0
MAGANA JARI CE LITTAFI NA DAYA


LABARIN WANI AKU DA MATAR UBAN GIDANSA


Labarin Wani Aku Da Matar Ubangidansa
      Wata rana wani tajiri za shi fatauci, sai ya bar matarsa a gida. Yana kuma da wani aku. Suna nan tare, sai matar ta rika fita yawo, don ta ga mijin ba ya nan. Barorin gida da suka ga abin ya dame su, ba su da damar su yi magana, kada matan nan ta sare su wajen mai gidan in ya komo. Saboda haka suka zura mata ido.

Ana nan ran nan sai mai gida ya dawo. Ka san al’amarin duniya ba shi boyuwa, sai wani ya tsegunta masa abin da matarsa ta yi ta aikataa bayan ba shi nan. Da mai gidan nan ya ji haka, sai ya kira matar, ya same ta ya yi ta zagi. Ya dauki sanda kuma ya ba ta kashi.

Da matan nan ta ga haka sai ta yi yaji, aka komo da ita. Ta ce a ranta, “Ba wanda ya fadi abin nan sai aku.” Ka san mu, Allah ya ba ka nasara, bakin jini gare mu kwarai, tun ba game da mata ba. Suna cewa mun faye tsegumi. Saboda haka, ta bari mai gida ya tafi kasuwa, sai ta kama aku, ta fige shi da rai, ta wurga shi wage ta taga, ta ce, “Daga gare ni ka bar tsegumi!” Allah ya sa aku bai mutu ba, ya tsallaka har ya kai wani hurumi ya sami kabari ya shige, ya yi ta jiyya.

Da mai gidan nan ko ya dawo, sai matar ta ce wai bayan fitarsa kadan kyanwa ta cinye aku. Ko da ya ji haka sai ya san karya ta ke yi, kashe shi ta yi, don tana tsammani shi ya gaya masa tana fita da ba shi nan. Saboda haka ya fusata kwarai da gaske, ya same ta da duka kamar ba zai bar ta da rai ba. Ya kore ta daga gidan, ta tafi wajen hurumin nan tana kuka. Ashe aku na nan kusa da ita cikin wani kabari, yana ji.

Sai ya ce mata, “Yi shiru, bari kuka, in Allah ya so kya koma dakinki. Amma akwai sharadi guda, sai ki je ki aske kanki sarai, sa’an nan ki dawo nan, gobe zan taimake ki ki koma.”

Matan nan ta duba, ba ta ga kowa ba. Abinka da mace, sai a yi tsammanin wani matacce ne ke yi mata magana. Nan da nan ta tafi gidan iyayenta, ta sa aka aske mata kai kwal. Da gari ya waye, maraice ya yi ta nuho wajen hurumi, kai na kalli sai ka ce na namiji.

Da isowarta sai ta tafi wajen kabarin. Abinka da jahila, ta durkusa, ta ce, “Na asko.”

Sai aku ya ce, “To, kin san dalilin da ya sa na ce ki aske kanki, domin kin zalunci wani dan tsuntsu, kika targe shi a kan abin da bai ji ba bai gani ba, har kika fige shi da ransa, kika wurgo shi bayan gida. A wannan na yi miki sauki, na ce ki aske gashin kanki kawai, amma in kih kuskura kika sake yi wa wani tsuntsu haka, ki kuka da kanki. Amma akun nan da kika kashe zai komo duniya, yadda zan mai da ke dakinki, shi kuma zan mai da shi gare ki. To, ki lura da shi da kyau, ki sa mijinki ya ajiye yaro guda mai Kuma ki tsawata wa yara su bar kiransa aku kuturu.”

Matan nan ta kara dukawa, ta ce, “Na ji.”

Da za ta tashi sai aku ya ce, “Da saura. Yau kin ga sha biyu ga watan Safar. To, ko wace shekara sha biyu ga watan Safar ki aske kanki, don ya rika tuna miki aku dai da ki ke ganinsa banza-banza ba banza ba ne. Amanar Allah ce ya sa hannunku ‘yan Adam, ya fi kyau kuwa ku lura da ita da kyau. Watan duk da ya zo ba ki aske kanki ba, yadda na gaya miki yanzu, ki tabbata ba ki shekara. Shi ke nan, gobe kya koma in sha Allahu. Tafi gida abinki. Amma ki kiyaye gargadin nan da na yi miki, ki kuwa yi kirki, ki bi mijinki sau da hannu. Allah ya gama mu da alheri a Darassalamu!”

Mace ta koma gidansu. Aku ya tashi yana tsalle, har ya kai gidan tajirin nan, ya ce masa, “Ka san ni?”

Tajirin ya dubi aku ba gashi, ya ce, “Yaya zan yi in san ka, ban taba ganinka ba?”

Aku ya ce, “Ba ta taba ganina ba? Ai ni ne akunka wanda kyanwa ta cinye.”

Tajiri ya ce, “Tun da kyanwa ta cinye ka, yaya kuma aka fara har ka yi rai? Da ma dai ba kyanwa ta ci ka ba akwai yadda aka yi.”

Aku ya ce, “Daga cikin kyanwar aka nufa in fito, don in shaida maka duk abin da matarka ta fadi na batun kyanwa ta cinye ni gaskiya ne, Dada ka zarge ta. Amma in kana sona, zan kara dakatawa kuma wurinka, I yi gashi in koma kamar da, har Allah ya kari kwanana gaba daya. Amma sai ka mai da matarka, ka yafe mata, ku yi zaman lafiya.”

Mai gida ya ce, “To.” Ya aika matar ta dawo, ya gafarta mata suka sake zamansu. Daga ran nan ta zama matar kirki, duk gari ba wadda a ke so sai ita a kan kirki.

Musa ya tashi zai fita, aku ya dube shi, ya ce, “Wallahi, yallabai, ba ka ga yadda ka rame ba. Maza ka tafi kada zulumi ya halaka mana kai a banza,yadda ya tashi halaka Sarkin Zairana.”

Musa ya waigo, ya ce, “Ina ne Zairana kuma? Zulumin mene ne haka ya sami Sarkin, har ya tashi halaka?”

Aku ya ce, “Yallabai, me ka mai da zulumi ne?”

Post a Comment

 
Top