabo a gurinta kodai dan ta manta komai ne, amma miyasa baya neman tane!? Tace koma miye xata tuna daga baya. Koda ta fito Ahmad ya kwanta, Itama ta kwanta a gefenshi, Can cikin dare ta farka taji Ahmad yayi nisa wajen shafar jikinta, ko ta ina jin hannuwanshi take, nunfashinshi na fita sama sama cikin kunnenta ya zura harshenshi yana kiran Sufee sufee.... da sauri ta tashi zaune ta Kunna fitila..nan da nan Ahmad ya dawo cikin hankalinshi, ya kalleta fuskarshi da gani da alamar tambaya, bata ce masa komaiba, can kuma sai ya tashi ya sa kaya ya fice, bai ji dad'in abunda ya faru ba ya tabbatar da taji yana kiranta da wani suna, shi ya hanashi komawa d'akin ya koma reception din hotel ya cigaba da duba aiyukanshi a computer.

 Koda asuba tayi nan yayi sallarshi ya ci gaba da aiki, k'arfe 10 ya aika mata da breakfast, Sannan ya fita yayi masu booking appointment da Doctor da zai gansu ranar monday mai zuwa, bai samu komawa d'aki ba sai gaf da la'asar, duk da Suhaila taji haushin abunda taji yana fad'a, amma tunda ta manta komai dole ta hak'ura har ta tuna. Yana shigowa lafiya lau ta tarbeshi, sai dai ta nuna damuwarta kan rashin ganinshi duk yinin ranar, ya ce "naje nayi mana booking din ganin Doctor ne zamu ganshi in sha Allah ranar monday, nan da kwana biyu kenan," "to Allah ya kaimu Ameeen.." ki shirya Zamu je wani wuri, ta tashi da sauri tana ta murna, ta shirya,dan zaman ya isheta karatunma tayi ta gaji. Gown tasa material orange colour, ta dora jacket a sama sai takalminta da jaka masu kyau, duk Ahmad ne ya saya mata su kafin su taho, ta daure gashinta, ta dora dan mayafinta mai kamar hijab,tayi kyau sosai, sai kallonta yakeyi tabbas ya yi dace, haka shima, yan k'ananan kaya yasa fari da bak'i, ta lura yana son kaya fari da bak'i,kuma suna mashi kyau sosai, Wani k'aton gida suka nufa, inda ta iske duk mutanen gidan na jiransu, sukai ta rungumeshi ita kuma suna bata hannu, cikinsu akwai Angelin data tarbesu a airport, sai iyayenta, akwai kuma masu aiki a gidan, sai murna suke kamar sunga wanda suka dad'e basu ganiba. Angalen ce tazo gefansa ta zauna maimakon ya hana sai ya barta, ya kamata ya yi mata bayani fa..... 

 Ana chin abinci ana hira Angelin sai wani rawar kai ta ke yi, gashi taje kusa da shi ta zauna, ta kasa sakin jiki ta ci abinci, sai tunini ta ke waye wannan haka? Ta wani zo ta zauna mata kusa da miji, haka har aka k'are cin abinci itakam sai wasa da cokali tana jujjuyashi.! "Kai amma matarka kyakykyawa da ita," samee ke fada suna k'arasawa cikin makeken d'akin gidan, kowa yayi dariya, nan sukayi ta hira, da lokacin sallah yayi Suhailah ta nemi da a bata wajen da zatayi sallah, Angelin ce ta kaita wani d'aki sama, Subhanallah! Ai Dak'er ta yi sallar nan, wani tangamemen hoton Ahmad ne rungume da wata yarinya kamarsu d'aya da Angelin, farko tama d'auka itace daga baya ta gane ba ita bace, Sannan ga hotunan yarta Surayyah nan kala kala a wajen tun tana baby. Tana nan zaune duk abun duniya ya dameta ita kam ta shiga uku, wai ita wacece, miye alak'ar mijinta da wa'annan mutane!? Tana cikin wannan tunani sai ga Ahmad ya Shigo, ko kallonsa batayiba, shima haka yayi sallah, yana gamawa ya ce su tafi, mutanen gidan sunso su k'ara zama, amma sam Ahmad yak'i ya ce hotel dinsu akwai nisa, taji dad'in hakan dan cikinta fam yake da tambayoyi,... Ta lura da yadda ya b'ata ranshi cikin dan k'ank'anin lokaci, amma wannan bazai hanata ta tambayeshi bayanin abunda ta ganiba..... 

Sun isa gida, ya na wani d'aure fuska, aranta tace "abanza dan wallahi sai ka bani amsoshina," yana kwance tazo tace, "Abban twins, ya kamata ka sanar dani a k'alla wasu abubuwa game dakai," abunda ta tambayeshi ke nan, daga kwancen bai dago ba ya ce "me ki ke son sani,..!?" Tace "Wacece naga hotonku tare can gidan da mukaje d'azu ? Ya mata shiru, ta matso kusa dashi ta yaye bargon da ya rufe jikinsa dashi, tace ka min bayani mana, yasan idan ya barta zata birkita masa lissafine kuma gashi bayason ya kusanceta yanzu, " Suhaila nace miki zaki tuna komai a hankali please kiyi hak'uri " kamo hannun sa ta zaunar dashi, ta matso kusa dashi, abinda Ahmad yake gudu kenan , " please ka amsamin wannan tambayar kawai". Ya kalleta, ya yi jeem sannan ya ce "matatace Sufee, amma ta rasu bayan haihuwa" take gabanta ya fadi tana fada a zuciyarta, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...Ta kalleshi, idonta sun kad'a sunyi jaaa dan bala'een abinda ta ke ji, tace "wa ta haifa?" Yace " Surayyah!" "Wato Surayyah ba y'ata bace kenan !?" Yace "'yar kice mana amma ba ke kika haifetaba," wayyo Allah Suhailah Kamar an dab'a mata wuk'a a k'irji ta ke ji, dan tsabar bak'in ciki. Ita dai dama wata zuciya na gaya mata Kamar yarannan ba nata bane, ta kalleshi jiki a mace tace "Rukayyah fa!?" Ya kamo hannun ta, Please Suhailah ki bari zaki tuna komai a hankali," ta kalleshi da rinannun idanuwan ta, ta ce " fad'a min kawai" yanda tayi ni kaina Jabo ta bani tausayi, janyota yayi jikinsa, kusan minti biyar yana shafa bayanta kamar jinjira, sannan ta d'ago tace" Rukayyah itama ba y'ata bace!?" Shiru ya mata, saida ta k'ara tambayarsa, Ya ce "eah ita yar yayana ce ya rasu" Wai.!!! akace ranar wanka ba'a boyon cibi, yau dole ya gaya mata, amma ba haka yaso gaya mata komai ba, ya ma so sai ta tuna da kanta ne, duk laifin Angelin ne, dan ta gaya mashi tana son shi, kuma tanason suyi aure tun bayan rasuwar yayarta, ya gwada mata hakan bazai yiwuba, yasan da gangan tayi hakan dan ta shiga tsakaninsu. Yana kallon ta ta zame daga saman gadon, rik'o hannunta yayi, hawaye ya gani suna sauka a kumatunta, ya kamota ya rungume ta sosai, yana d'an bubbugar bayanta yana bata hak'uri, ta kasa magana sai tafarfasa da xuciyanta yakeyi.

Dak'er ta samu ta d'an k'wace jikinta daga gareshi, ta juya ma sa baya, amma sam bacci ya gagareta, lokaci d'aya kukan da take ta dannewa ya kwace mata, kukan da take yana ci ma Ahmad rai, matuk'a har ga Allah bai so cuta mataba, bai son ta samu matsala a brain d'in ta ba, ya matsa kusa da ita ya jawota kusa dashi, ya k'ara had'a ta da jikinsa yana rarrashinta, ta bashi tausayi, tayi iya bakin k'ok'arinta ta kwaci kanta daga garesa amma ta kasa, yace "Suhaila kiyi hak'uri zaki tuna komai a hankali kinji, cikin sheshekar kuka tace " to ka sakeni bana son ka rik'eni..

." Yace "ba abunda zan miki inason kawai ki daina kukan da kike ne.." ta jawo rigar ta ta goge fuskarta tace na daina kukan ka matsa wajenka plsx". yadan sassauta rungumar da yayi mata amma yananan tare da ita. Tace "wai wane irin accident ne yaja mani shiga wannan mummunan hali !? Ace mutum ya kasa tuna komai a rayuwarsa," kuka yaci karfinta, lokaci d'aya ya tashi zaune, karki wahalar da kanki, memory d'inki zai dawo a hankali, ki kwanta kiyi bacci, ta tuna su surayya yara kyawawa masu shiga rai, wai ace ba 'ya'yanta bane, ta kalleshi sai ta ce "ni ban haihu ba kenan, ko bana haihuwa ne!?" maganar ta so ta bashi dariya sai yace, "kina haihuwa mana, zaki haihu, ki haifa mana yara 12 masu kama dake," tunanin hakan kawai yasa Ahmad farinciki yakai hannu yana murmushi zai shafa fuskarta ta bige mashi hannu, "ki zo yau ma mu sami twins" kauda kai tayi, ta watso masa wata tambayar, "shekara nawa da aurenmu..!?" ta tambaya, yana murmushi ya juya ya kwanta ya bata baya, bai bata amsaba, "na ma zama Abun dariya ko, dole ka mini dariya tunda na zama mahaukaciya wacce bata haihuwa" har cikin zuciyarsa yaji maganar ta amma dole ya shanye, yana jinta taci gaba da kuka. Yaso ya k'yaleta amma ya kasa dan haka shima ya tashi zaune, Yace "Suhaila kukan da kike bazai dawo maki da memory dinki ba, sai dai kawai ya bata maki rai a banza, kinaji likita yace a kwantar miki da hankali, a haka ya zaki ki tuna wani abu?, ya kalleta, sai kukanta take rerawa, "kece kin cika tambaya, a hankali komai naki zai dawo, Suhailah ni ba zan cuce kiba, saboda ni mijinkine...." Ta katse shi da cewa "to Meyasa bazaka gaya mani abinda na tambaye ka ba, wannan wace irin rayuwace, mutum ya zama kamar wani mahaukaci, ba abinda ya sani a rayuwarsa, kuma wai...".

. Ya katseta shima "tambayeni duk abunda ki ke so zan sanar dake inna sani, ta goge k'wallan dake zuba daga idonta tace "kayi alkawari?" Yace "Eh" Tace " Meyasa ban haihuba, ko bana haihuwa ne?" " Saboda ban taba kusantarki a matsayin mata ba," ta zaro ido tana kallonshi cike da mamaki ko alamar tambaya a fuskata..! da sauri ta jawo bargo ta lullube jikinta ruf har fuska, ya kuwa fashe da dariya, tad'an janye bargon ta lek'o da fuskarta tace "yaushe mukayi auren..!?"yace kintuna randa ki ka fara ganin su surayya, ta girgiza kanta alamar eh, yace to rannan ne kwananki na farko a gidana a matsayin mantata". Gaskiya ta ma Suhailah yawa, watau wata d'aya kenan da aure, shine take rungumarsa, shikenan zaice mata yar iska tasan maza, ta Koma ta kwanta jikinta a sanyaye, har taba kanta tausayi, shikuwa Ahmad dad'i yaji kamar ya d'auke wasu kaya daga bisa kanshi, ya juya shima ya kwanta nan da nan bacci mai dadi ya yi gaba da shi, Suhailah kuwa kwana tayi tana juyi tana ta tunanin mayasa ta manta da rayuwarta a baya, batasan takamaimai lokacin da bacci yayi awon gaba da itaba. Motsi taji kusa da ita ta farka koda ta bude ido rungume suke da juna ita da Ahmad, tayi sauri ta sakeshi ta matsa, shi kuwa sai da ya k'ara rungumeta ya yi mata kiss mai zafi a baki Sannan ya ce barka da tashi, sannan ya mike, kunyarshi ta kamata tunda ta gano cewa ita amarya ceeee....

Post a Comment

 
Top