NAMANTA KOMAI
By Yasima Suleiman
NAMANTA KOMAI
Amadadin Marubuciya Hauwa M Jabo
THE END
Kissing d'insa ta shiga yi kamar me, duk da bawai ta wani iya bane, ogan naku dama ana nema, tuni ya saki jiki yana maida martani dan shi har ya fita zak'ewa, tunda hannun sa har yayo kasan rigar ta, tana jinsa ta gyaleshi Saida ta tabbatar da ya fita hayyacinsa, sannan ta kwace jikinta a hankali, ta bud'e masa k'ofa ta dawo ta kwanta, tsaye yayi yana kallon ta, amma kwata- kwata ya manta ta cewa ana jiran sa wani guri, biyo ta yayi yana kiran sunan ta, ya d'an tabata, batasan lokacin da tace dashi " budurwarka fa tana jiran ka kada ka makara, yanzu har hud'u da rabi" tsaki yayi ya janyo ta, ta fuskanceshi, ta wani d'aure fuska kamar ba itace ta k'are tsu tsarsa ba d'azu, duk ta tayar masa da hankali, "miye haka Suhailah?" banza ta masa, kamar ba da ita yake ba, yayi shiru yana kallon ta, ranshi ya baci, a hankali ya tashi ya tube kayan sa, ya koma saman laptop d'insa yaci gaba da abinda yakeyi, tana ji wayar sa na k'ara alamar SMS, saidai ya karanta ya ijiye, aka kira yayi rejecting, har aka daina kiran. chan bayan magreeb taga wayar ta matsa da kira, shi kuwa ogan yak'i ko motsi, sai ta tashi taje ta d'auki wayar, yana kallon ta, tana d'auka taji mace na bashi hakuri, batace komai ba saida ta k'are, ta kashe wayar, SMS ya shigo, wai ga tanan zuwa gurinsa, ta ijiye wayar, ya kalleta "waye ne?" Tace " sister d'in ka ce" tana fad'ar haka ya gane Angelin ce. Yaci gaba da lazimin sa saida ya k'are ya shirya zai fita, " ina zaka? " " zan dan zaga ne, na gaji da zama" " okay jirani nima na gaji da zama, wai yaushe zamu koma gida " ya kalleta wannan yarinya akwai masifa," cikin satinnan nan, insha Allah " inason na yiwa yarana siyayyah ne" " OK muje yanzu " " yanzu ai kanada bak'uwa saidai wani lokacin " kallon ta yayi, "Suhaila kishina kike wai?" Takalleshi ido cikin ido, " no ina kishin su Rukayyah ne, banason naga Dady dinsu yana bin mata," maganar ta sosa mishi rai' BIN MATA, "kinji kuwa abinda kika fad'a min Suhailah " "of course'' dawowa yayi ya zauna, ya fara magana bai damu da ko tana jinsa ba, sai da ya k'are tace "kurungus muje ko" ta bashi haushi ba kadan ba, tsaki yaja, kamar zata rama sai ta fasa, sun fita sun zaga gari ba wanda yake ma dan uwansa magana suka dawo, yan kwanakin da sukayi duk zai fita sai tace saidai su fita tare ta gaji da zama, ta hanashi sakat, har suka tashi dawowa gida, tama yaran ta siyayyah sosai, 'yar bak'a ma ta mata, da kaka rabi, bata siyawa kanta komai ba, amma ta kula Ahmdy ya siyo mata, kuma duk abinda ya siya ya burgeta.
Sun iso gida guraren hud'u na yamma, cike da shauk'i ta shigo Palo, ido hud'u sukayi da Rukayyah, da gudu ta taso tana murnar ganin Mumy, ta rungume ta, Surayyah ma ta fito anan suka dabai bayeta, suna murnar ganinta, itama tayi missing d'in yaran ta, dukda yanzu tasan matsayinsu a gunta amma bata daina jin sonsu a ranta ba, duk inda tayi suna biye da ita suna bata labarai, itakam yanzu bayan sonsu da take, tausayin su ya k'aru a zuciyarta, marayun Allah, basu barta ba saida ta basu tsarabarsu da ta kaka Rabi suka kai mata sannan ta sami kwanciyar hankali, tayo d'aki ta shiga wanka ta fito daure da towel ta d'an kwanta tayi baya da kanta, tana tunanin rayuwarta, koda ta bud'e ido Ahmdy ta gani tsaye yana kallonta, rufe idon tayi taci gaba tunanin ta, ya gaji da tsayuwa ya wuce d'akinsa, saida ta gaji da tunane tunanenta sannan tayi baccinta, Sun dawo da sati d'aya ba abinda ya chanza daga halayen Suhaila na shariya, bata kula shi shima ya baiwa babu ajiyarta, ta shirya zuwa ganin gida, bai mata gaddama ba, ya bata duk wani abu da zata buk'ata, kuma yasa driver ya kaita, tafiyar ta da kwana uku, Angelin tazo Nigeria, gun wani aiki da bincike da zasuyi akan company babansa, kuma tak'i sauka hotel ta nace sai gidan sa zata sauka, yaso ya ijiyeta hotel har su k'are amma tak'i, dole ya barta gidan sa, sabida ta nuna mai kamar yana nuna mata wariyar launin fata, bayan itama 'yar uwarshi ce, hakan yasa ya barta, suna aikin su na binciken kayan mahaifinsa da ita lafiya lau, Suhaila ta dawo, baisan cewa zata dawo ba ranar sam, sun dawo daga wani guri gun wani bincike shida, Angelin kawai sukayi kichibis da Suhaila, ta kalleshi ya ya kalleta ta kalli Angelin, shi kanshi yaji wani iri dukda cewa yana da gaskiyarsa, amma ya razana, ta matso kusa dasu tafa musu tayi saida tazo dai-dai su ta tsaya, ta kalleshi cikin tsiwa " Abinda kukayi a Landon bai isheku ba, sai ta biyoka har gasar ka ko? A gasar ma a gidan ka," ta dafe kai, ta rasa mi ke mata dad'i "wai kishi takeyi ko miye," ta hareresa, " da anyi magana sai ka kishi kishi, banida ai ki sai kishinka," ta dago ta kalli Angelin kallon tsana, kamin tayi magana Angelin ta tambayi Ahmdy"mi yasa take ihu ne?" Suhaila ta k'ule saukar mari kawai naji, nima Jabo bansan lokacin da akayi marin ba, kamin na juyo naji na gani da kyau naji an sauke na biyu, abinka da farar fata, tuni tayi jaaa, Ahmdy ya juyo zai yiwa Suhailah magana, ta kasteshi, shima ya wanke ta da mari, Angelin da gudu ta wuce d'akin da aka sauketa tana kuka, tana shiga ta fara hada kayan ta, Ahmdy yabi bayan ta, yana rarrashi, hadda su rik'e mata hannu...
Suhaila ta dafe kunce tana jinjina wa, koda ta d'ago ido, ta ganshi yana k'ok'arin rik'e ma Angelin hannu, ta juya ta wuce d'akinta tana kuka, tana zaune tana kukan ta, yaranta ne suka shigo ta daka musu wata tsawa, tuni suka rud'e sai kuka, suka fito suna kuka, Shi kuma da gyar Ahmdy ya samu ya lallabi Angelin da sharad'in zata koma hotel da zama, dama itace da naci da jaraba, tace sai gidan sa, ita dole sai ya sota, yana fitowa yayi karo da yaran suna kuka, suna hangoshi sukayo kansa, Dady, "Mumy batason mu" ya tsuguna ya rik'e hannuwansu, "kuyi shiru tana sonku, kawai batada lafiya ne amma da taji sauk'i zata soku kunji" suka gyada kai alamar eh, har sun kama hanyar d'aki sai Rukayyah ta juyo, " Dady kada ka daketa, muna sonta," murmushi kawai yayi, ya wuce d'akin nata, ya sameta, kuka take sosai, ita babban abinda yafi bata haushi dukan ta da yayi gaban karuwarsa, yanzu sai ta rainata, yazo ya tsuguna gabanta ya kamo hannuwanta da sukayi wani zafi, yana rarrashin ta, ko alif bata ce masa ba, har ya k'are sunbatunsa ya mik'e, har yakai bakin k'ofa, ya waigo "idan na dawo zan miki bayani," itakam taci kukanta, ta k'are tayi wanka tayi sallah, Amma bata sauko k'asa ba, bare taci abinci, nan bacci yayi awon gaba da ita..
*******
Yana fita yaje ya kai Angelin hotel ya bata hak'uri, kuma ta hak'ura, har suka fara wasu ayyukan, cikin nasara kuma suna samun ci gaba, suna k'arewa yayo gida, ya tarar tana bacci, chan cikin baci taji ana kiran sunanta, sai ta bud'e ido ta ganshi sai kawai ta rufe idonta, anan ya fara koro mata zance, daga zuwan Angelin Nigeria, da duk wani abu da yasan zata fahimta ya mata bayani, ya rufe da cewa "duk akan mahaifina nakeyi, sabida inason nasan cewa yana raye ko yana mace, amma insha Allah na miki alk'awarin cewa gobe zan mayar da Angelin k'asar su, ni zanci gaba da ayyukana matuk'ar hakan zai cire miki shakku na aranki, amma ki sani ban taba kasan cewa mai neman mataba, tunda Allah ya halicceni, kuma bana fatar hakan ta kasance dani insha Allah" yana kaiwa nan ya mik'e ya wuce, ta bud'e ido, ta tashi zaune, ta fara tunani "idan na mishi haka ban mishi adalci ba, musamman idan na bari ya maida Angelin gida," ta mik'e tsaye, miye matifa?
Tana zagayen dakin har chan kawai ta yanke shawarar bari ta bishi tace kada ya maida Angelin yayi hak'uri, musamman sabida mahaifinsa, ta fito d'akin ta, ta tsaya kalle- kalle, nan ta tuna cewa ya taba gaya mata dakin sa, nan ta tuna wulak'ancin da ya mata lokacin da take tambayar sa abinda ta manta, taja ta tsaya wani haushi ya turnuk'eta, sai kuma ta kawar da wannan tunani, tabi hanyar da yace mata d'akin sa ne, ta dad'e bakin k'ofar d'akin kamin ta yanke shawarar fad'a wa, a hankali ta tura k'ofar d'akin ta shiga, yana zaune gaban wani table ya d'aura kansa akai, har ta k'ara so bai san ta shigo ba, tazo a hankali tace" Abban twins " da sauri ya d'ago kansa cike da mamaki suna had'a ido, ta masa wani kwauron murmushi, hannu yasa ya kamota ya matso da ita kusa dashi, ya zaunar da ita saman chinyarsa yad'an shafa fuskarta a hankali, bata ce masa komai ba, chan tace "please kada ka mayar da Angelin gida, ka bari sai kun kammala, Allah yasa a dace," yaji dad'i sosai, ya kalleta na tsawon lokaci, sannan yayi numfashi, " Suhailah!! Miyasa bakya sona" ta kalleshi da sauri sai ta sunkuyar da kan ta, batace komai ba, sai ta mik'e idonta suka kai kan wani hoto wanda duk inda taga pic zata ganeshi, ta kalleshi "Abban twins ina kasamu wannan hoton?" Yace " My princess kenan " matsowa tayi ta rik'e shi, "My princess kaine dama!? Kaine mijina,?" Kuka ya kubuce mata ya kamota ya had'a ta jikinsa, yana rarrashi....
Anan suka k'ara fahimtar juna, suka baiwa juna hak'uri, bayan sunyi sallar magreeb da nafilolin su, a ranar dai har Allah ya baiwa Ahmdy damar aikata sunnar Annibi, (S.A.W) abinka da sabon shiga, shi kuma tsohon kai an saba saidai an dad'e ba'a had'u ba, ta ji jiki irin yanda duk macen da batasan namijiba a daren farkon ta takeji, Allah sarki Suhailah manya, ta tashi tana kunyarsa shi kuma sai kallon ta yakeyi cike da farin ciki yana saka mata albarka, yaso ya tayata wanka amma tak'i sai ya barta. Da safe bayan sun karya yana zaune sai sunkuyar dakai takeyi. Wayarsa ce tayi k'ara, koda ya duba Angelin ce, ya kalli Suhailah ta sunkuyar da kanta k'asa, murmushi kawai yayi ya d'auki wayar, bayan ya k'are ya mata bayanin komai,
**********
Ahmad da Angelin aiki suke babu kama hannun yaro, sunyi bincike sosai cikin nasara, daga k'arshe suka gano komai da sa hannun Alhaji Isma'el a ciki, basu tsaya wata-wata ba suka sa aka kamashi, bayan bincike ya nuna yana da hannu akan komai, saida yasha wahala sannan ya yi bayani, ya fad'i gunda mahaifin su Ahmdy yake, an dauko shi duk yabi ya hargitse ya k'ara tsufa, abin ban tausayi, family sunyi murna da ganin sa, ashe yana raye, bayan da yawa sun fitar da rai akan cewa za'a ganshi, daga k'arshe Allah ya fito dashi, a dai- dai lokacin ita kuma Suhaila tana d'auke da cikin Ahmdy wata biyar. Soyayyah suke zubawa kamar me, musamman Suhailah data ta karance wannan book na yanda ake kula da miji girki shagwaba duk ba'a barta a baya ba, sabida sune jigon rik'e miji, munsan cewa duk macen da take son ta zama mowa a gurin mijinta, to dole ta zama mai tsabta, girki, kwalliya shagwaba uwa uba kwanciya, to Suhailah duk ta had'a su, ga k'amshi da takeyi kamar me.
*************
"Wai waye yake taba min yarinya,? " ta fad'a tana saukowa downstairs, " Laa Ashe Abbah ne, Sannu Abbah!," ta fad'a cikin kunya, Suhailah ce taji ihun su Surayyah take masifa, koda ta fito sai taga mahaifin su Ahmdy ne yake wasa da yan jikokin sa, su kuma suna masa ihu, yaron da rik'e a hannun ta, ya fara mik'a hannu alamar shima a d'aukeshi, Abba ya mik'o hannu ta mik'a masa yaron, d'an shekara d'aya da watanni, yanata dariya, tunda mahaifiyar Ahmdy ta rasu mahaifin su Ahmdy ya dawo gidan Ahmdy, part dinsa daban, amma kullum yana cikin yan jikokin sa suna faran ta masa, rayuwa tama su Suhaila alhamdulillah, saidai muyi musu fatan alkhairi...
TAMMAT BI HAMDILLAH. Wasallahu ala Muhammad wa alihi wa sabihi wa sallam. Godita ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, Ina mik'a gaisuwa ga masoyana HASKEN IDANUWANA, masu bibiyar wannan littafin dama sauran littafaina, Allah ya saka ya bar zumunci. Musamman Yan group dina, M. JABO MUNBARIN NOVELS. Da yan kungiyar mu ta NAGARTA WRITERS ASSOCIATION. Da sauran groups, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci.
THE END
Post a Comment