0
NAMANTA KOMAI 

By Yasima Suleiman

NAMANTA KOMAI


 NAMANTA KOMAI 

Amadadin Marubuciya Hauwa M Jabo

   Episode 27 to 32


Bayan sun kusa gida, ya tsaya ya yi musu siyayyah, gurin bata ledar hannayensu suka had'u dana juna, saida yaji wani iri, sun iso gida, ta wuce d'akinta, biyo bayanta ya yi ba tare da ta sani ba , tana k'ok'arin cire kayan jikinta, ya shigo d'akin, duk da cewa taji wani iri daya ganta ba wasu tufafin, sai kuma tace mi zan boyewa mutumin da ya dad'e da sanina hadda yaran mu biyu... Ahmad kam yaji wani iri, yad'an sosa kai ya duk'ar da kanshi k'asa dan yaji wani iri sosai, gashi ya dad'e ba mace tun bayan rasuwar matarsa, ya zauna sai ya juya mata baya dan yana gudun kar a samu matsala. Saida ta k'are saka kaya ta na neman hanyar fita, Yace "Suhailah baki tambayi result din hospital d'inki ba?" Tace "to ai na san zaka gaya mani indai na in sani ne", ta d'an yi murmushi, da alama ta d'an saki jikinta, ya ce "kin d'an samu accident ne ki ka buga kanki, shine kuma ya ja maki wannan lost of memory din, amma Dr. ya tabbatar mani da cewa zaki koma normal cikin d'an lokaci kad'an, dan haka karki tada hankalinki kinji?", ya fad'a yana kallon ta, "kinga yanzu saboda haka ne na ke so in kai ki Holland dan a k'ara dubaki, in sha Allah nan da kwana biyu zamu tafi," wasu kwalla suka zubo daga idanuwanta, tasa bayan hannunta ta goge, ta dago kai ta dubeshi ta ce "to na gode", harda murmushin karfin hali, har ya mik'e zai fita tace "dan Allah ka gaya mani wani abu about My self kila zan tuna," hakikanin gaskiya, tun lokacin da hannayensu suka had'u ya farajin sha'awar da ya dad'e baiji irinta ba, kusan tun rasuwar matarshi baya da lokacin mace, aikinshi kawai yasa gaba da binciken abubuwan dake faruwa da wa'danda suka faru a baya, ga addini ya rik'e hannu biyu , mafari kenan Alhaji Ibrahim yayi sha'awar hadashi da Suhaila dan Ahmdy akwai addini .

 "Zan gaya miki amma saida safe". Ya tashi ya wuce dakinshi, amma kuma ogan naku ya kasa sukuni, gashi an dad'e ba'a haduba, ya fito da niyyar ya d'an kalli fuskarta ne kawai, amma sai ya isketa ido biyu, yasan matarshice halaliyarshi, amma sai da yaddarta, da kuma lafiyarta ya ke son ya kusanceta, kuma yanzu gashi har tunani take wai ta haifa mashi yara, zayyi k'ok'ari ya danne sha'awarshi har yaga ta dawo cikin hankalinta kafin ya kusanceta a matsayin matarshi, alk'awarin da yayi ma kanshi kenan To ko zai iya kuwa?? Har wata zuciya ta bashi shawarar ya koma d'akinshi abunshi, amma sai ya kasa yazo yace "to matsa mani na kwanta", zuciya d'aya tunda gani take komai ya riga ya faru ta yaye bargo ta matsa mashi ya zauna kusa da ita, ya kasa kwanciya sai ya jingina da gadon, yace "to daga ina zan fara" ya fada yana Murmushi, a lokaci d'aya ya jawo bargo ya lullube k'afarshi, ta matsa kusa dashi sosai tace "babana shine wanda yazo ko? mamana da k'anena sune wayanda nayi waya dasu ko? To Ina da yayye?" ya yi dariya sosai yace "kinason family da yawa kenan?", ta zaro ido "bani dasu ne? Ko ba sune nawa ba", yadda tayi ya bashi dariya, kallonshi take sosai ta cire bargon ma sama daga jikinta ta lank'washe k'afafuwanta, ita hankalinta kwance da yar rigar baccinta, shara shara, ya d'auke idonshi da kyar daga kallon duk inda jikinta ya bayyana, dan kayan baccinta kamar yar singleti ce da short wando rabin cinya gasu shara-shara.

 Ahmad ya samu kanshi da rik'o hannunta, kamar zata anshe sai kuma ta bar shi ya rike tunda mijintane, ya yi murmushi ganin ta amince da hakan, ya ce kina da yaya d'aya Ameen, kina da abokin haihuwa Suhail, ke kuma sunanki Suhailah, ku twins ne," "laaa shi isa na haifi twins", ya dai bata dan labarin da ya sani game da ita da asalin babanta da mamanta, yana kauce ma duk wani abunda zai sosa mashi rai, dan labarin family dinta ba a iya rabashi da na family din shi, tace "to na ji na wa, saura na ka, a ina mu ka hadu da kai, har mukayi aure?" Ya ji wani rass gabanshi ua fad'i, yace "kibari zaki tuna a hankali, "Pls ka gaya mini," ta wani langwabe kai ta matsa jikinsa sosai, tare da d'an matse hannunshi da nata cikin shagwaba tana wani farfar da ido, mutumin fa ya fara daukar zafi, ya na jan nunfashi da k'arfi yana fitarwa, ya runtse idanuwanshi yana neman natsuwa, ya bud'e bayan d'an lokaci kad'an yace "mun had'u tun da dad'ewa bayan nan mun k'ara haduwa a bikin su Al- Ameen sai daga baya kuma mukayi aure," tace "yauwax", ta k'ara matse mishi hannu, "to wayafi son wani ni da kai?", bai amsa tambayar ba ,saboda ya aureta ne dan mahaifinta ya ba shi ita, "yaranmu yan biyune ko,? D'azu kace min maman twins haka kake kirana dama?",yace kin cika tambaya, tace "da banida yawan tambata hala?", Ya daga mata kai, dan ya riga ya d'au zafi ko magana baya son yi, ta ce ''to na daina", ya ce "ya akayi baki mance da sallah ba?", ya tambayeta dan ya ji tana ce ma yaran su zo su yi sallah, tace "wallahi ban sani ba," to Ina son ki natsu kiji abunda zan gaya maki, "Suhailaa you are a Doctor," ai sai ta mik'e kan gado tana tsalle da rawa, shiyasa taga wani k'aton littafi a cikin kayanta wai shi "internal medicine," duk sadda ta samu lokaci tana karantashi, data natsu ya kamo hannunta yana magana a hankali kamar baya so, yace "bani son kowa yasan kin samu wannan matsalar dan kar ya jawo maki matsala a gaba, dan haka kar ki gaya wa kowa, kinji?", gobe zamu kira su mama ki k'ara gaishesu kuma kiyi masu sallama, jibi zamu tafi", tace "to In sha Allah ba wanda zai ji....

 Suhaila yarinya ce mai ban sha'awa, bare kuma yanzu da ta ke cike da farin ciki ganin mijinta ya dawo mata, kawai sai ya ji ta rungumeshi ta ce na gode, shima ya rungume ta yana shak'ar k'amshinta da ya bai baye ko ina cikin d'akin. a hankali ya ke neman natsuwa, amma tana neman ta rikita mashi lissafi, ya runtse idanuwanshi. Dai-dai kunnenshi ta ce "wane suna nake kiranka dashi, Ahmad haka nake kiranka ko?" Dak'er ya daure cikin natsuwa ya ce "sai ya ce sunana kenan ai," ta ce "amma nima haka nake kiranka dashi?" "No" ya fada ya na d'an murmushi. "To ya nake kiran ka dashi?" Ta tambaya. "kar ki damu za ki tuna yanda kike kirana". "Ok, yanzu tell me about you," tana k'ok'arin ta tashi zaune daga d'an kwantawar da tayi a jikinsa, aranshi yavce wannan yarinya akwai jaraba, ta k'ara gyara zamanta tana kallonshi.

 "To....." Ya katseta, ya ce aa, ya isa haka, ki kwanta kiyi bacci dare yayi sosai,da kanshi ya gyara mata kwanciya, ya lullubeta, ya mik'e zai tafi, har zai tafi ta rik'o hannunshi, "please ka kwanta dani, ko dan banida lafiya kake guduna ko kuma dama ba tare muke kwana ba!? "Innalillahi! Wannan yarinyar so take ta kasheni" abunda ya fad'a kenan a zuciyarshi, ta jawoshi tare da matsa mashi, inda zai kwanta kusa da ita, "oya zo ka kwanta" haka ya samu kansa da kwanciya inda ta matsa mashi. Tunani ya ke ya san fita da ita zuwa k'asar Holland bazai masa wuya ba, dan yasan can sosai, visa ma ba zaya sha wuyar samu ba tunda ya zauna can ya dad'e, kuma ya na da mutane da yawa acan. Bawan Allah Ahmad sai gaf da asuba bacci yayi awon gaba dashi, dak'er ya tashi yayi sallah, Sannan ya tashi Suhailah, itakam duk da tajita daban kamar ba ta saba da irin hakan ba da suka kwanta ya rungumeta, amma tayi bacci mai dad'i, ta bar shi akan dan ta manta komai ne yasa ta ke jin hakan, suna had'a ido ta masa murmushi, itakam gani take kamar ta fishi sonsa, amma so take ta danne har ya gaya mata gaskiya wayafi son wani ita dashi. Tayi alwala tayi sallah, ta nemi guri ta kwanta amma sai taga Ahmad zaune yanata lazimi, tadan matso kusa dashi, tace "nima ina wannan zaman bayan salla asuba ada!?" Yayi mata murmushi, sai ta kanne masa ido, yayi sauri ya kawar da ganinsa gareta, yace "wani lokaci kinayi wani lokaci kuma bakya yi," tace "heheeeee irin yaune banayi dan kuwa bacci zanyi, ta dubeshi, ka mini addu'a na haifi namiji, tunda inada mata har biyu," baice mata komaiba, hasali ma kasa lazimin yayi dan sai hada masa zafi takeyi, tazo gefensa ta kwanta.!

 *********** 

Rannar ya dawo gida da wuri, ba kamar da ba, da sai tayi bacci, yanda Ahmad ke son yaransu ya birgeta sosai, taji ta k'ara sonsa tunda yanason yaranta, yau kam duk tare sukaci abinci rana da ita dashi da yaran su, yaran sam sukak'i yadda su ci su kad'ai, wai sai sunci abinci tare da ita a plate d'aya ganin Ahmad na murmushi yasa ta biye masu, suka cinye har suka k'ara, bayan sun k'are 'yar bak'a ta kwashe yaran da kwanuka, bayan sun gama tayi masu shirin bacci, ita kuma Suhaila ta gyara inda sukaci abincin har Ahmad d'in na tayata, sai abin ya burgeta, aranta tace, "kilama ada haka mukeyi, Ashe dai mijina ya had'u, yauma sau biyu hannunsu na haduwa, garin wanke kwanuka, inda suhaila kejin wani irin sak'on da bata saba jiba na mata yawo a kowace kafa ta jijiyoyin jikinta, batajin dad'in hakan, sai taji kamar ta bar mashi aikin kawai. Wajen bacci ma haka yaran suka nace su da Dady zasu kwana, ba wayonda ba'a musuba amma sukak'i yarda. Haka Suhailah tayi ta juyi ita adai a gado ta kasa bacci, dan ta saba tun randa tazo tare suke kwana da yaranta sai jiya da sukaje asibiti suka kwana da Ahmad, yanzu gashi ba yaran ba uban, tsaki tayi ta juya har ta fara bacci. Can cikin dare taji an bude kofar d'akinta an shigo har taji dadi a zatonta su Surayya ne, murmushin dake fuskarta tuni ya bace ganin Ahmad har ya karaso gaban gadonta, nan suka tsaya suna kallon kallo, na dan wani lokaci sannan ya zauna daga gefen gadon, tuni ta gyara zamanta ta matsa dayan gefen gado, yace "miye haka kuma!? Da sauri ta k'irk'iro murmushi tace "laaa ba komai, zo ka zauna ta na k'ok'arin janyo hannunsa..

Post a Comment

 
Top