0
MAGANA JARICE LITTAFI NA DAYA

labari na goma sha daya


LABARIN WANI JAKI DA SA


Labarin Wani Jaki Da Sa

      Wata rana an yi wani mutum wai shi Sale, wanda Allah ya yi wa arziki kwarai. Kullum dare mutumin nan sai ya yi ta addu’a, yana rokon Allah ya ba shi ilmin fahintar maganar dabbobi. Duk inda ya ji duriyar wani shaihun malami, sai ya aika masa da kudi, ya yi masa roko Allah ya biya masa wannan bukata.

Ana nan, a kwana a tashi, Ubangiji maji kan bawa ya karbi rokonsa. Ran nan Sale na barci, ko da ya farka da asalatu sai ya ji wani zakaransa ya ce, “Kikiriki!” Sai wata kaza ta ce wa zakaran, “kai, maigida kana da murya! Yanzu caran nan taka duk garin nan ba inda ba a ji ta ba.”

Zakaran ya kada fiffike, ya ce, “Don ma ina mura yanzu ba na iya yi da karfi. Da sa’ad da na ke lafiya ne, in na yi ai duk kasan nan a ji.

Sale ya bingire da dariya, har ya rasa abin da ya ke ciki. Ya yi godiya ga Allah bisa ga amsa rokonsa da ya yi. Ya tashi ya yi alwala, ya yi salla, ya fita zaure wajen yaransa, aka yi ta tadin duniya, kowa na fadin albarkacin bakinsa.

Da rana ta yi zafi, sai Sale ya shiga gida, don ya kwanta kafin azahar. Da ya hau gado ya kwanta, sai ya ji ya kasa barci, ya dauko buzu ya fito gindin dabi a barga, ya kishingida. A cikin dabin nan kuwa da ya ke akwai sansa na noma da jakinsa na hawa, suna daure kusa da kusa. Yana nan kishingide, sai ya ji san nan ya ce wa jakin, “Kai dai ka ji dadi. Barorin gidan nan ko yaushe hankalinsu na wajenka. Dubi har wanka su ke yi maka, su ba ka abinci irin wanda ka ke so. Ni kuwa ga ni kullum sai a daura mini kaltibeta, a sa maketacin bawan nan ya tafi da ni gona, in yi ta aiki tun daga fitowar rana har ya zuwa faduwarta. Ba wannan me ke ba ni haushi ba, sai dukana da ya ke yi in na dan tsaya in sarara. Don Allah dubi wuyana ka gani, duk ya kuje domin wahala. In mun dawo gida kuma ba wani abinci mai dadi ba za a ba ni in ci. Shin wanda ya ke haka don ya ga kyashin wadansu, ai bai kamata ba a ga wautarsa.”

Da jaki ya ji haka sai ya ce, “Af, ai wanna duk sakarcinka ya sa su ke raina ka haka. Tun da su ke zuwa daura maka kaltibeta, ka taba tunkuyin wani daga cikinsu? Ko ba ka tunkuye su ba ma, in kana tasam musu kamar za ka danne su, ka ga sun fara rage maka azaba. Ga shi Allah ya ba ka karfin da za ka neman ma kanka girma da shi, amma waurtarka ta hana. Kuma ai ko ba ka fito musu ta haka ba, ka ce su kan kawo maka rubabbiyar dusa, to, in sun kawo kada ka ci, in ka sunsuna ka kau da kanka. Wallahi in ka bi wannan dabara tawa, ka ga al’amarin ya yi maka dadi har ka gode mini.”

Sa ya kama abin nan da jaki ya gaya masa, ya yi masa godiya bisa ga nasiharsa. Sale dai na kishingide, yana jinsu. Da gari ya waye sai bawan nan ya dauko kaltibeta ya daura wa sa, ya tafi da shi gona. Suka yi aiki, suka komo.

Da dare, ko da bawan nan ya zo ya daure shi, sai ya ga ya tasam masa kamar zai halaka shi, ya ruga ya dawo, sa ya yi gunji, ya rasa yadda zai yi ya daure shi, sai ya rufe dabin, ya bar shi a sake. Ya’kawo dusa da kaikayi ya tura masa, yana cewa, “Yau san nan lafiya ya haukace? Ko kuwa yana jin kishiruwa ne?” Ya tafi rijiya ya jawo ruwa, ya tura masa, sa ya ki ko dubansu.

Da gari ya waye bawa ya dawo ya ga kwanan sa, sai ya tarad da shi kwance, ya mimmike kafafunsa, yana nishi, ya dubi kwandon dusa da na kaikayi, ya gan su yadda ya ajiye, sa bai ko taba ba. Ga ruwan kuma da ya kawo, ba abin da ya taba shi.

Da ganin wannan bawan ya ce, “Haba, na san a yi haka, haukacewar da san nan ya yi jiya ba banza ba. Ashe yana da gaskiya, shi kadai ya san abin da ya ke ji. Yau dai bai kamata a je da shi gona ba.” Ya ruga ya gaya wa Sale haka.

Da Sale ya ji, sai ya lura watau san nan a bi shawarar da jaki ya yi masa ne, Saboda haka ya ce wa bawan nan ya je ya kama jakin, ya tafi da shi gona. Ya ce ya daura masa kaltibeta, ya yi noma da shi maimakon sa, kada kuwa ya ji tausayinsa ko kadan.

Bawan ya tafi ya kama jaki, ya kai shi gona, ya daura masa kaltibeta, ya yi ta aiki da shi, in ya dan dakata don rashin sabo, sai bawan ya aza masa kulki tim, jaki ya kara mai. Suka yi ta yin haka tun da sayin safe har rana ta koma ga Ubangiji, sa’an nan bawan ya koro shi zuwa gida, ya kawo shajaran majaran.

Sale na kofar gida zaune, ya ga sun dawo. Ya dubi jaki, ya ga lalle kamarsa ta sake. Ya tambayi bawan yadda suka yi da jaki, ya gaya masa duka. Sale ya ce a ransa, “Bari in bi jakin in ji yau kuma me zai ce wa sa.”

“Daure jakin ke da wuya sai ya fadi yana nishi, ya dubi sa, ya ce, “Kai, yau in an kawo maka abinci, me ka kulla kuma za ka yi?”

Sa ya ce, “A’a! Har da wata dabara ce da ta fi wannan da ka gaya mini? Ga shi yau duk ranan nan da aka yi sai kwance na ke cikin inuwa ina hura hanci. Ai ni wannan makwabtaka da kai ta yi mini amfani.”

Jaki ya harare shi, ya ce, “Kai sakarai, kana nan kwance ba ka san abin da a ke kullawa a yi maka ba. Yanzun nan da zan shigo na ji ubangijimmu na cewa bawan nan nasa, tun da ya ke ba ka iya cin abinci, balle ka yi wani aiki, gobe sai ya je ya kira Sarkin Fawa, ya zo a yanka ka a yi rarraba. Da kamar in kyale ka, sai na ga dai yadda ka yarda da ni haka, har ka ba ni shawara, bai kamata ba in ci amanarka. Don an ce kowa ya ci amanar wani, ko ba jima ko ba dade, ya ga sakayyar Allah. Abin da na ga ya fi yanzu, in sun kawo maka abinci ka sa hankalinka ka yi ta ci, sai ka koshi. Wallahi in ba haka ka yi ba, in gaya maka gaskiya, gobe war haka kai kuma sai labari.

Wannan magana fa ta kama sa, nan take ya kama kiwo ba ji ba gani. Yana ta godiya bisa ga wannan nasiha da jaki ya sake yi masa. Sale ya kura wa sa ido, yana dariya da ya ga ya takarkare ba ya ko daga kai, in ya ci dusa ya juya ga kaikayi, sai cika bakinsa ya ke yi kamar mahaukaci.

Sale ya yi ta mamaki, yana cewa a ransa, “Ashe duk abin nan da mu ke yi wa dabbobi sun sani, Allah dai ne bai ba su bakin da za su furta mana ba. Yadda Allah ya hore mana su haka, ba don karfimmu ba, ba abin da ya fi sai mu rika sawwake musu wahala matsananciya. Mu tuna duk abin da mu ke ji, su ma suna ji, mu lura da su yaddda za mu lura da kammu, kada mu gode wa Allah da mugun aiki.”

Ya tashi, ya kira bayinsa, ya hore su da rika lura da dabbobinsa da kyau, kada su sa su abin da za su wahala fiye da kima.

Musa ya ce, “A! Ashe har mutane na iya jin maganar dabbobi ko? Wannan abu da ban mamaki!”

Aku ya ce, “Ai ko ni na taba ba wani ubangijina maganin jin, sa’ad da ya auro wata karuwa da ta matsa mana lamba. Ta wannan hanya na raba su. Af! Kai, kada in tsai da kai da labarin, sai ka yi shiri ka fita kafin gari ya waye.”

Ya yi shirin fita sai aka yi asalatu. Ba dama ya kela ko waje, tun da ya ke kowa ya farka. Ya koma gida, tun safiyan nan har magariba yana ta tunanin dabarar da zai yi wa aku ya samu ya fita, ba da ya tsai da shi ba.

Zuwa asubahin fari, da ya ji bayi sun yi baci, sai ya zo ga aku, ya ce, “Yau ba na son wani labari. Abin da na ke so sai ka gaya jin maganar dabbobi, in tafi. Shi kadai na ke so, ba kome ba.”

Aku ya e, “Ka ko yi tambaya ga dan gida.” Ya tsirgo, ya soma.

Post a Comment

 
Top