MAGANA JARI CE LITTAFI NA DAYA
labari na biyar
LABARIN AUTA DAN SARKIN NOMA
Labarin Auta Dan Sarkin Noma Da Namun Jeji
Wata rana wani manomi ya ce wa dansa Auta kullum ya san yadda zai yi ya harbo musu abin da za su yi miya. Auta ya ce “To.” Kowace rana sai ya je daji, yau in ya harbo zomo, gobe ya harbo batsiya ko gada. Kullum haka har ran nan bai samo ba, uban ya yi ta yi masa fada har ya ba shi kashi.
Yana cikin haka, ran nan har namomin daji suka gaji da kisa, suka kai kara gun zaki, Sarkinsu. Zaki ya ce, “To, yaya za mu yi? Kun sani fa Allah abin tsoro ne, mutum ma abin tsoro ne.”
Sai kura ta ce, “Ai, ranka ya dade, babu wata dabara sai mu yi kokari mu kawo maka yaron nan, kai kuwa ka yi abin da ka ga dama da shi.”
Sauran dabbobi suka ce, “Ai kuwa haka ne, abin da kura ta ce shi ne gaskiya.” Suka sallami Sarki, suka watse.
Ran nan yaron yana yawon harbi sai ya ci karo da dila ya ja baka zai harbe shi, sai dila ya ce, “Tsaya! Na ce ko abinci ka ke so? Zo in kai ka inda za ka huta da wahala.”
Auta yana tsammani gaskiya ne. Ya bi shi, suka mika har wani katon kogo inda zakin nan ya ki mulki. Da shigarsu dila ya ce ya ajiye bakansa daga waje don kada a ce shi maharbi ne. Suka shiga, sai dila ya komo da baya ya boye bakan yaron. Suka tarad da zaki a zaune, duk ga namomin daji sun kewaye shi, ana fadanci. Dila ya fadi, ya yi gaisuwa. Kura ta dubi yaron nan, ta ce, “Kai, ba ka gai da Sarki?”
Auta ya ce, “Ke, me ya sha miki kai? Ke kika aiko ni?”
Ya duka ya yi gaisuwa. Da suka zauna, zaki ya dubi dila, ya ce, “Shi ne wannan da ya dame ku?”
Kura ta amshe ta ce, “Shi ne, ranka ya dade. Kuzajje mai kai kamar kodago!”
Zaki ya ce ma Auta, “Kai samari, me ya sa ka ke kashe mana ‘yan’uwa?”
Kafin ya amsa tambayar Sarki sai kura ta ce, “Ranka da dade, raina mu dai ya yi dubi jikinsa, dan nema, jemamme!”
Auta ya durkusa, ya ce, “Ranka ya dade, shin kai ne Sarki, ko kuwa kura?”
Da zaki ya ji haka, sai ya yi fushi da kura, ya ce, “Kada in sake jin kin yi magana a nan. Fadi jawabinka, samari.”
Auta ya sake durkusawa, ya ce, “Dattijan garimmu suka ce in zo in rika kashe ku, don mu ga idan abubuwan da kura ke fadi na labarinka gaskiya ne.”
Zaki ya ce, “Me kura ke fadi na labarina?”
Auta ya ce, “Mu da nufimmu mu fid da Sarkimmu na mutane, don ba shi da hakuri, mu nada ka, ka yi mulkin dabbobi kuk da mutane baki daya, mu gama kammu mu bi ka, duk abin da ka ce mu yi, mu yi, abin da ba ka so mu bari. To, muna cikin wannan shawara sai ran nan kura ta shigo gari ta ce ka aiko ta, wai ba abin da ke tsakanimmu da kai sai kisa. Muka sake tambayarta, ta ce duk Sarakunan duniyan nan babu azzalumi irinka. Wai da an yi maka dan laifi kadan sai ka ce a kashe mutum. Saboda haka aka ce in rika kashe ku, mu gani ko ka sa a kashe ni. In ka sa an kashe ni, lalle maganar kura gaskiya ce. In kuwa ka yafe ni, kura ta zama makaryaciya.”
Zaki ya dubi kura, ya buga mata tsawa ya ce, “Wa ya aike ki ga mutane?”
Ta zabura, zawo na fita, ta ce, “Karya ya ke yi, ban taba shiga gari ba.”
Auta ya ce, “Wa ke maki karyar, zaki da kansa? Kin manta har muka ba ki kujera kika zauna, don girmamawar Sarki da kika ce ya aiko ki?”
Za ta yi magana zaki ya zabura, ya sa gaba ya banke ta, duk namun daji suka hau mata, mai yaga na yi, mai cizo na yi, har suka kashe ta. Zaki ya sallami yaron nan. Ya ba shi kaya mai yawa irin wanda su ke kwacewa daga fatake. Yaro ya yi dogiya, ya ce zai je ya gaya wa mutanen gari abin da ya auku. Wannan shi ya sa ko yaushe in ka ga zaki a daji ka durkusa, ka ce, “Ranka ya dade,” ba zai cuce ka ba.
Musa ya duba haka, sai ya ga gari ya waye. Bai ko tsaya ba ya ji ko labarin ya kare, ko bai kare ba, sai ya yi tsaki, ya juya ya shiga gida. Yinin ran nan duk ya ki ko zuwa wurin aku, har magariba ta yi. Bayin Sarki suka ce abinci suka zauna hira, sai can barci ya kwashe su.
Da Musa ya ji alamar bayi sun yi barci sai ya tasam ma wajen aku. Da hango shi sai aku ya bushe da dariya. Musa ya dube shi, ya ce, “Me ka ke wa dariya haka, kai kadai kamar mahaukaci?”
Aku ya ce, “Ai ba ka san abin da aka yi ba jiya da dare. Shigara ke da wuya, sai na ji bayin can naka na babban zaure suna hira. Sarkin Gida na yi musa tatsuniya. Da na ga ba na jin barci, ni kuma na tafi in taya su. Da Sarkin Gida ya kare tatsuniyoyinsa, ni kuma na ba su labarin wani bakauye da wadansu ‘yam birini.”
Musa ya ce, “Ashe Sarkin Gida tsofai-tsofai a shi nan, har ya kya tatsuniyoy?” Labarin me ka tarar yana yi musu?”
Aku ya ce, “Ba wani labari mai dadi ba ne, tun ina yaro na san shi. Kokawa da aka yi cikin labarin ne, in na tuna ta ke ba ni dariya.”
Muse ya ce, “Yaya suki yi?”
Aku ya ce:

Post a Comment