0
NAMANTA KOMAI 

By Yasima Suleiman

NAMANTA KOMAI


 NAMANTA KOMAI 

Amadadin Marubuciya Hauwa M Jabo

 Episode 41 to 45

Shigar da kanta tayi cikin bargo tanata tunani kala- kala, da dauko wannan ta had'a da wanchan ba abinda take tunawa daya wuce daga zuwan ta gidan Ahmdy zuwa yau. A hankali ta rik,'a tuno yarintar ta, ta tuno wanda takeso yazo asibiti amma daga nan bata tuna komai daya wuce haka, tana tuna fuskarshi yana yaro har fad'a warta ruwa saida ta tuna, tanaji ya fito wanka, tayi tseet kamar tana bacci a hankali yazo ya yaye bargon, yana kallon ta, idonta a rufee suke amma duk sun kunbura, ya d'an shafa mata sanyin hannun sa a fuska dole ta motsa Amma tak'i bud'e ido saima juyawa da tayi taci gaba da baccin k'arya, d'aukarta yayi chak, ta bud'e ido da sauri ta fara k'ok'arin saukowa, amma saida ya kaita bayi, ta bud'e ido "miye haka kuma?" Murmushi yayi, kin fini sanin miye hakan" "oya tube kayan ki na miki wanka, dan mun makara," ta zaro ido ta juya masa baya, "nidai ka fita" " lallai mutum da matarsa, wanka zan miki yanzu," bata ankara ba taji yana k'ok'arin cire mata riga, ta rik'e hannun sa da sauri, a shagwabe tace " Allah ka fita bana so" ya kwaikwayeta" Allah bazan fita ba inaso " harararsa tayi ta murguda masa baki, ya matso yana k'ok'arin kissing d'in ta, "sai na cije bakinnan mai jujjuyawa," dagyar dai ta samu ya fita ya barta, ta dad'e a bayin tana tunani tana wanka, dukkan alamu dai love married sukayi, tunda gashi yana mata soyayyah, ohh Ashe wayanchan ba yaranta bane, wani haushi taji ya turnuk'eta, ta kuma tuna ita kam ma budurwa ce, tayi shiru, ta dad'e tana tunani, saida ya fara bubbuga k'ofar bayin sannan ta fito, kanta a sunkuye, tayi sauri ta nemo hijabi ta saka, ya fita musu order breakfast, koda ya dawo har ta shirya, tana burgeshi yanda ta iya dressing, irin na fita waje, suka wucee asibiti. 

 Sun sami ganin likita, likita yace a basu guri, likita ya fara mata tambaya tana bashi amsa, daga k'arshe yace ta zauna akan wata kujera, ta zauna " ki natsu kinaji" ya d'auko wani abu kamar pencil amma ba pencil bane, " ki kalli wannan abin, kuma kada ki daina kallon sa, duk inda yayi kici gaba da kallon sa kawai, kinji " tace masa " ok" ya saka wannan stick d'in a wani machine gaban ta a hankali stick d'in ya fara juyawa yana kaiwa yana komowa, kusan minti goms a haka, har ta fara ganin jiri, sannan Dr yazo gafenta ya zauna, " ya fara mata tambayoyi tana bashi amsa, iya abinda zata tuna, daya fahimci iya abinda take iya tunawa kenan na shekara takwas sai ya gano daga nan zai mata tambayoyi ya kula tana maimaita maganar saurayinta na asibiti "so nake ki gaya min miya faru da saurayinki a lokacin" kawai ji tayi tana zance, sabida lokacin duk tunanin ta da komai nata ya dawo gun Dr. Sai yanda yayi da ita, irin lokacin da zaice ta kashe kanta zata kashe ne batare da ta masa musu ba, ba tareda ta san mi take fad'a ba ta fara" yazo gurina muna magana kuma sai ya gudu ta window ban k'ara ganin sa,.....

 Haka Suhailah tayi ta watso zance a hankali har ta kawo gurinda Sa ya kwashe ta ya zubar a k'asa ta suma, tananan zaune kamar gumki sai bakinta ke antayo zance, saida likita ya tabbatar da cewa komai nata ya dawo kuma ta fad'a sannan yace ta kwanta saman gado, ba musu ta kwanta yace tayi bacci ta kuwa runtse ido sai bacci, ya kira Ahmad, wanda dama yana kallon su a wani TV amma bayajin abinda suke fad'a, ya shigo likita ya masa congratulations, coz ta tuna komai, kuma tana tashi daga bacci zata dawo normal, Ahmdy kam ga murna ga zullumin yanda zata karbeshi, aka mata allurai aka bata magunguna, bata farka ba sai guraren hud'u, na yamma tana tashi wata nurse ta shigo, da wani matsanancin ciwon kai da jiri ta tashi, wanda sai da aka taimaka mata sannan ta iya mik'ewa tsaye, sai da tayi kwana biyu a asibiti sannan ta dawo normal, likita ya hana kowa ganinta sai ranar da za'a sallameta akace Ahmdy yazo ya d'auketa, yana shigowa suka had'a ido, ta tuna shi tsab, daga zuwan sa gidan su har accident d'in da tayi sanadiyar shi, ta tuna yanda yake mata yana wani rungumarta dan sharri, wani tsanarsa taji ya diru a ranta, ta tamke fuska fuska d'aure, "sannu Suhailah " ko kallonsa batayiba ta masa banza, ya tattaro yan kayan ta suka fito asibiti suka nufi gida, tana zuwa gida, fuskar nan a d'aure kamar an aiko mata da manzon mutuwa, yana ta mata magana tana shareshi har dare yayi, ta sauko k'asa tayi kwanciyarta, bai matsa mataba, dan yasan yanda akayi Auren..... 


************************

 Yau kwana biyu da dawowar Suhailah hayyacinta amma ba abinda ya chanza, ko d'aga kai batayi ta kalleshi, bare ta masa magana, shi kuwa abin ya fara damun sa, ko banza yana buk'atar mace, tunda yanada lafiya, gashi ya saba da ita d'an kwana biyu nan da sukayi tare, ga yanda take masa sam baya jin dad'i, yana zaune gaban laptop yana danne danne, tace " please Ina buk'atar waya na, zan yi amfani da ita ne," saida yaji sanyi ko banza ta masa magana yau, "anjima ki shirya sai na kaiki ki siyo ko," bata ce komai ba ta shirya tazo ta tsaya masa, " na shirya" ya kalleta, " kinyi kyau sosai amma ki goge Jan bakin nan bana son ki fita wani ya kalle min ke" ya fad'a yana murmushi ban za ta masa, ya tashi ya shirya har sun kawo waje ya kula da bata goge jan bakin dake bakinta ba, murmushi kawai yayi, saida suka kawo cikin dan dazon mutane ya rik'e hannuwanta biyu da k'arfi, ya fara kissing d'inta, tayi ture ture ta kasa kwace kanta, saida ya lashe jan bakin tatas sannan ya saketa, turus tayi ta tsaya kalle- kalle taga ba wanda ya kula dasu, tsaki tayi a ranta, "Amma guy d'innan ya iya wulak'anci wallhy, " taji haushin abinda ya mata sosai, juyawa tayi ta koma gida, shi kuma ya ci gaba da tafiya ba tare da yasan ta koma ba, saida ya tari taxi koda ya juyo bata, murmushi kawai yayi abinsa haka ya wuce yaje ya siyo mata wayar ya dawo, a reception ya sameta ta makure kamar munafuka, ko kallon sa batayiba shima haka, ya wuce ciki, ya kusan awa daya sannan ta shigo ciki, ta balbalesa da maseefa, tayi tayi ta gaji tayi shiru, ta zauna, tana mayarda numfashi, kamar wacce tayi danbe, ya mik'o mata wayar ba kunya ta karb'a, ta bud'e wayar ta mata kyau, ta kunna ta saka Sim card, amma kuma ba number kowa, ta juya taga yana aikinsa , tashi tayi ta dauko wayansa, hotonta ta gani ita da yara, tana dariya, yaran sun wani chakumeta dayar kuma ta janyo mata gashi, ita kanta hoton ya mata kyau, ta d'an murguda baki, wayar akwai pin, a notifications din wayar wani sak'on daya ja hankalinta shine " miss u too, don't forget it's 4 o'clock." Ta ijiye wayan da k'arfi, saida ya juyo, ya kalleta, "sorry kawo na saka miki number su Dady," dungura wayar tayi, ya taso yazo ya d'auka ya kunna Bluetooth din wayar, yayi marking numbers duka family d'inta da yake da, ya tura mata, ya mik'o mata, ta kalli agogo taga k'arfe 3 da rabi ta gota, tana zaune tana danna wayar ta taga ya janyo wayarsa ya duba sai yayi d'an tsaki, ya ijiye ya mik'e ya shiga wanka tana zaune taji wayar tashi tayi 'yar k'ara kad'an, taje ta duba, SMS ne, wai " Ina jiran ka please" murmushi tayi ta ijiye wayar, ya fito daga wankan sa, ya duba wayar sauri sauri ya shirya, yayi kyau, ya juyo ya kalleta, "okay zan fita" yasan ba kulashi zatayiba kawai ya fita hakkin tane, abin mamaki murmushi ta masa, wanda saida ya k'ara juyowa ya gani shin da gaske ne murmushin ta masa, mik'ewa tayi tsaye ta biyo bayan sa, yana zuwa yaji k'ofa a kulle, juyowan da zaiyi sai sukayi kichibis da juna, a hankali ta tallabo kansa, ta matso kusa dashi sosai ta fara kissing d'in sa.


Post a Comment

 
Top