0
IDAN ZUCIYA TA GYARU 
 By yasima Suleiman




IDAN ZUCIYA TA GYARU


 Episode 7 to 8

****************


Iyayansa da kansu sun lura da halin da ya shiga don haka sun dukufa gurin yi masa addu'a da sanyawa ana masa sauka. Yau kam ya dira a cikin gidan nasu, Suna soro da Zaid bisa tabarma suna karatun Sahihul Bukhari yana mata kari ya shigo da sallamarsa, suka yi kallon kallo da Zaid sannan suka gaisa Zaid ya hade littafansa yana fadin, "Zainabu bari naje na dawo, daman na gaya miki ina da Interview da azahar, zan shigo da dare." Ta bishi da kallo tana fadin, "To sai ka dawo." Sannan ta maida kallonta ga Mustafa dake tsaye hannuwa zube cikin aljihu ya sha kunu matuka, ta yi murmushi sannan ta ce, "Bawan Allah ka zauna mana, irin wannan kumburi haka kamar zaka rufeni da duka." Ya yi kwafa sannan ya zauna yana fadin, "Rainin hankalin naki ne naga yana neman wuce gona da iri, yanzu haka ina ofis a zaune na gaza tsinana komai saboda rashin sanin matsayina a gurinki kullum raina yana cikin fargaba da dar-dar, an ya Zainabu duniya da gaskiya za ki so wani da raina da lafiyata?" Ta dan yi murmushi gami da gyara hijab dinta ta ce, "Malam Mustafa kenan, nice da baki na na gaya maka ina son wani ko gaya maka aka yi?to sai an gaya mini? ai duk wanda ya ga yanda kuke da Zaid ya san kina son sa, don wata gulma wai karatu yake koya miki kullum yana manne da ke, duk makarantun garin nan basu yi miki ba sai nashi karatun eye, ni kam na gaji da ganin wannan abu ki sanar da ni matsayina a gurinki kawai Zainabu.

" Ta yi jim sannan ta ce, "Mustafa ai kafi kowa sanin matsayinka a gurina ko na fada ko ban fada ba duniya ta shaida irin son da nake maka, kuma wallahi har abada ina sonka, sai dai duk son da nake maka kayi mini nisa ka haramta a gareni dole na hakura da kai, dole na yi amfani da karin maganar hausawa da suka ce 'idan so cuta ne hakuri magani ne', domin wallahi ba zan kuma yadda na sabawa Allah da gangan ba, zuciyata ta gyaru don haka ina son duk kan mu'amalata da aiyuka na suma su zama gyararru." Jikinsa yayi sanyi idanuwansa suka sauya launi ya ce, "To Zainabu baki ganin muna da sauran dama, ina ce kwanaki mun yi maganar auran kisan wuta da zaki yi sai mu mai da auranmu? Amman muddin kika auri Zaidu nasan na rasaki har abada domin wallahi ina ganin irin son da yake miki cikin kwayar idonsa, ki taimake ni Zainabu kece ruhina don Allah." Idanuwanta suka ciko da kwalla sai taji wani son Mustafa ya kuma taso mata, sai dai tsoron Allah yayi tasiri a zuciyarta matuka don haka ta ce, "Mustafa muji tsoron Allah mu daina tsarawa kanmu rayuwa bama tuno da mutuwa, yanzu ka duba ina Sala take, wane irin buri ne bata ci ba a rayuwarta, shin buri nawa ta sami damar cikawa? babu ko daya, don haka ka sanya a ranka ko yau ko gobe ko yanzu zaka iya amsa kiran Allah, don haka ni kam bazan boye maka komai ba na yanke shawarar zan auri Zaid aure na tsakani da Allah, ba zanyi aure da niyyar na fito ba, sai dai idan Allah ne ya kaddara mini, idan Allah yayi da rabon zama a tsakaninmu zamu sake yi a gaba idan kuma babu mu godewa Allah da duk yanda ya tsara mana, amman ni kam babu batun auran kisan wuta a gabana, kai ma ina so kaji tsoron Allah Mustafa.....

kuka ya ci karfinta saboda yanda zuciyarta ke tafasa da son Mustafa, ji take kamar ta kwanta a jikinsa taji sanyi, amman ina yayi mata nisa har abada domin dai tana rokon Allah ya sanya mutuwa ce zata raba ta da Zaid. Kamar zai kuma cewa wani abu amman sai ya kasa kawai ya mike a zuciye ransa yana tukuki ya fice. Ta mike ta bishi da sauri don kada ya yiwa kansa illa ta taddashi har ya shiga motar ta leka kanta ta windo ta ce, "Mustafa ka tuna kai musulmi ne cikakke, kuma imaninka ba zai cika ba sai ka yadda da kaddara, lallai rabuwarmu muna son juna tana cikin kaddarar da Allah ya shirya mana, kayi imani ka amsheta hannu biyu, ka kula da kanka kada kayi tukin ganganci, kayi ta zikiri ga Allah zaka samu sauki da rangwame a zuciyarka." Ya kura mata ido ganin yanda hawaye ke malala a kuncinta ya sanyaya masa jikinsa, ya tabbatar Zainabu na son sa sai dai kaddarar zata raba su kamar yanda ta ce, yayi kokarin kakalo murmushi yana fadin "Na gode Zainabu zan dawo wani lokacin amman ina ji a jikina yau ce rabuwarmu ta karshe ko na mutu ko kuma na rasaki har abada, zan rungumi Zainab da Zainabu ne sune zasu maye mini gurbinki, Insha Allah zan zama mai kokarin juriya da rashinki, ina fatan zaki yafe mini duk wani laifi dana taba yi miki a rayuwarki.

Post a Comment

 
Top